Free chapter · Read without an account
4. The Evening Hangout
by Zainab · TSAƘANINMU
TSAKANINMU
Kwana biyu Jawahir babu inda take zuwa har makaranta ma tayi missing lectures nata guda biyu.
Da Abba ya tambaye ta ya makaranta kwana biyu bata tafi ba tace mishi bata da lectures.
Kuma abinda aka mata a gida har yanzu bata dena jin zafin shi ba. Kuma babu yanda zata yi ne shiyasa take gaida Yaya Khalifa saboda idan dai ta gan shi dole ta gaida shi bata isa ta wuce ya wuce babu magana ba.
Tana cikin kuka ranar ta kira Ashraf take faɗa mishi abinda ya faru. Shiru yayi yana sauraron ta be ce tayi shiru ba. He let her be herself. He let her vent her anger. And that's one of the reasons why they are still the best of friends.
Dawowar shi kenan a gida daga wurin aiki. Kwantawa yayi a gado ya rufe idanun shi. Tun lokacin da ta kira shi tana mishi complain abinda aka mata gida yake son mata magana he'd like to take her out amma aiki ya mishi yawa kuma yanzu ya lura he's not getting out of that too much work phase anytime soon. So he'll just have to squeeze time and give them that time. He'd love to be the person to help clear her mind.
Wayar shi ya jawo daga gefen shi a gado ya kira ta. Muryar shi very husky tana ɗagawa yace "Can I have you at The Nordic, Jawahir?"
"The Nordic?"
"Yeah, at 5 PM"
"Okay, I'll see to it"
"It's just an evening hangout. You look so down to me these days. I'll want you to be that vibrant Jawahir again"
Murmushi Jawahir tayi tace "Thank you, Ashraf. I'll be there"
"Thank you"
Ajiye wayar shi yayi yana kwance be tashi ba.
Intercom na ɗakin shi aka kira ya tashi tsaye yaje ya ɗauka.
"Your favourite food is at the dining, Sir"
"I won't be available. Tell Ammi to keep the fruits for me but not the food"
"Okay Sir"
"Thank you" yace tare da ajiye intercom ya wuce bathroom domin yin wanka.
Be wani jima a bathroom din ba ya fito ya shirya cikin denim trouser da Black v-neck t-shirt da baƙin takalmin shi na 'under armour'.
Makullin motar shi ya ɗauka ya fito daga ɗakin shi. Ɗakin Ammi ya fara wucewa, daga ƙofa yace mata "Ammi zan fita"
"Ina zaka tafi? An faɗa min kace ba zaka ci abinci ba. Ba yanzu ka dawo daga aiki ba?"
"Ammi zan je The Nordic ne with a friend"
"Da sai ka kira kace kar a dafa abincin yanzu anyi wasting abinci kenan"
Shiru Ashraf yayi, Ammi ta sake ce "Bana so ana wasting abinci anyhow Ashraf. Ba kyau fa"
"Ammi ayi haƙuri"
"Haƙuri na shine kaje ko spoon uku ne kayi tukuna se ka tafi"
"Okay Ammi in sha Allah"
Wucewa Ashraf yayi be tsaya ko ina ba se a dining. Sphagetti ce irin manya manya da pepper soup na kifi. Zama yayi ya fara ci da zafin ta sosai daga gani ma se da ya kusa isowa gida aka dafa. Yaci abincin kaman yanda Ammi tace sannan ya tashi ya koma inda take ya ƙara mata sallama ya wuce zuwa The Nordic.
The drive to The Nordic was serene yana tuki yana tunani har ya isa.
Parking motar shi yayi ya fito ya wuce ciki be tsaya nan haraba ba. Kaman yadda waje yake da green plants da ya ƙawata wurin, haka ma ciki yake ɗauke da kujeru da table ash masu kyau wanda mutum yake zama very comfortable idan ya zauna. Da akwai green plants a ciki yasa wurin ya ƙara ƙawatuwa.
Zama yayi a table ɗaya, ya ɗan jira minti biyar amma be ga Jawahir ba. Wayar shi dake ajiye a table ya ɗauka ya tura mata text. A daidai lokacin ita kuma ta shigo ciki ta ɗan ɗaga idanun ta tana neman table nashi. Ganin shi be mata wuya ba saboda yanda wurin yake neat and not crowded.
Hannu ta mishi waving cikin farin ciki tun kafin ta ƙarisa inda yake. Murmushi Ashraf yayi da ya bi lips nata ya gane harda kiran sunan shi tayi a yayin da ta waving mishi hannun ta. Ƙarasowa inda yake tayi ɗauke da murmushin akan fuskar ta.
A zaunen da yake suka yi hugging juna ta zauna a hankali daura dashi. Tana sanye da baƙin doguwar riga na yadi wanda bayi da kwalliyar komai, plain ne. Se kuma mayafin ta shima baƙi irin yadin ta ta yafa tun daga saman kanta jelolin shi guda biyu na sauka a each side na kafaɗar ta.
Fuskar ta bata da komai se kwallin dake cikin idanun ta se kuma lip gloss da ta shafa a lips nata.
"Thought you won't make it"
"And here I'm" ta faɗa cikin murna. Murmushi Ashraf yayi ya kuma nodding kanshi.
"Ina ji na rasa kanki kwana biyun nan shiyasa nace why not go to The Nordic?!"
"I appreciate it. Truly, Ashraf. Thank you for this"
Girgiza kai yayi sau ɗaya yace "Don't mention, Jawahir.
Shiru kowannen su yayi se kuma tace "You look modern and......" rufe idanu tayi ta buɗe tana yin fari da idanun ta tana neman kalmar da zata yi amfani da ita wurin bayanin yanda yayi kama "You know those fair guys that are neat and handsome. Yes, that's the look. Thank God you don't look Asian today"
Dariya Ashraf yayi sosai yace "You have never told me that I look like one of them Asians"
"You look like them but sometimes"
"You don't like it?"
"To me, you're more handsome when you look like our men"
"Our men!" ya kwaikwaye muryar ta tayi dariya
"Me zaki ci? zan fito fa haka nan ban ci abinci ba Ammi tace bata so a mata wasting abinci"
Murmushi Jawahir tayi tace "Se da kaci ka fito kenan"
"Toh Ammi tace kar ayi wasting abinci"
Wani murmushi Jawahir ta sake yi kamar wata me tunanin wani abu tace "Ni bana jin kewar mahaifiya ta. Ban san dalili ba"
"Saboda baki san ta bane ba, Jawahir. Baki yi rayuwa da ita ba. Kuma Abba da duka Yayun ki sun maye miki gurbinta"
Gyaɗa kai tayi tana me yarda da abinda yake faɗa IImata "Mutum yana kewar abinda ya saba dashi ne"
"Ohh! Shiyasa nake kewar Yaya Hamdan da Aunty Madina"
"Shiyasa kike kewar su, Jawahir"
"Yaya Hamdan yace min zasu zo gida wannan Eid"
"Zaki bi su ne idan sun zo?"
Rolling idanun ta tayi tace "Nutrition and Dietetics ɗin kuma fa?"
"Gashi kuma kina aji biyu a second semester naku"
"Yawwa, kaga, ana maganar shiga aji uku kenan. But I really miss them especially Yaya Hamdan. Daga shi se Yaya Rashid kaɗai ke kauna ta a gidanmu se Abba na kuma. Nasan Yaya Khalifa ne ya haɗa mu da Abba shekaran jiya"
Ajiyar zuciya Ashraf ya sauke yace "A wani wuri wannan hoton bashi da matsala. Kin san muna da mabanbantan al'adu da addini"
"That's the norm fa. Yaya Khalifa is just....." kaɗan tayi tsaki tace "Ban san abinda yake damun shi ba"
"I'm sorry you went through that phase. Now, what'd you eat?"
"I'm full fa"
"Ai kuwa baki isa ba. Na kashe kuɗin mai na nazo nan mu haɗu dake kuma ki ƙin cin komai. Ni bari na zaɓa miki abinda zaki ci. Kar ki ce Ashraf ya cika ki da surutu ya bar ki da yunwa"
Dariya Jawahir tayi sosai shi kuma ya kira waiter yayi order beef suya kebabs da cocktail.
Bada wani jimawa ba se ga waiter yazo da order'n Ashraf.
"I'm treating Jawahir today!" Ashraf says with a big smile on his face
"Yeah, thank you, my good friend"
"I hope this treat is healthy enough?"
"It's healthy"
"Toh kar kice ba zaki ci ba saboda baya bada lafiya"
"Ai baku da hutu dani tunda nake karantar Nutrition and Dietetics"
Murmushi yayi yace "Idan kika gama, zaki yi aiki a asibiti ne?"
"I really don't know. Amma idan asibiti zanyi aiki, then I'll go to Nizamiye. A chan kaga ina kusa da Yaya na, Yaya Rashid"
"I thought outside Abuja!"
Dariya suka yi su biyu tace "Se na zauna kusa da Yaya na kuma, Yaya Hamdan"
"Of course, you get it. But on a serious note, Jawahir. I thought you have bigger dreams"
"I have big dreams, Ashraf. Even my brand was once upon a time a dream. So after school, I'll maybe go to Nizamiye or be a private consultant on Dietetics"
"That's the Jawahir I know. So eat"
Murmushi tayi ta fara cin suya kebabs ta sha cocktail kaɗan saboda ya mata sanyi sosai.
Bayan sun gama da order'n su, Ashraf ya kira waiter yazo ya kwashe kayan.
"Thank you for having me, Ashraf. It's a pleasure sitting here at The Nordic with you. I like the atmosphere. It feels warm and serene"
"Anything for you, Jawahir"
Ashraf yace se suka tashi tare. Side by side suke tafiya har suka fito daga cikin The Nordic zuwa haraban. Jawahir ta tsaya a kafaɗar shi wurin tsawo saboda itama tana da tsawon ta daidai.
Har wurin motar ta ya raka ta.
"Take care of yourself, Jawahir. Thank you for coming"
Ashraf ya faɗa ya kuma placing a kiss on her forehead.
"Thank you for treating me"
"See you some other time" yace tare da rufe hannun shi ya nuna mata knuckles nashi itama ta rufe nata hannu suka haɗe knuckles nasu as a way of their own greeting and goodbye. Se bayan Jawahir ta shiga motar ta tukuna Ashraf ya shiga nashi ya wuce shima.