Free chapter · Read without an account

Chapter 3

by Amanarcool · MUGUN KUDURI

Ƙarfe uku na yamma, su Amira suka gama shirinsu na tafiya islamiyya, sallama suka yi wa Umma suka tafi, Umma ta bi su da addu'a, tana jin ƙaunar yaran nata sosai a zuciyarta. A duk lokacin da ta kalle su, ta kan yi wa Allah godiya da ya azzurta ta da su. 

A hankali suka fito daga gida, kasancewar islamiyyar tasu babu nisa ya sa suke zuwa a ƙafa, cikin natsuwa suke tafiya suna hira. Duk wanda ya gansu sai ya ji sun burge shi, saboda komai nasu iri ɗaya ne, hatta tafiyarsu iri ɗaya ce, jama'a da dama su kan yi mamaki idan suka san cewa ba ƴan biyu ba ne. Hatta kaya kala ɗaya suke sakawa. Abu ɗaya ke sa a bambanta su shi ne, ta ɓangaren halayyarsu, saboda Amra da yawan mutane sun santa da tsiwa da rashin tsoro, saɓanin Amira. Duk da wani lokacin idan ba su so a gane su ba, Amra ta kan zuwar ma mutum a siffar Amira domin ta rikita shi. 

"Amira, Amira, Amira." Suka ji ana faɗa a bayansu. 

Tsayawa suka yi, ba tare da sun juyo ba. 

Ya ƙaraso inda suke, fuskarsa ɗauke da fara'a yake bin su da kallo. Ya ce "Ni gaba ɗaya rikita ni kuke yi, don Allah wacece Amira a cikin ku?" Nura ya ce yana murmushi, sai da gaban Amira ya buga da ƙarfi, saboda har ga Allah ba ta son bibiyar da Nura yake yi mata, ita gaba ɗaya sabgar mazan ce ba ta dame ta ba. Don haka ta kalli Amra ta ce "Kin ga Amira, ni na tafi, kya biyo ni daga baya." 

Tana gama faɗar haka ta bar wajen, Amra ta yi murmushi, saboda ganin yadda ƴar'uwar tata ta yi masa ɓaddasau, ta mayar da dubanta ga Nura, cikin natsuwa ta ce "Ina yini."

Washe baki ya yi, cikin jin daɗin yau ta tsaya saurarar shi, ya ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah Amira ya gida?"

"Alhamdulillah" ta ce a taƙaice. 

Nura ya ce "Na so mu yi magana dake kuma ga shi naga za ku je makaranta."

Amra ta ce "Eh, za mu je islamiyya ne, idan ba damuwa ka yi haƙuri har wani lokacin, ban cika son tsayuwa a hanya ba." 

"Tom shikenan babu damuwa, in sha Allah zan zo har ƙofar gidanku, na gode sosai da saurarata da kika yi." 

"Babu komai, sai anjima." Amra ta ce, daga haka ta juya da sauri ta tafi, ta ƙaraso inda Amira take tsaye nesa da su tana jiran ta. 

"Kin kyauta Amira, shi ne za ki gudu ki bar da wannan mutumin? Allah kin yi sa'a ƴan mutuncinne a kusa da sai na nuna masa ba Amira ba ce Amra ce." 

Amira ta yi dariya, ta ce "Ai na san ba za ki iya dizgani a gaban jama'a ba, shi ya sa na yi hakan, Amra ba na son bibiyar da mutumin nan yake yi mini, idan har magana yake son yi da ni ya same ni a ƙofar gidanmu mana, amma ba ya tare ni a hanya yana yi mini magana ba." 

Amra ta ce "Yanzu dai ya ce zai zo gida ya same ki, ni Allah ne ya gyara da na iya riƙe dariyata a gurin nan. Yasin duk na kalli kansa ji nake kamar in fashe da dariya, yadda kika san an mulmula sakwara." 

"Kai Amra Allah ya shirye ki, halittar Allah ce fa."

"Astagafirullah." Amra ta ce tana dariya. 

Suna isa islamiyya Amra ta yi ido huɗu da Malam Yusuf, cikinta ne ya yi wani irin ƙugi da ta tuna abin da ta aikata jiya kafin ta bar makarantar, mazewa ta yi, suka ci gaba da tafiya ita da Amira, suna ƙoƙarin shiga aji suka ji ya ƙwala musu kira. 

Amra ta ce "Ka da ki juya Amira, mu shiga aji kawai." 

Amira ta ce "A'a Malam Yusuf ne fa yake kiranmu." 

"Eh, ai na san shi ɗin ne, amma wallahi ba zan je ba."

Amira ba ta ce komai ba, ta mayar da dubanta inda Malam Yusuf yake ta ce "Malam magana kake yi ne?" 

Ya ce "Eh, Amra ta zo ina son ganinta." 

Amra na jin haka ta afka cikin aji da sauri tana faɗin "Billahillazi babu inda zan je." 

Amira ta juya ta isa inda yake, tana zuwa ta ce "Malam barka da yini." 

Ba tare da ya amsa gaisuwarta ba ya ce "Amira ce ko Amra?" 

"Amra ce." Amira ta ba shi amsa. 

"Jiya ba ki ji ina kiranki ba ne?" 

Wuƙe-wuƙe ta yi da ido, ta rasa me za ta ce masa.

"Ba tambayarki nake yi ba? Saboda ba ki da kunya, kin raina mutane kina jina ina yi miki magana kika tafi ko? Saboda kin san ba ki da gaskiya?" 

Da ƙyar Amira ta ce "Yi haƙuri Malam, tuba nake ba zan sake ba." 

"Ba zan haƙura ba, kin kuru ba a jiya ne na kama ki ba, da hukuncin da zan yi miki sai yafi wanda zan yi miki a yanzu. Maza ki ɗauki bokiti ki ɗebo ruwa ki je ki wanke banɗakin da yara ke amfani da shi, ki tabbatar ya fita sosai, idan kika gama ki cika randunan can da ruwa." Ya yi maganar yana nuna mata randunan da ake zuba ruwan da ɗalibai suke sha, sannan ya ɗora da faɗin "Kuma wallahi kika yi ƙoƙarin guduwa ko ƙin yin abin da na saka ki, hukuncin da zan yi miki sai yafi wannan, mara kunyar banza." Juyawa ta yi jiki a sanyaye ta nufi aji domin ta ajiye jakarta.

Tsawa ya daka mata, ya ce "Kar ki kuskura ki shiga aji ba tare da kin gama aikin dana saka ki ba! Zo ki ajiye jakar a nan ki wuce." Dawowa ta yi, ta ajiye jakar sannan ta wuce. 

Malam Yusuf yabi bayanta da harara, a ransa ya ce "Ji ta kamar wata saliha."

Amra na can cikin aji sai dai hankalinta yana ga Amira, tana ta addu'a da fatan Allah ya sa kar a dake ta.

Amira ba ta gama aikin da aka saka ta ba sai wajen ƙarfe huɗu, Duk da ba yau ta saba karɓar hukuncin laifin da Amra take yi ba. Amma na yau ya yi mata ciwo sosai, yadda aka saka ta wanke banɗakin da duk yara sun lalata shi da kashi. Kuma aka saka ta ɗibar ruwa, abin da ta tsana kenan a rayuwarta. Gaba ɗaya haushin Amra ne ya kamata, ko da ta gama ta je ta ɗauki jakarta. A mugun gajiye ta isa ajinsu, ko kallon inda Amra take ba ta yi ba, ta nemi guri ta zauna, tana jin wani iri a jikinta, kamar tana warin kashin da ta wanke. 

......

