Free chapter · Read without an account
Yar mai gadi Chap 4
by Quenneriya · Yar mai gadi
Bayan Asiya ta gama sallah ta fito , INNA na zawne tana kwallen wani film a MBC Bollywood
Ta karaso ta zawna kusa da INNA tace ….
my Rabin Rai bari naje Ummy tace na dawo zamuyi aiki….
Inna tace Toh … karkije ki dawo ki sani ah gaba da ciwon kaii koh ciwon kafa .,..
Asiya tace!!! A’a ni girki kaway zamuyi…
ta huce ta fita daga dakin ta bar inna na mita ita bataso anaa yawan sakamata ya aiki….
Asiya har ta kama hanyar zuwa sashin su kaway ta tuna abinda ya faru dazu !!! sai ta cenza hanya zuwa cikin gida direct !!!!
Tana shiga da ta Rabka Uwar Sallamu taba kara kutsa kanta cikin falon …. cen ta jiyo muryar Ummy da. yar aikin ta ah kichten din…
me makon ta huce ciki kaway sai hankalin ta yakaii kan TV din dake cikin. falo anaa haska wani KOREA FILM tuni ta manta da wani aiki da zasuyi a kichten ta zawna kasa kan capet din tana kwallon
Ummy wace taji sallamar Asiya tun shigowar ta jin shuru saita leka falon tana cewa… Asiya ki shigo mana ya kika zawna ah falo kaida zamuyi aiki
Asiya tayi kwal kwal da ido tace toh ta mike still hankalinta na gurin TV din Ummy ganin haka ta karasa shigowa cikin falon taga abinda take kwallon tayi murmuchi tace Shikenan yi zamanki tunda kikaga wanan film din toh bah lalle ne bah kiyi abun kirki a kichten din…
Ai Asiya najin haka ta koma ta zawna dama haka take so …..
Ummy ta huce kichten din tana jinjina yadda yarinyar ke mugun son Korea film dan wataran ssai taji kamar tana yaran su…
Tana so ta dinga shiga cikin kichten din da ita dan Yarinyar ta koyi wani abun tunda tasan Zara’u bah wani ganin ta take sosai bah kullun tana tare dda inna kuma ita inna bah koya mata take bah … tunda a mafi yawan lokacin daga nan ake kaiii mata abinci…
wanan umarnin mai gidan nan !!!
amma duk da haka wataran haka inna zata zake ta shiga madafar dake bangaren ta tayi girkintaa…
kuma bata saka Asiya aikin komai saii uban lele da take mata……
Asiya na zawne ah falo har kusa sallar Magrhib
lokacin Alhadji Usman ya shigo Rike da jakar aikin shi …
yayi sallama ya shigo har lokacin Asiya na zawne Alhdji a kwalli TV yayi murmushi dan kowa yasan irin yadda take son Korea film
batama san ya shigo bah saida ya zawna sanan ya kwalleta yace ….
Daughter kwallo kike ne Asiya wace sai ah lokacin taga Alhadji tace Abbi ina yuni sanun da zuwa ya aiki
duk ah lokaci daya tayi wanan gaisuwar kumai cikin kulawa dan idan ba cemaka akayi Asiya bah yar shi bace toh bazaka sani !!!
dede nan hadjia Binta wato Ummy ta huto daga kichten din dan. kamar muryar shi taji shineh ta dan leko ta kuma kichten dan kayo mishi ruwa…
sai sanan kuma Abbi yace Lafiyya lau ya gida Ina Rabin Ranki haka Yake cewa Asiya idan yana son tsokanarta dan yasan tana son sunan
yana son yarinyar sosai dan randa yaji tana cewa mamarshi rabin rai yaji dadii sosai kuma yayi ta dariya su inna na cewa ….
Asiya kamm akoy wayo kiji wani suna salon yaudda….
yana tunanin kaway yaji wayarshi na kara yana dubawa sai yaga farin cikin zuciyarshi ne ke kiranshi wato Muhammad da ‘ daya tilo da Allah ya bashi….
ya daga tare da amsa sallamar sanan suka gaisa
yana cikin fira da yaron nashi Ummy ta dawoo falo da tire shake da abubuwan motsa bakin kafinta gama girkin…
Asiya nason tashi ta fita ta basu waje amma tana so ta fadawa Abbi cewa ace kowa yace babanshi yazo ah school za’ayi meeting ne akoy takarda da aka bada toh ita ta rasa inda ta saka tata… Dole Abbi ne zaije dan shi yasaka ah makarantar kuma komai idan ya taso shikeyi wanda shineh ya dawrawa kanshi haka….
nan Abbi ya juyar da wayar juwa video call lokacin da Ummy ke zuba mishi juice a kofi ayy
Muhammad ganin mahaifiyarshi sai ya kwara washe hakura yana cewa su Ummy yan soyeya
haka yaran yake ya mayar da iya yenshi tamkar abokananshi suyi raha , suyi wasa da dariya kuma yana mugun girmamasu
Ummy ta karbi wayar tana mishi mitar tsokanar ta da yayi tace Ibni yaushe zaka dawoo sawra wata nawa ne waii??? karatun nan ya isa haka gashi dady kah ya gama gina maka asibitin kah kaii kaway muke jira..
Muhammad yace sawra 2 month insha’Allah aii zaku zo celebration da za’a yi koh ???
Ummy tace insha’Allah…..
sai Muhammad yajiwo muryar asiya ba fada Abbi sakon school din su tace ta batar da takarda…
Muhammad yace
Ummy muryar wa nake jin haka??? Anifa ce !! yana nufin autar uncle dinshi dake abuja wato Habib ….
Ummy tace a’a Asiya ce …
Muhammad yace yar mai gadi Ummy tace yar Inna daii dan kasan gurin inna take kuma yar Dadyn kace ! So an riga an zama daya …
ya tabe baki dan shi sai ya lisafa so nawa yaga Yarinyar duk zuwanshi huto….
Sam yarinyar bata mishi bah gata fara kamar zabaya kumai sai iya yin …. shi duk da cewa yana cikin larabawa Algeria baya son farin mutun sosai irin farin nan cen duk da cewa shima fari amma bah sosai bah
gashi Asiya irin yaran nan ne fari fatt kamar zabaya…
Asiya taji komai dab wayar ah speaker yake…
taji haoushi sosai ita sam wanan Muhammad dinbeyi mata bah dan koh yazo hutou bata barin su hadu … haoushin take jin kamar ddan wulakancineh halinshi daya da Salma yar kayun sa dake abujaedan idann sun zo gidan lokacin nan saii sun ringa ce mata yar mai gadi saida inna ta tsawatar musu…
Asiya ta mike tace Abbi bari naje kar inna ta fara nema na dama nace nata zan taya Ummy aiki ne ..
Ummy ta tsaraf tace a’a kin daiyi kwallo dan ni banga abinda kikayi bah … sanan tayi murmushi ta huce zuwa bangaran su dan gaida Baban ta amma har yanzu tana tsoran haduwarta da Mamar ta ..