Free chapter · Read without an account
Page 27
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 27
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Yau ta kasance Wednesday kuma gobe zamu fara bikin, ranar Thursday za'a yi kamu ranar friday kuma daurin aure da yini.
Gaba daya na kara figewa sai ido da suka fito tubarkalla, Mimi kuwa sai murna take ana bikin Maa dinta ta tana ta shiga tana fita, itama duk kayan da zata sa a bikin Mami ce ta kawo mata.
Muna zaune a shagon Aunty Baby, ana aka wanke mana kai aka zuba mana lafiyayyan kitso, ga lalle ja da baki bayan an wanke kafar.
Sai bin hannu na nake da kallo nayi kyau sosai lallen yayi kyau ya zanu kamar dora shi akai, murmushi nai ina kallon Aisha dake waya sai zuba shagwaba take.
Juyar da kaina nai cike da tausayin ta sai murna take bata San ko waye shiba, sai la'asar muka koma gida a kofar gida Naga cilla tsayawa nai nace ma Aisha ta shige.
Cikin sanyin jiki cilla yace "uwar dakina ynxu jibi zaki tafi ki barmu"
Juya kaina gefe nai Jin idona yana kawo kwalla, daure wa nai nace "ai zamu dinga haduwa a makaranta, kuma kai baxa Ka dinga zuwa gidan nawa ba"
Zaro ido yai yace "rufa min asiri uwar dakina, haka kurin naje gidan ki ango ya karya ni"
Harara na maka masa nace "waya isa ya karya aminin Batul"
Sai muka sa dariya a tare, mun dade muna hira sai da Umma ta aiko kirana sannan nai masa sallama muka shiga gida.
Gidan mu ya cika da Yan uwan Umma, dama yan uwan Abba na nesa a babban gida aka sauke su, sai bayan Isha'i Aunty Bilkisu da wadanda suka je mana jere suka dawo sai yaba gidajen suke.
Washe gari aka tashi da hidimar kamu wajen la'asar aka tafi hall din da aka kama, dama iya Mata ne.
Munyi kyau sosai nida Aisha mun sha lace dinmu maroon colour, an mana makeup mun yi kyau har mun gaji don sosai Abba ya sakar ma Umma kudi don shima yace mune matan da zai fara aurar wa kuma na karshe.
An sha hidima sosai a gurin event din sai bayan Isha'i aka tashi, nidai jikina duk yayi sanyi ga faduwar da gabana yake in na tuna cewa gobe an daura min aure da Yusuf.
Muna komawa gida wanka na shiga nai, na wanke fuskata sosai jikina sai kamshi yake yana sulbi, murmushi nai bayan na shiga daki a can karshen katifa na kwanta kawai sai na fara tunanin Khadija da yadda muke cewa tare za'a mana aure, kuka na fashe dashi don mutuwar ta sabuwa ta dawo min yau dinnan.
Ganin kukan baxai min amfanin komai ba na mike na fita zuwa tsakar gida, har lokacin da akwai masu hada hada gurin yanke yanken kabewar da za'a yi amfani da ita gobe, wuce su nai zuwa toilet alwala nai na koma daki.
Na dade ina sallah ina addu'a akan Allah ya min jagora akan sabuwar rayuwar da zan fara, sannan na nema wa yar uwa ta rahamar Allah da gafarar sa akan sallayar bacci ya dauke ni...
Washe gari tunda na tashi gabana yake faduwa, muna gama karyawa muka tafi shagon Aunty baby don makeup din daurin aure data yini za muyi baxa mu chanja kayaba sai za'a kai kowa dakin mijinta.
Karfe 12 aka gama mana muka koma gida, kowa sai tsokanar mu yake nidai nawa murmushi ina tare da Asma'u data zo duk da girman cikin ta don haihu yau ko gobe.
Ina zaune a dakin su Kamal sai duba agogona nake gabana yana wani irin bugawa ganin karfe biyu tayi duk yadda akai ynxu an daura....
***********
Lumshe idonsa yai Jin sanarwar daurin auren sa, yana sanye da wata lafiyayyar shadda fara an mata dinki da zare light blue ya kafa hula light blue yayi kyau har ya gaji, Amma fuskar sa ba alamun farin ciki shifa ji yake an daddaure sa taya za'a aura masa Mata biyu rana daya lallai kuwa za'a sha fama.
Dafa sa Haidar yai yace "mutumina gaskia kai Mai sa'a ne irin wannan aure haka na gata, Mata biyu rana daya wo Kai mai budurci."
Yatsina fuska yai yana ture hular kansa yace "kai kar Ka dame ni fah bana son hayaniya, ji nake kamar kaina zai fashe".
Dariya Haidar ya tuntsire da ita yace "ni muje na taya ka parking angon mata biyu don Abie yace daga yau ya yaye Ka daga kwana a gidan sa."
Dan dagowa yai ya zuba wa Haidar ido yana kankance idonsa sai kuma ya gyada kai yana wani shegen murmushi yace "muje"
Kin tafiya Haidar yai yace "meye Naga kace muje nifa rashin gardamar Ka akan auren nan yana ban tsoro."
Tabe baki yai yace "so kake nayi gardama a ce nayi rashin kunya, badai sun aura min Mata biyu ba ai sun gama nasu ynxu kuma turn dina ne"
Baki sake Haidar yake binsa da ido har sai da yaga Azlan ya shige mota sannan yayi saurin daga kafa shima kar ya tafi ya barsa tunda yasan kadan daga cikin aikinsa.
**********
Muna zaune su Kamal suka dawo sai murna suke an daura auren, nan da gida ya cika da guda da murna.
Ni kam ji nake kamar na tsunduma ihu Allah ya sani bana son Yusuf Amma ya zanyi an riga da an daura.
Fitowa mukai aka shiga Kidan kwarya an kewaye mu nida Aisha, murmushi ne ya kubuce min ganin Mimi da Hidiya sai rawa suke sun kama kugun su sai juya wa suke.
wajen karfe 6 Aunty Bilkisu ta samu wanka shirya wa mukai cikin atampa iri daya nida Aisha aka rufa mana mayafi, tuni na soma kuka Aisha ma haka, feshe mu da turare Aunty Bilkisu tai aka kaimu gurin Umma dake zaune a Palour.
Nasiha tai mana sosai nida Aisha muka rungume ta muna kuka, tsaki Umma tai tana kokarin mai da kwallar idon ta tace "bana son sakarci Maza ku muke Allah ya shige muku gaba yai muku albarka"
Kara rungume ta nai ina kuka sosai, da kyar aka rabani da jikinta kasancewar motocin daukar amare sunzo dukkan su kuma an riga an fada musu sai Aisha ta rakani gidan hakan yasa da muka shiga aka nufi damu babban gida don acan su Abba suke dasu Kawu Nasiru.
Mama da Yakumbo ne suka shigar damu palourn Kawu Nasiru, sai da suka gaishe su sannan suka mana nasiha muma.
Miko min Kudi Kawu Nasiru yai yace "ga sadakin ki dubu dari an daura miki aure da baban Mimi, dama kuma dashi din za'a aura miki abinda yasa aka boye Miki kike ganin kamar shi zai auri Aisha sbd kin nuna kin amince wa da auren tin farko, bayan kuma mun san rabuwa da Mimi zai Miki wahala haka shima baban nata baxai yadda ki tafi da ita wani gidan ba a matsayin agola.
Aisha da kike ga tana waya da zance duk da Yusuf take shiyasa shi ya janye jikin sa daga gare ki, ita ynxu matar Yusuf ce Allah yai muku albarka gaba daya ya baku zaman lafia, sannan kuma bake kadai bace matar sa ku biyu aka aura masa yau"
Wani irin bugawa kirjina yai ni aka aurawa Mr Wicked, kuma wai mu biyu aka aura masa tabdijan....
"Ameen" mutanen palourn suka fada, Abba ma nasiha yai mana shima sannan yasa mana albarka, fito wa mukai a mota daya aka ajiye mu nida Aisha Yakumbo na gefena sai Mama a gaban sit.
Ni aka fara mikawa gidana sai santin gidan suke, basu dade ba suka fita gaba dayan su ko mutum daya ba'a bari ba, suna fita ana kawo Zeey, wannan ya tabbatar Kenan Batul ce uwargida..
Ina zaune akan gadon har akai sallar Isha'i, mikewa nai na shiga toilet nayi alwala akan carpet din tsakiyar dakin, ina zaune akai har bacci ya dauke ni ban sani ba...
**********
A bangaren Zeey kuwa ana kaita part dinta nan Yan uwanta suka fara caa akan delay din da sukai na kin kawo Zeey tunda rana gashi an fara kawo kishiyar ta kuma itace uwar gida.
Zeey Kam ko magana ta kasa sai kuka da take sbd bakin ciki, duk saurin da sukai ana idar da sallah aka taho kawo ta sai gashi amma wai sbd bakin ciki ynxu itace amarya kuma knn sai Azlan dinta ya fara kwana a dakin ta kafin ita.
Wannan abin yafi komai bakanta Mata rai, itama dai haka aka watse aka barta zaune tana jiran angon ta ya shigo ya ga kwalliyar da aka masa.
*********
Ban garen Azlan kuwa yana kwance a daki sai magana Haidar yake masa akan ya tashi ya shirya ya rakasa gidan sa amma yaki, sai da ya fadawa Mami ta shigo tai masa magana sannan ya mike ya shiga wanka.
Shiryawa yai cikin three quarter fari sai riga armless ash colour ta dame sa sosai yayi kyau, kwallin sa ya dakko ya rambada a idonsa sannan ya tura shi cikin alijun wandon Kar ya manta, a ransa yana fadin sai ya koma gurin da yake siyan kwallin wannan da aka kawo masa bashi da quality.
Turare ya fesa ta gyara sumar sa ya juya yana kallon Haidar daya zuba tagumi yana kallon sa, hade rai yai yace "muje don Allah bacci nake ji"
Tsaki Haidar yai yace "kaji shi kamar zai iya baccin bayan yana da tsala tsalan Mata har biyu"
Kankance idonsa yai yace "Haidar yaushe kaima ka iya vawulence wai, ya kake so Ka iskan tani kai baka san tsoron Mata nake ji ba."
Hararar sa Haidar yai yace "a tsoron matan Ka yi cikin Mimi ba"
Datse lip dinsa na kasa yai yana rike haba yace "ynxu shiknn kowa kallon mara budurci yake min koh"
Salati Abie dake bakin kofa yai yace "yaushe hankali zai shiga kanka wai Azlan baxa Ka daina irin wannan maganar ba"
Langwabe kai yai yace "Abie maganar gaskia ina kaunar budurci na wancan ma nasan garin kuruciya ne ya tafi Amma ynxu d akwai wani"
Juyar dakai Abie yai yace"bana son shakiyancin zoka wuce gidan Ka"
Marairaice wa yai kamar zaiyi kuka yace *Abie nifa tsoron Mata nake ji maganar gaskia bara na fada, haka kurin azo a lalata ma ni in dinga bin....."
Dakuwar da Abie yai masa yasa shi fashewa da dariya yana shafa kansa, murmushi kawai Abie yai ya juya yana girgiza kansa Yana ma Azlan fatan shirya da farko ya dauka ya shiryu da yaji ya daina maganar budurci Ashe lambo ya musu.
Part din Mami suka je itama ta dade tana masa addu'a sai shagwaba yake zuba mata, dakyar ta kora Shi suka fita.
A mota koda Haidar yace su tsaya a siya kazar amare, Azlan cewa yai ai ba mayu bane su da za'a siya musu kaza.
A kofar gidan yasa Haidar ya ajiye shi ya shige gidan, yana shiga yasa Mai gadi ya rufe gate din, bai tsaya ko ina ba ko kallon gidan bai tsaya ba direct part dinsa ya shige ya rufe kofar ba tare daya shiga part din amaren nasa ba.....
Ynxu aka fara wasan🏌️♀️
***