Ta daɗe a ɗaki tana kuka, fuskarta har ta kumbura saboda kukan da ta yi, da ƙyar ta tashi ta fita waje, sake ɗebo ruwan ta yi a rijiya, tana ƙoƙarin shiga banɗaki Saude ta fito daga ɗakinta tana hautse ne fuska tare da hura hanci ta ce "Ke Raheema ɗan jira ni, ina da uzurin shiga banɗakin nan." Wani takaici ne ya sake kama ta. Ta dire bokitin ruwan ta koma gefe ta tsaya tana jiran Saude ta shiga ta yi abin da za ta yi ta fito. 

Saude ta zo za ta wuce da gayya ta sa ƙafarta ta ture bokitin da Raheema ta ajiye, gaba ɗaya ruwan suka zube, ta yi shigewarta banɗakin. 

Umaima dake zaune a ƙofar ɗakinta tana kallon abin da ke faruwa, ta ce "Amma dai Saude ba ki yi sa'ar hali ba, ke wace irin mata ce? Saboda ke ga yarinyar nan babu ruwanta duk abin kike yi musu ita da uwarta ba sa ce miki komai, shi ne kike taka su yadda ranki yake so." 

Jikin Saude har tsuma yake yi ta fito daga banɗakin.

Inda Umaima ke zaune ta ƙarasa tana bin ta da wani wulaƙantaccen kallo, ta ce "To Jaɓa, sa baki a bar miki, uwar Iya, mai cinikin Iya, ina ruwanki da abin da nake yi? Umaima ba za ki daina saka mini baki a al'amurrana ba? Ba na son munafurcin nan da kike yi mini, ban da neman suna me ye naki na tarewa kishiya faɗa?."

Umaima ta miƙe tsaye ita ma tana kallon Saude a wulaƙance, ta ce "Saude, ke ce Jaba ba ni ba, na faɗa, na sake faɗa, abin da kike yi ba kya kyautawa, haka kawai saboda kin ga mata babu ruwanta sai ki zauna kina yi musu cin kashin da kika ga dama. Ki isko ta da mijinta amma ki zo kina nuna mata fin ƙarfi saboda babu Allah a ranki. Gaskiya ce wallahi ba zan fasa faɗarta ba." 

Ɗaga hannu Saude ta yi za ta kai mata duka, da sauri Umaima ta riƙe mata hannu tana faɗin "Dalla gafara can wawuya kawai. Yanzu ba kamar da ba ce, na yi hankali, na kuma san ciwon kaina, ba zan sake haɗa jiki dake ba kina shafa mini warin hammata. Ƙazamar banza. Kin saka ƙaramar yarinya a gaba sai ka ce kishiyarki." 

Ƙarfi da yaji Saude ke son cakumar Umaima su yi dambe, amma kasancewar Umaima ta fita kaurin jiki ya sa ta haɗe hannayenta waje ɗaya ta riƙe. 

"Ki cika mini hannu juyar banza, shekara da shekaru kina zaune sai dai ki ci ki yi kashi, ki bari sai kin san zafin haihuwa sannan ki dinga saka wa mutane baki a al'amurransu."

Cikin baƙin cikin gorin da Saude ta yi mata, wanda ba yanzu ta saba yi mata shi ba, ta ce "Alhamdulillah, duk da ban haihu ba, ke da kika haihu ɗin ban ga abin da kika fini da shi ba, sannan wannan ba da ni kike ba, da Allah kike yi, saboda kin san shi ne mai bayarwa ga wanda ya so, kuma ya hana ga wanda ya so, ke da Allah ya bawa haihuwar ba don yafi son ki ba ne ya ba ki, sannan ni da bai bawa ba, ba don baya sona ne ya hana ni ba. Jahilir banza wadda ba ta san abin da take yi ba. Ni ba kamar Karima ba ce da kike faɗa mata abin da ranki yake so ta ƙyale ba. Duk kika faɗa mini cuta sai na faɗa miki mutuwa." 

Raheema na tsaye tana kallonsu, cikin baƙin ciki ta koma ɗakinsu ba tare da ta sake yunƙurin yin wankan ba. Karima na jin su amma ta yi musu banza ba, ta ci gaba da aikin da take yi.

Bilki ce ta fito da ƙyar ta ja hannun Saude tana hararar Umaima suka bar wajen.

Umaima ta ce "Fitsararriya kin harari uwarki, mai kama da mushen Jaki." 

Ɗaki suka shiga, Saude ta ci gaba da masifa tana jiran dawowar Baba, saboda wannan cin mutuncin da Umaima ta yi mata ba zai tafi a banza ba.

......

"Momy, a gaskiya ba na jin daɗin abin da Dady yake yi, na rasa me ya sa ba ya so a yi wa Yaya Maleek faɗa ko kaɗan, kuma wallahi Momy abin da Yaya yake yi baya kyautawa, sai kin ji yadda jama'a ke surutu a kansa saboda wulaƙanta mutane da yake yi."

Cikin damuwa Momy ta ce "To ya za mu yi Najwa? Duk abin da Maleek yake yi laifin Dadynku ne, shi ne yake goya masa baya yana yin duk abin da yaga dama, ni kaina ba na jin daɗin wannan halayen nasa, amma babu yadda zan yi da shi, sai dai in ci gaba da yi masa addu'a."

"Momy ki yi wa Dady magana ya daina barinsa yana yin duk abin da yaga dama, wallahi ba na jin daɗin surutun da ake yi a kansa, baki abin gudu ne, wani ba ka san yadda bakinsa yake ba, ya je can ya yi maka muguwar fata, ko ya faɗi wata kalmar da ba ta dace ba a kanka ka shiga uku. Ni shi nake jin tsoro ."

"Babu abin da za mu yi sai addu'a Najwa, Maleek ya riga ya sangarce da yawa."

Ci gaba da jan zancen Najwa ta yi cikin damuwa.

....

Bayan an tashi daga islamiyya, Amira suna tafe a hanya ta dubi Amra ta ce "Gaskiya Amra kina ba ni ciwon kai da yawa. Don Allah me kika yi wa Malam Yusuf da har ya saka ni wanke banɗaki da ɗebo ruwa?."

Amra ta ce "Wanke banɗaki da ɗebo ruwa? Kut! Kuma kika yi?."

Harararta Amira ta yi, ta ce "To idan ban yi ba ya kike so na yi tun da kin gudu kin bar ni? Ko so kike in ce masa ba zan yi ba ya dake ni?."

Amra ta ce "Allah da ni ce ba zan yi ba sai dai a dake ni, wankin banɗaki fa? Shi ma dai yana son yin mugunta ne, haka kawai daga ya kira mu jiya zai saka mu aiki ni ban je ba, shi ne zai saka ki wanke banɗaki da ɗebo ruwa?"

"Ai ko me aka yi mini ke kika ja mini, kuma na fara gajiya da halinki, zuwa zan yi in daina karɓar hukuncin laifin da ba ni na aikata ba, saboda na lura idan na biye miki wata rana sai kin saka an yi mini dukan da zan kasa tashi." 

Amra ta ce "A'a ke fa kike ɗorawa kanki Amira, me ya sa idan kika ga na maze a kan abu kike bayyana kanki a matsayin ni? Ai da kin dinga yin shiru kamar yadda nake yi mana." 

"In yi shiru a haɗa mu duka a dake mu ko? Ai daga yanzu kai tsaye zan dinga nuna musu ke, tun da na lura ba za ki taɓa daina nemo mana magana ba."

Dariya Amra ta dinga yi mata, saboda ta san faɗa kawai take yi ba za ta iya ba. Amira ta yi mata banza. A haka suka ƙarasa gida. 

Da sallama suka shiga gidan, sai dai wanda suka tarar zaune a tsakar gidan saman tabarma ya sa lokaci ɗaya annurin fuskarsu ya ɗauke.



Amanarcool
***





Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol