Free chapter · Read without an account
Chapter 1
by Amanarcool · MUGUN KUDURI
Tashin hankalin da ya yi mata katutu ne ya sa ta kasa tsayuwa da ƙafafunta. A hankali ta durƙushe a ƙasa ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, iya karfinta ta fara magana "Wace irin bahaguwar rayuwa muke fuskanta a wannan duniyar ne? Shin ko mun aikata wa Allah wani zunubi ne ya zaɓi ya hukunta mu ta wannan hanyar? Shin mu kaɗai ne muke rayuwa cikin wannan baƙar ƙaddarar, ko kuwa akwai wasu kamar mu? Me muka yi wa Allah? Yaushe ne wannan ƙuncin da ya yi wa rayuwarmu dabaibayi zai ƙare? Umma, ki faɗa min idan akwai wani laifi da kuka aikata wa Allah ke da mahaifinmu mu nemi gafararsa wataƙila ma samu sassauci daga wannan baƙar ƙaddarar da ta mamaye rayuwarmu." Matashiyar budurwar ta ƙarasa maganar tana kallon matar da ke kwance a kan dandaryar ƙasa ba ta motsi, abin da ke nuna tana raye kawai shi ne hawayen da ke gangarowa daga cikin idanunta babu ƙaƙƙautawa. Cikin tsananin ɓacin rai da ruɗadin zuciya ta sake cewa, "Yaya ake so mu yi da rayuwarmu? Me ya sa mutane suka mayar da zulunci abin yi? Me ya sa taimakon ƴan uwa ya yi ƙaranci a wannan zamanin? Me ya sa aka daina daraja zumunci? Me ya sa komai sai kana da kuɗi ake yi da kai a wannan duniya? Me ya sa? Me ya sa Umma?" Ta ƙarasa maganarta tana jijjiga matar da ke kwance a ƙasa tamkar gawa, yayin da ita kuma ke gunji kuka. Ba zato ba tsammani, ta dakata da kukan nata sakamakon kukan ƙannenta da ya mamaye mata kunne. A hankali ta ɗaga kanta ta kalle su cikin wani yanayi mai cike da tausayi da raɗaɗi. Sannan cikin murya mai rauni da karkarwa, ta ci gaba da magana "Dole ne na fita neman kuɗi ko domin rayuwarku ta inganta ƴan'uwana. Dole zan nemi kuɗi ko ta wace hanya ce. Dole zan samo kuɗi domin na rama irin ƙunci da wulaƙancin da aka jefa mu a ciki saboda talauci." Ta ƙarasa maganar cikin rawar murya, dubanta ta mayar ga mahaifiyarta, cikin sanyin murya ta ce, "ki yafe min, Umma. Amma tabbas ko ta wace hanya ce, zan fita neman kuɗi, ko da hakan yana nufin na sadaukar da mutuncina."
.....
Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare. Garin ya yi tsit ba a jin komai, kowa ya kama gabansa domin samawa ruhinsa da gangar jikinsa natsuwa. Kwance take saman madaidaicin gado. Duk da kasancewar babu wadataccen haske a ɗakin, amma idanunta a buɗe suke tana kallon silin ɗakin cikin wani irin yanayi na damuwa, lumshe idanunta ta yi, a hankali ta sauke numfashi, tare da ɗora hannunta saman ƙirjinta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri, sake runtse idanunta ta yi da ƙarfi, ƙwaƙwalwarta ta shiga tunanin halin ƙuncin rayuwar da take ciki. Ƙarar faduwar abu ta ji a ƙasa, hakan ya sa ta buɗe idanunta a firgice.
Shiru ta yi ba tare da ta motsa ba, tana jin yadda bugun zuciyarta da ke neman fasa ƙirjinta ta fito ya tsananta. A hankali ta kunna wutar ɗakin, sannan ta mayar da dubanta ga ƙofar ɗakin da ke buɗe. Wani irin sanyi ne ta ji ya ratsa jikinta. Cikin natsuwa ta sakko daga kan gadon, mutum ta gani kwance a ƙasa. Ja da baya ta yi, cikin wani irin firgici take bin fuskarsa da kallo. Babu shiri ta durƙusa a gabansa, cikin tsananin tashin hankali ta fara girgiza shi tana faɗin. "Don Allah ka tashi! Ka buɗe idanunka ka kalle ni."
Sai dai ta ga ko alamar motsi bai yi ba.
Hannunta ta ɗora saman ƙirjinsa, nan ma ba ta ji alamar yana numfashi ba, wani irin kuka ne ya zo mata. Da sauri ta sa hannunta ta rufe bakinta saboda kukan da ke neman kufce mata, hawaye suka fara zarya saman fuskarta, idanunta ne suka sauka a kan hannunsa, wata ƙaramar takarda ta gani riƙe a hannun nasa. Cikin rawar jiki ta miƙa hannunta ta ɗauki takardar, buɗe ta ta yi, rubutu ne a ciki layi ɗaya.
Zaro ido ta yi waje, lokacin da ta gama karanta takardar. Ta ɗora hannu a kai za ta kurma ihu, sai kuma ta tuna da kashedin da aka yi mata, a take haɗiye kukan, wayarta ce ta fara kawo haske alamar shigowar kira. Ba don ganin mai kiran nata da babu abin da zai sa ta ko kalli wayar balle har ta ɗaga kiran. Cikin sanyin jiki ta kara wayar a kunnenta. Shiru ta yi tana sauraren na cikin wayar.
Muryarta na rawa ta ce "Amma ba ka da imani wallahi, kai wane irin mugun mutum ne? Ai ba haka muka yi da ku ba. Yanzu ya kake so in yi da shi? Me kake nufi da ni ne? Me na yi maka da kake ƙoƙarin jefa rayuwata cikin matsala? Me zance wa ƴan'uwansa idan..." Maganarta ce ta maƙale sakamakon shigowar da aka yi ɗakin ana bin ta da wani irin kallon da ta kasa tantance ko na me ye. Sauke wayar ta yi a kunneta, jikinta ya ƙara tsananta rawa. Ja da baya ta fara yi tana girgiza kanta cikin matsanancin tsoro.
...
Zaune suke saman 3seater, matasan samari ne ƴan biyu masu matuƙar kama da juna, komai nasu iri ɗaya ne, wanda ya san su sosai ne kaɗai zai iya bambance su. Sai dai duk da kasancewarsu tagwaye, suna da bambancin halayya. Husaini ya kasance mutum ne mai sauƙin kai, saɓanin Hassan da yake da zafi. Suna zaune kowannensu riƙe da wayarsa yana dannawa, fuskar Husaini ɗauke da murmushi, ya yin da Hassan fuskar nan tasa take a murtuƙe. mahaifiyarsu ce ta shigo falon hannunta ɗauke da filet ɗin abinci. Ta tsaya a gaban Husaini tana faɗin "Husainina, ga abincinka nan ɗana, na san kana son irin wannan abincin, shi ya sa na yi maka shi da kaina." Ta ajiye filet ɗin a gabansa, tana shafa kansa cike da ƙauna. "Allah Ya raya mini kai Husaini, tabbas kai ne farin cikina."
Murmushi Husaini ya yi, ya ce "Na gode sosai Mamana ta kaina."
"Ba komai ɗan albarkata, kai dai ka kular mini da kanka. Allah ya ba ka sa'a a kan al'amuranka, ya yi maka jagora."
Ya amsa da "Amin."
Hassan ya ɗago da kansa ya dubi abincin da aka ajiye wa ɗan'uwansa, sannan ya mayar da dubansa ga mahaifiyarsu, fuska a murtuƙe ya ce "Mama ni ma yunwa nake ji, ina nawa abincin?."
Kallonsa ta yi, ta ce "Yana kitchen ka je ka ɗakko da kanka mana, tun da kai ba ƙaramin yaro ba ne da za ka ce sai an ɗakko maka."
Cikin damuwa Hassan ya ce "Amma Mama me ye bambancina da Husaini? Ni ma fa ɗanki ne."
"Kaga Hassan, ba na son yawan ƙorafi, kai kullum cikin ƙorafi kake? Ka koyi haƙuri akan duk wani abin da za ka ga an yi wa ɗan'uwanka mana."
Sunkuyar da kansa ya yi cikin damuwa, ransa ransa ya ƙara ɓaci saboda yadda iyayensa suke nuna fifiko tsakaninsa da ɗan'uwansa.
Mahaifinsu ne ya shigo, fuskarsa ɗauke da murmushi yana kallon Husaini ya ce, "Husaini bawan Allah, kaga ɗan gatan Mamansa da Babansa, abinci ake ci ne? Ina sauran ƴan'uwan naka?" Ya yi maganar yana zama kusa da shi.
Husaini ya ce "Suna school ba su dawo ba."
"Sannu da zuwa Baba." Hassan ya ce yana kallonsa.
"Kai don Allah rufe wa mutane baki, ba na buƙatar gaisuwar taka, ka je can, ka ƙarata da faɗin ran da kake fama da shi, kaga ka daina zama kusa da Husaini, saboda ba na son ya koyi ɗabi'u irin naka, ni wallahi ban so kuka zo a ƴan biyu masu kamanni ɗaya ba, na so a ce kowa ya zo da tashi kamar da ban, ta haka ne za a dinga gane ku kai tsaye, ana tantance waye na gari a cikin ku."
Idanun Hassan sun canza kala daga fari zuwa ja, ya kalli mahaifin nasa cikin ɓacin rai ya ce "Yanzu Baba tsanar da kuke yi mini har ta kai haka?."
"Eh, tama wuce haka, ni ko ƙaunar ganinka ba na son yi a gidan nan, tashi fita, ka bari sai na bar gidan sannan ka dawo."
"Kora ta kake yi Baba? Yanzu ba ka ƙaunar ganina a gidan nan? Baba ni ma fa ɗanka ne."
"Eh, na faɗa, ba na son ganinka a gidan. ka tashi ka fita na ce." Tashi ya yi cikin ɓacin rai, ba tare da ya sake yin magana ba ya bar falon, yana jin wannan barin da ya yi masa, ya bar shi kenan ba zai sake dawowa cikinsa ba. Yana fita kai tsaye ɗakin mahaifin nasu ya wuce, wani lungu ya shiga, sai gashi ya fito da wata ƙatuwar jaka a ciki. Murmushin jin daɗin ya yi, ya tsaya yana ƙarewa ɗakin kallo. Sannan ya saɓa jakar a kafaɗarsa ya bar ɗakin. Tsayawa ya yi yana ƙarewa tsakar gidansu kallon. Kafin ya bar gidan cikin tsananin damuwa, zuciyarsa na yi masa zafin barin gidan nasu da ya yi, bari kuma na har abada.
....
Misalin ƙarfe biyar na yamma, zaune suke a ƙofar gida saman dakali hira suke yi cikin farin ciki da annashuwa.
Kallonta ya yi cike da so da ƙauna ya ce "A duk lokacin dana kalle ki, na tuna da cewa sati ɗaya ya rage mini in mallake ki a matsayin matata, ni kaɗai na san irin farin ciki da nake ji, wallahi ji nake yi duk duniyar nan nafi kowa sonki."
Fuskarta ɗauke da fara'a ta ce "Allah ko masoyi?"
Ya ce "E mana, ai kema kin tabbatar da hakan."
Ɓata fuska ta yi, ta ce "Ni dai ban tabbatar ba, sake sanar da ni ya kake jin sona a zuciyarka?"
"Baby, Idan har akwai abin da nake alfahari da shi a rayuwata, to kasancewarki a cikinta ne, ban san yadda zan bayyana miki irin son da nake yi miki ba, kin zama wani ɓangare na rayuwata da ba zan iya ciri ki, ba tare da na ji kamar na rasa rayuwata ba. Ba ina sonki ne saboda kin fi sauran mata kyau ba, ina sonki ne saboda Allah, da kuma kyakkyawan dabi'un da koke da su. Ina roƙon Allah daya ba ni ikon kula dake har ƙarshen rayuwata. Baby ba na fatan ranar da zan ga hawayenki ya zuba ta dalilina."
Wani irin farin ciki take ji a zuciyarta mara misaltuwa. Kallonsa take yi cike da ƙauna, ta buɗa baki za ta yi magana kenan suka fara jiyo ihun mutane da guje-guje, a firgice ta tashi tsaye tana faɗin "Subhanallah! Me yake faruwa n..?" Ba ta ida rufe bakinta ba, sautin ƙarar harbe-harbe suka ji yana kusanto inda suke, a mugun tsorace ta ce "Masoyi zo mu shiga ciki, ina garin babu lafiya." Ta yi maganar tana duƙar da kanta ta ɗakko dardumar dake shimfiɗe a gurin. Ɗago kan da za ta yi taga ya saita ta da bindiga, fuskar nan tashi a murtuƙe kamar bai taɓa dariya ba, razana ta yi, tare da murza idanunta da sauri domin tabbatar da abin da take gani.
Ma...ma...masoyi me zan gani a hannunk..?"
"Shut up." Ya faɗa da ƙarfi yana ƙara saita bindigar a goshinta.
.....
Garin Kano
Kwance suke saman madaidaicin gadon dake cikin ɗakin suna bacci. A hankali ta fara motsi har ta buɗe idanunta, tare da yin miƙa ta tashi zaune, agogon ɗakin ta kalla, kafin ta kalli gefen da ƴar'uwarta ke kwance tana baccinta hankali kwance. Hannunta tasa ta dake ta kaɗan tana faɗin "Amra, Amra, ki tashi ki yi sallah, kar muyi lattin zuwa school."
Amra ta juya tare da ƙara janyo bargo ta rufe jikinta, cikin ƙunƙuni ta ce "Ke kika san da wata makaranta, ni ban santa ba, dan Allah Amira ki bar ni in yi baccina mana!"
Amira ta yi murmushi, ta ce "Ba zan bar ki ba, Amra ki tashi kar ki janyo mana faɗan Abba don Allah." Taski Amra ta yi, ta tashi tana mita ta fita tsakar gida, ruwa ta ɗiba a bokiti ta shiga banɗaki. "Wannan jarabar har ina? Kullum muna hanyar zuwa school, ni gaskiya na fara gajiya da yawon nan." Ta yi maganar a lokacin da take ƙoƙarin watsa ma jikinta ruwa. A gurguje ta yi wanka ta fito, ko da ta fito tuni Amira ta gama shirinta, da ma can ta yi wanka da asuba kafin ta yi sallah, kasancewar Amra na fashin sallah ya sa uniform kawai ta saka. Duk wanda yaga Amira da Amra zai rantse da Allah ƴan biyu ne, saboda tsananin kamar da suke yi da juna, ko mahaifiyarsu wani lokaci sai ta tsaya ta ƙare musu kallo da kyau kafin ta gane wace ce a gabanta saboda hatta muryarsu iri ɗaya ce. Amira ta kasance mace mai haƙuri, gata da kunya, uwa uba nutsuwa, kuma gata da sauƙin kai, saɓanin Amra da take da tsiwa da rashin kunya, ga rashin tsaro, kowaye kai muddin ka taɓa sai ta rama, ko da kuwa za ka yi gunduwa-gunduwa da manta ne, wani lokaci ba ma sai an tsokane ta take yin rigima ba.
Tana tsaye a gaban ƙaramin madubin dake ɗakin nasu tana gyara fuskarta, Amira na zaune bakin gado tana jiranta, Usman ne ƙaninsu ya shigo ɗakin da sallama yana faɗin "Aunty Amira, Umma ta ce ku zo ku karya, ku wuce school kar ku makara." Ya yi maganar yana buɗe zef ɗin jakar Amra da ke ajiye a gurin ya saka hannunsa a ciki.
"Uban me ka ajiye a jakar nan da kake mini bincike?!" Amra ta daka masa tsawa.
Da sauri ya fito da na hannunsa ya ce "Yi haƙuri Aunty Amra was.." ai bai ƙarasa maganar ba ta wanka masa mari tana faɗin "Jakar tawa ce za ka yi wasa da ita? Oya tashi ka bar ɗakin nan kafin na yi ball da kai." Da sauri Usman ya bar ɗakin dafe da kuncensa yana kuka.
Amira ta dube ta ce "Haba Amra, yanzu dan ya buɗe jakarki ne za ki mare shi?"
"Eh, na mare shi ɗin, idan kin ji haushi sai ki rama masa."
"Wai Amra ni ba yayarki ba ce? Ko don kin ga girmanmu ya zo ɗaya ne ya sa kika raina ni?"
"Amira shekara ɗaya ce fa kika ba ni, shikenan saboda kin girme ni da shekara ɗaya ne zai sa na bari ki taka ni? Ke ma kin san impossible wallahi."
Shiru Amira ta yi, ba ta sake magana ba, sai da ta gama iyayinta sannan suka nufi ɗakin Umma, suna shiga suka gaishe da ita, Umma ta amsa tana kallon Amra ta ce "Ke Amra, me yarona ya yi miki kika dake shi daga ya je kiranku?"
"Umma jakata buɗe, ban sa abin da ya ajiye a ciki ba da zai taɓa mini abu."
"Don ya taɓa miki jaka shi ne za ki dakar min yaron? Ke kullum zuciyarki a baki take? Ba kya ganin yadda ƴar'uwarki take tattalin ƙannenku ne? Ki daina zaluntar mini yara Amra."
"Umma ki daina haɗa halina dana Amira, ba na fatan in yi ko yi da ita, saboda baƙin ciki zai iya kashe ni idan aka yi mini ban rama ba."
Girgiza kai Umma ta yi, ta ce "Ubangiji Allah ya shirya mini ke Amra, Allah ya canza miki wannan halin." Tura baki ta dinga tana mita ƙasa-ƙasa. A haka suka gama karyawa, kafin suka yi wa Umma sallama suka bar gidan. Amra sai mita take yi saboda a ganinta ana shiga haƙƙinta ne, da ake zama tura ta school kullum.
.....
Wata baƙar mota kirar Mercedes-Benz ce ta shigo harabar makarantar, bayan ta tsaya, Direba ya fito da sauri ya buɗe ƙofar motar, wani matashin saurayi ne dogo fari, kyakyawa ya fito cikin takun isa da ƙasaita. Babu alamar fara'a a fuskarsa. Cikin izza ya fara taku a hankali yana tafiya kamar wanda baya son taka ƙasa.
Wasu ɗalibai dake zaune a ƙarƙashin wata bishiya dake kusa da inda aka ajiye motar, bin sa suka yi da kallo. "Wow Hafsa ga mutumin mu nan ya shigo yau, gaskiya ina son bawan Allahn nan da yawa, ina ma zai sone, ai da na gama dacewa a Duniya."
Wadda aka kira da Hafsa ta yi tsaki, tana faɗin "Ke ni na gaji da wahalar da kaina a inda ba a ma san ina yi ba, na bar miki ke da kike ganin za ki iya sai ki yi."
"Da kin taimaki kanki Hafsa, ni wallahi mugun haushinsa ma nake ji, mutum ko da yaushe zai shigo makarantar cikin izza da taƙama yake, ni narasa uban me yake zuwa yi a school ɗin nan." Amra ta faɗa tana harararsa kamar wanda yake ganinta.
Dariya suka yi, suna faɗin "Kai Amra ba ki da kirki, idan ya jiyo ki fa?"
"Yo ya jiyo ni mana sai me? Allah ne shi da zan ji tsoronsa? Yana fama da wani ja kamar an soya ƙosai."
"Amra wai ke me ya sa ba kya iyayin shiru da bakinki ne? Ke kaɗai kika fi kowa a gurin nan? Ina ruwanki da shi? Wallahi idan ba ki daina ba sai na kai ƙararki gurin Dady." Amira ta yi maganar cikin jin haushi da takaicin halin ƙanwarta tata, kallonta Amra ta yi, ta tunzura baki ba tare da ta ce komai ba. Sai dai a ƙasan zuciyarta ta ji haushin yayarta, amma ko kaɗan ba za ta yi mata rashin kunya a gaban jama'a ba, duk abin ta, tana matuƙar girmama Amira idan suka fita waje, a gida ne dai take yi mata iskanci son ranta.
Suna nan zaune sai gashi ya fito, direba ya sake buɗe masa motar ya shiga, sannan ya zagaya ya shiga ya ja motar tare da baɗe su Amira da suke zaune da ƙura. Kallon jikinta Amra ta yi, yadda gaba ɗaya ƙurar ta ɓata musu kaya.
"Kan bala'i, amma dai mutanen nan sun ci uban rainin wayo, ni za a nunawa kuɗi a ɓata mini kaya? To wallahi ba zan yafe ba." Ta yi maganar tana ƙoƙarin bin bayan motar. Sai dai Amira ta riƙe tana faɗin
"Ina zi ki je?"
Ƙwace jikinta ta yi da sauri, ganin motar ta fita daga get ɗin makarantar, ya sa ta juya ta shiga Aji a hasale, tana ji a ranta duk ranar da suka dawo makarantar nan sai ta karta musu rashin mutunci.
Amanarcool
***