Free chapter · Read without an account

Page 26

by khadijah danasabe · TASWIRAR KADDARA

*TASWIRAR KADDARA*



  DijahAM(Oum Amani)




Page 26




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM





  

  Sunkuyar da kai kawai Azlan yai ya kasa dago kansa ya kalli, kowa.



Kallon sa Baffa yai yana son yai magana don shirun sa tabbas ya bashi tsoro, a yadda yasan Azlan tabbas bai tsammanin zai yi shiru ba.



Abie ma kansa shirun Azlan a ynxu ys ba shi tsoro a yadda yasan danshi ba irin sune ake ma dole ba akan abinda basu da ra'ayi ba amma gashi an bashi mata biyu a rana daya kuma dukkan su ba ra'ayin sa ba har ansa rana amma baiyi magana ba.



Ajiyar zuciya Baffa ya sauke yace "zaki baka ce komai ba"



Sai da yadan dau seconds sannan ya dago idonsa da suka yi wani irin jaa sbd bacin rai, murmushin gefen baki yai yace "mai zance tsoho kun gama yanke hukunci Allah ya kaimu"



Mikewa yai kawai ya fita daga gidan gaba daya...



Shiru palourn yai kafin Baffa ya sallami kowa, bayan ya fadawa Abie ya Kira Abba ya fada masa su san nan da 7 months tym din Aisha ta gama secondary.







**********

Wani irin ihu Zeey tai ta fada jikin Mummy tace "Mummy ynxu dai nan da 7 months zan zama matar Ya Azlan?"



Murmushi Mummy tai tace "ln shaa Allah kuwa, matsalar kawai auren da Baffa yace zai masa da waccen shegiar duk da naji baban yarinyar ya Kira yana ma baffa wata magana amma banji ba Allah yasa ma suce baza su bashi auren ba"



Zama zeey tai tace "Mummy ai ni wannan auren da za'a masa sam baya gabana, nasan kowa za'a aura masa baxa ta kama kafata a komai ba don haka kar ma ki damu, kuma ina shiga ciki zamu San yadda zamuyi mu fita da ita."



Murmushi Mummy tai ta shafa kan Zeey tace "dama ai ke nake ji kar ki tada hankalin ki Amma tunda kin kwantar da hankalin ki ynxu kawai zamu shiga gyara kine yadda in ya shiga gonar ki sai ya raina kansa".



Wani juya ido zeey tai tace "yauwa Mummy na shiyasa nake sonki sosai".



Dariya sukai suna tafawa









*********

Tunda abin ya faru gaba daya na Zama wata suku suku bama dana ji Umma tana gayawa Aunty Bilkisu data zo cewa ansa ranar biki wata 7, ga Aisha ynxu ta koyi wasu kalar hauka bata da aiki sai karatun littafan Hausa, da na mata magana sai cemin tai wai zaman aure take koya da yadda zata Kula da Mijin ta.



Yau sati daya da faruwar abin knn muna zaune a tsakar gida nida Aisha sai Umma, Mimi na daga kofar kitchen tana gera kayan wasan ta wai girki take yi.



Hira muke wanda yawanci Umma ke mana nasiha da yadda ake rike Miji da kuma Kula da jiki da tsafta.



Janyo wayar ta tai tace "bara na Kira Bilkisu ma na tuna mata kar ta manta ta kawo min maganin sanyin nan a fara baku, don ynxu sanyi duk ya wa mutane yawa”



Nidai banyi magana ba sai Aisha ce take kallona tana wani murmushi, harara na maka Mata ina jan tsaki.



Shigowa kamal yai dauke da sallama, Zama yai akan tabarmar sannan ya kalli Mimi yace "Mimi Daddyn ki yazo yana waje"



Da gudu Mimi ta taho gun kamal dafa gwiwowin sa tai tace "da gaske Daddy na yazo Ya kamal"



Dariya Kamal yai yace "yana waje ma"



Da gudu ta kwasa tayi waje, ni kuwa da tunda kamal yace Mr Wicked yazo naji wani irin bugawa da kirji na yai sai kawai na saukar da kaina kasa ina duba wayata duk da kuwa ba abinda nake gane wa.



Kallon Aisha kamal yai yace “Ya Aisha kije wai yana jiranki”



Da sauri na dago na kalli Aisha don Jin wani amsa zata bawa Kamal, sai dai ga mamaki na sai Naga ta kalli Umma, daga mata kai Umma tai hakan yasa ta mike da sauri ta shige daki, minti kadan ta fito sanye da hijab ta dan fesa turare ta gyara fuskar ta.



Raka ta nai da kallo har ta fice, juyawa nai naga Umma ta zuba min ido tana kallo na, juyar da kaina nai amma ji nake kamar na dora hannu a Ka na fashe da kuka.



Bata dade ba ta dawo fuskar ta a washe sosai, kallon Umma tai tana sosa kai tace "Umma yace wai in tambaye ki in kin yarda zamu rakasa super market nida su khalil da Mimi".



Murmushi Umma tai tace "Allah ya kiyaye in har da su Khalil ne ai baxan hana ba, ko ba komai yayi spending tym da Mimi."



