Free chapter · Read without an account
Chapter 2
by Amanarcool · MUGUN KUDURI
Zaune take a gaban mahaifiyarta, cikin damuwa take kallonta da idanuwanta da suka cika da ƙwalla, ta ce "Inna."
Inna ta ɗago da kanta ta kalle ta, ta yi mata shiru ba tare da ta amsa kiran da ta yi mata ba.
Ba ta damu ba ta ci gaba da faɗin "Inna, me ya sa Baba baya sona yafi son su Bilki? Me na yi masa ne da yake hantara ta? Ni ma fa ƴarsa ce, amma kullum sai ya nuna ya fi sonsu a kaina." Ta kai ƙarshen maganar hawaye na zubo mata.
Ajiyar zuciya Inna ta sauke cikin damuwa, zuciyarta na yi mata zafi, sai dai ba ta bari ƴar tata ta fahimci haka ba. Ta ce "Raheema, ban hana ki irin wannan maganar ba? Me ya sa ba kya jin magana ne? Na sha gaya miki Babanku yana sonki. Duk gidan nan ba na tunanin akwai yaron da Babanku yake so kamar ke, amma kullum ba ki da zancen daya wuce ki ce baya sonki, kar in sake jin kin furta wannan maganar a bakinki."
Tun da Inna ta fara magana take bin ta da kallo, wani irin mamaki ne yake kamata a duk lokacin da Innar ta ce mata Baba yana sonta fiye da kowa, bayan babu wadda yake nunawa tsana sama da ita a gidan.
"Inna, Baba baya sona, wallahi baya ƙaunata, faɗa kawai kike yi, amma ba ni yake so ba, su Bilki yake so. Tun da na yi wayo, ban taɓa ganin Baba ya nuna yana sona ba daidai da rana ɗaya."
"Ƙarya nake yi miki kenan?"
Raheema ta girgiza kai, ta ce "A'a Inna, ni ban ce kin yi ƙarya ba, sai dai ina mamakin yadda kike ƙoƙarin ɓoye mini abin da na riga da na daɗe da sanin shi." Tana gama faɗar haka ta tashi ta bar ɗakin, tsakar gidan ta fita, Bilki ta gani tsaye a ƙofar ɗakinsu tana waya tana murmushi, bokiti ta ɗauka ta je bakin rijiyar dake cikin gidan ta ɗebo ruwa. A ƙofar ɗakinsu ta ajiye bikitin ruwan, ta shiga ɗaki domin ta ɗakko soso da sabulu.
Bilki na ganin haka ta yi sallama da wanda take waya da shi, ta ɗakko bokitinsu ta ƙaraso gurin da sauri da juye ruwan.
Raheema da fitowarta kenan taga abin da Bilki ta yi.
"Me ya sa za ki juye mini ruwa?."
Cikin tsiwa Bilki ta ce "Saboda na isa ne."
Cikin zafin nama Raheema ta je za ta karɓe bokitin ruwan a hannunta.
"Ke, me ye haka kuke yi ne?" Suka jiyo muryar Baba da shigowarsa kenan.
Marairaice murya Bilki ta yi, ta ce "Baba ina so zan yi wanka ne, kuma ba ni da lafiya, sai na juye ruwan da Aunty Raheema za ta yi wanka da su, shi ne take ƙoƙarin karɓe ruwan." Ta kai ƙarshen maganar tana matsar ƙwallar ƙarya.
Kicin-kicin da fuska Baba ya yi, ya kalli Raheema ya ce "Ke wace irin babbar banza ce? Ba ƙanwarki ba ce? Ko lafiya ƙalau take ai za ki iya ɗebo mata ruwa ta yi wanka, maza ɗauki ruwan nan ki kai mata su banɗaki kan na ɓata miki rai yanzun nan."
Wani irin baƙin ciki ne ya ƙume zuciyar Raheema, ta duƙa jiki a sanyaye ta ɗauke bokitin ruwan ta nufi banɗaki ta kai mata.
Ɗakin Saude ya wuce yama mita.
Raheema ta fito daga banɗakin tana goge hawayen da suka zubo mata, kallonta Bilki ta yi tana dariya gami da yi mata gwalo, ta ce "Sai baƙin cikina ya kashe ki Raheema, matuƙar kina saka damuwa a ranki na son da Baba yake yi mini ni da ƙanina, gara ma ki haƙura don babu yadda kuka iya da mu daga ke har uwar taki mai saka ki a ɗaki tana yi miki huɗubar Jaki."
Raheema ta kalle ta ta ce "Bilki, duk abin da za ki faɗa ya tsaya iya kaina ki daina saka mahaifiyata a ciki."
"An ƙi a daina ɗin, idan kina da abin da za ki yi sai mu gani, ƙarya na yi? Ba uwarki ce ke ƙara ziga ki kina jin haushi a kan son da Baba yake yi mana ba?" Buɗe baki ta yi za ta yi magana, ta ji Inna na ƙwala mata kira. Jiki a saluɓe ta raɓa ta gefenta ta wuce.
Tsaki Bilki ta yi, tare da cewa "Munafukan banza, a haka dai za ku ƙare a munafunce, kuma ta Allah ba ta ku ba."
Baba ya shiga ɗakin Saude yana mita, Saude ta ce "Ai Malam ka daina ganin laifin Raheema, duk abin da take yi laifin Karima ne, ita ce take cusa mata ƙiyayyar ƴan'uwanta a zuciyarta, ni na rasa dalilin da ya sa take yin wannan abin, a tunanina su Bilki ai ƴaƴanta ne kamar yadda Raheema take ƴarta. Sannan idan ma son da kake yi wa yaran nan ne ya sa take jin haushi ai ita ma Raheeman kana sonta, tun da ƴarka ce ita ma. Amma ita kwata-kwata ba ta gani."
Shiru Baba ya yi mata ba tare da ya tanka mata ba, wanda hakan ba ƙaramin haushi yake ba ta ba. A duk lokacin da take yi masa zance makamancin wannan baya cewa komai, sai dai ya yi mata shiru. Ita ba haka take so ba, so take yadda yake hantarar Raheema ita ma Kariman ya fara yi mata haka. Duk da wani lokacin ya kan haɗa hadda ita ya yi musu faɗan a tare idan yana yi wa Raheema.
Tashi ya yi ya fita daga ɗakin. Kai tsaye ɗakin Inna ya shiga, ko da ya shiga tana yi wa Raheema faɗa a kan me ya sa ba ta ƙyale Bilki da ruwan ba, ta janyo wasu? Tana ganin ya shigo ta yi shiru da bakinta.
Kallonta ya yi ya ce "Karima ya kuma kika yi shiru? Ci gaba da maganar da kike yi mana."
"A'a ba magana nake yi ba Malam."
"Ok, kurma nake kenan? Da kunnena na ji kina magana, kuma hadda sunan Bilki na ji kin ambata, anya Karima abin da Saude take faɗa ba gaskiya ba ne na ke kike hurewa yarinyar nan kunne?"
Ta kalle shi da kyau, zuciyarta na yi mata zafi ta ce "Allah Sarki! Ashe ma ziga ta nake yi? A kan me zan ziga ta Malam? Me ake yi mata a gidan da zai sa in ziga ta?"
"Yo ai ke zan tambaya Karima, bari ki ji in gaya miki, idan ma ziga ta kike yi to wahala za ta sha a banza. Ke ma kin sani, matsayinta dana Bilki ba zai taɓa zama ɗaya ba a gurina, tun wuri gara ta kama kanta."
"Amma Malam naga dukansu ƴaƴanka ne ko?"
"Karima magana za ki gaya mini? Yaushe na yi lalacewar da har zan fitar da yawu kina haɗiyewa? Ki kiyaye ni fa."
"Allah ya ba ka haƙuri."
Juyawa ya yi fuu ya bar ɗakin yana bambami.
Raheema ta ce "Inna kin ga abin da nake gaya miki ko? Da ma ni na san Baba baya ƙaun...."
"Kul! Kar na ji kin furta wannan kalmar a bakinki." Inna ta katse ta, kafin ta ci gaba da faɗin "Har gobe babu wanda mahaifinku yake so a gidan nan sama dake. Ko da wasa kar ki yadda in ji kin furta wata mummunar kalma a kansa."
Fashewa Raheema ta yi da kuka, saboda sosai take jin zafin abin a ranta. Ga Inna da take hana ta yin magana.
Tashi Inna ta yi, ta fita waje ta kama sabgoginta ta bar ta nan a ɗaki tana kuka.
.....
Har aka tashi daga makaranta Amra masifa take yi da mutumin da bai san da zamanta ba, suka fito daga cikin makarantar. A bakin titi suka tsaya suna taron abin hawa. Sun ɗan jima tsaye a gurin kafin wani mai napep ya tsaya a gabansu, kai tsaye Amra ta shiga ciki ba tare da ta tsaya kallon mai napep ɗin ba tsabar masifar da take cikinta.
Amira ce ta sanar da shi unguwar da zai kai su, suka yi ciniki kafin ta shiga.
"Wai ke Amira a komai naki sai kin tsaya sanya ne? Mai napep ɗin nan ya tsaya ba sai ki shiga mu tafi ba, ma yi masa bayanin inda zai kai mu daga baya, amma kin tsaya ɓata mana lokaci."
Amira ta girgiza kai, ta ce "Ubangiji Allah ya rangwanta miki Amra, Allah ya sanyaya miki zuciyarki, ya yaye miki wannan zafin ran da kike fama da shi."
"Ba Amin ba, ba na fatan in yi sanyi hali irin naki Amira."
Sai da mai napep ɗin ya juyo ya kalle ta, kasa haƙura ya yi, ya ce "Haba ƴar'uwa, bai kamata ki ce haka ba tun da addu'a ce ta yi miki, sai ki amsa da Amin."
"A'a ka ga bawan Allah dakata! Ina ruwanka da maganarmu? Ina ce da Yayata nake magana ba da kai ba? Me ye naka a ciki?"
"Allah ya ba ki haƙuri." Daga haka ya ja bakinsa ya yi shiru, takaici ne ya ƙume Amira ta ji kamar ta kai mata duka.
Ko da suka isa gida, kallo ɗaya Umma ta yi wa Amra ta san cewa ba a daidai take ba. Su Usman na ganin yanayinta gaba ɗaya suka sha jinin jikinsu, kowa ya kama kansa, musamman Rumaisa da take da shegen tsoro. Amira ganin ƙannin nasu a takure duk sai ta ji babu daɗi, a ranta ta din ga addu'ar Allah ya shirya mata ƴar'uwarta, ya sa ta rage zafin ran nan nata. Abinci ma ita kaɗai ta ci, ba tare da ta bi ta kan Amira ba ta shiga kitchen ta zuba nata.
Umma ta ce "Amira rigima kuka yi da mutuniyarki? Ko kuma dai taɓa ta aka yi a makarantar?"
Amira ta yi murmushi ta ce "Umma, babu fa abin da aka yi mata, ai kin san halin ƴar taki, shegen halinta ne ya tashi, kawai daga wasu mutane sun zo makarantar, Amra ta din ga sukar wani bawan Allah da bai san tana yi ba, shi ne da suka zo wucewa motarsu ta tada ƙura a inda muke zaune har ta ɗan ɓata mana kaya, shikenan Amra ta din ga masifa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba."
Umma ta ce "Ikon Allah, to da gayya suka tada muku ƙurar ne?"
"Umma ba su fa san sun yi ba, rigima ce irin ta Amra, hadda ƙoƙarin biyar su ta yi sai da na hana ta."
Umma ta ce "Oh ni Fatima! Allah ya shirya mini wannan yarinyar." Amira tana dariya ta amsa da Amin, tana sake sanar da ita yadda suka yi da mai napep. Kasa magana Umma ta yi, ta rasa a ina Amra ta ɗakko wannan masifar, ita dai ba ta da faɗa, Abbansu ma haka. Duk gidan nan ita kaɗai ce take da wannan halin, wanda take tsoron kar wata rana garin rashin haƙurinta, da neman maganarta, ya sa ta janyo musu masifa.
......
Wani katafaren gida ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, harabar gidan babba ce, an ƙawata ta da furanni da shuke-shuke, da suka haɗu suka ƙara ƙawata gidan. Duk da kasancewar rana ce, hakan bai hana bayyanar hasken da fitillun da aka ƙawata harabar gidan da su fita ba, haske ne mai kyau da ɗaukar hankali, ga ruwa na fountain yana tsiyaya a tsakiyar harabar, gidan ba ƙaramin haɗuwa ya yi ba, ya tsaru iya tsaruwa. Wani irin mahaukacin hon ake yi a ƙofar gidan, da sauri mai gadin gidan ya tashi jikinsa na tsuma ya je ya buɗe get ɗin. A guje aka shiga da motar ciki, a katafaren parking space na gidan aka yi parking. Direban ya fito da sauri ya je ya buɗe masa ƙofa, kafin ya koma gefe tsaya yana jiran fitowarsa ya rufe ƙofar, kusan minti biyar sannan ya zuro ƙafarsa ya fito, ba tare da ya kalli gefen da Direban yake ba, ya fara tafiya cikin isa da taƙama. Ma'aikatan gidan sai gashe shi suke yi amma bai bi ta kansu ba balle ya amsa gaisuwar da suke yi masa.
Falon gidan ya shiga, ba tare da ya yi sallama ba, Momy ya tarar a falon tare da Dady, sai ƙanwarsa Najwa dake kwance saman 3seater tana danna wayarta.
Fuskar Dady ɗauke da murmushi yake kallonsa, ba tare da damuwar shigowar da ya yi bai yi sallama ba ya ce "Oyoyo ɗan albarka. Yau ina ka shiga? Tun ɗazu nake kiran layinka baya shiga."
Ya ƙarasa kusa da Dady ya ce "Dady yau na yi tafiya mai nisa ne, shi ya sa na rufe wayoyina saboda ba na son damuwa."
"Maleek!" Momy ta kira sunansa da ƙarfi.
"Momy." Ya taɗa yana tsare ta da ido.
Cikin ɗaga murya ta fara yi masa faɗa "Kai ba musulmi ba ne da za ka shigo gida babu sallama? Maleek sau nawa zan gargaɗe ka a kan shigowar nan da kake yi babu sallama? Me ya sa ba ka jin magana ne?."
Kafin Maleek ya yi magana Dady ya ce "Haba Sara, Maleek ɗin kike yi wa tsawa haka? Me ye a ciki don ya shigo bai yi sallama ba? Kin ga ki kiyaye ni fa, ba na son abin da kike yi wa yaron nan. Duk kin bi kin tsangwame shi kamar ba ke kika haife shi ba." Cikin damuwa Momy ta ce "Alhaji duk kai kake ɓata yaron nan, shi ya sa yake yin abin da ya ga dama."
"Eh na ɓata shi ɗin." Ya faɗa yana kallon Maleek da ya yi kicin-kicin da fuska, saboda a rayuwarsa ya tsani a yi masa faɗa, ba don Momy ɗinsa ba ce da babu abin da zai hana ya nuna wa koma waye kuskurensa na ɗaga masa murya da ya yi. Dady ya ce "Sorry Maleek, ka yi haƙuri, ka san halin Momyn taka ta fiye mita."
"Haba Dady, taya da girmana da komai Momy za ta din ga yi mini faɗa a gaban ƙanwata? Gaskiya ba na jin daɗin abin da take yi mini."
"Na yi maka faɗan dan ubanka zo ka dake ni, wallahi sai in sharara maka mari in gani idan za ka rama ne."
Zaro ido Dady ya yi, ya ce "Sara! Kina da hankali kuwa? Maleek ɗin za ki mara? Da giman nashi za ki mare shi?"
"Alhaji a gurinka ne yake da girma, amma ni a gurina yaro ne, har yanzu bai wuce in hukunta shi ba, idan ta kama har dakunsa sai in yi." Tana gama faɗar haka ta bar falon, saboda ta san idan ta tsaya za ta iya samun saɓani da mijin nata.
Ran Maleek ba ƙaramin ɓaci ya yi ba.
Ya kalli Najwa da ta zuba masa ido tana kallonsa ya ce "Ke, tashi ki bar gurin nan." Da sauri ta miƙe ta bar falon.
"Wallahi Dady, in dai Momy ta ci gaba da yi mini abubuwan nan, tabbas zan bar gidan nan, in daina zuwa gaba ɗaya."
"A'a yi haƙuri Maleek, in sha Allah za ta daina, zan yi mata magana."
Tashi tsaye ya yi, yana faɗin "Da dai ya fi, idan ba haka ba za a daina ganina a gidan nan." Daga haka ya sake fita ya bar gidan.
Amanarcool
***