Free chapter · Read without an account

4

by Zainab Amzah · Nour Ayn

✨𝐍𝐨𝐮𝐫 𝐀𝐲𝐧✨



𝐁𝐲 𝐙𝐚𝐢𝐧𝐚𝐛 𝐀𝐦𝐳𝐚𝐡


***

***


*PAGE 4*

Faruk yana shiga ɗakin, ya tarar da Nadiya tana ta fama da Mimi domin ta ci abinci, amma sam ta ƙi. Tea kawai take sha, sai kuma cookies da ta ci kaɗan ba da daɗewa ba. Sallama ya yi sannan ya shiga ɗakin. A lokaci guda, ƙamshin turarensa mai daɗi ya cika ɗakin. Nadiya ta amsa masa, sannan ta sake gaishe shi. A sanyaye Mimi ta ɗago idanunta da suka kumbura saboda kukan da ta sha, haɗe da dogon barcin da aka sa ta yi. Tana ɗagowa suka haɗa ido, cikin sauri ta sauke kanta ƙasa. After some seconds, ta sake ɗagowa cikin sanyin muryarta da take fita a hankali ta ce,

“Yaya, ina wuni?” Lafiya, ya jiki?” Ya faɗa cikin yanayi na wanda ba shi da niyyar tsawaita magana. 

“Alhamdulillah. 

Bayan sun gaisa, ya ƙarasa inda take, ya cire mata drip ɗin saboda ya riga ya ƙare. Ya kalli Nadiya ya ce, “Ta sha magani?”

“A’a, Yaya, ba ta sha ba, kuma ta ƙi cin abinci. Tea kawai take sha, shi ma ba da yawa ba.”

Shiru ya yi kamar ba zai yi magana ba. Zuwa can ya ce,

“Miƙa mata abincin.”

Nadiya ta miƙa mata plate ɗin dake hannunta kamar yadda ya ce, cikin sanyin jiki Mimi ta karɓi abincin, hawaye na taruwa a idanunta. Tana karɓa ya kalleta, sai da ya daure fuska sannan ya ce “Maza ki cinye abincin nan da sauri yanzu, kar ki ɓata mini lokaci inada abin yi. Yana gama faɗa ya jingina jikinsa da bangon ɗakin, ya rungume hannuwansa a ƙirji yana kallonta. Fuska babu alamar wasa. Share hawayen da ya fara gangaro mata ta yi. Allah ya sani ko abinci ba ta son gani tun da ta fara ciwon nan bare akai ga maganar cin sa, ba ta da yadda za tayi tunda ba zata iya yi masa musu ba, haka nan ta daure ta fara cin abincin ba don tana so ba, shi dai Faruk yana tsaye yana kallonta cike da mamaki. To yanzu minene abin kuka kuma daga saƙata cin abinci? Gaskiya yarinyar nan an sangartata ta da yawa. In ba don Fahad ya roƙe shi ya saƙata cin abinci ba yaushe zai zauna yana bata lokacinsa a kanta? Sannan shi da kan sa ya san shi kaɗai ne zai iya sakata cin abincin ta ci, duk faɗin gidan kuwa, domin babu wanda zaiyi mata tsaye har sai ta ci abincin yadda ya kamata, sai dai kawai su yi ta bata lokacinsu suna lallaba ta kamar wata yarinya. Akan me? Abin da ba zai iya yi ba kenan. Sake kallonta ya yi ya ga yadda take cin abincin, shi abun ma dariya yaso ya ba shi, da ka ga yadda take cin abinci ka san dole aka yi mata, sai kace ba a cikin ta zata saka ba. Hidimar yarinyar nan yawa gareta, ko wacce rana da kalar salon da zata tsiro, shi har ya fara tausayin Fahad wallahi. A haka yake ce wa zai ɗauketa. Ko da yake shi ya ji zai iya, kuma dama training ɗinsa ce. 

Kallansa ta yi ta gefen ido ta ga still idonsa na a kanta. Haka ta daure ta ci gaba da tura abincin duk da ba daɗin sa take ji ba saboda ta yi loosing appetite dinta, sai da taji kamar abinci zai dawo mata sannan ta ɗan ɗago ta kalleshi, suna haɗa ido ta yi saurin sauke kanta ƙasa gabanta ya na bugawa da sauri da sauri, ɗan marairaicewa ta yi ta ce, “I’m stuffed."

Kallonta ya yi yaga ta ɗan ci abinci da yawa ba laifi. Ya dubi Nadiya ya ce “Miƙa mata maganin ta sha. Ba tare da musu ba ta karɓa ta sha, don babu wani sauki a tattare da fuskar Faruk da zai sa ta kuskura ta yi masa musu. Bayan ta sha maganin allura ya saƙe yi mata sannan ya bar ɗakin. Yana fita ba da daɗewa ba wayar Nadiya ta ɗauki ƙara, tana dubawa ta ga Yaya Fahad ne, daman ta san ba zai wuce shi ɗin ba, don kiran da ya yi mata yau babu adadi duk saboda Mimi. Picking call ɗin tayi cike da tsokana ta ce “Bae, Inawuni?” Ta fada ta na wani irin murmushi, tun kafin ya ce komai ta ƙara da cewa, “To Allah ya yi dai Bae ta tashi sai hankalin ka ya kwanta yanzu, dariya ta kuma yi sosai sannan ta miƙa wa Mimi wayar. Sallama ta yi cikin yar ƙaramar murya irin ta marasa lafiya tare da gaishe shi. Ajiyar zuciya ya sauke, bayan ya amsa sallamar ta. Allah kaɗai ya san yadda ya ji a cikin waɗannan hours ɗin da ya ɗauka ba tare da ya ji muryarta ba. Ya ce, “Babe, ya jiki?” A hankali ta ce, “Da sauƙi.”

“Kin ci abinci?”

“Eh, na ci.”

“Are you sure?” Ta gyada kanta kamar yana wurin. “Maganinki fa? Nadiya ta ce mini kin ƙi cin abinci, sai tea kaɗai kike sha. Me ya sa, babe? Ko ba ki son ki warke ne?” “Ina so in warke mana, kuma na sha maganin yanzu ai. Yaya Faruk ya ba ni ba da daɗewa ba.” Yaji daɗin jin hakan, duk da ya san Faruk ba ya supporting alaƙarsa da Mimi, amma duk abin da ya ce ya yi mata yana yi, ko da bai so kuwa. A cewarsa yana zubar musu da mutunci ne, wanda shi a ganinsa ba komai ba ne don kana da ra’ayi ko burin yin auren dangi. 

Ya ce “What about your phone?” Sai a lokacin ta tuna da wayarta da rabon ta da ita tun da safe da cikinta ya fara yi mata ciwo ta wurgar da ita. 

“Tana nan, ba ta da caji.”

“Ok, ki saka shi a caji zan kira anjima. Allah ya ƙara lafiya.” “Amin ya rabbi.” Bayan ta kashe wayar ta miƙa wa Nadiya wayarta. Bacci ta sake komawa saboda maganin akwai mai saka bacci. Sai bayan ta kwanta sannan Nadiya ta yi wanka ta saka pyjamas ɗinta ta kwanta tana chatting da Halim, har ba ta san lokacin da barci ya ɗauke ta ba.

Washegari Mimi ta tashi da sauƙin jiki sosai, ko da ta tashi already Nadiya na kitchen da maid ɗinsu suna haɗa breakfast, dokar Ammi ce bata yarda 'ya'yanta mata su zauna gida jibge basa aiki, sai dai komai a ce masu aiki suyi. A cewarta wannan ba gata bane ka bar 'ya'yanka mata a gida ba sa aiki sai dai komai a yi musu. Ita ba ta cikin wannan layin duk da arziƙun da suke da shi kuwa.
Dole ne 'ya'yanta su yi aiki ko ba sa so, ko don saboda halin rayuwa, sau da yawa idan tana son a yi mata wani abu, duk da akwai masu aiki, ba za ta saka su ba sai dai ta saka ‘ya’yanta. Wani lokacin kuma ta haɗa su duka gabaɗaya. Training ɗin da tayi musu kenan tun basu saba ba har suka saba da hakan, duk lokacin da za su yi girki tare suke yi gabaɗaya. Musamman idan Faruk na gida. Don ba ya cin abincin masu aiki sai dai wanda Ammi ta dafa ko sisters ɗinsa. Wanka ta fara yi, bayan ta fito daga wanka zaunawa ta yi sai da ta gama shafe-shafen ta sannan ta ciro doguwar riga bou bou na adire ta saka, ta daura scarf a kanta, ta yi kyau sosai duk da ba wani abu ta shafa wa fuskarta ba, har ta miƙe za ta bar wurin ta tuna da wayarta da take a kashe tun jiya. Ɗauka ta yi ta saƙa chargy. After 10 minutes ta kunna wayar, kamar abun jira sai ga call ɗin Fahad ya shigo, zaunawa ta yi har saida suka gama waya sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Ammi. Da sallama ta shiga ɗakin, sai da taje har gabanta ta zauna kusa da ita sannan ta ce “Ammi Ina kwana? Da fara'a Ammi ta jawo ta jikinta tare da ba ta ɗa side hug ta ce “lafiya lau Mimi, ya kike ya jikin ki? Tace “Da sauƙi sosai.” 
“I hope ba ki jin ciwo kuma?”Ammi ta tambaye ta cikin kulawa, girgiza kai ta yi tare da ce wa “Ba ni jin ciwo Ammi, kawai dai ina jin pain kaɗan-kaɗan.” Cike da kulawa Ammi ta ce, “Sorry daughter, insha Allah zai bari, wata rana ma za ki nemi shi ki rasa gabadaya.“
 “To Ammi, Allah yasa, don wallahi ba ki ji yadda nake ji ba, bayana ya yi ta ciwo.” “Kar ki da mu, ki ci gaba da addu'a kin ji?” Nima ina yi miki sosai, zai bari insha Allah.” “To Ammi Allah yasa, nagode sosai da addu’ar ki.” Ammi ta yi murmushi ta ce “Nazo dazun ai kina barci” Murmushi Mimi ta yi ta ce “Allah sarki kuma banji shigowar ki ba.” Suna cikin magana Nadia ta shigo, bayan sun gaisa da Mimi ta sake yi mata ya jiki tace “Ammi, breakfast is ready.” Tashi suka yi gabaɗaya suka nufi dining area. Zaune suke a dining ɗin cike da so da ƙaunar junan su gabaɗaya, ba su daɗe da zama ba Faruk ya shigo, tun kan ya ƙaraso ƙamshin turarensa mai daɗi da tsada ya cika wurin, ya yi kyau sosai cikin shirinsa na fita, sai wani irin ƙamshi yake mai azabar dadi, gaishe shi suka yi gabaɗaya. A hankali ya zauna sanna ya gaida Ammi. Bayan sun gaisa ta ce, “Ya naganka da shiri kamar za ka fita? Kuma yau sunday.” Cikin natsuwa ya ce, “Mujahid ya kira ni yanzu wani emergency ne ya taso Ammi so I have to leave.” 

“Ok, Allah ya taimaka ya bada sa'a.”  “Amin.“ Nadiya ta mike ta yi serving dinsu gabaɗaya, kowa ya faɗa mata abinda zaici ta saƙa masa. A gurguje Faruk yake yin breakfast saboda fitar da zaiyi. Toasted bread Mimi ta ci sai tea kaɗan da ta sha, ba ta jima da fara cin abincin ba ta tura plate dinta gefe. Ammi ta dube ta ta ce “Har kin yi me?” Murmushi mimi ta yi sannan ta ce “I am full, ganin irin kallon da Ammi ke yi mata yasa tayi na rai-na rai da ido, cikin yar shagwabar da ta zame mata jiki ta ce “Na ci da yawa ai Ammi.” “Yanzu wannan ne kin ci da yawa?” Ammi ta tambaye tana nuna plate din da Mimi ta tura gefe. Dan shafa kanta ta yi tana ta ce “Eh Ammi.” Ammi ta ce “To shikenan ayy, ki dinga cin abinci dai yadda ya kamata, shiyasa har yanzu ga ki nan ba ki ƙara girma, ba ki gaba, baki baya, kullum kina nan yadda kike, ba ki ganin yadda 'yar uwarki take cin abinci? Ko hakan bai burge ki?” Nadiya ta yi dariya ta ce “Ahto, faɗa mata dai Ammi.” Mimi dai murmushi kawai take yi, zuwa can ta ce “To shikenan, insha Allah zan dinga ci da yawa Ammi. But yanzu I am full, I promise anjima zan ci da yawa.” “To, Allah yakaimu anjima lafiya.” Ta ce “Amin." Miƙewa ta yi a hankali ta na duban Ammi ta ce “Zan je in sha maganina,”

 “Ok. Allah ya kara lafiya.” Ɗaki Mimi ta nufa don daman a takure take, duk idan Faruk ya na wuri ita dai bata sakewa, ba ta san dalili ba, to ko don jinin su bai haɗu ba tun farko? Ta tambayi kanta, taɓe baki ta yi, ta cire zancen a ranta. Tana shiga ɗaki ta taras da wayarta tana ringing. Tana dubawa taga Daddy ne ke kira, da sauri ta yi picking call ɗin tare da yin sallama, bayan sun gaisa ya ce “ya jikinki mamana?” A kunyace ta ce “Alhamdulillah Daddy, Ina samun sauki sosai.” “Masha Allah. Ina fatan kina cin abinci?” “Eh daddy, ina ci. “Kin tabbata?” Ya fada cikin kulawa. “Eh daddy, yanzu ma na gama yin breakfast tare da su Ammi.” “That’s good mamana, magani fa?” “Shima yanzu nake shirin sha” “Good, ki sha magani da kyau please mamana. Ina son in ga kin samu lafiya.” 

“Insha Allah Daddy, yaushe za ka dawo? Munyi missing dinka.”
“Na kusa dawowa insha Allah.”
“Allah ya dawo da kai lafiya.”
“Amin mamana, ki kula da kan ki sosai.” “insha Allah daddy, bye.” Daga haka ta kashe wayar..


*Ina mai farin cikin sanar da ku muna siyar da kaya kala-kala masu kyau da* _quality direct from Egypt_ 🇪🇬  
Abaya, Jalbabs, Boubou, Scarfs, Jersey Hijabs, Jersey Veils, Comfy Gowns, Tie Back Caps, Crinkle Turban Caps, Nightwears_ and lots more.

Muna yin installment ga wanda ba shi da halin siya lokaci ɗaya.  
Masu son fara business suma muna maraba da su.

*For more info: +201508856397*  
WhatsApp only
+201508856397 My WhatsApp number_  
TikTok_ @amzaah  
Instagram_ @zainabuh Amzah
Snapchat_ @zainabuh Amzah
Wattpad @zainabuh Amzah
Arewa pen @zainab Amzah

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol