Free chapter · Read without an account

Chapter 21&22

by A'ISHATU OUMBHANAT · HAƊUWAR ƘADDARA

     💦HAƊUWAR ƘADDARA💦
               (Hatsari da Rai)

Story and writing by ✍️
AISHA (Oumbhanat)✍️❤️‍🔥

Follow my WhatsApp channel 
***

Follow this link to join my WhatsApp group 
***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W\.A)*
*Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi*.✏️

Wannan shine Littafina Na farko dan haka sabuwar marubuciya ce, idan Anga kuskure Aciki to Ayimin Uzuri. 

FREE BOOK 

                 ~●~●~●~●~●~●~
       BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

PAGE 21

           ●○●○●○●○●○●○●○●

Yammaci ne mai cike da daddaɗar Iskar sanyin da ya fara shigowa yanayin ya yi matuƙar daɗi a jikin mutane suna ta walwala.

Yana zaune akan darduma da Nanah ta shimfiɗa masa ya yin da ita kuma take kan kujera irin ta zaman tsakar gida suna fira cike da farinciki ya kalle ta fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce.

“Please mana gimbiyata dan Allah ki ce kina sona mana, wallahi na kasa jurewa fa, jan ran ya isa haka Nanah sai yaushe za ki faɗamin na fita a fargaba .” Hamza ya yi magana fuska a marairaice.

Murmushi ta yi tana kallonsa sai kuma ta ɗauke kai daga garesa ta ce.

“Ai wannan zaman da muka yi ma ya isa ya amsa maka tambayar ka, dan da ba ka samu karɓuwa ba da ba zan saurare ka ba ma.”

“Alhamdulillah! Kai amma na ji daɗi, yau dai na samu nutsuwa na fita daga fargabar rasaki, kin ga yanzu sai ki ba ni damar ganin Baba ko?.”

“Haka da wuri?.” Ta fada ido a waje alamar mamaki.

“Eh mana to me za'a jira Nanah ko so kike in tsaya kallon ruwa kwaɗo ya yi mun ƙafa?.” Ya faɗa yana kallonta.

“To ai na ga ba mu wani saba ba, ba ka san komai a kaina ba haka ni ma ban san ko mai a kanka ba ta ya za ka fara maganar aure yanzu?.”

“Kin ga Nanah magana ce ta bincike, dama ina kika taɓa ganin an yi aure ba'a san juna ba dole wannan gaɓar za ta zo.” ya ɗan numfasa kafin ya ɗora da.

“Dama tun da fari na faɗa miki sunana Hamza Muhammad Garki, ni ɗan jihar Jigawa ne iyayena da sauran ƴan uwana duk suna can a garin Garki, ni Jam'in ɗansanda ne ina aiki a Ɗorayi division sannan ina business ɗin shigo da motoci, matata ɗaya da yara biyu mata, to kin ji waye Hamza ko?.” Ya tambaye ta fuskarsa ɗauke da murmushi.

Ita ma murmushin ta yi tana girgiza kanta.

“Sannan ta ce toh shi kenan zan faɗawa Baba sai ka ba ni lokaci.”

“Ok, gobe Mahaifiyata za ta zo ganin likita in sha Allah zan yi magana da ita duk yanda muka yi zan faɗa miki ta waya.”

“To ba damuwa Allah ya kawo su lafiya ya kuma ƙara mata lafiya.”

“Ameen ya Allah na gode.” ya faɗa cike da farinciki, dan abu ne da bai saba jin sa a bakin Samira ba.

Sallama ya yi mata ganin magriba ta kusa ya tafi bayan ya ajiye mata laida cike da kaya.

                ■□■□■□■□■

Tunda ta shigo gidan idanu ya dawo kanta, musamman Mama da Inno wadda ta zubawa laidar hannunta ido.

“Kawo nan in ga me ya kawo miki, Allah yasa ba irin mijin Uwani ba ne marowaci uban mammaƙo.”

Faɗin Inno a lokacin da Nanah ta ƙaraso inda suke zaune, miƙa mata ledar ta yi ba tare da ta ce komai ba.

“Lalalah!, wannan ai shi ne mijin da ake fata irin wannan kyauta haka oh ni Inno jikata ta yi goshi.” Ta ƙarashe da rangaɗa guda.

Gabaɗaya hankalin kowa ya dawo kanta ganin yanda take fito da kayan kwalliya da turaruka da kayan ciye-ciye.

“Ahh wannan saurayi na Hadiza irinsa ake nema Allah ya tabbatar da alkairi.”

Gabaɗaya aka amsa da amin ban da Mama wadda baƙincikin duniya ya taru ya yi mata katutu arai, in ban da yaƙe ba bu abun da take yi, a ranta tana ayyana ‘wallahi duk yanda zan yi sai na raba su yanda Zainabu ta hanani farinciki a gidana ita ma sai na ƙunsa mata akan ƴaƴanta ba su isa su fi nawa gidan miji ba wallahi’ sannan ta saka hannu ana ta ɗaga kayan ana sam barka.

            ~♡~♡~♡~♡~♡~♡~

JAZY

Gudu yake zubawa akan machine ɗin Sa kamar zai tashi sama, wani irin taƙuƙun baƙinciki ne yake cin ransa, ‘me zan wa matar nan da zai bar mata tabon da baza ta taɓa mantawa ba kamar yanda ta yi wa rayuwata?’ Ya ayyana hakan a ransa.

Ƙarawa machine ɗin gudu ya yi yana ƙara shiga cikin wani daji, ya yi kusan tafiyar minti 40 daga cikin gari kafin ya isa gaban wani
 incomplete building ya tsaya, kashe machine ɗin ya yi ya sauko ya turo shi daga cikin ginin.

Wani irin gini ne mai lunguna da yawa duk ta inda ka shiga akwai ƙofofi wasu a kulle wasu a buɗe, tafiya ya fara yi bayan ya kafe machine ɗin,ya dinga shiga lungu nan yana wuce ƙofofi har ya kai gaban wata ƙofa wadda take buɗewa ƙwayar idonu, idonsa na hagu ya saita a wajan take ƙofar ta yi ƙara kaɗan sannan ta buɗe.

Duhu ne dunɗum ba'a iya ganin ko tafin hannu, wani madanni ya taɓa a take haske ya mamaye ko ina sai ga wani ƙaton ɗaki mai kama da lap ne ya bayyana, table ne a jere da yawa ko wanne ɗauke da sinadaran gwaje gwaje da na haɗa magunguna iri-iri, wajan coffee maker ya je ya haɗa ya dawo kan wata kujera da ke gaban wani table da laptop ya fara dannawa da sauri.

Dannawa yake kamar ana yaƙi saboda yanda zuciyarsa take tafasa, dama idan irin hakan ta faru nan ne wajan da yake zuwa ya samu sukuni.

Ta shi ya yi ya fita daga nan ya shiga wata ƙofa da ke can bayan ginin wadda ake buɗewa da thumbprint, babban ɗan yatsansa ya saka a mabudin take ƙofar ta buɗe ya kunna kai ciki wani dogon lungu ne mai tsawo tafiya ya fara yi yana wuce wasu ƙofofi kafin ya kai ƙarshen lungun ya sha kwana ƴar tafiya kaɗan ya yi ya isa inda yake son zuwa nan ma dai sai da ya buɗe ƙofar da ɗan yatsa sannan ya shiga.

Wani ƙaton ɗaki ne cike da mutane suna ta aikin haɗa ƙwayoyin magani kala-kala, tunda ya shigo ake gaishe shi hannu kawai yake ɗaga musu har ya isa inda ake jere kwalayen magungunan da aka gama haɗawa.

“Barka da zuwa shugaba.” faɗin daya daga cikin masu aiki a wajan.

“Barka dai Amiru, an gama haɗa komai.?”
Jazy ya tambaya . 

“Eh shugaba, yanzu za'a fara fitar da su.” ya ba shi amsa.

Jinjina kai Jazy ya yi yana nufar inda ake zubawa a cikin kwali, wato manyan kwalaye ne na magani wanda ake yin su bisa ƙa’ida amma acan ƙasan kwalin haramtattun ƙwayoyin saka maye ne masu Hatsari, idan aka zuba su a can ƙasa sai a rufe su da kwalin kamar yanda ƙasan ko wanne kwali yake daga sama kuma a saka magunguna masu kyau dan ɓoye waɗancan.

Wani ɓangaren kuma garin maganin suke haɗawa ana zuba su a cikin robobin powder fara wanda ke ɗauke da stickers na powder kamar dai powder ta gaske.

Jinjina kai ya yi ganin suna aikin yanda ya dace, sannan ya juya ya fice daga sashen ya koma inda ya fito ɗazu.

Zama ya yi akan kujerar yana dannawa wata number video call, hoton wani babban mutum ne ya bayyana akan screen ɗin yana faɗin.

“Babban yaro ya ake ciki ne kun kammala aikin?, kasan fa ana buƙatar kayan nan da gaggawa dan kuɗinsu sun fara shigowa shigowa.”

Kallonsa ya ɗan yi na wani lokaci kafin ya buɗe baki ya ce.

“Wannan karon kaya ba za su shigo ba sai ka gama biyan kowa haƙƙinsa, ba zan ci gaba da saka yara aiki ba bayan bakwa basu abun da yake haƙƙinsu ne, ka turo min kuɗina yanzu na sallame su, dan komai ya kammala aikawa ya rage.” ya ƙarasa maganar yana yamutsa fuska shi a dole ya yi magana mai tsawo.

Dariya mutumin ya yi sannan ya ce.
“Baka da matsala yanzu za ka ji alert har da ƙari wannan karon zan yi muku saboda kun gama aiki akan lokaci.”

Yana kaiwa nan ya datse kiran, mintuna uku bayan nan wayarsa ta yi ƙara, kallon inda take ya yi kafin ya saki guntun murmushi ya miƙe ya fice a ɗakin.

Wato Jazy ba ƙaramin guru ba ne a wannan harkar, ɓangaren pharmacy ya yi karatu sannan kuma ya yi wasu courses akan ilimin haɗa magunguna da sinadarai, da ace ana bawa irin su dama da tuni ƙasarmu ta rage yawan shigo da magani daga waje, amma ga shi a karan banza wasu ɓatagarin shugabanni suna amfani da irin su wajan lalata goben matasanmu…✍️

OUMBHANAT✍️❤️‍🔥

    💦HAƊUWAR ƘADDARA💦
              (Hatsari da Rai)

Story and writing by ✍️
AISHA (Oumbhanat)✍️❤️‍🔥

Follow my WhatsApp channel 
***

Follow this link to join my WhatsApp group 
***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W\.A)*
*Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi*.✏️


FREE BOOK 

                 ~●~●~●~●~●~●~
       BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

PAGE 22

                 ☆☆☆☆☆☆☆☆☆

SAMIRA 

Tunda ta ji su Inna za su zo ranta yake a jagule ‘Ita fa wallahi ba ta son irin wannan abun abar mutum ya wataya da mijinsa amma dan masifa sai an zo an takura mai, wai wani ganin likita duk tarin Asibitocin da suke a Jigawa sai an zo Kano kawai dan tsabar sa ido’ ta ayyana hakan a ranta tana jan tsaki.

“Lafiya, kike tsaki?.” Hamza da ke gefenta a kwance ya tambaya.

“A'a ba komai cikina ne ya ɗan murɗa min.” Ita sam ta manta yana gefenta tsabar ɓacin rai.

“Ok, ki tashi mu je na tayaki gyara gidan ke sai ki yi girkin tunda kin ga da wuri za su zo.”

Ya faɗa yana kallonta a lokacin da ya sauko daga kan gadon sannan ya juya ya fara tafiya zuwa falo.

Yaƙe ta aro ta yafawa kanta kafin ta yunƙura ta miƙe tsaye ta bi bayansa ganin har ya kai ƙofar ɗakin ‘Aikin banza wai dan uwarsa za ta zo ne zai taya ni aiki munafircin banza kawai’ ta faɗa a zuciya tana fita daga ɗakin.

Cikin lokaci ƙanƙani suka gyare gidan tsaf yana ta ƙamshin turaren wuta kafin Samira ta shiga kitchen ta ɗora tuwon shinkafa miyar kuɓewa ɗanya a cewar ta shi suka saba ci, har ta kammala ta gyara kitchen ɗin tana faɗin.

Ai wallahi in dai da wannan marar kunyar yarinyar aka zo ita ce za ta na gyara kitchen ɗin nan ba zan wa wata ƙatuwa aiki ba.

Wayarta da ke kan fridge ce ta yi ƙara Mommy shine sunan da ya bayyana akan screen ɗin ɗagawa ta yi ta kara a kunne tana faɗin.

“Mommyna fatan kun tashi lafiya.”

“Lafiya lau Samira ya jikokina suke.”
Aka faɗa daga ɗayan ɓangaren.

“Suna lafiya Mom.” Ta bata amsa.

“Yauwa dama faɗa miki zan yi bikin ƴar gidan Hajiya Hamida jibi ne fa.” Faɗin Mom.

“Umm ai Mom da ƙyar idan zan samu zuwa, wai Innarsa ce za ta zo yau tun safe yake saka ni aiki wallahi.” Ta ƙarashe maganar a shagwabe.

“Ahh lallai ba shakka yanzu akan uwarsa za ta zo ya mai da mun ke boyi-boyi, lallai Hamza ya kai in da ya kai, to kina ji na ko, wallahi zuwa biki babu fashi, ki faɗa masa ma tun yau kada ma sai ranar ya ce bai san zancen ba.”

“To Mommy zan faɗa masa.” daga nan suka yi sallama.

maganganu ta fara ji daga falon hakan ke nuna baƙin sun iso, tabe baki ta yi sannan ta goge hannunta ta nufi hanyar fita daga kitchen ɗin.

A falon kuwa wata ƴar kyakkyawar dattijuwar mace ce matsakaiciya, sanye da hijabi milk colour kamilalliyar fuskarta ɗauke da murmushi, tana riƙe da hannun yaran da suka rungumeta ta ƙarasa shigowa falon, wasu matasa biyu mace da namiji suna biye da ita, zama suka yi a kujerun da suka zagaye falon.

Durƙusawa Hamza ya yi a gabanta fuska cike da farinciki ya fara gaisheta, amsawa take ita ma da farincikin ganin ɗan nata mai matuƙar yi mata biyayya, tana tambayar sa ina Samira.

Kafin ya ba ta amsa sai ga ta nan ta fito daga kitchen ɗin fuska ba yabo ba fallasa ta dafa hannun kujera tana gaishe da Innar, da murmushi ta amsa tana tambayarta suna lafiya.

Matasan ne suka gaishe su suka amsa Hamza yana tsokanar macen da faɗin.

“A'a kaga budurwar ƙauye yau ta shigo birnin Kano, to ya kika ga garin?.” Ya ƙarasa da murmushi.

“Kai Yaya ni ce budurwar ƙauyen, Inna kin gan shi ko?, wallahi garinmu ba ƙauye ba ne ba.” Raihanan ta faɗa, ƙanwarsa ce ƴar abokiyar zaman Inna amma a hannun Innar ta taso tun daga yaye ta riƙe ta saboda Ita ba ta da yara mata duk maza ne ƴaƴanta.

Dariya suka fara yi mata ganin yanda ta kwaɓe fuska kamar za ta saka kuka.

kallon Samira Hamza ya yi wadda ta gama cika famm ya ce.

“Ki kawo musu ruwa mana Samira.”

“A'a ƙyaleta bama jin ƙishin ruwa sai dai ko anjima.” Inna ta faɗa da fara'a da alama dai ita ɗin mai fara'a ce dama.

Hira suka shiga yi ana dariya in ban da Hajiya Samira da take bin su da idanu da kuma murmushin yaƙe idan an sako ta a maganar.

            ♤♤♤♤♤♠︎♤♤♤♤♤

MAMA

Wuni ta yi zuciyarta cunkushe da baƙinciki da hassada, a ganinta yaranta suka dace da wannan abun ba ƴaƴan Zainabu ba, dan haka ko da gari ya waye ta shirya ta fita sai gudan aminiyarta Rakiya

Zaune suke a ɗakin Rakiya wanda ba komai a ciki sai wata tsohuwar katifa da wata yagaggiyar ledar tsakar ɗaki sai tarin kayan sakawarsu a jibge.

“Wallahi ba ki ga abun da ya kawo mata jiya ba kaya ne masu tsadar gaske, kwana na yi ban yi barci ba ina tunanin mafita.” 

Mama ta faɗa tana kallon ƙawarta wadda take ta taɓe baki kamar ta ga kashi.

“Yoh Hajara yanzu me zan miki, tun farko sai da na baki shawara amma kika sa ƙafa kika shure, sai da abu ya kwaɓe sannan za ki zo gareni to in miki me?.” Rakiya ta faɗa tana watsa hannaye gaba.

“Kefa tsiyata dake kenan ana ga gabas kina ga yamma, tunda kika ga na zo da ƙafata ai mafita nake nema.” faɗin Mama kenan tana haɗe rai dan ta ji zafin maganar Rakiya.

“To kin amince a je wajan Malam na hayi kenan, sai ki tanadi ƴan kuɗaɗenki a hannu muje ko gobe ne.” Rakiya ta bata amsa tana kallonta.

“To shi ke nan, kin ga har Inno yanzu ta fara mantawa da tsanar da ta yi wa Zainabu saboda ta ga abun duniya wallahi ba ki ga rawar jikin da take ba jiya da ganin kayan nan.”

Rakiya ta yi carab ta karɓe zancen da faɗin. “Yo ke Hajara wa yaƙi abun duniya, ai wallahi ko ni ce ke zama zan na dangwali arziki, wa yaƙi banza.” Ta ƙarasa magana tana dukan cinya.

Mama ta taɓe baki a sanda ta mike tsaye tana faɗin.
“Ai kuwa baƙinciki bai barni na karɓa ba da aka ba ni, sai Habiba ce ta riƙe duka ta haɗa.” Ta faɗa tana dosar ƙofar gidan Rakiya dan komawa nata gidan.

“To ai kin ji wa yake fito da baƙar aniyarsa a fili ai sai ki yiwa kanki sagegeduwa. 

Dawowa ta yi bayan ta raka Mama ƙofar gida tana faɗin.

Haka za ki ƙare in dai muna tare bazan bari kiyi abun arziki ba Hajara.

          ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤

NANAH 

“Ni kuwa Nanah ina kika samo wannan me kuɗin haka.” faɗin Inno tana cin biscuit ɗin da aka kawo jiya tana kaɗa kai tsabar daɗinsa.

Dariya duka ƴan ɗakin suka saka ana ta tsokanar ta wai santi take yi.

“Ku bari ƴaƴan nan wallahi biskit ɗin ne da ɗan karan daɗi ba irin wanda na saba ci ba ne.” Innon ta ƙara faɗin hakan tana kallon Nana alamun jiran amsa take yi.

“Wallahi Inno ban san a ina ya ganni ba kawai na ga ya zo gidan nan ne, kuma fa Inno ɗan sanda ne.” Nanah ta bawa Inno amsa.
 
“Fakare Inno ta yi da biscuit a hannukamar ba ta gane me aka ce ba, Sai can ta yi firgigit ta ce na shiga uku, ɗan sanda kika ce Hadiza, yo ke meye gamin ki da ɗan-doka.” Ta faɗa tana kame haɓa alamar mamaki.

“To Inno meye da ɗan sandan na ga duk kin wani firgita kamar zai kama ki?.” ɗaya daga cikin yaran gidan ta faɗa mai suna Shafa’atu.

“Ke kuwa Shafa ɗan sanda fa, waɗan nan mugayen mutanen mene abun so a wajansu.”

“Kai Inno a dinga kyautata zato ba duka aka taru aka zama ɗaya ba ko ina akwai na ƙwarai.” Faɗin Salima ƙanwar Shafa’atu.

“Eh kuma hakane fa, to Allah yasa wannan yana cikin na ƙwarai.”

Da ameen suka amsa gabaɗaya, sannan suka ɗora da hirarsu.

“Yauwa Habiba anjima zamu je ki rakani gidan Aunty Binta zan ƙarbo wani style ɗin ɗinki a wajan Hanifa.” Nanah ta faɗa tana danna wayar hannunta.

“Ok, ba damuwa Allah ya kaimu.” Faɗin Habiba.

“Ameen.”
          ◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇

RAUDA

“Yaushe kika zama Addicted da kayan maye haka Rauda?.” 

Mommy ta faɗa tana riƙo hannayen Rauda.

Kallon Mommyn ta yi kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce.

“An daɗe Mommy tun ina school ne, friends ɗina na ga suna sha shi ne ni ma na gwada dan na ji meye suke ji idan sun sha, daga nan kawai na fara.” Ta fada ba tare da wata fargaba ba.

Girgiza kai Mommy ta yi ranta cike da ƙunci tana kallon Raudan ta ce.

“Amma kin san hakan haramun ne a daddini ko, Allah ya haramta shan duk wani abu da zai gusar da tunanin ɗan-adam, haka kuma ya tanadi azaba da zai wa wanda suka mutu ba tare da sun tuba ba kina so ki kasance ɗaya daga cikin waɗan nan mutane ne Rauda?, sannan shan kayan maye yana ƙeƙashe zuciya ta zama ba ta tsoron Allah bare ɗan adam, sannan ba ki da lokacin ibada a nutse saboda koyaushe ba kya cikin hayyacinki.” Ba ta jira ta yi magana ba ta ɗora da cewa.

“Sannan ko a Al’adance zubar da ƙimar kanki ne a ganki kina tafiya cikin maye ba tare da kin san irin abun da kike aikatawa ba, babu wani mutum da zai ƙara kallanki da daraja daga ranar da ya san kina shan kayan maye, sannan ko a lafiya ma shaye-shaye na da matuƙar illa ga lafiya, yana lalata Hunhu (lung) da Hanta haka kuma yana taɓa zuciya, da karya ƙarfin garkuwar jikin ɗan-adam daga ƙarshe ma ya taɓa ƙwaƙwalwa ka haukace gaba ɗaya.”

Ta numfasa kafin ta ci gaba da magana.

“Ba burgewa ba ce abun da kike yi face cutar da rayuwarki da kuma tozarta mu iyayen ki.”

Gabaɗaya jikin Rauda ya yi sanyi, yau ɗaya maganar Mahaifiyarta ta ratsa jini da jijiyar jikinta karo na farko da ta ɗauki aniyar gyara rayuwarta.

Ɗagowa ta yi idonta cike da ƙwallah tana kallon Mommyn wadda ita ma hawaye suka cika mata idanu,sai kawai ta rungumeta suka fashe da kuka su duka.

Sai da suka sha kukansu kafin Mommy ta rarrashi Rauda tana faɗa mata maganganu masu daɗi na irin tanadin da Allah ya yi wa bayinsa masu tuba har hankalinta ya kwanta ta ƙudiri niyyar daina shaye-shaye✍️😓

OUMBHANAT✍️❤️‍🔥

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol