Free chapter · Read without an account

Chapter 1

by Zainab Amzah · Nour Ayn

✨*𝐍𝐨𝐮𝐫 𝐀𝐲𝐧*✨



𝐁𝐲 𝐙𝐚𝐢𝐧𝐚𝐛 𝐀𝐦𝐳𝐚𝐡

***

***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

*As you read this book, I kindly ask you to pray for my late mother. May Allah forgive her shortcomings, illuminate her grave, and grant her eternal peace in Jannatul Firdaus. Ameen. 🤲🏻🙏🏻*

_Wannan labari kirkirarre ne, kuma ba a rubuta shi da niyyar ɓata wa wani ko wata ba ko cin zarafin kowa ba. Duk wani kamanceceniya da sunan mutum, halayyarsa ko wani abu da ya faru a rayuwarsa, idan ka/ki ga wani abu da ya yi kama da labarinka/labarinki a yi haƙuri please._🙏🏻

*PAGE 1*

Kyakkyawar matashiyar budurwa ce, wacce ba za ta wuce shekara sha takwas ba. Fara ce, amma ba fara tas ba. Tana da matsakaicin tsayi, ba za mu ce doguwa ba ce, kuma ba gajera ba ce. Allah Ya yi mata kyau da wani irin sura mai jan hankali. Sai dai a saman ta, ba ta da cikar ƙirji sosai. Duk da a kwance take, Amma za ka iya ganin yadda jikinta yake da kyau, kwance take a kan wani katafaren gado na alfarma dake cikin ɗakin, wanda aka k’awata shi tamkar ɗakin amarya. Komai na ɗakin ya nuna tsantsar tsada da haɗuwa, tun daga kayan ɗakin har zuwa labulen da aka saka a tagogin ɗakin. Tana sanye da kyawawan kayan barci silk pyjamas, masu launin pink, waɗanda suka kwanta luf-luf a jikinta. Lulluɓe take da duvet mai shegen kyau da laushi, sai juyi take yi a kan gadon, tana sauke wani irin nishi saboda tsananin ciwon mara da take fama da shi.

(Period cramps.)

Ta yi amai har ta gaji. Ba ƙaramin wahala take sha ba ko wane lokaci, domin kuwa duk zagayowar wata, sai ta shiga wani irin hali na rashin lafiya da yake hana ta gudanar da abubuwan da ta saba yi a rayuwarta. Wani lokacin ciwon kan yi tsanani har ta kasa tashi daga kan gado. Wani lokacin kuma Amai ne yake damunta, tare da ciwon baya da kuma kasala da take ji a dukkan jikinta, ba ita ce mace ta farko da take fama da ciwon al’ada ba, amma irin azabar da take sha a duk wata ya bambanta da yadda mutane da yawa suke sha, wannan ne ya sa take jin tsoron zagayowar wata fiye da yadda za a iya zato.

A duk lokacin da wata ya kusa zagayowa, takan shiga damuwa, zuciyarta takan yi nauyi saboda tunanin irin azabar da za ta sake fuskanta. Wani lokaci ma tun kafin lokacin ya yi, sai ta fara jin fargaba, tana tunanin ko wannan karon ma za ta sake shiga irin halin da ta saba shiga.

Ba ita kaɗai ce take shiga wannan fargabar ba, gabaɗayan su sukan kasance cikin zullumi da damuwa a duk lokacin da wannan lokaci ya zo, musamman ƙawarta kuma ‘yar’uwarta, wacce ta fi kowa sanin halin da take shiga ciki saboda tsananin kaunar da take mata, takan ji ciwon nata har cikin ranta, tare da tausayawa halin da take ganinta ciki.

Wani lokacin ma, tun kafin ciwon ya zo, Nadiya kan fara tambayarta ko tana jin wani abu a jikinta. Idan kuma ta lura da yadda Mimi ta canza saboda murɗawar da cikinta yake yi mata, sai ta kasa zama lafiya har sai ta tabbatar ta samu sauƙi. Domin kuwa ba ta iya jure ganin Mimi cikin azaba.

A wannan lokacin Mimi tana kwance, ta haɗe ƙafafunta wuri ɗaya, tana riƙe da cikinta da hannayenta biyu. Ta lumshe idanunta sosai, tana ƙoƙarin jure wani sabon ciwo da ya sake ratsata.

“Ya Allah Ya Rahman!”

Ta furta a hankali, yayin da hawaye suka taru a gefen idanuwanta suka fara zuba a hankali a kan kuncinta.

Ta juya zuwa ɗayan gefen gadon, amma hakan bai taimaka mata ba, sake juyawa ta yi, tana ƙoƙarin nemo yanayin da za ta ji sauƙi ko da na ɗan lokaci ne.

Amma ina!

 Ciwon kamar ƙara ƙamari yake yi. A hankali ta buɗe idanunta ta kalli agogon da yake jikin bango. Ta yi ƙoƙarin miƙa hannunta zuwa kan bedside drawer domin ta ɗauki wayarta ta kira Ammi, amma kafin ta kai gare ta, sai wani sabon nishi ya kufce mata sanadiyyar murɗawar da cikinta ya sake yi mata, da sauri ta mayar da hannunta, ta sake kwanciya, tana jan numfashi a hankali. 

A wannan lokacin, da akwai wanda zai iya ɗaukar mata ko rabin ciwon ne, da tabbas ta ji daɗi. Amma babu, sai ita kaɗai, da wannan azabar da take fatan ta ƙare.

A daidai wannan lokacin ne wata matashiyar budurwa, wacce ba za ta wuce shekara goma sha tara ba, ta shigo ɗakin cikin gajiya, dawowarta kenan daga school, kuma tun daga lokacin da ta shigo gidan take ta mitar fitar da ta yi tun safe. Ta tsani Saturday lectures, shi ya sa ba ƙaramin daɗi ta ji ba da aka soke lecture ɗin da za su yi daga ƙarfe biyu zuwa huɗu na rana. Aƙalla za ta samu damar yin barcin da ba ta samu yi ba da safe. Da shigowarta ɗakin, kai tsaye ta nufi gadon kamar yadda ta saba, tana cire mayafinta.

“Mimi! Mimi!”

Ta kira sunanta da ƙarfi cikin babbar murya, Amma babu amsa. Jin ta yi shiru ba ta amsa mata ba, hakan ya tabbatar mata da cewa barci take yi, domin ta san halin Mimi sosai. Indai wurin barci ne, babu na biyunta, musamman da ya kasance weekend. Idan har Nadiya ta dawo gida ba ta ga Mimi a kitchen ko ɗakin Ammi ba, to tabbas ta san tana nan ɗakinsu, ko dai tana kwance tana game da wayarta ko kuma tana chatting da bae ɗinta.

Sake kiran sunanta ta yi.

“Mimi! Mimi!”

Amma har lokacin babu amsa.

Nadiya ta yi murmushi kaɗan, tana girgiza kai. A ranta ta ce, “Wannan yarinyar barci ya zamar mata kamar ibada!” Yadda kasan kasa haka take indai wurin barci ne. Bata wasa da chance, ko min kankantar sa idan ta samu sai ta rimtsa.”

Ajiye kayanta Nadiya ta yi a kan gado, sannan ta zagaya ta nufi wurin Mimi, tana shirin jan bargon da ta rufe kanta da shi domin ta tashe ta.

Amma me?

Tana ƙarasawa sai ta tsaya cak, tana kallon yadda hawaye suka kwanta a kuncin Mimi, idanunta a lumshe, yayin da hannayenta suke riƙe da cikinta. Sosai fuskarta ta nuna irin azabar da take ji, har hakan ya sa Nadiya jin wani irin tsoro a zuciyarta.

“Mimi!”

Nadiya ta kira sunanta cikin sauri, sannan ta zauna a gefen gadon tana dubanta.

“Mimi!”

Mimi, what happened?”

Jin ta yi shiru, sai ta yi sauri ta ɗago ta,ta rungumeta jikinta tana ƙoƙarin kallon fuskarta sosai. Ganin yadda hawaye suka jika kuncinta ya sa zuciyarta bugawa da sauri.

“Mimi, me ya sa kike kuka? Me yake damunki?”

Duk a lokaci guda ta jero mata tambayoyin, cikin muryar dake nuna tsantsar damuwa.

Mimi ta kasa magana, sai dai a hankali ta ɗaga hannunta, ta nuna mata cikinta. Nan take Nadiya ta fahimci abin dake faruwa.

Period cramps!

“Ya Allah!”

Ta furta, tana dafe ƙirjinta, wanda har lokacin bai daina yi mata duka ba. Domin da farko ta ɗauka wani mummunan abu ne ya faru da Mimi bayan fitar da ta yi zuwa school.

A hankali Nadiya ta fara shafa mata baya, tare da cewa, “Sorry, sis, ki daina kuka, Allah Ya ba ki lafiya ya yaye miki dukkan tsanani da ciwo.” 

Ta ƙarasa faɗa muryarta a raunane, kamar ita ma za ta yi kuka. A duk lokacin da wani abu ya samu ɗayansu, idan abin farinciki ne, sukan kasance cikin farinciki gabaɗaya. Idan kuma abin damuwa ne, sukan shiga damuwa gabaɗayan su.

Wata irin ƙauna da shakuwa mai girma ce a tsakaninsu. Ba wai don ’yan’uwa kawai ba ne, a’a, sun kasance abokan juna ne ta kowace fuska. Nadiya ta san abubuwa da yawa game da Mimi, har ma da waɗanda wasu daga cikin ’yan gidan su ba su sani ba. Haka Mimi ma ta san duk wani abu da ya shafi rayuwar Nadiya, domin ba sa ɓoye wa junansu damuwarsu, komai ƙanƙantarta. A duk lokacin da al’adar Mimi ta zo, Nadiya kan fi shiga damuwa fiye da yadda take shiga a sauran lokuta. A duk wata, sukan kasance cikin fargaba saboda yadda Mimi take shan wahala.

Za mu iya cewa kusan tare suke shan jinyar, sai dai idan Nadiya tana makaranta. Ko da ba a jikinta ciwon yake ba, Amma tana jin kwatankwacin zafin a cikin zuciyarta saboda yadda ƙanwarta take shan wahala a duk wata, sosai hankalinta ke ta shi ganin yadda ciwon yake hana ta cin abinci ko yin barci cikin kwanciyar hankali, wannan ne ya sa take tausaya mata sosai. Tana jin kukan da take yi a cikin zuciyarta.


“Did you take your drugs?”

Nadiya ta tambayeta cikin kulawa.

Girgiza kai Mimi ta yi a hankali.

 Nadiya ta dafe goshinta ta ce, “Mimi! Why didn’t you take your medication when you knew you were supposed to take it before the pain got worse?.”

Ta ƙarasa faɗa cikin damuwa. 

Mimi ta buɗe baki kamar za ta yi magana, amma sai ta kasa. Ta sake lumshe idanunta, tana ƙoƙarin jure wani sabon ciwo da ya ƙara taso mata. 

Miƙewa Nadiya ta yi cikin sauri, ta nufi bedside drawer inda suke ajiye magungunansu. Ta buɗe shi, ta fara lalube cikin sauri, tana ɗaga ƙananan kwalaye da sauran kayayyakin dake ciki.

Amma ba ta ga maganin da Mimi take sha ba.

Sai da Nadiya ta sake bincika drawer ɗin tsaf, amma ba ta samu magani ko ɗaya ba.

Hakan yana nufin maganin ya ƙare kenan. Ta juya ta kalli Mimi, wadda har yanzu take kwance tana nishi, at the same time tana kuka.

“Ya Allah, what am I going to do now?”

Nadiya ta furta a hankali, tana jin damuwa na ƙara mamaye zuciyarta. Cikin sauri ta fita daga ɗakin, ta nufi ɗakin Ammi da ’yar damuwa kwance a fuskarta.

Zaune ta samu Ammi a kan prayer mat, ta idar da sallar Azahar, tana addu’a.

Nadiya ta shiga da sallama a bakinta. Bayan sun gaisa, Ammi ta ɗago kai ta kalleta.

“Har kin dawo, Nadiya?”

“Eh, Ammi,” Nadiya ta amsa a sanyaye.

Ammi da ta lura da yanayin sauyin fuskarta gabanta ya dan fad’i, ta danne ta ce, “Tun yaushe kika dawo?”

“Just now. Na shigo na ga kina sallah ai, sai na wuce ɗaki.”

“Okay. Amma yau kin dawo da wuri, ke da idan kika fita sai yamma kike dawowa.” 

Nadiya ta ɗan yi murmushin da bai wuce baki ba ta ce “Eh, lecturer ne bai zo ba, so morning lecture kaɗai muka yi, shi ya sa na dawo da wuri.”

Ammi ta gyada kai.

“Okay.”

Kafin ta ci gaba da magana, Nadiya ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta dubeta cikin damuwa ta ce, “Ammy, Mimi tana ɗaki kwance, cikinta ya fara yi mata ciwo.”

Da jin haka, Ammi ta ɗago kai da sauri. “Subhanallah! Ciwon ciki kuma?” Eh, Ammi, baki ganta ba wallahi sai kuka take yi. Ina shiga ɗakinmu yanzu na same ta kwance ta riƙe cikinta tana kuka.”

Ammi ta yi shiru na ɗan lokaci, tana kallon Nadiya da mamaki.

Bayan wasu seconds ta ce, “Ikon Allah! Kin san ban daɗe da dawowa daga ɗakinku ba? Na ganta a kwance, sai na yi tunanin barci take yi, sai na ce bari in barta in yi sallah. Idan na idar ban ji motsinta ba, sai in koma in tashe ta. Ashe ba ta jin daɗi?”

Eh, wallahi Ammi, ni ma ban sani ba sai yanzu, nasan dai lafiya lau na barta ɗazun da safe lokacin da zan wuce makaranta. Amma da na shiga ɗaki yanzu sai na same ta kwance tana kuka.” Nadiya ta ƙarasa faɗa a raunane.

Ammi ta sauke ajiyar zuciya.

“Allah sarki! Na ji shirun ya yi yawa fa tun safe da muka yi breakfast ban ƙara jin motsinta ba. Na zata barci take. Ashe shi ya sa yau ba ta shigo kitchen ba kwata-kwata. Haba, ni dai na san ba haka kawai na ji ta yi shiru ba. Allah Ya ba ta lafiya.”

“Amin, Ammi.”

 Nadiya ta faɗa cikin damuwa, sannan ta ɗaura da cewa, “Wallahi, Ammi, tausayi Mimi take ba ni saboda yadda ciwon nan bai zo mata da sauƙi, tana shan wahala sosai.”

Ammi ta sake sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce, “Haka ne, Nadiya. Ni ma abin yana damuna sosai, wallahi. Allah Ya ba ta lafiya, Ya yaye mata wannan ciwon.”

“Amin, Ammi,” Nadiya ta amsa a hankali.

Ammi ta miƙe, ta ɗauki wayarta ta ce, “Mu je in duba ta.”

Tana gama faɗin haka ta fara neman lambar Faruk a wayarta, tana ƙoƙarin kiransa a lokaci guda tana tafiya zuwa ɗakin su Mimi.

Shigarsu ɗakin ke da wuya, suka tarar da Mimi har lokacin tana kwance a inda Nadiya ta barta, cikin mawuyacin hali. Duk wani ƙarfinta ya ƙare saboda yawan amai da ta yi. Sosai fuskarta ta nuna irin galabaita da azabar da take ciki, yayin da idanunta suka yi ja saboda kuka. 

Cikin sauri da tashin hankali Ammi ta matso kusa da ita, ta zauna a gefen gadon. Cikin kulawa ta ɗago ta ta kwantar da ita a saman ƙafafunta, tana shafa bayanta a hankali.

“Sannu, Mimi.”

Ta ɗan dakata kafin ta ci gaba.

“Ba ki da lafiya, shi ne ba za ki faɗa mini ba? Har sai da Nadiya ta shigo ta ganki a kwance sannan ta zo ta sanar da ni.”

Ta faɗa cikin tausasa murya.

Mimi ta ƙara manne jikinta da na Ammi, tana kuka a hankali.

Ammi ta ci gaba da magana.

“Yanzu da ba ta dawo ba, haka za ki ci gaba da zama da ciwo ba zan sani ba? Haba, Mimi, me ya sa kike haka? Idan ba za ki iya zuwa wurina ki faɗa mini ba, ai ko a waya ya kamata ki kira ki sanar da ni.”

Mimi dai kuka kawai take yi, tana riƙe da cikinta. Ta kasa ba Ammi amsa, domin ciwon da take ji ya fi ƙarfin abin da za ta iya faɗa a wannan lokacin.

Ammi ta share mata hawaye, sannan ta ce, “Kin sha maganinki kuwa?”

Mimi ta girgiza kai a hankali.

 Kafin Ammi ta sake tambayarta wani abu, Nadiya ta ce, “Ammi, maganinta ya ƙare gabaɗaya. Kafin in zo wurinki, sai da na duba mata, amma ban samu ko ɗaya ba.”

Ammi ta ce, “Subhanallah! To, me ya sa ba ku sanar da ni cewa maganin ya kusa ƙarewa ba? Ai na ce maku ku dinga faɗa mini da wuri, ba sai ya ƙare ba tukunna za ku faɗa mini ba.”

Nadiya ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce, “Ki yi haƙuri, Ammi.”

Ammi ta sauke numfashi.

“Ba komai. Yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne mu tabbatar ta samu kulawar da take buƙata.”

A daidai lokacin ne Mimi ta fara ƙoƙarin tashi daga kan ƙafafun Ammi.

Ammi ta kalleta.

Tun kafin ta yi magana, Mimi ta miƙe da sauri, ta nufi toilet.

Cikin sauri Nadiya ta bi bayanta, amma kafin Mimi ta ƙarasa toilet, sai ta fara amai a ɗakin. 

Da sauri Nadiya ta isa wurinta, ta dafa bayanta tana yi mata sannu. Bayan Mimi ta gama amai, Nadiya ta taimaka mata ta gyara jikinta. Ta wanke mata baki, sannan ta taimaka mata ta dawo ɗakin. Ko da suka fito, Amina, wadda Ammi ta kira a waya domin ta gyara wurin da Mimi ta ɓata, suka tarar har ta kammala gyaran wurin. Ta ɗauko turaren wuta na Scents by Teemah ta saka musu a ɗakin.

A hankali Mimi ta koma kan gadon, ta kwanta tana jan numfashi.

Ammi dake zaune ta dubi Mimi cikin tsananin damuwa ta ce, “Sannu, ’yata. Allah Ya ba ki lafiya.”

Mimi ta buɗe idanunta a hankali, ta kalli Ammi, amma ta kasa magana. Ammi ta ɗauki wayarta ta sake kiran faruk amma har wayar ta yanke bai ɗauka ba, kiran sa ta sake yi har lokacin bai ɗauka ba.

Wayar Ammi ta duba, sannan ta dubi Mimi, sai ta sake gwada kiransa a karo na uku, amma bai ɗauka ba. Sosai damuwarta ta ƙara tsananta. Ba wai don Faruk bai ɗauki wayar ba kawai, sai don tana ganin yadda Mimi take ƙara galabaita a gabanta. Ba ta son ɓata lokaci tana jiran wani abu da ba ta san lokacin da za ta same shi ba. 

Ajiye wayar ta yi, ta dubi Nadiya ta ce, “Mu kai ta Hospital.”

Nadiya ta gyada kai da sauri.

“Yes, Ammi. I think that’s the best thing to do.”

“Please get her hijab. We need to rush her to the Hospital now.”

Cikin sauri Nadiya ta buɗe press ɗinsu, ta ciro hijab ɗin Mimi, sannan ta dawo ta taimaka mata ta saka. Bayan sun shirya, Nadiya ta kama Mimi a hankali, yayin da Ammi ta tallafa mata. A hankali suka fito daga ɗakin, suka sauka downstairs. Malam TK, direbansu, yana zaune tare da Shafi’u, mai gadi, suna hira a bakin ɗakin Shafi’u. Tun dawowarsa daga ɗaukar Nadiya daga makaranta suke zaune a wurin, suna ta hirarsu kamar yadda suka saba. Ganin Ammi da Nadiya sun fito suna riƙe da Mimi, hakan ya sa Malam TK cikin sauri ya katse hirar ya miƙe tsaye, ya ƙaraso wurinsu.

Bayan ya gaida Ammi, ta ce, “Mimi ce ba ta jin daɗi, za mu kai ta Hospital.”

Da sauri Malam TK ya buɗe musu ƙofar mota.

“Allah Ya ba ta lafiya.”

“Amin,” Ammi ta amsa. Suna shiga mota, Mimi ta kwanta a jikin Ammi, domin ko zama ba ta iya yi saboda tsananin ciwon da take ji a cikinta da bayanta.

Nadiya ta zagaya front seat ta zauna, tana kallon Mimi ta cikin madubin mota, tana ƙara jin tausayinta. A duk lokacin da ta ga hawayen Mimi, sai ta ji wani irin zafi a zuciyarta. Da ace tana da ikon ɗaukar wani ɓangare na ciwon ta rage wa ƙanwarta, da ta yi hakan tun tuni.

Malam TK ya yi sauri ya shiga mota, ya tada ta, ba tare da ɓata lokaci ba, ya ja motar suka bar gidan.

Kai tsaye ALYSHA PREMIERE HOSPITAL dake garin Abuja ya nufa da su. Kasancewar ya san nan ne asibitin da iyalan Gimba suka fi zuwa, saboda haka bai buƙatar ƙarin bayani. Sannan a nan ne Dr Faruk yake aiki, Ammi’s first born.

A cikin motar, Mimi tana kwance a jikin Ammi, tana ƙoƙarin jure ciwon da yake tsananin damunta. Ammi ta ci gaba da shafa bayanta a hankali, tana yi mata addu’a. Nadiya kuwa ba ta daina kallonsu ta madubi ba. A duk lokacin da ta ji Mimi ta yi nishi, sai ta juyo da sauri, ta yi mata sannu cikin tsananin tausayin da take ji. A ranta tana tunanin, ina ma ace za ta iya raba ciwon gida biyu, ta ɗauki wani ɓangare domin rage wa ’yar’uwarta raɗaɗin da take ji.

Amma babu abin da za ta iya yi a wannan lokacin, sai addu’a.

Ta sake kallon Mimi ta cikin madubi, sannan ta share hawayen da suka taru a gefen idanunta. 

'Ya Allah, ka ba ta lafiya ka sa ta samu sauƙi.'

Ta yi addu’ar a cikin zuciyarta.


*Ina mai farin cikin sanar daku muna siyar da Kaya Kala Kala masu kyau da quality direct from Egypt Abaya, jalbabs,  boubou, scarfs, jersey hijabs, jersey veils, comfy gowns, tie back caps,crinkle turban caps,nightwear’s and lots more. Muna yin adashe na kome kake so  ga wanda bashida halin siya lokaci daya.. Masu son fara business su ma muna maraba dasu.*

For more info
 +201508856397.

+201508856397/0806671505
My WhatsApp number 
Tiktok @amzaah
Instagram @zainabuh_Amzah
Snapchat @Zainabuh Amzah 
Arewa pen @ZainabAmzah.
Wattpad @zainabuh Amzah
Facebook @zaina yahaya Amzah.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol