Free chapter · Read without an account

BABI NA HAMSIN DA SHIDA

by Zainab · Zaren Rayuwar Mu

Zaren Rayuwar Mu 

AN SA LOKACIN auren Ahmad da Laila. Abu na farko da na fara yi shine duba lokacin auren nasa ko zan samu na dawo Nigeria ayi auren shi dani. Dubawar da zan yi ne naga banda lokacin dawowa har ayi bikin Ahmad dani. Kiran shi nayi be ɗaga ba. Se bayan wasu mintuna ya maida kirana. Ɗaukar wayar nayi na ɗaura a kunnena. 
     “Hey” naji Ahmad ya faɗa cikin muryar bacci 
   “Bacci kake?” nace tare da duban agogon bangon ɗaki na. Tunawa nayi da lokacin mu ba ɗaya da Nigeria ba amma kuma babu wata tazara me tsawo a tsakaninmu.
  “Ban jima da kwantawa ba”
   “Na ɗauka ka fara shirye-shiryen biki”
Kwancen da Ahmad yake ya tashi tare da cire wayar shi a kunne ya ƙara duba kwanan wata da kuma watan da ake. “Na ɗauka gobe ne ɗaurin auren” Ahmad ya faɗa cikin wasa tare da ajiyar zuciya nasan he's not serious about what he just said
   “Se gobe ne ɗaurin aure tukuna zaka fara shirye-shirye?”
   “Baffa kar ka dame ni fa. Aure se wani wata kake cewa shirye-shirye”
Dariya Baffa yayi saboda haka yake son ji daga wurin Ahmad. 
    “You are supposed to be here anyways for the wedding”
    “That's why I called you”
   “Ba zaka samu damar zuwa ba?”
        “Yup”
   “I was thinking ƙarshen watan nan zaka dawo ma”
    “Dawowar ne da wahala. Ina da aiki sosai anan. Second year of my Master's”
   “Yeah, I understand. No problem really. Laila tell me say she no go do any event so I'm just grateful for that”
  “I thought you guys go do dinner?”
Girgiza kai Ahmad yayi “Idan muka ce dinner zamu yi, nawa zamu kashe? Kaya anan Abuja are expensive”
     “I know right”
  “Shine dalilin mu”
    “Ɗaurin aure kawai za'a yi kenan”
       “Eh”
     “Alright Allah ya kai mu lokaci”
     “Amin. Kaifa? Is there even anyone?”
    “Babu kowa”
Shiru Ahmad yayi se chan yace “Did you had anything with Temi?”
     “That was in the past”
  “Have you ever loved her?”
Shiru nayi ina tunanin abubuwan da nake ji lokacin da ina tare da Temi “I have loved her. It was in the past”
   “But do you still love her?”
“C'mon Ahmad. She got married last month”
“Wait? Did you attend the wedding? Heard from you she's living in the States”
       “Eh na tafi”
   “A States akayi auren?”
     “Nope, here in the Canterbury Cathedral”
    “Okay okay” Ahmad ya faɗa “You should give someone a chance Baffa. Or will you spend the rest of your life alone?”
Abubuwan da suka faru a gidanmu suke min yawo a cikin kai nace “Ina jin tsoron commitment. Ina jin tsoron zama da macen da zan ji wa ciwo a zuciya. Bana so na aure mace mu zauna kamar ba ma'aurata ba”
   “Me yasa kake irin wannan maganganun?”
“Observation ne”
  “Daga wurin wasu mutane? Me yasa ba zaka kalla cikin gidanmu ba? Our parents are happily married. Even after so many years of marriage, they're still happy in their marriage”
Kaɗan na buɗe idanuna ina sauraren Ahmad. Be san abinda ya faru a gidanmu ba. Nasan gidanmu ba ze taɓa dawowa irin yadda yake a daa ba saboda abinda mahaifin mu yayi. Ni kaɗai nake jin crack da yake a gidanmu. 
  “Kowane aure yana da nashi kalubale. Idan kace bad side na aure zaka duba, ba zaka taɓa yin auren ba. But you should never forget Baffa, it's difficult doing life alone”
       “I know right”
  “Se de idan wani abu ka sani wanda ban sani ba. And besides, I think the good sides of marriage really outweigh its bad sides”
     “Naji Ahmad”
   “Dan Allah ka duba ka nemo yarinyar da zaka aura. Ka kusa ka gama Master's naka. Da ka samu aiki me zaka jira kuma? Idan ka samu a UK ina ga zaka samu sauƙin rayuwa”
“Ka bani yardar ka na samu yarinya daga nan ko a ina?”
   “Akwai Nigerian girls a UK. Idan kuma wasu kake so from entirely different tribe and race, then go for it, for what you love”
 “Umma zata yarda na kawo wata wanda ba ƴar Nigeria ba?”
   “Kayi magana da ita ka ji. Yawwa kuma nasan yanzu kana da wata yarinya a ranka wacce ba ƴar Nigeria ba”
Dariya nayi jin abinda Ahmad yace “Tunanin ka kenan?”
    “Of course, yes, kuma da gaske ne”
Murmushi nayi ina tuna first encounter ta da wannan yarinyar daga Lebanon, Joumana. 
  “Yanzu haka tunanin ta kake yi”
Murmushi nayi nace “Wata ce daga Lebanon”
   “There, i know it”
     “Saurara ka ji”
   “Ina sauraren ka”
 “She is a beautiful woman with a very kind heart”
   “What made her kind?”
    “I told you she is”
  “Then what is it that made her kind?”
   “Kaii sharrap”
Dariya Ahmad yayi “Zata yarda ta aura ɗan Nigeria?“
      “Ba maganar aure muke da ita ba”
   “To me kuke yi? Are you friends? Friends with benefits or you are in a relationship with no future?”
  “Relationship with no future”
 “Ban yarda da kai ba Baffa. Be careful out there”
 “I'll be. Thanks man. Talk to you some other time”
  “Okay yeah, some other time”
Bayan na gama waya da Ahmad ne na kira Umma. Farkon kiran bata ɗauka ba se bayan na sake kira wayar bata jima tana ringing ba ta ɗauka. 
  “Shekaran jiya muka yi waya da kai amma har ka ƙara haske, Baffa” Umma tace tana kallo na ɗauke da murmushi akan fuskar ta
    “Umma weather garin nan ne fa. Ranar bata da kaifi irin namu kuma suna da sanyi”
   “Haka kace Baffa. Kun huta da zafi”
   “Akwai lokacin heatwave, zafin bashi da daɗi”
    “Ai duk zafin ku baku kai na Sokoto ba”
      “Umma ai kin jima rabon ki da Sokoto se de Farida”
   “Ah! Ai ban baka labari ba. Farida da ta zo hutu wai ba zata koma ba first Ramadan nata a Sokoto da ƙyar take iya kai azumi. Tace da ba dole bane ba, da ba zata yi ba”
    “They have terrible weather there, Umma”
    “To ya zasu yi? Sun saba ai”
Murmushi nayi nace “Umma ana sabawa da rashin jin dad'i ne?”
 “To se de kuma haka. Kaga an sa lokacin auren Yayan ka ko? Injin zaka samu tahowa?”
    “Yanzu muka gama waya dashi Umma. Gaskiya ba zan samu dawowa ba”
     “Karatun ne ko?”
     “Shine Umma”
   “To yayi Baffa, Allah ya bada sa'a da nasara. Kai yaushe zaka yi naka? Wai ma tsaya, kana da budurwa ma? Ban taɓa jin kayi maganar wata yarinya bayan girman ka ba”
   “Umma babu kowa fa har yanzu. Ina ta nema ne”
     “Nace ka bari na nemo maka kace a'a”
   “A'a, baki san spec nawa ba Umma”
Wani kallo Umma ta min na wasa tace “To faɗa min na nemo maka harda ƙari”
   “Kede Umma zan nemo” nace ina kuma nazarin faɗa mata akan ƴar Lebanon. “Yawwa da akwai wata yar Lebanon. Sunan ta Joumana. Anan tare muke karatun Law da ita amma ba maganar aure muke ba”
     “Mesa baku maganar aure? Kuma Baffa har Lebanon? Ai ba Africa bace ba ko?”
    “Eh, middle east”
   “To me yasa ba'a maganar aure? Ba zaka yi auren ne ba?”
Shiru nayi Umma tasa min idanun ta tana kallona kamar harda observing. Kawar da idanuna nayi daga kallon ta saboda bana so taga abinda ke damuna. 
   “Mun gama wannan maganar Baffa. Ko har yanzu ba'a gama ba? Mu ba gashi mun yi moving on a rayuwar mu ba? Kai shikenan zaka zauna akan abinda ba da kai ya faru ba? Bana son shashanci fa. Auren ka akace irin na iyayen ka ze zama? Ka buɗe idanun ka da kyau ka nemo wacce kake ganin zaku iya zama tare da juna ku fahimci juna komai ɗacin rayuwa kayi rayuwar ka da ita. We're not perfect, no one is perfect Baffa. Please let it go”
   “I don't want to subject any woman to the same situation my father put you through, Umma”
   “Biye biye kake yi to?” tace tana kallona
   “Nope, I would rather not”
  “Then find you a good woman and settle down. I don't want to have a son who'll remain a bachelor all his life. Marriage is good when you find a good woman, ok?”
Gyaɗa kai nayi nace “You are a good woman Umma”
      “Your father too, is a good man. I have forgiven him. Forgive him too Baffa, for me”
Ajiyar zuciya na sauke na jawo jacket ɗina akan ƙaramar kujera ta “Zamu yi magana anjima Umma. Zan ɗan fita zuwa nearby coffee shop nan”
  “Okay to se ka dawo”


~~~~~~~~~


I can't believe we're done already. Thank you for reading my book 💕💕💕. It's a pleasure doing this with you all. Thank you. 


What are your thoughts on this book? 
Any questions?

I'll send an epilogue. Wait for it, yeass

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol