Free chapter · Read without an account
Chapter 4
by Amanarcool · MUGUN KUDURI
Amra ta yi kamar ba ta ga kowa ba, kai tsaye ta nufi ɗakinsu, ba ta ida shiga ba ta ji Abba ya ce "Amra ba ki ga baƙo ba ne? Ko ba ki lura da Alhaji ba?"
Tsayawa ta yi ta juyo, ta kalli Abba dake zaune tare da Alhaji Ataya, ɗan ɓata fuska ta yi ta ce "Yi haƙuri Abba ban kula ba ne. Da yake a gajiye na dawo." Ta yi maganar tana kallon Ataya daya zuba musu ido ita Amira ko ƙiftawa baya yi, kamar haɗin baki ita da Amira lokaci ɗaya suka ce "Sannu da zuwa Alhaji."
Washe baki ya yi kamar gonar auduga, cikin sakin fuska ya ce "Yawwa ƴan biyun Abba, kun dawo lafiya?."
Amra ba ta tsaya bi ta kansa ba ta yi gaba abin ta. Amira ce ta yi ƙarfin halin ce masa "Alhamdulillah." Ita ma daga haka ta wuce ɗakinsu.
Amira na shiga ɗakin Amra ta ja wani uban tsaki ta ce "Na rasa me bawan Allahn nan yake nufi da mu, ko kunya baya ji tsofai-tsofai da shi ya dinga kwaso jiki yana zuwa gidanmu da sunan gaisuwar sirikai. Ban da budurwar zuciya irin tasa taya zai ce yana son a aura masa ɗaya daga cikin mu? Amma ba laifinsa ba ne, fuska ya gani a gurin Abba shi ya sa har yake samun gwarin gwiwar yin wannan maganar, ni dai wallahi ko da wasa ba za a yi gigin haɗa ni da wannan tsohon ba."
Shiru Amira ta yi ba ta ce komai ba, ita kanta haushin mutumin take ji. Kuma ta lura da Abbansu a shirye yake daya aura masa ɗaya daga cikinsu kamar yadda ya buƙata, wanda ta san daga ƙarshe abin a kanta zai ƙare.
Tana jin yadda Amra ke mita, tana ta kushe shi.
Alhaji Ataya bai wani daɗe ba ya tafi, da ma hanya ce ta biyo da shi ta unguwar shi ne ya biyo su gaisa.
.....
Washe gari, misalin ƙarfe goma sha ɗaya na rana, Raheema na kwance a ɗaki sai murƙususu take yi saboda yunwa, ji take kamar an yi mata yaso a cikinta, tashi ta yi cikin ƙarfin hali, ta fake idon Inna ta fice daga gidan. Cikin sauri-sauri take tafiya, fuskarta jiƙe da hawaye. Kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci cewa gaba ɗaya hankalinta ba ya tare da ita a wannan lokacin. A daidai wani tamfatsetsen gida ta dakata da tafiyar da take yi, ta tsaya daga nesa da gidan tana ƙare masa kallo, kauda idanunta ta yi daga kallon gidan, ta sauke nannauyan numfashi, ta ci gaba da taka ƙafafuwanta cikin sanyin jiki. A hankali ta isa bakin haɗaɗɗen gate ɗin gidan, ta kai hannu cikin sanyin jiki ta danna door bell ɗin da zai sanar da zuwanta, sannan cikin sanyin jiki ta sauke hannunta ƙasa, ta sunkuyar da kanta tana jiran a ba ta izinin shiga cikin gidan. Tana nan tsaye kusan mintuna biyar shiru ba a buɗe mata ba. Ganin haka ya sa ta ƙara daga hannu da nufin sake danna door bell, sai dai kafin ta kai ga sake dannawar ta ji an ce "Who's there?"
Hakan da ta ji ne ya sa ta ɗago da kanta a ɗan razane, cikin rawar murya ta ce "Ni... ni... ce."
Shiru ta ji an yi ba a sake cewa komai ba, har ta cire ran za a sake yin magana, sai ta ji an ce, "Me kike nema a nan?."
Wannan karon a nutse ta ɗago da kanta, ta ƙurawa ƴar ƙaramar camerar da ke maƙale a jikin ƙofar ido, a hankali ta ce "Na zo gurin Baba Alaji ne."
Siririn tsaki aka yi, kafin aka buɗe mata ƙofar. Cikin sanyin jiki ta shiga cikin tafkeken gidan, tsirarin ma'aikatan gidan ne ke kai-komo a harabar gidan. Cak ta tsaya tana ƙarewa harabar gidan da ma'aikatan kallo. A ranta take tunanin ina ma a ce ita ce ta samu gatan yin aikatau a gidan. Duk da kasancewar tana da alaƙa da masu gidan, amma ta san ƴan aikin gidan ma sun fita gata da matsayi.
Cike da burgewa take ci gaba da kallon mutanen da ke ta kai-komo hankalinsu a kwance. "Raheema ke ce da tsakar ranar nan?"
Da sauri ta juya bayanta inda ta ji maganar ta fito. A hankali ta ƙaƙalo guntun murmushi ta shimfiɗa shi a fuskarta, ta ce, "Eh nice Baba Ladi, ina wuni?" Wadda ta kira da Baba Ladi ta yi murmushi ita ma ta ce, "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, ya gida? Ya iyayen naki suna lafiya?" Raheema ta ce, "Alhamdulillah Baba Ladi."
Baba Ladi ta ce, "To madalla. In ce dai ba gurin Babanku kika zo ba?" Raheema ta yi murmushin ƙarfin hali jin ta ambaci Baba Alaji da Babansu, ta ce, "Eh Baba Ladi, gurinsa na zo. Don Allah a yi min iso." Baba Ladi ta sauke numfashi a ɓoye, sannan ta ce, "To Raheema, bari a sanar wa da Hajiya."
Raheema ta jinjina mata kai ba tare da ta ce komai ba. Baba Ladi ta nufi cikin gidan, bin bayanta ta yi da kallo, kafin ta janye idanunta ta mayar da su kan ma'aikatan gidan da ke ta hada-hadarsu, Ba a ɗauki lokaci ba Baba Ladi ta dawo wajen ta kalle ta fuska ba yabo ba fallasa ta ce, "Raheema, za ki iya shiga, Baban naku ma yana ciki."
Raheema ta ce, "To na gode Baba Ladi."
Baba Ladi ta bar gurin ba tare da ta sake magana ba, ganin haka ya sa Raheema ta nufi ƙofar falon, a zuciyarta take tunanin wataƙali wani wulaƙancin aka yi wa Baba Ladi shi ya sa taga jikin matar ya yi sanyi, ta isa jikin ƙofar. A buɗe ta same ta, ba ta yi mamakin ganin hakan ba, domin ta san ba mamaki Baba Ladi aka sa ta bar mata ita a buɗe saboda kar ta yi knocking ta cika musu kunne. Bakinta ɗauke da sallama ta sanya kai cikin falon, duk da ta san ba lallai a amsa mata ba, kai tsaye ta ci gaba da kutsa kanta cikin tafkeken falon da ke ta zuba ƙamshin turaren wuta da room freshener, ga wani ni'imtaccen sanyin air-conditioner da fanka daya fara ratsa ƙashi da tsokar jikinta. A tsakiyar falon ta yi wa kanta masauki a kan lallausan carpet ɗin da ke malale a falon. Ko kaɗan ba ta yi gigin hawa manyan kujerun alfarmar da ke falon ba, domin ba ta manta irin rashin mutuncin da aka yi mata ita da Ummanta ba a zuwan su na ƙarshe da suka yi gidan ba, saboda sun zauna saman kujera, "Ku wane irin sakarci ne wannan? Wane irin abu ne haka za ku zo ku zauna mana a inda muke zama ni da ƴaƴana? Wa ya ba ku wannan izinin? Hajiya, maza kira Sama'il ya zo a fitar min da waɗannan kujerun kafin mu zauna ni da yarana mu kwashi cuta, don Allah kaɗai ya san irin cututtukan da ke jikin waɗannan mutanen. Shi dai talaka kullum burinsa ya cuci mai kuɗi saboda baƙin ciki da ciwon hassada." Ajiyar zuciya Raheema ta sauke bayan ta tuna abin da ya faru a wancan lokacin, ta tuna yadda aka sa aka fitar da kujerun falon saboda ita da mahaifiyarta sun zauna a kan ɗaya daga cikinsu.
Jigum ta yi a falon zuciyarta na mata suya. Ta ɗaga idanunta a hankali ta kalli dining area inda ahalin gidan ke zaune kaf ɗinsu suna cin abinci, hankalinsu kwance tamkar ba su lura da wanzuwarta a falon ba. A hankali ta janye idanunta daga kansu ta sauke idonta ƙasa, lokaci ɗaya ta ji ƴaƴan hanjinta na kuka, ta tuna yadda ta baro Umma a gida tana jin yunwa, yau babu abin da suka sa a cikinsu, suna kallo Baba ya bawa Saude kuɗin abinci amma su ya hana su, saboda kawai jiya ta sanar da shi abin da Umaima ta yi mata saboda su, rabonsu da abinci tun barbaɗen garin da suka jiƙa jiya da dare suka ci, ko sugar babu. Su kuwa nan ga su gabansu shaƙe da abinci kala-kala cike da nama da kalolin abubuwan sha. Hannunta ta kai kan fuskarta ta goge ƙwallar da ta ziraro mata, cikin rawar murya irin ta wanda ya soma kuka ta buɗe baki yadda ta san za a ji ta ta ce "Baba Alaji, barkanku da rana." Tai maganar a sanyaye.
Sai dai tana gama rufe bakinta aka fara tari a dining table ɗin, da sauri ta ɗaga kanta. Anisa ta gani, autar gidan, tana ta faman tari, kafin ta ankara ta ga sun nufi yarinyar suna tambayarta me ya same ta ta ƙware? Daga inda Raheema take ta ji cikinta ya ɗuri ruwa, ba ta ƙara tsorata da lamarin ba sai da ta ji muryar Anisa cikin kuka tana faɗin, "Momma, waccen ce ta ba ni tsoro. Abeg, get her out of my sight, I don't want to see her."
Anisa ta ƙarasa maganar cike da iyayi tana ci gaba da ƙaƙalo tari, da sauri suka dubi Raheema da Anisa ta nuna musu, cikin faɗa Alhaji Taheer ya ce, "Ke! Me kike a nan wajen muna tsaka da cin abinci?"
Da rawar jiki Raheema ta miƙe tsaye jikinta na karkarwa, cikin rawar murya ta ce "Baba Alaji, ban san Anisa za ta ƙware idan na yi magana ba. Don Allah ku yi haƙuri, ba da gangan na yi ba."
"Kika ce ba da gangan kika yi ba? Ƙarya ake yi miki kenan?" Momma ta yi maganar fuska a tamƙe, Nazir dake rungume da Anisa ya juyo a fusace ya watsa wa Raheema wani mugun kallo, a tsawace ya ce "Get out from here!" Ya yi maganar yana nuna mata ƙofar fita. Kuka Raheema ta fashe da shi, jikinta na ci gaba da rawar tsoro. Duk da ba ta gane abin da ya faɗa ba, ta gane me yake nufi sakamakon hanyar ƙofar da ta ga ya nuna mata.
Cikin kuka ta ce "Don Allah Yaya Nazir kar ka kore ni, wallahi taimako na zo nema gurin Baba Alaji, ku yi haƙuri. Anisa ki yi haƙuri, ba da gangan na tsorata ki ba."
Nazir da haushi ya kama shi ganin ta ƙi fita, ya nufo ta yana huci, ganin haka ya sa Raheema ta juya da sauri ta fice daga falon tana fashewa da kuka, ƙwafa Nazir ya yi, sannan ya juya ya nufi dining ɗin.
Raheema na fita ta ci karo da Isma'il a ƙofar falon, yana tare da matarsa Meenat, kaɗan ya rage jikinsu bai haɗe da juna ba, ja da baya ya yi kaɗan, yana kallonta.
Jikinta ya sake ɗaukar rawa, da sauri Meenat ta toshe hancinta tana kallonta a wulaƙance, "Ke, ba ki da hankali ne? Ke wawuyar ina ce? Ba ki gani ne da kike ƙoƙarin haɗa jikinki dana mijina? Salon ki saka masa wannan tsamin da kike yi? Dalla ɗaga ba mu guri duk kin ɓata gurin nan da wari."
Ɗago da kai Raheema ta yi ta kalle ta, ba ta ce komai ba ta raɓa ta gefensu za ta wuce, a fusace Meenat ta janyo ta da ƙarfi, ta ɗaga hannu za ta mare ta. Da sauri Isma'il ya riƙe mata hannu, fuskarsa babu yabo babu fallasa ya kalli Raheema ya ce "Yi tafiyarki kin ji."
Jikinta na rawa ta bar gurin
Meenat ta dubi Isma'il da mamaki, tun da take da shi, bai taɓa yunƙuri hana ta abin da ta yi niyyar yi ba, duk da kuwa rashin dacewar abin matuƙar zai saka ta farin ciki zai bar ta ta yi, ta ce "Honey, me ye haka? Me kake nufi da hana ni dukan yarinyar nan da ka yi? Ina ruwanka da abin da zan yi?"
Kasa yi mata magana ya yi, ya saki hannunta, ya shiga ciki. A zuciye tabi bayansa tana jin yadda zuciyarta ke bugu da ƙarfi.
....
Ƙarar kaɗe-kaɗe ce ke tashi a cikin katafaren club ɗin, mata da maza ne haɗe a tsakiyar filin suna rawa cikin baɗala da rashin kunya.
Yana zaune a wani ɓangare na musamman a gurin tare da abokansa, ya jingina jikinsa da kujera, kunnensa sanye da Bluetooth, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallon mazan dake rawa tare da mata a gurin, waƙar da ke tashi a hankali a cikin kunnuwansa ba ta hana shi jin dariyar da abokansa ke yi ba, duk da kasancewarsa a cikinsu, akwai wata irin izza da girman kai da ke tattare da shi da ke sa abokanan nasa ke jin cewa har yanzu ba su kai matsayin da za su yi masa magana yadda suka ga dama ba. A cikinsu Yazid ne kaɗai yake da damar gaya masa magana yadda ya ga dama, Ya ja shisha ya hura hayaƙin sama. Cikin isa ya kalli Yazid ya ce "Yazid, ƴan matan nan sun iya rawa fa."
Dariyar shaƙiyanci Yazid ya yi, zai yi magana kenan sai ga wata yarinya ta zo gurin tana taku ɗai-ɗai, cikin yanga ta isa kujerar dake kusa da Maleek ta zauna. Ƙanƙance ido ta yi, tana bin shi da wani shu'umin kallo.
"Sannu fa."
Ta faɗa cikin iyayi.
Wani mugun kallo Maleek ya yi mata, ya kawar da kansa.
Matsawa ta fara ƙoƙarin yi kusa da shi, da sauri Yazid ya ce "Ke! Dakata! Kar ki kuskura ki matsa kusa da shi, idan kuwa kika yi gangancin hakan, to komai ya faru da ke ke kika jawowa kanki, oya tashi ki bar gurin nan, ba ma buƙatar wanda ba mu gayyata ba a inda muke."
Kallon mamaki take bin Yazid da shi
"Da ma wanda za a gani a irin gurin nan zai iya haramtawa kansa ƴan mata ne? You see, I didn't come to your place, so mind your language."
Yazid zai sake yin magana, Maleek ya ɗaga masa hannu, da wani irin rikitaccen kallo ya dube ta.
Lokaci ɗaya ta ruɗe da ganin irin kallon da yake bin ta da shi, babu shiri ta miƙe da sauri ta bar gurin tana waiwayensa. Dariya Yazid ya saka tare da sauran abokansu.
Maleek ya yi tsaki yana faɗin "Stupid." Ya mayar da dubansa ga Yazid ya ce "Ni za a nunawa bariki? Da ta tsaya yadda na kalle ta ɗin nan ko." Ya jinjina kai yana tuna yadda ya so ya kar ta mata rashin mutunci.
"Ai ta rufawa kanta asiri ta tafi." Yazid ya ce yana dariya
Maleek ya lumshe idanunsa yana tuna wani abu, da sauri da ya buɗe su tare da duƙar da kansa yana kallon ƙasa.
Kamar wanda aka tsikara ya tashi a hanzarce ya bar gurin, yana jin su Yazid na kiran shi amma bai tsaya ba ya fita, kai tsaye gurin motarsa ya nufa, ya shiga ya fige ta da ƙarfi ya bar gurin.
Amanarcool
***