Free chapter · Read without an account

Chapter 7

by Hauwa Salihu · MATAR SALMAN

*đź’«MATAR SALMAN đź’«*



➡ *PART ONE*
*Page 7*


Zuwa yanzu kam na saba da rayuwar jami'a nima na kara wayewa da kuma gogewa domin gaskia Jami'a kam duk wanda ya samu ya shiga dole kawai ya waye.

Muna waya da Fa'iza da Sakina sosai suna fama da ABU dinsu suma, sai anyi hutu zasu dawo amma ni ko wani asabar in mun gama lectures gidan mama nake tafiya sai Monday nake sammako na dawo makaranta.

Akwai wani satin da Mama bata gari sun tafi umrah da maigidanta, Don haka gidan Kawu na koma.

 Ranar asabar da yamma mai adaidaita ya saukeni a kofar gidan na sauka na biya kudin sannan na shiga ciki a tsakar gidan na samesu gabadaya har kawu Inna ce da girki Mmn Sakina na wanki Zainab na shara Kawu ma na zaune a kan kujera.

Nayi sallama Kawu ne ya amsa cike da fara'a yace ”Maraba da ƴar jami'a.”

Murmushi nayi nace ”Yawwa Abbah.”

Maman sakina da Zainab suka min sannu da zuwa Inna kam sai cewa ta yi ”Sai yau kenan kika ga damar zuwa ki ganmu da yake uwarki bata gari ko.”

Murmushi nayi nace ”A'a Inna wannan karon dama ko Mama na gari ma nan nayi niyyar tahowa weekend.”

Tace ”Ba wani nan ke dai.....”

Kawu ya katseta da fadin ” Haba Shatu kya bata ruwa tasha tukunna dai ko?”

Mmn sakina tace ”Gaskiya kam. Zainab jeki palon Abbanku ki kawowa Rumaisa ruwa a fridge.”

Nace ”Na gode Mama amma banjin kishin ruwa yanzu.”

Anan na gaidasu, Kawu yana tambayata labarin makaranta mun jima muna tattaunawa dashi, sannan na wuce dakin Inna na canzo kaya na fito na karbawa mata aikin girkin.

Bayan sallar isha na tafi gidan Sadiya wacce rabona da gidanta tun aure. Gaskia banji dadin yanayin da na sami gidan Sadiya ba, gabadaya kamar ta yi shekara biyar alhalin ko haihuwar fari batayi ba, gida duk kazanta ga tarin kayan wanki ga wanke wanke a zube a waje, abinka da damina kuma ko ta ina a jijjike sai karni ke tashi ba karamin daurewa nayi ba na shiga palon da sallama.

Da kyar ta amsa min tana kwance duk ta yi baki ta rame.

Muna hada ido na shiga tafe hannu nace ”Sadiya lafiya?”

 Ta yamutsa fuska da kyar tace ”dama kece kike ta doka sallama kamar wata bakuwa?”

Tsabar haushinta ko zama na kasa yi nace ”Yo ba dole in ta doka sallama ba, ai na ma dauka kun kaura don gidan naku baiyi kama da gidan amare ba, wai Sadiya meye haka me zan gani?”

Dan tsaki ta yi tace ”Ba kya ganin halin da nake ciki ne wai?”
Ta fadi hakan yayinda ta jawo wani gwangawani ta bude ta zuba yawu, nace Wayyo a zuciyata. Kauda kai nayi da sauri ina toshe hancina.

Cikin jin haushi tace ”Ke Rumaisa banson iskanci fa, in rashin mutunci kika zo kiyi min na rokeki ki fita ki bar min gida.”

Girgiza kai nayi nace ”Sam bashi ya kawoni ba nazo na gaisheki ne dama.”

Tace ”To sai ki zauna ai kin wani tsaya min kerere akai kamar kina bina bashi.”

A kyamace nake ganin ko ina nace ”Ni bazan iya zama a gidan nan ba Sadiya, amma me zai hana tunda baki da lafiya Jafar ya samo miki yarinya wacce zata miki su shara kamin nan ki sami sauki, amma zama cikin kazanta haka babban matsalace Allah zaki iya samin damuwa da mijinki gaskia, ni bazan iya dogon bayani ba don gaskia karni ta isheni, zan daure na dawo gobe tare da Zainab inga abinda zamu iya yi miki a gidan.”

Ban saurari me zatace ba na juya ko sallama ban mata ba na fita kayana.

A get din fita na hadu da Jafar muka gaisa da fara'a yace ”Hajiya Rumaisa kece a gidan namu ashe, ya makaranta?”

Nima da murmushi nace ”Alhamdulillah muna fama.”

Yace ”to Allah ya taimaka.”
Nace ”amin nagode.”

Har zan wuce yace ”Bakiji ba Hajiya Rumaisa.”

Juyowa nayi nace ”Na'am.”

Ya danyi shiru sannan yace ”Wallahi akan matsalar yayarki Sadiya ne abubuwanta sun fara isata a gidan nan, kwanan nan duk inata tunanin ko gida ma zan turata kawai ta huta.”

Nace ”Subhanallah me ya faru haka Yaya Ja'afar?”

Yace ”Rumaisah wlh Sadiya tunda ta sami cikin nan ta koyi ɗan banzan lalaci da kazanta, bata kula da komi na gidan nan ko girki ma batayi wlh ni gabadaya na gaji da da abinda Sadiya keyi a gidan nan.”


Nace ”Ya Jafar kayi hakuri, kasan sabon ciki da laulayi sai a hankali, babu abinda baya sakawa, amma insha Allah in cikin yayi kwari zata koma kamar yanda kake so dinnan.”

Ya danyi shiru sannan yace ”Hmm lamarin Sadiya sai addua nafa dauko mata yarinya domin ta dinga kula da gida, amma sai ta dinga zargen wai son yarinyar nake, in tazo gidan wai sai in dinga shishshige mata ina yabonta kedai sai kinji maganganu kam.

Murmushi nayi nace ”Ya Jafar kasan Sadiya tana sonka sosai shiyasa take kishinka don Allah ka kara hakuri inshaa Allah komi zai wuce.”

Yace ”To shikenan Rumaisa tunda kin dai ki laifin 'yar uwar taki.”

Dariya nayi nace ”Ah'ah wallahi ba haka bane?

Yace ”Shikenan amma dai na aikeki, ki gayawa Inna tayiwa Sadiya fada ta dinga hakuri a rayuwa.”

Nace InshaaAllah kuwa zan isar da sakon ka.

Daga nan mukayi sallama na dawo gida, daki na wuce na dauko handout dina na fara karatu kenan naji karar wayata ina dubawa naga Ya Salman ne.

Sai na tsinci kaina da yin murmushi sannan na dauka, sallama nayi masa kamar kullum can ya amsa muryarsa kasa kasa Murmushi na kuma yi nace ”Yaya ina wuni?”

Yace ”Lafiya lou.”

Nace ”Ya aiki?”

Kamar bazaiyi magana ba yace ”Kin cika dogon gaisuwa...... zanzo Kano gobe insha Allah Inna tace min kinzo, so nake kije gidanmu ki share man dakinmu don Salim ma zaizo.”

Nace ”To Yaya Allah kawoku lafiya.”

Yace ”Ameen nagode.”

Daga nan kashewa yayi har lokacin fuskata daukeda murmushi. ”Gaskia na gama yarda nikam tuni zuciyata ta fara dawainiya da son Ya Salman, da dai nakan karyata zuciyata amma yanzu na yarda sonshi nake shiyasa a koda yaushe burina bai wuce inga na raba shi da Salima ba...... to Fa'iza fa? To ai baisan tanayi ba......ai ni dinma kuma bai san dani ba hhhh!”

Inna ce ta shigo ta katse min tunani na shirme, ta zauna a gefan gadon tace ”Ya kika sami Sadiyan?”

 Mikewa nayi na zauna sannan na kalli Inna duk da ina tsoron yadda zata karbi maganar amma hakan nan na dake na fada mata komai.

Aikuwa ranta ya bala'in baci tace ”Amma Sadiya anyi lalatacciyar yarinya mai taurin kan tsiya, a zamanin yanzun nan wani namiji ne zai yarda da wannan halin kazantar? So take taja mana abin faɗe a danginshi, shikuma ya kara aure ko ya shiga neme nemen mata daga karshe ya sakota ta dawo gida, wayyo ni Shatu ka haifi da baka haifi halinsa ba wallahi.


Nace ”Hmm kiyi hakuri Inna, tunda kinga ai lalurace, dama so nake gobe muje da Zainab muyi mata shara da goge goge mu gyare ko'ina mu tattara kayan wanki mu ba ko almijiri ya wanke in yaso daga nan sai a sami wacce zata zauna da ita har Allah ya yaye mata.”


Dan tsaki Inna tayi tace ”Duk da nasan laulayin ciki ba abinda baya sakawa, amma ɗaurewa akeyi ana ɗan kama jiki mana...... Kince zakuje da Zainab gobe to gashi Salman yace suma zaki share musu dakinsu kuma zai turo cefane ayi musu girki, inaga bikin wani abokinsune zasu zo, don haka kawai ke ki zauna ki masu aikin don ni bazan iya girke girkenku na zamani ba.”

Nace ”To Inna Sadiyan fa.....”

Ta katseni da fadin ”Barni da ƴar banza zanje da kaina in ci ubanta tunda batada hankali so take ta tona mana asiri ina zaune asirina a rufe, zamuje da Zainab din.”

Ta mike ta fita nikam tabe baki nayi naci gaba da karatuna har bacci ya kwasheni da haka.

Washegari naso na makara da kyar na tashi nayi sallar asuba daga nan ban koma bacci ba,na karbi makullin gidan su na tafi sharewa. Ban tsaya bata lokaci ba na share tsaf nayi moping na wanke toilet na canza bedsheets da yake kowanne da dakinsa Palo a tsakiya da toilet, na fesa roomfreshner ta ko ina na rufe sannan na dawo gida.

Ina kwance ya salman ya kira na dauka na gaisheshi kamar kullum ya amsa sannan yace ”Kin mana sharan ko?”

Nace ”Eh har na gama Yaya.”
Yace ”Good, na tura Sadiq kasuwa zai kawo miki cefane ki mana girki pls ni tuwon semo nake so da miyar kubewa sai kunun gyada irin wanda Inna ke min,
Salim yace fried rice da pepper chicken sai Orange juice za'a musu inaga da salad, kin iya ko dai sai an nuna maki?”

Murmushi nayi nace ”Babu damuwa Yaya Allah ya kawo Ku lfy.”

Yace ”ameen.” Daga nan ya kashe.

Azahar na gama komai har na kai musu can gidan nasuma, na dawo sai lokacin su Inna suka dawo daga gidan Sadiya ta cire hijabinta ta kalleni tace ”Allah sa dai kin gama don yunwa nakeji ko ruwa bansha ba tunda mukaje dama azumi na dauka ma.”

Nace ”To Inna me yasa?”

Ta harareni tace ”A gidan Sadiyan kike so naje na bude ciki naci abinci Rumaisa? Zuwa gidan ma kamawa tayi ai.”

Dariya ne yaso ya kubuce min na kanne na je palon Abba na dauko mata ruwa mai sanyi sannan na dauko mana kulan abinci da plets. Tace ”wai ina Rabi ne?”

Nace ”Ta shiga wanka.”
Tace ”To gaskia bazan jirata ba in tazo taci tare daku.”

Nace ”Sai dai Zainab don gaskia ni sai nayi wanka ji nake ko ina jikina karni da warin hayaki.” Bata ce komi ba taci gaba da diban abincinta.

Bayan nayi wanka zama nayi na bata lokaci wurin tsara kwalliya na jan hankali dogon riga na saka na atamfa green Wanda yasha stone work na dage na daura dankwali gashina yasha parking har gadon baya da rivoms, na dauko akwatin sarkana don in zaba sai naji sallamar ya Salim anan naji su Inna na musu sannu da hanya nayi maza na gama sakawa har zan fita kiran Fa'iza ya shigo wayata kamar bazan dauka ba na daure na daga nace ”Hello sis ya kk?”

Tace ”Lafiya qalau 'yar uwa don Allah Rumaisa ki kulan min da Sojana naji suna Kano dazu ya Salim ke shaida min wai zasuyi bikin abokinsu don Allah kar ki bari waccar banzar taje kusa dashi.”

Jikina ne yayi sanyi nace ”hmm Fa'iza kema kinsan ban isa in hana Salima zuwa kusa da Yaya Salman ba.”

Tace ”Oh my God! wallahi Rumaisa wannan karon muna samun Hutu Kano zanzo, shawararki kuma zanbi kawai in cire kunya in fadawa Ammie tunda ai muna hira sosai, Tunda shi har yanzu ko kallo ban ishe shi ba, baima san inayi ba, hmm Rumaisa wallahi son Yaya Salman na wahalar da zuciyata.”


 Gabadaya naji maganar ta gundureni na dai daure nace ”Eh hakan zaifi ai sis akan ki ta zama kina wahalar da kanki kullum ai gwara ayita ta kare ki fadawa Ammie kawai.”

Tace ”Shikenan sis hakan za'ayi kawai na gode da shawarwarinki gareni.”

Nace ”Babu komai sis, bari inzo I will call you back.” Ban saurareta ba na katse wayar. Dafe kai nayi nace wayyoni Rumaisa gaskia gara in koya wa zuciyata hakura da son Ya Salman da ta fara domin faiza ta fini sonsa,gefe guda kuma ga Salima...Ɗan tsaki nayi a dai dai lokacin da naji Inna na kwalan kira na tashi da sauri ina amsawa na fito tace ”ana ta kira ni na dauka bacci kike to yi maza ki kai musu makulli ke suke jira.”

Da sauri na koma daki na dauko keys da gyalena wanda ban ko yafashi da kyau ba don sauri, na fita tuni har sun shiga gidan suna jirana a bakin kofar paalon, su ukune tare da wani da ban sanshi ba. Tun daga nesa suke kallona nikam duk na tsargu na dai karaso kaina a sunkuye nace ”Barkanku da zuwa.”

Ya Salim ne da mutumin suka amsa, sai na rasa wa zan baiwa key din a cikinsu, kawai na wuce na bude musu kofar
Nace ”bismillah.”

Ya salim yace ”Yawwa mun gode Rumaisa.”

Murmushi nayi ina tsaye suka wuce ciki Ya Salman kamin ya shiga ya kalleni yayi kasa kasa da murya yace ”tafi kije ki sanyo hijabi sai yawo kike tsirara a cikin mutane kefa ƴar kauyece har yanzu.”

Haushi naji shikam tuni ya wuce ciki kayanshi, wai har yanzu bazai bar ce min Ć´ar kauye bane?

 Da sauri na bar gidan na dawo ai ko minti biyar banyi ba ya kira ni wai nazo na saka masu abincin. Haka na tashi na saka hijabi na sake komawa.

Na tarar tuni Ya Salim da abokin shi sun fara cin abinci shi kam Ya Salman yana wanka ma tukunna.

Anan na zauna na gaishesu Ya Salim yana zolayata yace ”Rumaisa kinga Ra'is sai santi yake ni na masa waigi.”

Sunkuyar da kai nayi ina murmushi kawai

Murmushi shima Ra'is yayi yace ”hakane girkin yayi dadi kwarai da gaske kanwata.”

Nima murmushi nayi nace ”nagode sosai.”

Ya Salim yace ”Rumaisa wannan shine abokinmu Ra'is ko kina jin sunansa gun Fa'iza shekararsa biyu a Malaysia sai cikin satin nan ya dawo.”

Nace Ayyah da fatan ka dawo lafiya.”

Yace ”Lafia lau Alhamdulillah kanwata ya naku karatun?”

Nace ”Alhamdulillah muna fama.”

Yace ”Allah ya taimaka.”

Nace ”amin.”

Anan Ya Salman ya fito sanye da 3 quarter da rigan shan iska. Ya zauna kan kujera yace ”Sai yanzu naji normal.”

 Ya Salim yace ”kai dai ka saba da sanyin Lagos in ba haka ba aini dai dai nakeji ba wani zafi.”

Ya Salman yace ”kai dama can ai bajin zafi kake ba.

Ya kalleni tace ”A min serving yanzu na gama.”

Nace "to” Nan na mishi serving tuwon semo miyar kubewa na cika masa kunu a cup na kawo masa ruwan wanke hannu.

 Nan suka shiga zolayarsa wai shi dan gargajiya ne. Baima kulasu ba ni dai ya hanani tafiya sai da ya gama na tattara na gyare wurin tsaf sannan ya barni na tafi duk na gaji.”

Da sassafe kuwa na tashi na shirya tafiya makaranta don muna da lectures karfe 7:00am. Lokacin da na fita na sameshi a waje shikadai sanyeda kayan motsa jiki.

Na ɗan rage tsawo ”Yaya ina kwana?”

Ya dago da alamun yanzu ya ganni yace ”Lafiya lou.”

Daga nan na wuce don ko na kara bazai amsa ba. Sai dai kamin na isa kan titi sai gashi nan da mota ya sauke glass yace min ”zagayo.” 

Ba musu na zagaya na bude na shiga sannan na rufe baice min komai ba yaja muka tafi har muka isa sannan yace min ”Yaushe zaku tashi?”

Na danyi shiru sannan nace ”Karfe biyar.”

Yace ”Ok,zanzo in daukeki mu koma gida.”

"To" kawai naçe masa.

Daga nan na sauka na tafi har na danyi nitsa na juya sai naga har lokacin bai tafi ba ko me yasa oho. Da yamma kuwa mun tashi banje hostel ba ina jiran shi nida Maryam ne muna cikin hira sai ka wata bakar mota ta yi parking a gabanmu kyan motar ya dauki hankalinmu sosai ni da Maryam.

Mun shagala da kallo har mai motar ya fito wani saurayi ne É—an gayu dogo kyakkyawa ya fito sanyeda 3 quarter da t shirt kansa kuwa ya tara gashi Wanda yasha gyara idonsa sanye da bakar glass.

Lokaci daya muka kalli juna da Maryam sannan muka kalleshi murmushi naga ya sakar min hade da daga gira yayinda ya cire glass ya karaso gabanmu.

Ban taba tunanin sallama a bakinsa sai kuwa naji ya mana cikakken sallama.

Maryam ce ta amsa nikam kauda kai nayi ina jinsu suna gaisawa sannan yace ”Kawar taki bata magana ne?”

Maryam tace " tanayi mana.”

Yace ”Ni fa wurinta nazo amma kuma sai naga tana shashshareni.”

Maryam tace ”To nidai bari na baku waje.” Ta fada yayinda ta mike na kalleta fuska ɗaure nace ”Don Allah kiyi zamanki ba inda zakije.” Tace ”ke dai bari na dan baku waje.”

Da sauri na mike nima nace ”To muje kawai.”

Shima yazo gabana da sauri yace ”haba baby bai kamata ki min haka ba wallahi saboda ke na shigo BUK a irin wannan lokacin pls ko bazakice komi ba ki dan bani lokaci da zamu hadu da kuma Phone number dinki.”

Maryam dai tuni ta yi gaba. Kallonshi nayi cikin jin haushi nace ”Malam ban sanka baka sanni ba bamu taba haduwa ba kawai in dau number ta in baka? To kaga nifa ba irin 'yan matan da kake tunani bane don haka ka hakuri.”

Murmushi ya yi yace ”Wallahi na sani ke dabance ce mai tarbiya da kamun kai shiyasa ma nazo gareki domin in isar miki da sakon zuciyata. Ni sunana *AHMAD* mahaifina Alhaji Umar shine Governor na Kano state a yanzu....pls ki daure.....

Na katseshi da fadin ”Don Allah malam naji kuma na gode amma ni bazan fada maka wacece ni ba.”

Ya saki murmushi yace yana buda hannayensa yace ”Nop ba sai kin fada ba na sanima, sunanki RUMAISA IBRAHIM AHMAD.


Kallonshi nayi da mamaki ya daga min gira yana murmushi, nayi sauri na kauda kai kamin nace wani abu wayata ya soma ringing da sauri na ciro ta a jaka ina dubawa naga ya salman ne sai da zuciyata ta tsinke, a tsorace na dauka kamin nayi magana yace ”gani nan ina jiranki.”

Ya kashe ina juyawa gefe naga motarsa can yana tsaye ma a waje ya harde hannayensa a kan kirji yana hangomu innalillahi.”

Ai da sauri na wuce na bar wannan sarkin nacin a gurin babu shiri. Ya salman hade fuska ya yi sosai idonsa har ya sauya yana kallona rai bace yace ”Shi waye wancan dan iskan da kike tsaye dashi?”

Aikuwa hanjin cikina har rawa suke don tsoro nace ”nima yau na ganshi ......”

Ya katseni da tsawa ”Ke karki raina min wayo mana, zaki fada min gaskia ko sai naje na sameshi naci ubanshi tukunna?”

Jikina har rawa yake nace "wlh wlh wlh yaya yau na fara ganinshi nima.”

Ya kuma daka min tsawa ”shiga mota mu tafi.” Da sauri na zagaya na shiga tuni hawaye ya fara bin kumatuna don bana son tsawa a rayuwata.

Yana tsaye har Ahmad yazo ya wuce da motarsa sannan ya shigo mota ya kalleni kamar zai rufeni da duka yace ”bari na miki first and last warning, daga yau idan na kara ganinki da wannan dan iskan kai ko labari aka bani wlh na lahira sai yafi ki jin dadi kinaji na ai?”

Na daga masa kai a tsorace don naga har wani huci yake, ya tashi motar rai a bace ya fizgeta da gudu nikam da sauri naja belt na daura, ina addu'ar Allah kaimu gida lafiya.”

Kamin mu isa gida ya zagi mutane sunfi goma a hanya alhali kuwa shi yake tukin ganganci kana ganin fuskarsa kasan yanaji da bala'i don ma anci sa'a ba wanda ya tanka masa da sunsha mari ma, don ya sauka ya mari mutum ba matsalarshi bane a wannan lokacin, nace a zuciyata ko alluransa ne suka motsa.”

Allah dai ya kawo mu gida lafiya, da sauri na fita ina hamdala a raina na wuce cikin gida bakina alaikum, anan na sami Inna da Mmn Sakina suna ma Sadiya fada, ita kam saidsi kuka take har zan tambaya me ya faru sai ga Ya Salman ya shigo fuskar na a murtuke don haka shiru nayi sum sum na wuce daki kamar munafuka.

Ya na ganin Sadiya haka yace ”ke kuma me aka miki kike kuka?”

Inna ce ta karba ”me za'a mata kuwa? Dadine kawai ya isheta wai Jafar yace bazai dauko mata mai aiki ba sai ma ya turo kanwarsa tazo ta zauna da ita, don haka ba zata iya zama da yarinyar ba ta dawo gida.”

"Ta dawo?” Ya fada cike da mamaki yana kallon Sadiya yace ”ke tashi ki tafi.”

Ta kara fashewa da kuka tace ”Yaya wlh son yarinyar yake cin amanata suke ni bazan zauna da jafar ba, zama dashi ya isheni, ɗan iskane.....

Ya katseta da fadin ”Rufe min baki malama dama bakisan dan iska bane kika aura ko hauka zaki manna mana? To tun muna shiri da juna ki tashi ki bar gidan nan.”

Ta kara tirbinewa tace ”Ni wlh ba inda zan je sai dai in ta bar gidan.”

Yace " OK taurin kai zaki min da rashin kunya ko?”

Ya fara kunce belt a kugunsa ido na zaro nayi ciki da gudu kar ya hada dani.”

Sadiya ko kan ta ankare tuni ya fara sauke mata belt ko ta ina baya ko sararawa .
Ihu ta fasa tana wayyo Inna yaya zai kasheni wayyo Mama don Allah yaya kayi hakuri zan koma wallahi

Inna kam shiru ta yi tana kallonsu sai da Mmn Sakina ta tashi ta rike hannun Ya Salman tace ”Kai Salman lfyrka kk dukan matar mutum da ciki? Kai wa Allah ka barta zata koma ai.”

Ya kalli Sadiya a fusace yace ”zaki tashi ki tafi ko sai na kashe ki da duka?”

 Aikuwa da sauri ta mike takalminta a hannu ta yi waje,ya bita a baya da belt din hannunsa. Nikam sai godewa Allah nake da bai rufeni da duka dazu ba.

Na idar da sallar isha Inna tace nazo na dauki abincinsu kamar nace mata bazani ba don tsoro haka na daure don Zainab bata nan.

Na isa gidan har zan shiga Palo na jiyo muryarsa yana magana cikin fada kasancewar kofa a bude na danyi baya na ajiye abincin, a bakin kofa har na juya sai naji yace ”Look Salima in har sai na amince da alakar Ahmad da Rumaisa ne kamin a bani aurenki to sai dai a bari, don wlh bazan taba yarda Ahmad ya hurewa Rumaisa kunne ya lalata mata rayuwa ba.”

Na zaro ido yayinda na dafe kirji na.
Sai naji muryarta cikin tsigar lallashi ta na ”Don Allah Ya Salman ka bar Ya Ahmad yayi soyayya da Rumaisa ko na ɗan lokaci ne, InshaaAllah babu wani abu da zai faru. Kuma hakan shine zaisa Daddy na ya yarda muyi aure kaga fa tuntuni kake so a fara maganar aurenmu amma su Dad sunki saboda Ya Ahmad to yanzu Allah ya karbi rokonmu ya Ahmad ya daina kulani yanzu ya dawo Rumaisa yake so baka ganin wannan wata damace muka samu.....

Ya katseta da fadin " sai yanzu na fahimceki Salim, ashe ke muguwace? Nifa bari kiji ba don komai na jajirce da son aurenki ba sai don ina tausayinki, hadaki aure da Ahmad da za'ayi, don kinfi kowa sanin halinsa na shaye shaye da koyawa yaran mutane tantiranci, amma ke kina cewa wai na amince Ahmad ya batawa kanwata rayuwarta? Don kawai in aureki..... to bari na sake jaddada miki Salima idan akan Rumaisa ta yi soyayya da Ahmad ne gwara na rabu dake ɗin kije Allah haɗa kowa da rabon shi.”

Muryanta naji ta na kuka tace ”shikenan dama ba sona kake ba yaudarace kawai dama ashe tuntuni kana ta bata min lokaci, Nagode!”

Nima tuni na fara sheshshekar kuka daga inda nake,ban ma san ta fita ba, sai jin muryar Ya Salman nayi kusa dani yana ”Rumaisa me ya sameki?”

Na dago fuskata da ya jike da hawaye na kalleshi amma sai na kasa magana kawai durkusawa nayi gabanshi naci gaba da kuka.




 *RUMAISA SALMAN BY MAMAN KAUTHAR*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol