Free chapter · Read without an account
77
A irin yadda kwalliyar da aka yi wa Fullo ta canja fuskarta, da ace ta murmusa kawai, da tabbas za ta zama tamkar wata zinarar da mutum zai so ya sace ya gudu da ita, don tsoron kada wani ya riga shi samun damar mallakarta.
Siririyar fuskarta ta ƙara fitowa da wani irin kyau, da ba za ka taɓa cewa ita ce Fullo ba. Kwalliyar ta sauya mata kamanni ta hanyar da ta fito da kyawawan siffofinta, ta ba ta wata irin cikar kamala da jan hankali. Saƙi ne blue ta saka, an yi masa ɗinki na musamman, an kuma ƙawata shi da stones masu sheƙi waɗanda suka ƙara fito da darajarsa. Titi ce ta kawo kayan tun daga Abuja, kuma daga kallo ɗaya, zana san an yi sa ne musamman don wannan rana.
Sai dai duk wannan ƙoƙarin da aka yi wajen ƙawata amarya, abu guda ne ya rage ya sake fiddo ainihin kyawunta, wato murmushinta.
Ƴan uwanta da ƙawayenta su ne suka raka ta lokacin da ta fito. Maijidda ta kama ta suka yi gefe, tana jin kamar zata iya shawo kan zuciyar ƙawartata da kalmomi kaɗan kawai.
"Fullo don Allah ki daure ki yi murmushi mana. Ki kore wannan damuwar daga fuskarki. Kar ki sake yi mana irin na jiya. Kin ga yadda aka sha wahala wajen yin kwalliyar nan. Ki ɗan saki fuskarki mana, ko kaɗan ne. Babbar rana ce fa a gareki... Duk tarin mutanen nan da kike gani, duk domin tayaki murna suke anan."
Fullo ta yi ƙoƙarin bin umarninta. Ta ɗan motsa laɓɓanta, amma murmushin bai samu nasarar wanzuwa ba, kamar yadda ta yi ƙoƙarin ganin ta yi. Saboda da zarar ta tuna sakin da Turaki ya yi mata, sai fuskarta ta sake komawa yadda take.
Maijidda ta yi shiru na ɗan lokaci, ta kalleta cike da tausayi, ta sani, akwai damuwar da ƙawartata ke ɓoye mata, sai dai ba zata taɓa faɗa mata a yanzun ba, tunda ku san kwanaki nawa kenan ta bibiyarta akan ta faɗa mata matsalar, taƙi, sai idan ma ta matsa mata, kawai ta fashe mata da kuka, don haka a yanzun ma bata ta sake matsa mata ba.
Haka suka ci gaba da tafiya tare da ita har suka shiga parlon Maudo. A nan ne suka ji Daada tana ba da labari, cikin muryarta mai ƙarfi ,da ba ta san yadda za ta rage zafin kalmomi ba idan ta fusata.
"Ehh mana! Ai ni ban taɓa ganin tsohuwar banza irin wannan ba. Ke da na je asibitin ma, ban san lokacin da na tofar da yawu ba saboda yadda na ganta. Kin gan ta kuwa? A fige take kamar figaggiyar kazar da ba ta kama abinci ba."
Ta ɗan dakata, kamar tana sake ganin hoton abin da ya faru a gabanta a wancan ranar.
"Na ji haushin kaina ma. Na zauna waje ɗaya ina ta masifa, da ban je mun yi ido huɗu da ita ba tun farko. Yadda zata raina kanta! Muna haɗa ido na zabga mata harara. Na watsa mata kallon banzan da ya fi wanda take min, ta kama maganganun rashin kunya, ni kuwa ba son raini ba, da sauri na kira likita na ce masa ga sabuwar mara lafiya nan."
Daada ta ƙare maganar cikin wani irin fusata, alamar har yanzu tana jin haushin Boɗejo da rashin kirkin da ta yi musu.
Fullo bata san lokacin da siririyar dariya ta suɓuce mata ba, lokacin da suka shigo ta ji Daada na rattaba wannan bayanin, ba komai ya bata dariya ba, sai inda Daada ɗin ta ce Boɗejo kamar figaggar kaza, kuma wai ta cewa likita ga sabuwar mara lafiya nan.
Ƙaramar dariya ce, amma ta fito daga zuciyarta ba tare da ta shirya ba. Kamar yadda mutum yake iya ɗan mantawa da damuwarsa idan wani abu ya ba shi dariya ba zato, haka Fullo ta tsinci kanta tana murmushi, duk da tarin nauyin da ke a ƙirjinta.
Cikin sa'a kuwa, Nuratu ta ɗauke ta hoto a daidai wannan lokacin.
Da ƙyastawar hasken camera ɗin, Fullo ta ɗago idanunta kai tsaye zuwa inda camera woman take. Da farko ta yi kamar za ta sake ɓata fuska saboda hasken da ya ratsa ƙwayar idonta, amma sai ta ji yadda yanayin ɗaukar hoton ya burge ta. Wani irin yanayi ne da ita kanta ba ta yi tsammanin za ta iya jinta a cikinsa ba.
Sai murmushinta ya faɗaɗa. Kyawawan fararen haƙoranta suka bayyana, suna ƙara fito da annurin fuskarta. Idanunta suka lumshe na ɗan lokaci, sannan suka buɗe a hankali, ta ɗora kallonta kan wadda take ɗaukar hoton.
Wannan kallon nata yana da wani irin salo na musamman. Ba wai don ta yi wani ƙoƙari na jan hankali ba ne, a'a, kawai yadda ta ɗago fuskarta, yadda murmushin ya zauna a laɓɓanta, da yadda idanunta suka haska, sun haɗu sun samar da hoton da zai iya ɗauke hankalin duk wanda ya kalla. Kyawunta ya bayyana ne ba tare da ta nemi bayyana shi da kanta ba.
Nuratu ta sake ɗaukar wasu hotunan, tana ƙoƙarin kama wannan yanayin kafin ya ɓace. A wannan karon, Fullo ba ta iya samun ƙarfin ɓoye murmushinta ba.
Sai ga shi a cikin wannan ɗakin da ta shiga da fuskar damuwa, an samu abin da aka daɗe ana ƙoƙarin nema don kore damuwarta. Ba wata doguwar magana ce ta sa ta yi murmushi ba, ba kuma roƙo daga kowa ba. Labarin Daada ne da yanayin yadda aka ɗauketa hoto kawai, suka tsallake duk wani shingen da damuwar Turaki ta gina a fuskarta da ma zuciyarta.
Can sai aka fara tafawa, aka kuma fara waƙar da ta dace da irin tarukan nasu.
Sautin tafin hannu ya gauraya da waƙar, ya cika ɗakin da wani sabon yanayi. Damuwar da ke cikin zuciyar Fullo ta dinƙa ja da baya a hankali, tarin hawayen da suka daɗe suna cunkushe a ƙwayar idonta, na barin idonta da murmushi mai faɗi. Kuma a ɗan lokaci kaɗan, fuskarta ta manta da dukkan wani ƙunci.
GOMBE
"Ka yi wanka?"
Bello Ƙaraye ya tambayi Turaki lokacin da ya sauko daga upstairs.
Turaki bai ce masa komai ba. Ya wuce shi kai tsaye zuwa dining, tafiyarsa a hankali, har yanzu jikinsa bai gama warwarewa daga rashin lafiyar da ya yi ba. Duk wanda ya kalle shi zai gane cewa bai dawo da cikakken ƙarfinsa da kuzarinsa ba.
Bello ya biyo bayansa, shi ma ya isa dining ɗin, ya ja kujera ya zauna.
"Me za ka ci na zuba maka?"
Turaki bai ko kalle shi ba, can ya ce,"Mene ne a ciki?"
Bello ya nuna masa flasks ɗin abincin guda biyu da aka ajiye a kan dining.
"Nan fried spaghetti ce, nan kuma tuwan shinkafa da miyan agushi."
Turaki ya sauke numfashi, ya jingina kansa da bayan kujerar dining ɗin, sannan ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci.
"Couscous nake so da miyan hanta."
Bello ya zuba masa ido. Ya ɗan daɗe yana kallonsa. Daga baya ya tambaye shi, "Akwai data a wayarka?"
Turaki ya buɗe idanunsa ya watsa masa wani kallo. Kallo guda da ya isa ya nuna wa Bello, abokin nasa ba ya son silly question, ba a yanayi mai daɗi yake ba.
Bello ya ɗan gyara zamansa.
"To ni dai duk da ba a ji da ni a gidanmu, irin yadda ake ji da kai, na rantse da Allah ban taɓa shiga kitchen da sunan girki ba. Sai dai in shiga in kwasa. To tsakani da Allah, ta ina zan san yadda ake dafa wani couscous, balle miyar hanta?"
Ya ɗan karkata kai.
"Yunwar dare dai ta taɓa sa na dafa ƙonanniyar taliya. Idan kuma za ka ci irinta yanzu in shiga kitchen ɗin."
Turaki ya harare shi, ya ja tsaki mai nuna gajiyarsa da surutun da yake yi masa. Bello bai damu ba ya sake cewa.
"To ai shi ya sa na ce ka ba ni wayarka in yi downloading video. Ina ce ai kuna da komai a gidan ko?"
Turaki bai tanka masa ba. Bello ya yi shiru yana zuba masa ido. Duk ranar da za ace MT ya zama sarki, bai san ina zai kai girman izza ba.
"Yanzu dai tun da babu wani abincin da kake so, ka daure ka ci tuwon. Shi ma ai ɗan uwan miyan hantar ne. Ka ci ka ɗan samu ƙarfi kafin a kira Maama a gaya mata. Ka ga tun safe ba ka ƙara cin komai ba, kuma Dr ya hana ka zama da yunwa."
Ya zuba wa Turaki tuwon shinkafa da miyan agushi a plate, ya tura masa a gabansa. Turaki ko kallon abincin bai yi ba. Ya ɗora hannunsa a kan teburin, ya ture plate ɗin gefe. Bello ya tsaya yana kallonsa, kafin ya ɗaure fuskarsa ya ce.
"Ban da ma dai girman rashin lafiya, me zai sa in zauna ina biyewa ƙaton gardi irinka? Ehh to sai kuma girman ƴan'uwantaka. Amma ita ma gaskiya na ga za ka cutar da ni. Sai a koma abota irin ta haɗuwar gate, rabuwar bakin gate."
Ya ja tsaki, sannan ya jingina bayansa da kujera.
"Haka kawai mutum Allah ya yi masa gata, ya ba shi mace, amma ya tashi ya kora ta gidan iyayenta. Allah ma ya rufa maka asiri da wata, billahi da ka ɗanɗana kuɗarka."
Ya nuna kansa da yatsa.
"Ka bar ganin ina tare da kai, ba komai zan iya yi maka ba kamar yadda matarka za ta yi maka. Allah ya rufa maka asiri ma kwai wata, da ka gane baka da wayo. Shiyasa bahaushe ya ce gida biyu maganin gobara."
Ya girgiza kai, yana ƙara jin haushin Turaki.
"Ban da ma rashin tunani da rashin shawara irin naka! Da ka san Baffa ya yi maka gate da gidansa, ai da ka dawo sai ka ce ka mayar da ita. Da tuni yanzu kana gaban Maama, ana tarairayarka kamar ƙwai. Abincin ma a baki ake baka."
Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya sake duban plate ɗin da Turaki ya ture.
"Ni kuwa duk abinka wallahi sai dai ka ci da kanka. Ko kuma mu koma asibiti a ci gaba da zaman jinya. Ni kam na gaji da wannan gardamar taka da taurin kai."
Turaki ya ɗago kansa a hankali, ya kalle shi da wani irin takaici da ya haɗu da gajiyar rashin lafiyarsa.
"Bello, when za ka zama mai cikakken hankali?"
Bello wanda a lokacin yake kai lomar tuwo bakinsa, bai tsaya da taunawa ba kafin ya ba shi amsa.
"Ka siyo min hankalin kawai."
Turaki ya girgiza kai, ya juya fuskarsa gefe. Wani irin ciwon kai ya fara taso masa, sai dai bai ce komai ba. Ya shafa goshinsa a hankali, yana ƙoƙarin danne raɗaɗin da yake ji.
Bello ya ci gaba da cin abincinsa, yana yi masa kallon gefe-gefe, kamar yana jiran ya sake buɗe baki ya ba shi wata amsar da zai yi amfani da ita wajen ci gaba da tsokanarsa.
Sallama suka ji an yi a parlon. Bello ya kai idanunsa wajen ƙofar, sannan ya kalli Turaki da ya buɗe idanunsa a hankali. Abdulhamid ne ya shigo, yana faɗin bismillah yayin da yake ƙaraso wa inda suke zaune.
"Ku zauna." suka ce masa kusan a lokaci guda.
"A'a fa." Abdulhamid ya amsa, yana tsaye kusa da su. Ya kalli Turaki sannan ya ce, "Akwai room guda ɗaya da babu key ɗinsa."
Turaki ya lumshe idanunsa, ya ɗaga hannu ya shafo wuyansa. Ya yi kamar ba zai ce komai ba, daga baya ya tambaya,"Wanne room ne?"
"Wanda yake downstairs, wanda ake shiga ta kitchen."
Turaki ya ɗan sosa girarsa,"Bari na dubo maka."
Ya miƙe a hankali, ya nufi bedroom ɗin Ilham da ke downstairs. Yana shiga ya ƙarasa wajen madubi, ya buɗe drawer, sannan ya fara duba maƙullayen da aka ajiye a ciki.
Yana tsaye yana bincike, sai wani irin ciwon kai ya tsanantar masa. Ya dafe kansa, ya lumshe idanunsa, yana jiran raɗaɗin ya ɗan lafa.
Bayan ɗan lokaci, ya tattara maƙullayen gaba ɗaya ya fito. Ya miƙa wa Abdulhamid su.
"Ka gwada waɗannan. Ban san wanne ne na ɗakin ba."
Abdulhamid ya karɓa, ya yi musu sallama sannan ya fita.
Turaki ya tsaya na ɗan lokaci, ya shafa fuskarsa da tafin hannu kafin ya juya ya koma dining ɗin.
Bello ya bi motsin Turaki da ido. Fuskarsa ta sauya. Barkwancin da ya cika bakinsa tun ɗazu ya ɓace, sai fargaba da ya bayyana a idanunsa.
Ya dubi Turaki da kulawa, sannan ya tambaye shi cikin sanyin murya,"Dr ya kawo maka result ɗin ne?"
Turaki ya ɗan gyara zamansa, sannan ya ce, "Bai kawo ba. Ya dawo ranar, kuma sai ya tarar mun tafi hospital. But ya kira ni ɗazu ya ce she is not pregnant. Ni dama na san zance ne irin na Boɗejo kawai. Da na kusance ta ai ban bari sperm ya zuba a ciki ba."
Bello ya tallafi haɓarsa da tafin hannu, yana duban Turaki da wata irin fuska mai ɗauke da tambayoyi.
"Ɗan ƙara min haske mana MT. Ka ga ni ma na kusa shiga cikin wannan lamarin, kuma gaskiya bana so na fara tara ƴaƴa da yawa a lokaci guda."
Ya ɗan dakata, sannan ya sauya yanayin maganarsa.
"Anyway, before ka ce min ɗan iska, ni dai tsakani da Allah ban ga abin ƙi ba a tare da yarinyar nan Ilham ba, da har ka yi kuskuren sakinta, MT Mace irin cikakkun matan da ake so, wadda ta haɗa komai. Waccan kam idan ta zo sai ka sha wahalar raino, kamin jikinta ya ginu".
Turaki ya cika bakinsa da iska, ya sauke ta a hankali, sannan ya kalli Bello.
"A wurina sakin da na yi mata ba shi ne kuskure ba. Babban kuskure a wajena shi ne yadda na ke kasa riƙe sirrina. Dole sai na faɗa maka halin da nake ciki."
Bello ya ƙyalƙyale da dariya. Ya yi dariyarsa na wasu daƙiƙu, yana girgiza kai, kafin daga baya ya yi shiru ya sake kallon Turaki.
"Yanzu ma ai na san akwai abin da kake so ka faɗa min tun ranar nan, amma ka kasa. Kuma na tabbatar ba daidai ka aikata ba, shi ya sa kake shakkar faɗa min."
Ya karkata jikinsa gaba, ya ɗora hannayensa a kan dining table ɗin.
"Yanzu dai ina jinka. Me ka ƙara zuwa ka aikata ba tare da shawara ba, balle zurfin tunani? Domin na lura da kai tun ranar da masu jeren kayan nan suka zo, ka bi ka rikice kamar mara gaskiya. Na san akwai wani abu da kake ɓoyewa."
Turaki ya dafe kansa. Ya runtse idanunsa na ɗan lokaci, yana so ya tattara ƙarfin halin da zai buƙata wajen faɗin abin da ya daɗe yana danne wa a zuciyarsa.
Bai yi saurin magana ba. Ya ɗan zauna cikin shiru, yana jin nauyin abin da yake shirin faɗa wa Bellon. Amma da ya ga ba zai iya ci gaba da ɓoyewa ba, sai ya buɗe baki ya bayyana masa abin da yake ransa.
Bello ya saurare shi har ya gama.
Sai dai kalaman Turaki suna ƙarewa, fuskarsa ta sauya gaba ɗaya. Ya zuba masa ido tamkar wanda bai yarda da abin da kunnuwansa suka ji ba.
"Totally MT Ba ka da hankali!"
Ya faɗi hakan cikin mamaki.
"What are you telling me? Kai wai mistake ɗin farko ba ya zama maka izina sai ka aikata wasu da yawa? Har yanzu fa ba ka fita daga matsalar da kake ciki ba, shi ne za ka ƙara saka kanka a wata? Ko kuwa ɓacin ran iyayenka ne ba ya damunka?"
Ya bugi dining table ɗin da tafin hannunsa, ya nuna Turaki da yatsa, fuskarsa cike da fushi.
"Sam babu hankali a tare da kai. Abubuwan da kake aikatawa, masu lafiyar ƙwaƙwalwa ba sa yinsu."
Turaki ya ture yatsan da yake nuna shi da shi, yana kallonsa cikin ɓacin rai.
"Kada ka ƙara nuna ni da yatsa, kuma kada ka ƙara ce min ba ni da hankali. Damuwata nake faɗa maka a matsayinka na aminina. Mafita nake so ka taimaka min mu nema, ba wai ka tsaya kana faɗa min mara daɗi ba."
Bello ya ƙulu ya ce masa.
"An faɗa maka ba ka da hankali, ko ka yi abin da zai sa a kira ka mai hankali ne? Har yaushe za ka zauna ka yanke irin wannan ɗanyen hukunci a kan yarinyar da gaba ɗaya ba ta cancanci haka daga gare ka ba?"
Tsaye ya miƙe, ba zai ma iya zaman ba saboda ɓacin rai. Ya yi tattaki, sannan ya sake juyowa ya fuskanci Turaki.
"Kai ba za ka zauna ka yi shawara da mutum ba, sai bayan ka aikata abin da zai zamar maka damuwa. Kai ko wani ne ya ce ka saketa, ai sai ka zazzage shi. Amma saboda toshewar basira irin taka, ka aikata abin da ba ka auna sakamakon da zai biyo baya ba."
Muryarsa ta ƙara ɗaukar zafi yayin da yake ci gaba.
"Ka tuna, da ba don taimakon Allah da taimakon yarinyar nan ba, da yanzu ka zama tarihi. Ko kuma da har yanzu kana can cikin lalurar da aka kasa magancewa. Asiri fa! Asiri ta dinga ɗaukewa akanka MT! Ka fahimci abin da nake tuna maka kuwa?"
Ya ɗaga hannunsa, yana nuna Turaki da yatsa, saboda fushin da ya kasa dannewa.
"Akwai wanda zai iya saka kansa cikin haɗari haka ne, just to save someone's life? Ka yi tunani mana da hankali. Sunanka kawai ta sani MT! Ba ta san komai game da kai ba, amma ta taimaka har kake raye yanzu da ikon Allah. You disappointed me."
Ya girgiza kai, yana kallon Turaki cike da takaici. Takaici ya sa Bello yin shiru. Ya rasa ma a wane sashe zai saka Turaki a marasa hankali, balle ya san irin shawarar da ya kamata ya ba shi. Ya daɗe yana kallonsa, kafin ya ƙyasta yatsunsa biyu kamar wanda ya tuna wani abu, sannan ya ce masa.
"To bari ka ji na faɗa maka. Fushin Baffa a kanka ba komai ba ne idan aka kwatanta da fushin Mum da za ka gamu da shi. Sarai ka san tana son yarinyar nan. Kuma bari in ƙara faɗa maka abu ɗaya, ba zan waiwayeka ba a lokacin da ka faɗa cikin cakwakiya ta biyu. Ban san ka aikata ba, kuma ba ka nemi shawara ta ba kafin ka aikata. Don haka, kada ka kuskura ka neme ni."
Ya ƙare maganar cikin tsananin ɓacin rai, sannan ya juya ya fice daga wurin ba tare da ya waiwayo ba.
Turaki ya bi bayansa da kallo, yana da buƙatar ya tsaya, ya ba shi aron nutsuwarsa don ya fahimce shi, to amma ba zai dakatar da shi ba.
Ya san Bello ya fusata, kuma duk yadda ya so ya yi masa bayani, ya fahimci cewa a wannan lokacin babu maganar da za ta iya sauya tunaninsa akan yadda ya fahimta ɗin.
Ya zauna shi kaɗai na ɗan lokaci, kafin ya miƙe ya nufi ɗakinsa.
Abin da yake so a yanzu shi ne ya je gidansu. Ya gaji da zaman shi kaɗai, ya gaji da tunanin abubuwa masu yawa a cikin kansa. Shi bai sani ba, bai san da gaske Baffa yake yi masa ba akan kar ya ƙara zuwar masa gida har sai ya huce, to zuwa yaushe kenan? Har sai zuwa yaushe Baffa zai sauko daga dogon fushin da yake yi da shi?
Yana so a saurare shi, Mum da Maama, su yake da buƙatar su saurare shi. Baffa kuma ya kulle ƙofar.
Washegari da safe, Turaki yana kwance a ɗakinsa lokacin da aka murɗa handle ɗin ƙofar.
Ɗan motsin ƙofar ya sa shi buɗe idanunsa. Ya juya kansa a hankali zuwa wajen ƙofar, yana son ganin wanda zai shigo.
Ganin Maama, sai ya yi saurin miƙewa ya zauna.
Ta ƙaraso ciki kusa da gadon, zuciyarta cike da tausayinsa. Ganin ɗanta a haka ya taɓa mata zuciya, musamman yadda ya rame bayan rashin lafiyar da ya yi. Ta zauna kusa da shi, ta ɗora hannayenta a kafaɗunsa, sannan ta tambaye shi cikin sanyin murya.
"Ya ƙarfin jikin naka?"
"Da sauƙi sosai."
Ta ci gaba da kallonsa, tana nazarin yanayin jikinsa. Kumburin da ya yi a lokacin da yake fama da rashin lafiyar ya kau gaba ɗaya, jikinsa ya koma yadda ya kamata. Sai dai ramarsa ce ta yi yawa, har ta sa fuskarsa ta sauya kamanni.
Maama ta sauke numfashi, sannan ta tambaye shi, "Bello ya ce min ba ya gari, shi ya sa na taho. Ina drugs ɗin naka?"
Turaki ya kalleta, ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce, "Ƙarya yake yi. Fushi yake da ni, shi ne ya tafi."
Maama ta girgiza kai, tana murmushi kaɗan.
"Allah dai ya kyauta muku. Anjima ne za ku shirya ai."
Ta miƙe ta nufi teburin da ke tsakiyar ɗakin. Ta ɗauko magungunansa, ta dawo ta zauna kusa da shi. Ta ɓallo magungunan, ta miƙa masa su, sannan ta taimaka masa ya sha.
"Ka sha don ka ƙara jin ƙarfin jikinka. Anjima akwai dinner. Su ma suna kan hanya sun taho da Fullo. Amma ba nan ɗin za su kawo ta ba kai tsaye, za su sauka a wurinmu. Bayan an dawo daga dinner, sai mu kawo maka ita. Hakan ai ya yi ko mai babban suna?"
Bai san abin da maganartata ta haifar masa ba, kuma bai iya cewa komai ba.
Maama ta ci gaba da magana kamar ba ta lura da shirun nasa ba.
"Ka ga ba ka da lafiya, ni kuma ban zauna na yi shawara da kai ba. Amma ai ba komai."
A lokacin ne Samha ta shigo, tana ɗauke ne da basket ɗin kayan abinci, ta wuce ta ajiye a gefen gadon. Bisa umarnin Maama, ta zuba abincin a plate, sannan ta fita ta barsu.
Maama ta karɓi plate ɗin, ta gyara zamanta kusa da Turaki.
Kamar wani ƙaramin yaro, ta fara ciyar da shi da kanta. Ba ta damu da shekarunsa ba a wurinta, ɗanta ne da ya yi rashin lafiya, kuma tana son ta tabbatar ya ci abinci sosai kafin lokacin da za ta bar wajensa.
Turaki ya yi shiru yana cin abincin, lokaci-lokaci yana kallon fuskarta. Yana jin wani irin sanyi a zuciyarsa, sai dai a gefe guda, akwai abubuwan da suka cunkushe masa ƙirji, waɗanda suka hana shi jin daɗin kulawar Maama yadda ya kamata.
Maama ta shirya masa ruwan wanka mai ɗumi a cikin bathtube, ta tabbatar komai yana nan kafin ta bar shi ya shiga wankan.
Bayan ya gama wanka, ya fito ya shirya kansa. Da ya gama saka kaya, ya nufi hanyar fita daga ɗakin, sai ga Maama ta dawo.
"Ai ba fita za ka yi ba. Koma ka kwanta ka huta."
Turaki ya tsaya yana kallonta.
Ta ƙaraso kusa da shi, ta gyara masa wani ɗan abu a jikin rigarsa, sannan ta ɗaga kai ta kalle shi cikin kulawa.
"Alfarma ɗaya nake so a wurinka, mai babban suna. Ka cire damuwa, don Allah. Ka ɗauko rigar walwala da farin ciki ka saka. Yau babbar rana ce a gare ka. Ranar karɓar zaɓinka."
Turaki ya sauke idanunsa ƙasa. Ya buɗe baki kamar zai ce wani abu, amma sai ya kasa.
Maama ɗin kuma ta fahimta, hakan yasa ta shafo gefen fuskarsa ta ce,"Menene? Akwai magana a bakinka, ina jinka, ni ce a gabanka, Maamanka Muhammad."
A sanyin murya ya ce, "Maama, Baffa..."
Ta ɗaga hannu ta dakatar da shi.
"Sau nawa zan faɗa maka? Idan dai batun Baffanku ne, ka ajiye shi a gefe. Kai fa kujera ne a wurinsa. Kana zaune zai neme ka."
Ta ɗan dakata, tana kallonsa da tabbaci, kamar tana son ta tabbatar kalamanta sun samu karɓuwa a ruhinsa da gangar jikinsa.
"Duk wannan hawa saman da ya yi na ɗan lokaci ne. Tsohuwarsa na hucewa, shima zai huce. Space kawai yake buƙata. Kai ma kuma da ma kana buƙatar space ɗinsu."
Ta yi murmushi mai ɗan ɗaci, sannan ta ƙara da cewa, "Mu kanmu da ka gani, ba ya kula mu. Jiya ma ya bar mana gidan ya kaɗa inda ba mu sani ba."
Turaki ya ja doguwar ajiyar zuciya. Ya so ya yi magana, amma kafin ya samu damar faɗin abin da ke ransa, Maama ta sake katse shi.
"Bello zai zo maka da kayan da za ka saka anjima. Khalil kuma zai riga ku zuwa wajen dinner ɗin."
Ta ƙare maganar, tana sake kallonsa da irin kulawar da ta saba nuna masa, wannan kallon mai aminci, da ta banbanta shi da irin wanda duk take yi wa sauran Yaran nata. Duk wata kalma da take faɗa masa, tana faɗa masa ne da son ta tabbatar cewa komai zai daidaita a ƙarshe.
Ya gyaɗa kansa kawai kamar yaro, bai ce komai ba, har ta yi masa sallama ta fi ce.
******
Ƙarar zuge ƙofar gate ɗin gidan ta haɗe da hayaniyar motocin da suka bar harabar gidan. Sai dai a kunnen Fullo, ba ƙarar gate kawai ta ji ba ce, kamar an rufe wata ƙofa ce a rayuwarta, wadda ita kanta ba ta san ta yadda za ta sake buɗewa ba.
Tana tsaye ne a bakin tagar ɗakin, tana kallon harabar gidan. Sanyin iskar dare da ke ratsowa ta window yana sauka bisa fuskarta a hankali, ɗauke da wani daɗin ƙamshi da ya gauraye da yanayin garin, wanda ya sa take jin daɗin tsayuwarta a wurin. Hasken fitilun da suka ƙawata compoud ɗin gidan, ya sa wajen ɗaukar ido, har ma ba za ka yi tunanin cewa dare ne ba.
Kuma yadda iska ke busa fulawowin suna kaɗawa, shi ya ɗauke hankalinta, har take jin hakan na tafiya da kaɗaicin da aka tafi aka barta a ciki.
A lokacin da bata sani ba, ta ji wannan tarin ruwan hawayen da yake cikin idonta, wanda yaƙi ɗaukewa tun bayan tafiyar kowa, yana barin cikin idanun nata.
Idanuwanta suka lumshe, ta zuƙi iska sosai. Ta so ta tsaya a hakan, sai dai ƙarar buɗe gate da kuma sautin tsayawar mota da ta ji, shi yasa ta buɗe idanuwan nata babu shiri.
Akan motar da Turaki ta sauke su. Ta zubawa motar ido. Tana kallo ya zuro ƙafarsa guda ɗaya waje, ya ɗan jinkirta wajen fitowarsa daga motar. Irin yadda take kallon nasa, da jiran ganin fitowar tasa, sai ta ji kamar dama tana cikin jiran dawowar tasa ne.
A maimakon faɗuwar gaban da take tunanin zata riski kanta a ciki idan ta ganshi, a duk lokacin da aka kawota gidansa, sai ta ji saɓanin hakan. Domin kuwa wani irin abu take ji yana ratsata, wani sabon yanayi da bata taɓa jin irinsa ba.
Idanuwanta suka lumshe sannan ta buɗe su a hankali, a hankalin da suke sauka akan Turaki, wanda a lokacin ya fito gaba ɗaya daga cikin motar.
Abin mamaki, ganin sa bai haifar mata da faɗuwar gaba irin wadda ta yi tsammani ba. Maimakon haka, sai ta ji zuciyarta ta matse, wani irin matsewa da ba zata iya kwatantawa ba. Kamar dai akwai wani abu a cikin ƙirjinta da ke ƙoƙarin fashewa.