Free chapter 路 Read without an account

Chapter 25

by Gidan Iko 路 GARWASHI

*Wata rana komai zai wuce kamar ba'ayi ba. Wata ran ba wata ba wata ran ba duniya ce makaranta, wata ran Wanda ya San ka ma babu bare wanda ya San rayuwar ka, Allah ka sa mu aika alheri mu ruski alheri, alheri ya zamo makomar mu*


_Complete din littafin garwashi 1k ne ***_


*Gidan iko*

...............Na samu motar garin imo Amma kasancewar nayi Rana yasa na samu motar Babu kowa sai mutum Biyu kawai kasancewar Asubanci motar ke yi wurin tafiya shiyasa Wanda yazo da Rana Dole sai yayi jira Amma da Yake Ni ba sauri nake ba sai kawai na fada motar ban wani damu da Rashin yawan mutanen ba 

Ina zaune abayan motar Ina tunani Wanda Yake ta fassara min abubuwa masu tsanani Akan ba fa lallai na dawo na samu Maazi Nkem ba gashi Kuma na tafi ba tare da nayi musu sallama ba bare na fada musu zanje na karbi umarnin da suka bani tun farko  Amma Kuma da na tuna Dan Uwana Emmanuel yasan da tafiyar tawa shi zai fada musu na tafi wurin Gibson din in cika musu burin su kamar yadda suka bukata daga gareni tun farko duk da nasan ba wani burgesu zanyi ba tunda na Riga da na Bata Rawa ta da tsalle na Kuma zubar musu da garin su Wanda ba zai kwasu ba sai da kasa

Ina zaune cikin mota Ina ta faman tunananuka har mutane suka Soma shigowa motar don mun Kai mu takwas saura kadan kenan motar ta cika sai Kuma naji zuciya ta na gargadi na Akan abinda nake kokarin yi wato zuwa gidan yarima Gibson har ma na yarda yayi min ciki indawo sai na tuna nifa a yanzu ba yaren Gibson bace Kuma ba addini Daya nake dashi ba idan ban manta ba Umar ya fada min musulunci Bai yarda da Zina ba Kuma abinda nake kokarin aikatawa Zina ce haka Kuma ba ayiwa kowane irin abin halitta biyayya don sabawa Ubangiji kowaye kuwa ko da sun hada da iyaye ne Wanda a yanzu nake kokarin kyautatawa sai Kuma kyautatawar tayi karo da hanin Allah to Dole abar kyautata musu a kyautatawa Ubangiji don Haka sai kawai na fito daga motar wadda saura mutum Daya ta cika 

Dan kamashon Yana fadin duk Zaman da nayi na kusan awa biyu ban kosa ba Sai yanzu da motar ta kusa cika?
Ban tanka mishi ba na hawo napep na dawo gida Ina zuba tagumi sai Kuma zuciya ta ta fada min inje wurin Umar in bashi hakurin wulakancin da Amaka tayi mishi don Haka sai na dauko key din motata na fice Ina fita na zurma hijabi na na nufi kasuwa


Umar ya tarbeni Yana fadin Wai lafiya duk na Rame Haka? Don Ni ban San nayi wata Rama ba inda Kuma na warware mishi dukkan abinda ya faru tun daga Kan Al adar mu ta zaman daki har zuwa inda ake yau na Amaka dake gaba Dani da Kuma bakin cikin abinda yayiwa Maazi Nkem dalilin zuwa gadon Asibiti duk dai Akan Rashin bawa yarima Gibson hadin Kai


Umar yayi shiru Yana tunani kafin yace min
"Gaskiya ne abinda kikayi baya daga cikin musulunci musulmi ya kusan ci Zina Allah yace karma a kusance ta bare a aikata ta Amma Kuma su iyaye fa ko yaya suke Dole ne ayi musu biyayya Justina sai dai irin wancan Umarnin da suka bada in dai yayi taraiya da umarni ko Hani na Ubangiji to ba a kallon nasu na Ubangiji ake kallo misali idan Ubangiji yace suka ce kar ayi to sai ayi saboda Ubangiji ne yace ayi . Haka Kuma idan Ubangiji yace abari shima ko sunce ayi to Kar ayi saboda Ubangiji ne yace abari Amma yanzu ya Zama Dole ki koma garesu ki bi duk hanyar da Zaki bi don ganin kin daidaita dasu kin kuma kyautata musu Ubangiji da kanshi yace a kyautatawa iyaye Zaki Zo kan ayar da ta Fadi hakan ki Kuma fahimce ta


Nayi shiru ina sauraren shi inda Kuma na Gane indai hanyar da zamu zauna lafiya ce da Amaka da Maazi Nkem Zan Nemo da kaina to Bata wuce karbar yarima Gibson ba Wanda Kuma a yanzu tazarar mu take da nisa don Haka sai fada mishi Babu wata hanya a yanzu da zata daidaita Ni da su Amaka face yarda da Gibson har ya kunzuga min ciki Wanda zasuyi alfahari

Shima Bai bani goyon bayan hakan ba Amma Kuma ya fada min lallai lallai na Nemo duk hanyar da zata daidaita Ni da su Amaka ko da ba wannan bace don fushin iyaye hadari ne sosai da Haka nayi mishi sallama na taho inda Kuma na hadu da makel wani abokin Sony ya Kuma ganni cikin zurmemen hijabi inda na tabbatar da sai ya kwarmatawa Sony saboda ya taba cewa Yana Sona nace ya fita daga hanyata saboda Yana shaye shaye Kuma na taba Jin Sony yace har fashi da makami makel din yanayi shiyasa babu Ruwana dashi kuma ko yanzu din da muka hada ido dashi da sauri na dauke kaina na wuce na barshi yana min Rakiya da ido

Ina dawowa gida na samu Amaka da Maazi Nkem an sallamo su daga Asibitin don Maazi ya samu sauki Sosai 
Na zube Agaban shi Ina mishi sannu da jiki Yana kallo na Amaka kuwa tace na tashi a gaban shi Kuma tunda gani na Yana neman kashe mata miji ya Zama Dole nayi ta Zama daki matukar Maazi Nkem Yana gida Wai Kar ya ganni ciwon shi ya tashi Dole kuma na zabi zaman dakin kamar wata mayya indai Maazi Yana gida to Ni Ina daki har makaranta ma Amaka ta hanani zuwa Wai Kar tsautsayi ya sa na fito ko na dawo mu hadu da Maazi Nkem tunda zaman gida na ke so to sai nayi ta Zama a daki tunda yanzu Babu damar ta fita sai ayi ta nuna ta da hannu da Baki ana fadin tayi karya Wai tace yarta zata auri Dan gidan igwai Amma gashi an koroni daga gidan igwai


Ina daki zaune Babu abinda nake sai salla da sauraron karatun Alkur ani in Kuma Ina son debe kewa sai na kunna TV a dakina nayi kallo Wanda nafi son kallon Nigerian film Wanda nake ta Allah wadai da wasu Al adun namu da har ake gwada su a TV

Ina zaune Ina kallo sai kawai ganin Sony nayi ya fado dakina Yana Huci kamar wani gamsheka ya cakumo Ni ya fito Dani ya zube Ni a gaban Amaka dake ta cika saboda fushi

Na Soma Rabawa Amaka da Sony kallo don ban San Kuma me za ace nayi ba inda Kuma tamkar Amaka ta karanto abinda ke zuciya ta ta hanyar cillo min wayar Sony da tayi tana fadin duba min hoton cikin wayar Nan ki gani ki kuma fada min wacece a cikin hoton?

Na dauki wayar Ina Kai kwayoyin idanu na akan fuskar wayar inda nayi Arba da hotona cikin hijabi har kasa  inda Kuma gabana ya amsa tabbas tawa ta sameni tunda wannan hoton ya shigo wayar Sony har Yana gwadawa Amaka


"Makel ne ya turowa Sony wannan hoton yace ya ganki a kasuwa cikin wannan abin na hausa Man bana bukatar ki fada min komai tashi kawai ki fito min dashi wannan kayan na hausa man in kuwa ba Haka ba yanzu ne Zan saka Sony ya daka min ke tunda Ni kin Raina Ni
Na Mike babu gardama na dauko hijabin na Mika ma Amaka wadda ganin hijabin yasa ta fasa kuka tamkar wadda aka dadawa duka Wai na ganin hijabin ne

Sony ne ya fita da hijabin Ina kallo ya kyasta mishi wuta ya kone inda Amaka ke ta Rafsa kuka Wai nafi karfin ta Kuma Ni Zan kashe ta da Bakin ciki

Araina nace Ashe haka ake fin karfin iyaye? 
Amaka ta cewa Sony Kar ya sake Maazi Nkem yaji wannan zancen don Kar ciwon shi ya tashi inda ya so ta barshi ya jibgeni Amma tace ya barni ta kusa ta laance Ni


Kwana Biyu da faruwar hakan sako ya Riski su Amaka da Maazi Nkem cewa yarima Gibson Yana Asibiti babu lafiya Wai babu sunan da Yake Kira sai na Justina saboda ba da wasa Yake sonta ba Kuma Raba sun da igwai yayi shine da yayi dalilin da ciwon zuciyar shi ya tashi har yakai shi gadon Asibiti Yana neman macewa shi yasa likitan dake kula dashi yace lallai a kawo mishi wannan Justina din don Akwai Rawar da zata taka wurin samun saukin shi............................




Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran


Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI馃拑馃徔

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol