Free chapter · Read without an account
BABI NA HAMSIN DA ƊAYA
by Zainab · Zaren Rayuwar Mu
Zaren Rayuwar Mu
ZAID YAYI SATI biyu a Delta State kafin ya dawo. Bayan ya dawo komai na gidan ya koma akan shi. He'll make everywhere clean and he'll cook the food I can eat and he takes care of me. Shi yake kai ni wurin aiki ya ɗauko ni. A first trimester na na dena tara yawu a baki. Now I like olives koda yaushe ina dashi a fridge. Ina son shan kayan sanyi amma Zaid hanawa yake. Ni zafi nake ji shiyasa bana zama da kaya yanzu.
Na shiga second trimester na a tsakkiya. Har yanzu cikina be fito ba se de bosoms nawa da suka yi somewhat big. Duk lokacin da Zaid yana gari tare dashi muke zuwa awo. Journey na juna biyun nan nawa yana tare dani fully and wholly woke.
A wata na bakwai, na shiga third trimester nawa kenan juna biyun ya fara fitowa a cikina slightly ana ganin baby bump nawa. Bana so na shiga mutane a gida kawai nake so na zauna saboda bana jin daɗin jikina.
Idan na kwanta zuwa bacci bana jin daɗi na fara juye-juye kenan Zaid shi kuma baya bacci ze zauna a kusa dani yana kallo na duk ya damu.
Close to 8months of my pregnancy, koda muka je asibiti awo, jini na ya hau. Da muka shiga wurin Doctor take tambaya dalilin da yasa jinina yanzu ze hau. Kallon Zaid take tace “Me ya faru da ita Zaid?” shiru Zaid yayi yana kallona cikin tausayi.
“Dama kina da hawan jini ko dai na ciki kawai ne?”
Girgiza kai nayi “Bani da hawan jini”
“Baku dashi a family line?”
“My father, may God have mercy upon him, he had it”
Gyaɗa kai Doctorn tayi ta rubuta min maganin hawan jini muka wuce.
Da kuma sati ya zagayo lokacin awo na, jinin be sauka ba. Shiru Doctorn tayi tana kallona. A ranar suka ce zasu kula dani se idan ya sauko mu tafi gida.
Zaid yana nan tare dani har da dare tukunna muka dawo gida.
Cikina yana wata takwas, kaina naji kamar yana juya min. Zama nayi na dafa hannun kujera na sunkuyar da kaina ina jin dizziness. Waya ta dake gefe na na jawo na kira Zaid. Nan take yace min gashi nan ze taho.
Yayi waya da Yaya Hauwa tace mu wuce asibiti. A asibitin muka tafi muna zuwa naga Doctor aka mana bayanin all the possible things suka ce zasu yi inducing saboda hawan jinin. Gado aka bamu da tests muka je aka yi. Nayi wani ultrasound a duba position na baby. Aka nema jini in case of loss of blood.
Ina nan kwance a gadon asibitin su Mummy suka zo duba ni da Shahida da Muhammad da Zainab harda Khalil. Zainab da Shahida duk da abinci suka zo dashi.
Mun jima muna hira dasu tukuna Khalil da Muhammad suka fita. Nurse ta shigo ta fara duba bp na ya sauka kuma ya ƙara hawa. Allurar da aka ce za'a yi ta hawan jini ta fara haɗawa za'a min.
Ruwan allura na fara shiga a jikina naji kamar zan zauce na kwace hannuna daga wurin ta se hawaye. Mummy ce ta fara rarrashi na tana shafa kafaɗa ta “Yi haƙuri Hadiza” ta faɗa tana cigaba da shafa kafaɗa ta.
“Dama allurar tana da ciwo” Nurse ɗin ta faɗa tana kallona “Amma kinga ba za'a yi inducing naki haka da hawan jinin ba se ya sauko tukunna”
“Ki daure Hadiza. Da hawan jinin ya sauka zaki ga kin samu kin haihu in Sha Allah” Mummy ta faɗa.
Gyaɗa kai nayi hawaye na min zuba ji nake kaman na zauce na rasa hankalina.
“Zafi nake ji” na faɗa
“Zafi a ina?” Mummy tace tana kallona
“Yanayin gari”
“Yanayin gari?” Mummy tace tare da kallon ACn dake aiki a ɗakin da muke “Babu zafi Hadiza. Inaga jikin ki ne. A cire hular?” tace tare da cire hular dake kaina.
Hannuna Nurse ta jawo ta cigaba da min allura na rufe idanuna hawaye na fitowa ni kaɗai nasan irin zafin da nake ji. Bayan ta gama ne take ce min sorry. Shiru nayi ina sauke ajiyar zuciya babu abinda yake min daɗi a duniyar nan.
Su Mummy sun jima da dare suka wuce. Yaya Hauwa ce a tare dani da Shahida shima Zaid yana nan harda Khalil.
Dawowa akayi da daren ana duba bp na ko ya sauka. Ya sauka kaɗan ba irin na ɗazu ba. Allurar Nurse ɗin zata ƙara yi zaune kawai nake ina kallonta. Hannuna ta amsa da kanta ta fara min allura na riƙe kaina. Zaid na kallona ya taso daga inda yake ya dawo kusa dani. Sumar kaina dake sake a watse ya kama ya riƙe yana shafa gaban goshina ina jin muryar shi sama sama yana faɗin “Sorry” ko “Im sorry” ne yake cewa ban sani ba. Wannan karon har ta gama ban zubar da hawaye ba. Bayan ta gama ta cigaba da zama tana duba ko ya sauko sosai. Minti talatin da yin allurar tace wata zata ƙara yi.
“I don't understand” nace ina kallon ta tukuna na maida kallona ga Zaid “Kana gani fa. Wallahi ni na gaji. Allurar nan fa ciwo ne da ita na gaji fa”
“Ki yi haƙuri” Zaid ya faɗa
Yaya Hauwa ce ta zauna gefen gado a kusa dani “This has to be done. I'll be raw with you if the doctor wasn't. Idan akwai wannan preeclampsia an fi samun low chance of survival rate. Dan haka ki tsaya ki maida hankalin ki a miki abinda ya dace. Bada cikin ba wa ze kwantar dake anan ma?”
“Yaya tsoro kike bata da irin wannan maganganun. Kar jinin nata ya ƙara hawa” Shahida ta faɗa
“Baki ganin abinda take? Idan bata tsaya anyi abinda ya dace ba ya kenan?”
Ahankali na miƙa hannuna aka fara allura. Nurse ɗin tace wa Yaya Hauwa “Kina aikin asibiti ne?”
“No, why?” Yaya Hauwa tace
Shahida ta kalla Yaya Hauwa tayi murmushi, Khalil yace “She's a doctor”
“Nikam da nace” Nurse tace tana murmushi.
Waya ta ce ta fara ringing Yaya Hauwa ta bani. Ganin Umma na yasa na ɗauka.
“Har yanzu Hadiza?”
“Umma har yanzu”
“To ya maganar hawan jinin? Ya sauka?”
“Har yanzu be sauka ba amma suna kan min allura kuma ni na gaji allurar nan ciwo ne da ita”
“To ya za'a yi Hadiza? Haƙuri zaki yi jinin ya sauka. Ai se ya sauka tukuna za'a shiga labour room dake”
“Ni ban ga alamar yana da niyyar sauka ba”
“A'a ze sauka ki dai kwantar da hankalin ki. Allah ya sauke ki lafiya”
“Amin amin”
“Ko dai nazo?”
Yaya Hauwa na kalla ta girgiza min kai tace “Muna kulawa da ita Umma. Ba se kin zo ba in sha Allah zata sauka lafiya”
“To yayi mun gode da kulawa. Allah ya saka muku da alheri”
“Amin Umma. Tana haihuwa ni zan fara miki albishir”
Murmushi Umma tayi har ana ji tace “Mun gode sosai”
Sallama muka yi da Umma na ajiye waya ta.
Nurse na nan tana dubawa bayan minti goma sha biyar jinin ya fara sauka sosai.
Washegari aka fara bani maganin inducing. Komai ban fara ji ba har rana tayi aka ƙara bani wani nan ma shiru da dare aka ƙara bani wani. Da daren aka shiga dani labour room. Ina ciki ina jin yunwa aka kawo min tea. Komai bana ji maganin inducing din yayi failing aka ƙara bani wani the next day. A washegarin na fara jin wahala da ciwon da bana iya misaltawa. Yunwa nake ji amma bana iya cin abinci. Zuciya ta nake jin kamar wacce ta rufe na kira number Yaya Hauwa.
“Hadiza” ta kira sunana
“I'm so tired and hungry. I can't eat I don't have appetite”
“Ki yi haƙuri. Kin kusa haihuwa”
“Waya ce na kusa haihuwa?” nace cikin gajiya murya ta na yin ƙasa ƙasa
“cm nawa akace kike?”
“At 7 i think”
“At 10 ake haihuwa. You're close Hadiza just keep on praying. Allah ya sauke ki lafiya”
“Na gaji” nace se kuka
“Kinga matsalar ki ko? Yanzu kuka zaki yi saboda kin gaji? Ki yi haƙuri mafi yawa haka ake irin wannan abubuwan ki yi haƙuri”
Kuka na cigaba da yi ina sauraren Yaya Hauwa. Ganin kukan babu abinda ze ƙara min yasa nayi shiru nace “Okay, nagode”
“Yawwa ki cigaba da addu'a”
“In sha Allah. Kina nan asibitin?”
“Eh duka muna nan har su Shahida da Mummy”
Gyaɗa kai nayi tukuna na kashe wayar na aje.
Muna nan a haka ina wahala sosai ban haihu ba. Ina jin zafi a jikina wanda ban san inda yake fitowa ba har na dena. Ƙasa na koma na zauna da sauri Doctorn dake ciki ya dawo wurina “Hadiza menene haka? Dan Allah ki koma kan gado. Akwai infection fa kar ki yiwa kanki da baby illa. Tashi”
Da taimakon shi na koma kan gado hawaye na bin kuncina. Wata nurse tana kallona tana shafa min gefen kafaɗa tana cewa “Sorry Hadiza. You're getting out of this In Sha Allah”
“I'm never getting out of this. I'm tired”
Bata ƙara cewa wani abu ba ta cigaba da patting kafaɗa ta.
Ban san abinda doctor yasa min a private part ba amma ya sanya ni yin ihu se kuma nayi shiru ina jin kamar zan suma. Yana gama abinda yake nace “Ku kira min Zaid. Ina so na gan shi nan tare dani. Ku kira min Zaid. Ze faɗa muku ku min cs na gaji”
“Haba Hadiza! Ke da kike nan za'a yiwa cs? Za'a kira Zaid amma babu batun cs se idan ba zaki iya haihuwa ba” Doctor yace
“Ni nasan ba zan iya ba. Bani da ƙarfi a jikina na gaji mutuwa zanyi”
“Mutuwa kuma?” Doctorn ya faɗa ya dawo kusa dani sosai. “Me kike ji?”
“A jikina ne nake ji mutuwa zanyi ku kira Zaid. Zaid mijina”
“Bar zancen mutuwar nan bari a kira miki Zaid”