Free chapter · Read without an account

2

by Zainab Amzah · Nour Ayn

✨𝐍𝐨𝐮𝐫 𝐀𝐲𝐧✨



𝐁𝐲 𝐙𝐚𝐢𝐧𝐚𝐛 𝐀𝐦𝐳𝐚𝐡


***

***


*PAGE 2*

Koda suka isa Asibiti ko neman Faruk Ammi bata tsayi yi ba, saboda yanayin jikin Mimi sai gaba yake yi. Ko kafin su ƙaraso sai da ta kara yin amai a mota. Ba tare da ɓata lokaci ba, aka yi attending ɗinsu, kasancewar a san su sosai a Asibitin. Domin kusan duk wata sai Mimi ta kwanta a Asibitin, sannan kuma Ammi mahaifiya ce ga Dr. Faruk, one of the best gynecologists they have at the Hospital. Bugu da ƙari, nan ɗin wurin zuwan su ne. tun kafin Faruk ya tafi London yin master’s ɗinsa. Bayan ya kammala karatunsa ya dawo Nigeria, ya fara aiki a ALYSHA Premier Hospital. Tun bayan dawowarsa sai suka rage zuwa Hospital ɗin, shine yake kula da duk wani harka da ya shafi lafiya a gidan da Family ma gabaɗaya. Idan ka gan su a Asibitin, to akwai babban dalili da ya kawo su, ko kuma wani emergency kamar na yanzu. Ko kuma idan shi yazo da su for some examinations. Yanzu ma don Ammi ta kira sa bai ɗauka ba, ta san definitely akwai babban dalilin da yasa bai picking calls ɗin ta ba, don Faruk never jokes with anything da ya shafe ta. Sannan kuma ƙari da ganin yanayin halin da Mimi ke ciki, shine dalilin da ya sa ta yi deciding su taho Asibitin su sameshi a nan. Kwantar da ita aka yi bayan ta ga Likitan, because her body was already too weak. Aka saka mata drip tare da allurai da suka taimaka mata wajen samun sauƙi, har bacci mai nauyi ya ɗauke ta. 

Sai a lokacin Nadiya ta samu damar yin sallar Azahar da ba ta samu damar yi ba a gida bayan ta dawo daga school. Itama Ammi da ta ji ta samu natsuwa a lokacin ‘yar damuwarta ta kau sai ta aika Malam TK, ya je gida wurin maid ɗinsu ya amso musu abinci da duk wani abu da za su buƙata. Sai gab da Maghriba Mimi ta farka daga Bacci, cikin sauƙin jiki ta tashi, unlike yadda suka shigo da ita da ga farko. 

Bayan ta tashi daga bacci, Nadiya ta kama ta ta kai ta toilet. Sai da ta wanke bakinta, ta gyara jikinta sannan suka fito. Suna fitowa, Ammi ta dubeta cikin tausayawa 

“Nadiya haɗa mata tea. Sai ki zuba mata abinci kaɗan ta ci. Idan ta gama sai ta sha maganinta.”

Dan marairecewa Mimi ta yi tare da girgiza kai, a hankali alamun ba ta son cin abincin

 “Ki yi haƙuri Ammi ba zan iya cin abinci ba yanzu, sai dai tea zan ɗan sha kaɗan.”

Ammi ta bi ta da kallon tausayi

“Ki daure ko kaɗan ne ki ci, kin ji Mimi? Zama da yunwa babu daɗi, zai ƙara miki ciwo ne, ko ba ki son ki warke da wuri?”

Girgiza kai ta yi cikin sanyi jiki tamkar za ta saki kuka. "No Ammi, please later.” Ta ƙarashe faɗa cikin shagwaɓa.

Jin abun da ta ce ya sa Ammi murmushi tana duban Nadiya.

"Ki ba ta tea ɗin kawai tun da ba za ta iya ci ba amma lalle anjima dole ta ci abinci ko don ta ji ƙwarin jikinta." Mug din dake hannun Nadiya ta mikawa Mimi. 

Ta ya motsa fuska kaɗan ta karb’a. A hankali ta fara sipping tea ɗin, ba ta wani jima da fara sha ba ta ce ta koshi. Sai da Ammi ta matsa mata, da ƙyar aka samu ta shanye tea ɗin gabaɗaya. Bayan ta gama shan tea ɗin, magani Ammi ta ba ta sha. Tana gamawa ta sake kwanciya. Tun asali dama Mimi ba ta son cin abinci tun tana ƙarama. Tun abin yana damun Ammi har ya kai ta gane nature ɗinta ne hakan, bare yanzu da ba ta da lafiya kuma.

Faruk ne zaune an office ɗinsa, ba su daɗe da fitowa daga theatre room ba, dan haka a gajiye yake sosai saboda last surgery ɗinsu da ya ɗauki lokaci sosai kafin suka gama. Kai tsaye Masallaci ya wuce ya fara yin sallah sannan ya dawo Office ɗinsa. iPhone 17 Pro Max ɗinsa ya jawo zai duba time. He saw a lot of missed calls from different people. Daga cikin su akwai na Fahad, da na friend dinsa Mujahid da ya tafi garinsu an yi musu rasuwa, sai kuma na Ammi da bata daɗe da sake kiransa ba, ganin tarin missed calls ɗin Ammi, sai hankalinsa ya ɗan tashi. Ya san definitely akwai problem. If not, Ammi da ya sani da tayi masa kira biyu ba za ta sake ba muddin yana Hospital, duba da yanayin aikinsa. Dialing number ta ya fara yi, yana kira ta ɗauka.

Bayan sun gaisa, ya ce “Sorry, Ammi, Na fito daga theatre yanzu ne na ga missed calls ɗinki. Hope you’re okay?”

“Alhamdulillah, muna lafiya. Amma muna Asibitin ku Faruk.”

Da jin haka ya ɗan gyara zamansa. “Okay, wane ɗaki?” Ya tambaye ta cikin natsuwa. Tana faɗa masa ya ce, “Just a minute. I’m coming now.” Yana gama faɗa mata ya kashe wayar, ya fara tattara phones ɗinsa tare da duk wani important abu da zai buƙata. Ya yi switching off komai na office ɗin, sannan ya ɗauki car key ɗinsa ya fita. 

Kai tsaye ya nufi ward ɗin da suke, cike da mamakin waye kuma ba shi da lafiya tun da bai tsaya tambaya ba. Amma shi dai ya san lafiya lau ya bar kowa a gida. Da sallama ya shiga ɗakin. Nadiya, dake zaune kusa da Mimi tana chatting, ta yi saurin gyara zamanta. At the same time, ta aje wayarta gefe jin sallamar sa cikin muryarsa mai daɗin sauraro. Ɗan kallon sa ta yi sannan ta ce, “Yaya, ina wuni?” Cikin natsuwa ya amsa mata, sannan ya ƙara gaida Ammi. Ganin Nadiya da Ammi suna zaune a ɗakin ya sa ya gane wacce ba ta da lafiya, da kuma dalilin zuwan su hospital ɗin. Gadon ya zuba wa ido, tare da jan ɗan ƙaramin tsokin da ba lallai ma ka ji ba. After some seconds, ya nufi gadon kai tsaye, cikin takunsa mai ban sha’awa. Saurin rufe idonta ta yi da ta ji alamun yana tahowa, pretending as if she’s was sleeping. A lokaci guda kuma gabanta ya ci gaba da bugawa da sauri. Kallonta ya yi, sai kuma ya dubi Nadiya ya ce “Me ke damunta?” Duk da ya san dai ba zai wuce dysmenorrhea ba, amma still ya tambaya. “Cikinta ke ciwo,” Ammi ta ba shi amsa. Yace, “Okay. Allah ya ba ta lafiya.” “Amin,” suka ce a tare. 

Kallonta ya sake yi. Ya ga idanuwanta a lumshe, but still sun kumbura, alamun ta sha kuka ba kaɗan ba. Tabe baki ya yi sannan ya ce, “Lazy girl.” Duk da ƙasa-ƙasa ya faɗa, amma sarai ta ji shi. A ransa ya ce “Shi bai san wace irin ragguwa yarinya ce wannan ba, da ba za ta iya daure wa ciwo komai ƙank’antarsa ba, ga kukan banza da ba ta gajiya da shi.
Just period cramps, Amma ba za ta iya enduring ba, ta yi ta damun mutane da kukan banza.
Ashe duk ranar da za ta haihu, ba ƙaramin wahala za a sha ba?
Don ya san sai kowa ya ji a jikinsa, daga ita har Doctors ɗin.
Lallai akwai aiki.” Ya ɗan girgiza kansa sannan ya ɗauki folder da ya gani nata aje. Bayan ya duba yanayinta da kuma abubuwan da likitan da ya karɓe ta ya rubuta, Drip ɗin ya yi disconnecting sannan ya juya ga Ammi, zamu iya tafiya yanzu Ammi. No need to stay here. I’ll take care of her at home. Ku shirya kafin na dawo.” Bai jira cewar Ammi ba, ya fice daga ɗakin domin amsar mata sallama. Mimi kuwa tana jin duk abin da yake faɗa, amma ta ƙi buɗe idanunta.

A ranta ta ce, ‘Wai wannan mutumin ko tausayi ba ya da shi ne? Ni fa ba daɗi nake ji ba, Ina ta kaina amma shi sai ya zauna yai ta yi wa mutane faɗa yana kirana lazy girl, don bai san yadda nake ji ba ne, da mace ne shi wallahi da na yi masa addua Allah ya jarabe shi shima yaji yadda nake ji.’ Ta ɗan tura leɓenta gaba cikin ɓacin rai….


📢 SANARWA

*Ina mai farin cikin sanar da ku cewa muna siyar da kaya kala-kala masu kyau da quality, direct from Egypt: Abaya, Jalbabs, Boubou, Scarfs, Jersey Hijabs, Jersey Veils, Comfy Gowns, Tie-back Caps, Crinkle Turban Caps, Nightwears, and lots more.*

*Muna yin adashe na komai kake so ga wanda ba shi da halin siya lokaci ɗaya. Masu son fara business su ma muna maraba da su.*
For more info:
+201508856397
WhatsApp only.

My WhatsApp Number: +201508856397

TikTok: @amzaah
Instagram: @zainabuh_Amzah
Snapchat: @Zainabuh Amzah
Wattpad: @zainabuh Amzah
Arewapen: @zainab Amzah

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol