Free chapter · Read without an account
EP____________9️⃣
🕊️ DESTINED MARRIAGE 🕊️
*HAUSA EDITION*
🕊️ QADDARARREN AURE🕊️
SWRITES
A-K-A
YOUNG WRITER✍🏻
EP____________9️⃣
"Waye?". Hadiyyah ta tambaya.
"Ba wannan ba. Yanzu kinsan me zaki min? Ga wani mutum can sanye da Maroon Shirt, ki ɗan matsa ki kira sunan "Hashim" Ki ga ko zai juyo, idan har ya juyo to ta tabbata shi ɗin ne, idan kuma bai juyo ba, to ba shi ba ne".
"Ban gane ba? wane Hashim ɗin kike magana a kai wai?".
"Zan yi miki bayani daga baya, yanzu dai fara zuwa mu gani".
Hadiyyah bata ƙara cewa komai ba ta fara tafiya, sai kuma ta juyo sai dai kafin ta kai ga magana Faryal ta hankaɗa ta tana faɗin, "Dan Allah ki je Hadiyyah, ki yi sauri".
Hadiyyah ta ɗan kalle ta kafin ta nufi tsakiyar filin, inda Barr Hashim yake tare da wasu maza suna rawa.
"Hey Hashim". Hadiyyah ta kira sunan a ɗarare.
Barr Hashim wanda yake riƙe da tumbler ɗin dake ɗauke da alcohol, ya juyo gare ta. Ɗan zuba mata ido yayi yana ƙoƙarin tuna inda ya san fuskar duk da cewa a buge yake. Ɗan girgiza kansa yayi kafin ya ce, "Hey babe, what's up?".
Hadiyyah ta haɗiye yawu daƙyar kafin ta yi Murmushin yaqe ta ce, "Ya kake?".
Gyara tsayuwarsa yayi, idanunsa a kanta har lokacin, yana watsa mata wani irin kallo. Sai kuma ya miƙa mata tumbler din.
Hannun Hadiyyah ne ya fara rawa, ta ɗan girgiza masa kai tare da faɗin, "No, I'm Okay".
Ɗan ɗage kafaɗunsa yayi kafin ya miƙa mata ɗayan hannunsa da babu komai ya ce, "Can we......?".
Kallon dance floor ɗin dake cike da mutane tayi, maza da mata an cakuɗu ana ta rawa cikin rashin tsari, kafin ta mayar da dubanta kan hannun nasa, ɗan ja baya tayi, shi kuma ya Matsota yana ƙoƙarin jawo ta jikinsa, a dai dai lokacin kuma wutar wurin ta ɗauke gabaɗaya.
Faryal wadda take kallon duk abin da ke faruwa, ta nufe su cikin sauri a lokacin da taga abinda Barr Hashim ɗin yake da niyyar yi, sai dai kafin ta ƙarasa wutar ta ɗauke.
Ji tayi an riqo kafaɗarta, ta buɗe baki da sauri da niyyar yin ihu, taji an yi saurin rufe mata bakin da hannu, tare da jan ta zuwa wajen hall ɗin.
Suna fitowa wutar na dawowa. Faryal ta kalli Hadiyyah wadda ta cire hannunta daga bakin Faryal ɗin, saidai bata sake ta ba, ta ci gaba da jan ta zuwa wurin motarsu. Ta buɗe mata ta shiga sannan ta zagaya mazaunin driver ta shiga da sauri, ta ja motar suka bar wurin.
A cikin hall ɗin kuwa, lokacin da wutar ta dawo, Barr Hashim ya kalli matar da yake tunanin Hadiyyah ce, amma sai ya fahimci wata ce daban. Cikin sauri ya zare hannunsa daga waist ɗin ta, ya kurɓe sauran alcohol ɗin dake cikin tumbler ɗin, kafin ya fice daga hall ɗin yana rangaji.
Sai da suka kusan isa gida, sannan suka kalli juna kafin su sauke ajiyar zuciya a lokaci guda. Hadiyyah ta mayar da hankalinta kan titi kafin ta ce, "Baki bani amsa ta ba, Waye shi?".
"Ya amsa miki a lokacin da kika kira sunansa?". Faryal ta mayar mata da tambaya maimakon ta ba ta amsa.
"Eh!".
"Ya Allah! Wani na gani mai kama da Barr Hashim, shi ne na ce ki je ki tabbatar min ko shi ɗin ne, dan kammanin yayi yawa, duk da kuwa bana tunanin ganin sa a irin wannan yanayin". Faryal ta faɗa unbelievably.
"To kuwa ba kama bace, Barr Hashim ɗin ne dai da kansa. Kuma idan aka yi la'akari da yanayin sa, wannan ba shi ne karon farko ba. He's indeed a bad guy and a drunkard, kawai ya miki shiga shiga ba zurfi ne zai yaudare ki".
"But how Hadiyyah? I'm surprised, cox Barr Hashim is such an intelligent gentleman...".
Katse ta Hadiyyah tayi ta hanyar faɗin, "Ni kai na ina cikin al'ajabin lamarin nan saboda abin da kike faɗa min game da shi ya sha bamban da abin da na gani, amma fa ina so ki fahimci cewa duniya cike take da mutane masu fuska biyu. Idan kin san wani abu game da mutum, kada ki yi mamaki idan kika ga ainihin halinsa, dan suna nuna abin da suke son a sani ne kawai. Ko iyaye a wannan zamanin basu isa dukan kirji su ce sun san halin ƴaƴansu 💯 ba. Yanzu dai gashi nan kin ga asalin waye Barr Hashim".
Faryal dai ta rasa ta cewa, dan har yanzu ta kasa haɗa Barr Hashim ɗin da ta sani da wanda ta gani a wannan yanayin. Ta zaro wayarta, ta buɗe WhatsApp sannan ta shiga chat ɗin su inda taci karo da last message ɗin sa, "I just texted you cox I stood to pray Asr and you came across my mind, na yi miki addu'a sosai Faryal, Allah ya cika miki burikanki na alheri".
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Faryal ta faɗa tana sake kallon saƙon.
Haka suka ƙarasa gida ba me iya cewa komai, ɗakin su kawai suka wuce dan Allah ya taimake su basu haɗu da kowa ba tunda suka shigo.
Hadiyyah ta jefa jakarta kan gado sannan ta wuce bathroom, yayin da Faryal ta zauna a bakin gadon still in shock.
Cikin wannan yanayin wayarta ta fara ringing, sunan "Barr Hashim" ne ya bayyana a kan screen ɗin. Kashewa tayi, amma sai aka sake kira, sake kashewa tayi tana ɗagowa ta kalli Hadiyyah wadda ta fito daga bathroom ɗaure da towel, da alama wanka tayi.
"Wa ke kira ne haka?". Hadiyyahn ta tambaya.
"Barr Hashim". Faryal ɗin ta bata amsa.
"Shi ne kuma kike kashewa?".
"Ban gane shi ne nake kashewa ba? Me kike so kuma in ce masa Hadiyyah?".
"Ya kamata ki ɗaga ki faɗa masa an sanya ranar auranki less than a month, so ba za ki iya ci gaba da magana da shi ba, saboda wanda zaki aura ba zai amince da hakan ba".
"Ba yanzu ba Hadiyyah, I'm not in the right mind, maybe zuwa gobe, dan gsky ba zan iya ci gaba da hulɗa da shi ba bayan abinda ido na ya nuna min".
"It's Okay, amma ya kamata ki je ki yi wanka, ki tsarkake jikinki dan kasancewa a irin wancan wurin kana karo da kwalbar burkutu ai sai da wankan".
Faryal ta kwashe da dariya, kafin ta miƙe ta rage kayan jikinta ta wuce bathroom ɗin.
*** *** ***
Washegari, har Faryal taje aiki jikinta a mace yake, so bata ma daɗe acan sosai ba ta bar Company ta nufi gidan Manira. Bayan sun keɓe a ɗakin Manira, ta kwashe labarin abinda ya faru jiya ta faɗawa Maniran, wanda yasa ta a tsananin mamaki ita ma, dan sai ka rantse in an sawa Barr Hashim bindiga aka baisan hanyar club ba ballantana har a ganshi a irin wannan yanayin.
Sun daɗe suna tattaunawa kafin Faryal ɗin ta baro gidan su Manira ta wuce gida saboda ciwon kan da take ɗan ji.
Ko da ta isa gidan, duk kannen ta suna makaranta, so Maama kawai ta sanarwa ta dawo sannan ta nufi ɗakinta dan ta ɗan huta. Tana kwanciya wayarta ta fara ringing. Ba tare data bude idanunta ba ta amsa wayar, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta lokacin da ta ji muryar Fayyad.
Bayan sun gaisa, Fayyad ɗin ya sake cewa, "Are You Okay Faryal?".
"Yeah. Me ka ji?". Ta amsa a hankali.
"Zuciyata ce take faɗa min kamar something's wrong with the one I care about".
Faryal ta ɗan sake murmusawa, dan ako da yaushe kalamansa na sanyaya mata rai tare da sanyata nishadi ko da ace bata cikin good Mood. Dan haka ta ce, "Ki fada wa zuciyar taka cewa komai lafiya, ɗan ciwon kai ne kawai nake yi".
"Oh my God Faryal dan Allah ki koma gida ki samu ki huta, komai ai sai da lpy ake yi".
"Kar ka damu Fayyad, ina gidan ma yanzu haka, i came back a little while ago".
"Kin sha magani ne?".
"A'a, ina ganin idan na ɗan huta zai daina, it's just stress".
"Okay, amma idan bai daina ba, ki sha magani ko ki je hospital".
"In sha Allah Fayyad, Nagode".
Ɗan shuru suka yi kafin ya kira sunanta da wata irin tausasasshiyar murya, "Faryal!".
"Na'am Fayyad!". Ta amsa a hankali.
"Zan iya zuwa in duba ki zuwa anjima?".
Faryal ta ɗan lumshe idanunta duk da har yanzu bata san me take ji a kansa ba amma kasancewa dashi na sata nadamar lokacin da ta bata akan Hamdan tsawon waɗannan shekarun ba tare da ta san mene ne ainihin soyayya da kulawa ba, tunda ga shi a yan watanni kawai Fayyad yasa ta fahimci mene ne soyayya ta gsky ba irin wadda Hamdan ke mata ba, to ina ga ta bashi dukkan Zuciyarta kuma kamar yadda ta bawa Hamdan? Wani ɓoyayyen murmushi ta sake saki. Ba abin da ya fi melting heart ɗin ta ma irin yadda yake kaffa kaffa da ita, da kuma yadda yake neman izininta a kan komai. Katse tunanin nata tayi kafin ta ce, "Me zai hana Fayyad? Kana iya zuwa".
"Na gode sosai Faryal, thank you for giving me this expensive chance".
Ta ɗan yi dariya kafin ta ce, "Kai Fayyad, what kind of expensive Chance are you talking about?".
"Samun izinin zuwa ganinki mana".
"Kaji ka, sai kace wata kayan gabas".
Ya yi dariya kafin ya ce, "Ni a wurina, kin fi kayan gabas ma". Haka suka cigaba da hira kamar yadda suka saba har ta manta da wani batun ciwon kai ma kafin daga bisani su yi sallama ta kashe.
Tashi tayi ta fita, ta nufi ɗakin kakarsu. Acan ta ɗan zauna kafin ta tashi ta je ta faɗa wa mai gadi ya gyara mata falon baƙi.
Ɗakinta ta koma ta gabatar da sallar La'asar da taji ana kira, sannan ta sake shiryawa, duk da cewa ba ta san time ɗin da zai zo ba.
A haka Hadiyyah ta dawo daga makaranta, ta same su a falo ita da Maama. Riqe baki tayi kamar me tunani, tana kallon kayan jikin Faryal ɗin kafin cikin sigar zolaya ta ce, "Can i guess?".
"Maybe". Faryal ta Faɗa da ɗan murmushi.
"Fayya...".
"Ƙarasa mana, yar sa ido". Faryal ɗin ta faɗa tana ɗan harararta.
Dariya tayi Kafin ta ce, "Zai zo ko?".
Ɗan satar kallon Maama dake kallonsu tayi kafin ta ce, "Eh".
"Waye shi?". Maama ta tambaya.
Hadiyyah tayi saurin faɗin, "Sabon saurayinta ne Maama".
"A'a, to shi kuma Hamdan ɗin fa?".
"Sun rabu ai". Hadiyyah ta sake amsawa.
"Yaushe kuma?".
"He's not a perfect man for her". Hadiyyah ta sake faɗa tana ɓata fuska.
"Abin da na tambaye ki kenan? Dake ma nake magana ne ko da ita? Ko kuwa ke ce bakinta? Yar iya". Maama ta faɗa tana watsawa Hadiyyah kallon gargaɗi.
Dariya tayi kafin ta ce, "To ke kinji, sai ki buɗi baki ki yi magana". Ta ƙarashe tana barin falon ta nufi ɗakin Daadee tana faɗin, "Daadee, kina ina?".
"Faryal, me ya faru a tsakaninku kuma?" Maama ta sake tambaya.
Tsintar kanta tayi cikin jin nauyin mahaifiyarta ta, dan wannan shi ne karo na farko da mahaifiyar tasu ta nuna interest ɗin jin wani abu da ya shafi rayuwarsu. Duk da kuwa ako da yaushe cikin hirar Hamdan ɗin suke da kannenta kuma sau da yawa a gaban Maama ne, amma ba ta damu data kirata ta tambaye ta wani abu game da relationship status ɗin nata ba ballantana har ta bata shawara, ko kuma ta nemi jin abun da ke gudana a rayuwarta, ko mutanen da take hulɗa da su. Ita da ko wuce lokacin dawowa gida daga wurin aiki tayi, saidai idan har ita ce zata buɗi baki ta faɗa mata dalilin da kanta amma ita dai Maama baza ta taɓa tambaya ba. Sauke ajiyar zuciya tayi kafin ta ce, "I'm no more interested in him Maama".
A dai dai wannan lokacin kuma sai ga kiransa ya shigo, kamar ya san suna maganar sa. Zubawa screen ɗin wayar ido tayi kawai, cox tun bayan wancan lokacin da ya bar mata missed calls, bai sake bi ta kanta ba sai yanzu. "Hmm". Ta faɗa kafin ta saka wayar a silent ta miqe tana faɗin "Maama, bari in je ciki in ga Hadiyyah". Ta faɗa tana barin falon.
Ko da ta shiga ɗakin ba ta tarar da Hadiyyah ba, sai kawai ta zube a kan gado tana kallon missed call ɗin da Hamdan ya bar mata a wayar. Can kuma ta saki tsuka sannan ta jefar da wayar ta lumshe idanunta.
Sai da lokacin girkin abincin dare yayi sannan Hadiyyah ta shigo ta tashe ta suka fita. Sunyi nisa a aikin da suke yi Maama ta leqo tana faɗin, "Faryal, kina da baƙo a waje".
"Okay". Ta faɗa tana nufar wash basin, ta wanke hannunta sannan ta kalli Hadiyyah wadda ke kallonta tana murmushi cike da neman magana. Ɗan hararar ta tayi Kafin ta ce, "Mi?".
"Wai dama cewa nayi ko zan iya zuwa in raka ki?".
Hanyar fita daga kitchen ɗin ta nufa tana faɗin, "As you wished".
Da sauri Hadiyyah ta ajiye wuƙar da ke hannunta ta bi bayanta har tana haɗawa da ɗan gudu gudu tana faɗin, "To jirani mana".
A gurguje ta sake shiryawa cikin wani yellow lace mai touch ɗin Green, skirt da riga fitted, dan kayan dake jikinta sun ɓace a kitchen. Ta sake gyara ɗaurin gashinta zuwa sleek bun, sannan ta ɗaura ɗaurin ture kaga tsiya, ta murza lip gloss, ta fesa turare mai sauƙin ƙamshi, ta saka plat shoes ɗin ta green, ta ɗauki wayarta ta fice daga ɗakin. Hadiyyah wadda ta ɗaura kimono a kan light clothes ɗin dake jikinta, ta biyo bayanta tana faɗin, "Sai dai ke mamana, kina wuta Wallahi, wa yace damu ba mu ba muma mu ce dashi ba shi ba". Faryal tayi murmushi kawai tare da girgiza kai.
Tsaye suka same shi jingine da motarsa, yana ɗan danna wayarsa. Yayi kyau sosai cikin milk kaftan, ɗinkin zamani. Ɗagowa yayi idanunsa suka sauka akanta. Wani irin murmushi ne ya kwace masa, ya kure ta da ido ko kiftawa ba yayi har suka Ƙaraso wurinsa.
"Barka da zuwa ranka ya daɗe".
"Tare da ke beauty, kin yi kyau sosai, irin wannan kwalliyar haka, duk ma ni aka yi wa?".
Faryal ta ɗan gyada masa kai tana murmushi, yayin da Hadiyyah kuma ta gaishe shi, ya amsa yana faɗin, "Ga photocopy ki nan".
Hadiyyah ta yi ɗan murmushi kafin ta ce, "Haka kowa yake faɗa, amma ni dai ban ga kamannin ba".
"Eh to, ba lalle ki gani ba, dan ta fi ki haɗuwa gsky. Kar ma ki yi tunanin dan na ce kuna kama, ki ɗauka kin kai ta haɗewa ne". Ya faɗa cikin barkwancin sa.
"Ka faɗa mata gaskiya fa Fayyad, kar ka wani kumbura mata kai kasa tayi tunanin wani kyan azo a gani ne da ita". Hadiyyah ta faɗa tana hararar Faryal dake blushing.
"Kinga, karki bari mu sa ƙafar buje ɗaya da ke, ki yi kamun kafa idan kina so mu zauna lafiya".
"Kamun kafa da wa? Hmmm, bari dai kawai in shige ciki, dan na san kawai so kake in baku wuri. To kar ka damu, ni na wuce, a sha soyayya lpy". Ta faɗa tana juyawa ta koma ciki.
Fayyad ya kalli Faryal yana ɗan gyara tsayuwar sa ya ce, "Wai haka?".
Rufe fuskarta tayi da tafukan hannunta tana murmushi ta ce, "Mu shiga daga ciki ko".
"Yadda kika ce ranki ya daɗe". Fayyad ya amsa yana ɗan karkacewa ya nuna mata hanya da hannuwansa, in a romantic style. Jin ta tayi kamar wata sarauniya. Haka ta wuce gaba zuwa falon baƙin yana biye da ita. Suna zama Hadiyyah ta shigo da refreshments ta ajje musu sannan ta fice. Hira suka shiga yi inda cikin siyasa Fayyad ya fito fili ya bayyana mata sirrin zuciyarsa.
Ita ma Faryal wadda ta fara koyon salonsa, cikin siyasar ta bayyana masa amincewarta. Sun shafe kusan 40 minutes kafin ya tashi zai tafi ta rako shi wurin mota.
Suna tsaye suna sallama suka ga an buɗe gate din gidan, motar mahaifinta ta shigo. Kallonta yayi ya ce, "Ko Appa ne?".
Faryal ta ɗaga masa kai tare da faɗin, "Eh".
"To ai inaga ya kamata in je in gaishe shi ko, Are you Okay with that?".
Faryal ta sake ɗaga masa kai tare da faɗin, "Why not".
So bayan driver ya buɗewa Appa ƙofar motar ya fito, Faryal ta jagoranci Fayyad zuwa wurinsa. Ya durkusa cikin girmamawa domin gaishe shi, amma sai Appa ya miƙa masa hannu domin su yi musabaha. Haka dai a kunyace ya miqa masa hannun, Appan na tambayarsa ya aiki, ya amsa da, "Alhamdulillah".
"To, Madalla, Allah ya taimaka. Faryal idan kin gama, ki same ni a bangare na, Okay?".
"Okay Appa".
"To ɗan samari a gaida gida ko". Appa ya faɗa yana wucewa ciki. Fayyad ya bishi da kallo kafin ya ce, "Wallahi Faryal, Appa na da kirki sosai, gashi da saukin kai. Kalli fa yadda ya karɓe ni. Whl ya burgeni".
"Haka Appa yake ai, ba shi da matsala da kowa kuma ba shi da takura ko kaɗan". Ta ƙarashe tana kallon gate ɗin da aka sake buɗewa, motoci biyu suka shigo, ta farko motar da ake kai su Beta school a dauko su ne, ta biyun kuma baquwar mota ce da saidai tace ko baqi sukayi.
"To ni barin zo in wuce, naga kamar kun yi baƙi ma".
"Eh da alama kam. To Allah ya tsare hanya, ya kai ka gida lpy".
"Amin ya Allah, sai mun yi waya ko?". Tayi Murmushi tare da jinjina masa kai, ya buɗe motarsa ya shiga, ya ja, ya fice tana ɗaga masa hannu.
Sai da motar tasa ta fice daga gidan sannan ta juya ga Beta dake mata magana, sai dai kamar a mafarki idanunta suka sauka kan Barr Hashim wanda ya fito daga cikin motarsa, ashe shi ne biye da motar su Beta. Cikin sauri ta tura Betan cikin gida kafin ta nufi inda yake, tana haɗe fuskarta ta ce, "Me ya kawo ka gidan mu Barr Hashim?".
"Faryal kenan. Shin laifi ne idan mutum ya biyo abin da zuciyarsa take so".
"Amma Barr Hashim, ina ga zuwa yanzu ya kamata ka haƙura haka, ni fa da sharaɗin friendship na cigaba da mu'amalantarka, yanzu kuma an riga an tsayar da ranar aurena, and My fiance will not like seeing me communicating with someone else wanda ba muharrami na ba".
"Yanzu ita wannan karyar da kika shirya saboda zaki yi auren ne, ko kuwa saboda kin gan ni a wurin birthday party ɗin ƙawarki?".
Zaro ido Faryal tayi tana kallonsa cikin mamakin yadda akayi ya fahimci cewa ta gan shi, kenan shi ma ya ganta?
"Kin turo ƙanwarki dan ta tabbatar miki ko ni ne, kuma ta tabbatar ni ɗin ne. Amma ni ina ganin akwai yiwuwar mu fahimci juna, mu ji daɗin rayuwarmu kawai. Faryal please ki amince da ni, wahalarwar ta isa haka".
Faryal wadda ranta ya fara ɓaci ta ce, "Duba nan Barr Hashim, ni ba yar iska ba ce irin ka, shawara nake ba ka da ka ja motarka ka bar mana gida da ma rayuwata bakiɗaya, kaji ko".
"Oh really? Ashe ke ba yar iska ba ce kika je taron yan iska? Abokin barawo ai barawo ne Faryal, kawai feel free tunda dai yanzu kowa ya san asalin halin kowa. A baya nayi pretending saboda ina ganin ke yarinya ce mai kamun kai in kika san ainihin Hali na baza ki aminta dani ba, amma a yanzu tunda anyi walkiya, ya kamata mu fahimci juna, mu daidaita tsakanin mu. Kar ki damu, in dan saboda wannan wawan saurayin naki ne Hamdan, ƙawarki ta faɗa min komai, ni ina ga ba girman ki bane kici gaba da sauraron sa, ki tsaya kawai mu daidaita".
Faryal wadda ke masa wani irin Shocked glance, saboda jin da tayi yace wai ƙawarta ta gaya masa komai. Wato yana nufin ya sayi Walida da kuɗi ne dan ta gaya masa abubuwa game da ita? Kenan siyar da sirrinta Walida tayi?
Katse mata tunani yayi ta hanyar faɗin, "To yanzu dai yaushe za mu ɗan fita date haka?". Ya faɗa hankalin sa kwance.
"Whl Idan ka ƙara minti ɗaya a cikin gidan nan, sai na wulaƙanta ka fiye da yadda kake tsammani". Faryal ta faɗa tana watsa masa wani mummunan kallo kafin ta juya ta wuce ciki ta bar shi a wurin.
Ko da ta shiga ciki, kai tsaye ɗakinsu ta nufa, cikin ɓacin rai ta rufo ƙofar da ƙarfi. Hadiyyah wadda ke taimaka wa Beta wurin rage uniform ɗin jikinta ta ɗago ta kalli Faryal ɗin kafin ta ce, "Me ya faru kuma Faryal?".
Ƙarasowa tayi tana faɗin, "Ni da wannan ɗan iskan mana".
Hadiyyah ta kalle ta cikin rashin fahimta kafin ta ce, "Fayyad ɗin ne ɗan iska kuma?".
"Wani Fayyad, wannan Barr Hashim ɗin mana".
"Barr Hashim kuma? A ina kika gan shi?". Hadiyyah ta tambaya tana dafe kirji.
"Gashi can a compound ɗin gidan nan, ya zo yana gaya min wasu maganganun banza".
Hadiyyah ta juya ga Beta tare da faɗin, "Beta, je ki wajen Daadee, ina zuwa".
Da "To". Ta amsa sannan ta fice daga ɗakin, ita kuma Hadiyyah ta tashi ta riƙo hannun Faryal, ta jata suka zauna a bakin gado, kafin ta ce, "Me ya faru? Me ya kawo shi gidanmu?"........