Tsalle Aisha tai cike da murna tace "mun gode Umma bye," kallona tai tace "sai mun dawo Ya Batul."



Da harara na bita har ta fice daga gidan, juyowa nai na kalli Umma nace "ynxu Umma kika barsu suka fita tare da Mr Wicked bashi da hali mai kyau fa Umma kina kallo dai shine mahaifin Mimi"



Kure ni da ido Umma tai kafin tace "Batul ki shiga hankalin ki akan aibata wannan mutumin, ke ynxu in Mimi taji ki zata ji dadi ki sani duk lalacewar Uba, uba ne kuma kar na Kara ji kin fadi wata kalma mara dadi ko ba komai shine zai auri kanwar ki, yau da gobe kuma wataran zata ji haushin yadda kike masa."



Kwalla ce naji tana kokarin zubo min kawai na juyar da kaina ina wasa da wayata.



Ban san mai yasa ba amma tunda suka fita hankali na ya kasa kwanciya bini bini na kalli kofa ko na duba ogoga na.



Sai gab da magriba suka shigo hannun su dauke da manyan ledoji, sai walwala suke.



Nuna wa Umma sukai kayan kwadayi ne ya siyo musu sai kayan wasa dasu teddy daya siyo ma Mimi.



Ledar dake hannun Aisha ta mikawa Umma tace "Umma kinga mai ya siyo min" ta fada fuskar ta dauke da murmushi.



Karba umma tai ta bude iPhone ce mai kyau golden colour, kallon ta Umma tai tace "ke kika ce ya siya Miki"



Da sauri ta daga hannun ta tace "ba ruwana Umma cemin yai ina da waya nace a'a shine yace amarya kamar ni banda waya ni banma san ya siyo ba sai da muka dawo ya ban yace har SIM ya samin"



Ajiye ledojin Umma tai tace "angode sosai ku ajiye a Palour sai Abba yadawo a nuna masa"



Nidai ko uffan ban ce ba, koda Abba ya dawo aka nuna masa godia yai yace ma Aisha ta Kula da yadda zatai amfani da wayar.



Tunda ga lokacin kullum Aisha tana manne da wayar ta bata da aiki sai chatting da waya, sai kuma zance don ba'a sati ba tare da tai zance ba wataran da Mimi take fita wata ran kuma ita kadai.



Nidai nawa ido amma Allah ya sani ba karamin azabtuwa nake ba, bama in tana waya tana kashe murya ji nake kamar na karbi wayar na rotsa a kasa, nidai bansan mai yasa nake haka ba amma na barshi a matsayin kawai don bana son Mr Wicked ne kuma na tsane sa sbd abinda yai ma Khadija.



Aunty Bilkisu har gida tazo ta kawo mana magungunan sanyi, sosai Umma ta dage akan Kula da yadda muke amfani dashi, don ta hana mu tsarki ma da ruwan sanyi sai na dumi, kuma ta hana mu Shan abu mai sanyi.



Alhamdulillah kam maganin sanyin yana da kyau sosai don muna ganin amfanin sa, ganin kyaun sa yasa Umma itama ta fara sha don tace itama bata tsufa ba in dai gyara ne.



Cikin haka muka koma makaranta, result dinmu yai kyau sosai komawa ta makaranta shi yake dan rage min wani radadin, don tsaf na fita harkar Mr Wicked ko class dinmu ya shigo bana yarda mu hada ido, kuma abinda na Kula shima ya watsar da ni ba abinda ya shafe sa, in yazo abinda ya kawo Shi yake yi ya fita.



Sosai na maida hankali akan karatu na bana wasa, nida Asma'u mun Kara zama kawaye sosai har auren mu na fada mata date din amma ban ce mata Mr Wicked Aisha zata aura ba.



Itama ta dage sai fada min tips din rike miji take yi, sai dai kawai na zuba mata ido ina kallon ta don a ganina Mai zan dauka tunda har ga Allah nidai ba son Yusuf nake ba, ni ynxu ma sai muyi sati bamuyi magana ba dama dama a WhatsApp yana dan mun magana sama sama.



Kwanci tashi gamu yau mun gama exam din second semester Wanda yai saura wata daya bikin, Aisha ma tun wancan watan ta gama WAEC.



A gajiye na isa gida, a Palour na tarar da Aunty Bilkisu da Umma suna magana gyaran jikin da za’a fara mana gaishe su nai na shige daki.



Kallon Umma Aunty Bilkisu tai tace "munyi magana da ita tace sbd nice a gida zata musu na sati biyu, ga kayan da'a dai na karbo musu masu inganci wadanda za'a basu su tafi dashi gidan mijin."



Ajiye ledar kayan da'ar Umma tai tace "baxa a basu wani ynxu ba knn"



Murmushi Aunty Bilkisu tai tace "yaya Sadiyya nidai ba ruwana wallahi haka kurin a dura ma Yara magunguna mata azo miji ya musu fata fata, tsumin tsassaken baure kawai xamu basu sai zumar mata sun isa gaskia, sai a musu kaza da Hadin kankana in satin bikin ya kama."



Dariya Umma tai tace "hakan yayi, Allah ya nuna mana lafia, munyi magana da Abba ma akan kayan kitchen, nima nawa Mama magana ina so na siyar da gona ta a hada kudin ayi komai tunda daga kansu na gama kuma, sai na mike kafa na cigaba da kula da mazan"

“In Abba ya ba da kudin sai ki fada min Yaya Sadiya, muyi wa LittleNest by Kd magana. Tana siyar da kayan kitchen tun daga kan tukwane, flask, plates da bowls komai dai da kika sani kuma kayan ta da arha sosai” Aunty Bilkisu ta fada.

Da sauri Umma ta ce “kin san da ita amma baki taba fada min ba, ai kawai ki mata magana tun yanzu ta turo miki abubuwan da take da su a kasa”

Dariya Aunty Bilkisu tai ta ce “In sha Allah. A kano take fa kuma tana aika wa ko ina” (GA WANDA YAKE BUKATAR KAYAN KITCHEN YA TUNTUNI WANNAN NUMBERN ***)

Sun dade suna tattauna wa kafin Aunty Bilkisu ta shigo dakinmu ta samu a gaba tana fada mana sirrin rike Miji, nidai kaina na kasa sbd kunya don Aunty Bilkisu bata rufe komai, fada mana take.



Wani Abu da Aunty Bilkisu ta fada sai da Aisha ta fashe da dariya, girgiza kai kawai nai ina murmushi duk da bana cikin dadin rai.



Kusan rana daya aka kawo mana lefe nida Aisha, ni akwatuna 12 Aisha 10 kayane masu kyau a ciki da tsada.



Su Uwani da suka zo ganin lefen kamar zasu yi hauka sai sakin magana suke akan aikin banxa abinda ma mazinaci wata zata aura, ba Wanda ya kula Su haka sukai suka tafi.



Ni Kam tun ynxu na fara missing gida da kuma cilla don nasan rabuwa dasu ba abu bane mai wuya.



Sosai hidima ake kusan kullum Aunty Bilkisu sai tazo sai yawon kasuwa muke.




Sati biyu kafin bikin muka fara zuwa gidan Aunty baby gyaran jiki, kwana uku da fara zuwa mu kadai munyi wani irin fresh ba karamin gyara mu take ba har gashin mu turara sa ake, cikin sati daya gaba daya mun chanja duk inda muka gifta sai mun bar kamshin jikin mu Mai sanyi da dadi, gashin mu kanshi kamshi yake.



Duk yadda nake cikin bacin rai da auren nan bama yadda Yusuf baya zuwa zance kuma ynxu bama waya kwata kwata, amma wannan gyaran jikin da aka fara mana ba karamin faranta min rai yai ba, kullum cikin taba jikina nake, munyi fresh sosai Aisha ma tayi kyau sai shakiyanci take wai saura sati daya akai ta gidan miji taji mai ake ji.







**********

Bangaren Zeey ma sosai take Shan gyara gurin Mummy da Mama sai banka mata magungunan mata suke ko maganin sanyi na sati daya suka bata aka shiga banka Mata magungunan mata, gashi ta siyo supplement na Kara kiba sbd ta cicciko amma sam taki cikowar sai ramewa take.



Tunda kuma aka sa ranar bikin ko ta Kira Azlan baya daukar wayar ta duk da haka bata daddara ba kullum cikin tura masa messages take na soyayya.



A ynxu damuwar ta events din da suka hada wajen biyar don tun satin bikin zasu fara amma sam sun rasa ta yadda zasu fadawa Azlan..



A haka biki yazo aka shiga hidimaaaa amarya ba gyaran jiki sai magungunan mata kawai ake sha...





********



Kansa na kasa yana sauraran Abie, dagowa yai yace "duk yadda kake so kayi kawai Abie"



Shiru Abie yai yana kallon Azlan, shi ynxu Shirun yaron ya fara damunsa gaskia, kwata kwata baya magana komai aka ce masa cewa yake duk abinda aka ga ya dace ayi.



Ajiyar zuciya Abie yai ya kalli Mami da itama ta zuba masa ido yace "kina jin danki ko ya bude baki ya fada min wani irin gida yake son zama tunda Mata biyu zai aura amma yayi shiru"



Dan murmushi Mami tai ta kalli Azlan tace "kayi magana mana Azlan a wani irin gida kake son zama"



Shiru yai yana kallon carpet din kokari yake ya hana kansa murmushi don shi yadda ake lallabasa ynxu abin burgesa yake shiyasa yake shiru shiru kamar salihi.



A hankali ya dago ya kalli Abie yace "Abie duk Wanda Ka bani ina godia Allah ya saka da alkhairi"



Gyada kai Abie yai yace “shiknn akwai gidana a sultan road gobe in Allah ya kaimu zan bawa Malam habu driver mukullan part din ya kai gidan amaren naka, part uku ne na tsakiya naka ne na gefe da gefen kuma kowa ya dau daya.



Murmushi yai yace an gode daga haka ya mike ya fita daga part din zuwa nasa, yana shiga ya fada gado yace a daura auren ni kuma lokacin Zan koma asalin Azlan dina wani murmushi yai yana shafa gemun sa..







***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol