FreeArewaPen original
MUGUN KUDURI
- 1views
- 3chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
Tashin hankalin da ya yi mata katutu ne ya sa ta kasa tsayuwa da ƙafafunta. A hankali ta durƙushe a ƙasa ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, iya karfinta ta fara magana "Wace irin bahaguwar rayuwa muke fuskanta a wannan duniyar ne? Shin ko mun aikata wa Allah wani zunubi ne ya zaɓi ya hukunta mu ta wannan hanyar? Shin mu kaɗai ne muke rayuwa cikin wannan baƙar ƙaddarar, ko kuwa akwai wasu kamar mu? Me muka yi wa Allah? Yaushe ne wannan ƙuncin da ya yi wa rayuwarmu dabaibayi zai ƙare? Umma, ki faɗa min idan akwai wani laifi da kuka aikata wa Allah ke da mahaifinmu mu nemi gafararsa wataƙila ma samu sassauci daga wannan baƙar ƙaddarar da ta mamaye rayuwarmu." Matashiyar budurwar ta ƙarasa maganar tana kallon matar da ke kwance a kan dandaryar ƙasa ba ta motsi, abin da ke nuna tana raye kawai shi ne hawayen da ke gangarowa daga cikin idanunta babu ƙaƙƙautawa. Cikin tsananin ɓacin rai da ruɗadin zuciya ta sake cewa, "Yaya ake so mu yi da rayuwarmu? Me ya sa mutane suka mayar da zulunci abin yi? Me ya sa taimakon ƴan uwa ya yi ƙaranci a wannan zamanin? Me ya sa aka daina daraja zumunci? Me ya sa komai sai kana da kuɗi ake yi da kai a wannan duniya? Me ya sa? Me ya sa Umma?" Ta ƙarasa maganarta tana jijjiga matar da ke kwance a ƙasa tamkar gawa, yayin da ita kuma ke gunji kuka. Ba zato ba tsammani, ta dakata da kukan nata sakamakon kukan ƙannenta da ya mamaye mata kunne. A hankali ta ɗaga kanta ta kalle su cikin wani yanayi mai cike da tausayi da raɗaɗi. Sannan cikin murya mai rauni da karkarwa, ta ci gaba da magana "Dole ne na fita neman kuɗi ko domin rayuwarku ta inganta ƴan'uwana. Dole zan nemi kuɗi ko ta wace hanya ce. Dole zan samo kuɗi domin na rama irin ƙunci da wulaƙancin da aka jefa mu a ciki saboda talauci." Ta ƙarasa maganar cikin rawar murya, dubanta ta mayar ga mahaifiyarta, cikin sanyin murya ta ce, "ki yafe min, Umma. Amma tabbas ko ta wace hanya ce, zan fita neman kuɗi, ko da hakan yana nufin na sadaukar da mutuncina.".....Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare. Garin ya yi tsit ba a jin komai, kowa ya kama gabansa domin samawa ruhinsa da gangar jikinsa natsuwa. Kwance take saman madaidaicin gado. Duk da kasancewar babu wadataccen haske a ɗakin, amma idanunta a buɗe suke tana kallon silin ɗakin cikin wani irin yanayi na damuwa, lumshe idanunta ta yi, a hankali ta sauke numfashi, tare da ɗora hannunta saman ƙirjinta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri, sake runtse idanunta ta yi da ƙarfi, ƙwaƙwalwarta ta shiga tunanin halin ƙuncin rayuwar da take ciki. Ƙarar faduwar abu ta ji a ƙasa, hakan ya sa ta buɗe idanunta a firgice.Shiru ta yi ba tare da ta motsa ba, tana jin yadda bugun zuciyarta da ke neman fasa ƙirjinta ta fito ya tsananta. A hankali ta kunna wutar ɗakin, sannan ta mayar da dubanta ga ƙofar ɗakin da ke buɗe. Wani iri...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.