Free chapter · Read without an account
03...
by Zainab B. adam · SID
sake tasiri cikin zuciyarta, Bayan wasu ’yan mintuna, ta kai duba ga Inspector Deo wanda ya shigo parlon ya nemi gurin zama saman soba haɗe da tattara hankalinsa gareta, sannan ya buɗe littafin da yake riƙe da shi
“Ki daina damuwa da kanki yanzu Ina son ki gaya min komai daga farko, exactly yadda abin ya faru Kada ki ƙara ko ki rage wani abu”
Jiddah ta ɗaga idanunta masu nauyi zuwa gare sa, ta share hawayen da suka taru a gefen idanunta kafin ta girgiza kai
“Zan yi hakan” Inspector ya dora da cewa, “Kin san matar da muka samu?” “I don’t even know her, yallaɓai Nima haka na samu gawar ta cikin gidan nan” deo hesitated for seconds looking at her kafin ya sake cewa
“Where have you been dis night?” jiddah tace “munje asibiti nida mijina” “are U sure?” ta girgiza masa kanta cike da Gwarin gwiwa “ “Da wane lokaci kuka dawo?”Jiddah ta shiga tunani kafin ta amsa “Wajen ƙarfe 8:30”“Kusan tara kenan?” “haka ne yallaɓai” “ shi kuma mijin naki fah?” tace muryar da al’amun tsoro mun samu rashin fahimta Daga baya ya tafi” “Ya tafi ina?” cewar Inspector dake cigaba da kallan ta ta amsa masa da “Switzerland” “Shi kaɗai?”
“Eh, shi kaɗai ya tafi” “da Wane lokaci ya fita daga cikin gdn nan?”Jiddah ta yi shiru tana ƙoƙarin tuna lokacin “Ban san exact time ba Amma bayan tafiyarsa, lokacin da zan kira waya, na duba agogo na ga ƙarfe tara da minti goma”Deo ya ɗaga kansa daga llittafins “Bayan fitar sa meya sake faruwa?” Jiddah ta soma mgn “Na baro ɗakin sama na koma ɗakina” Inspector ya gyada kai “Bayan nan fa?” “Bayan nan na fito ina neman abin da zan ci Kasan cewar ban girka komai ba Na shiga kitchen daga nan na shiga store ɗin domin ɗaukar abin da zan girka” “Me kika je store ɗin nema?” “Noodles” ya ɗan ginjina kai bayan wani 'kc ya jefa mata tnby “Kin taɓa ganin matar nan kafin yau?” Jiddah ta girgiza kai nan take “A’a Ban taɓa ganin ta ba” “Sure?” “ very sure” Deo ya ɗan kalleta kafin ya ci gaba “Ki gaya min exactly yadda kika gano gawar”
jiddah ta runtse idanunta na ɗan lokaci kafin ta buɗe su “Na shiga store ɗin ne domin ɗaukar abin da zan girka Ban lura da komai ba har na yi tuntuɓe da wani abu Da na duba sai na gan ta kwance” “me kika bayan kin ganta ina nufin Kinyi ƙoƙarin taɓa jikinta ne?” “A’a Ni kaina ban da nutsuwa a wannan lokacin Na bar kitchen ɗin gaba ɗaya” “Bayan kin fito, kinyi kokarin sanar da wani abinda kika gani misali shi mijin baki ko jami’an iyan sanda?”
ta girgiza masa kanta hadi da cewa “Na kira sister ɗina Halima sede ban samu damar sanar da itaba duk da na kiran ta ne dan na faɗa mata kwatsam naji motar jami ai sunzo”yay shiru kamar me nazari sanna yace “Her name is Halima?” ya sake cewa “ but why don’t u call ur husband first?” jiddah tace “ na Kira Amma Bata reaching” Deo ya ci gaba da rubuce-rubuce na ɗan lokaci kafin ya sake kallonta “Bayan mijinki ya fita, babu wani mutum da ya shigo gidan?” Jiddah ta girgiza kai “Gaskiya babu wanda ya shigo” “Are you certain?” “ na tabbatar da abinda na faɗa” deo ya ɗan yi shiru kafin ya sake cewa “Shin akwai wani da yake da access zuwa gidan nan?”Jiddah ta ɗan yi jim kafin ta amsa “Masu aikin gidan da guards…
amma ban san ko wani ya shigo ba” Deo ya rubuta wannan ma “Kin ga mijinki ya bar gidan da idonki?” “ na gani yallaɓai ya” sake cewa “ “Kin san wanda ya san cewa zai tafi Switzerland yau?” Jiddah ta girgiza kanta haɗe da tabbatar masa bata sani ba Deo ya kalli agogon hannunsa sannan ya sake komawa kan Jiddah “Jiddah!! akwai wani abu da kike ganin ya kamata ki gaya mana tun yanzu?” Jiddah ta ɗaga idanunta, cike da damuwa “Babu… ban san komai ba game da wannan matar ba”
Deo ya kai duba ga Constable ɗin dake tsaye kusa da ƙofar, sannan ya rufe littafinsa “Okay, For now I need you to remain here while we complete our initial enquiries Kada ki bar gidan sai mun gama da ke” Jiddah ta yi saurin kallonsa a lokacin da yake mikewa “Yallaɓai… kuna zargina ne?” Deo ya yi shiru na ɗan lokaci “Ba na cewa ke kika yi komai ba Amma kin kasance mutum ta farko da ta gano gawar Saboda haka bayaninki yana da muhimmanci” Daga nan ya juya ya bar parlorn Jiddah ta dafe kanta tana kallonsa har ya fita..
A wajen kitchen kuwa, jami’an binciken sun ci gaba da aiki, An killace store ɗin, babu wanda ake bari ya shiga ba tare da izini ba Ana ɗaukar hotuna da bayanan abubuwan da ke wajen, yayin da officers suka fara tattara bayanan guards daban-daban Jiddah dake zaune shiru, tana jin tambayoyin Inspector Deo suna sake maimaituwa a cikin kanta, Ba a ce ita ce ake zargi ba Amma yanzu ta fahimci cewa duk wani ƙaramin bayani game da wannan dare na iya zama muhimmi a binciken…
Daren ya ja sosai A hankali gidan ya koma cikin wani irin shiru, sede a wannan karon ba shiru na yau da kullum ba ne, Fitilun police suka ci gaba da haskawa a wajen compound ɗin, yayin da jami'an da ke wurin suke gudanar da aikinsu, Inspector Deo ne tsaya a gefen corridor yana sauraron bayanin wani officer Daga baya ya dubi Diesel
“Ka tabbatar an killace wannan bangaren, Kada wani ya shiga sai jami'an da aka ba izini” Diesel ya gyada kai hadi da barin wajen a wannan lokacin wani officer ya iso da gaggawa wajen yana duban deo
“Inspector, Detective Inspector yana kan hanya” Deo ya ɗan yi shiru kafin ya amsa “Good Ka ba shi duk bayanan da muka samu zuwa yanzu”
For a few moments, wata motace ta shigo nan compound ɗin Wani matashin mutum ne ya fito daga ciki, sanye cikin kayan aikin sa, ID card dinsa maƙale jikin sa wanda hakan yay nuni daga Shashi buncike yake hesitate for a couple of time looking at d house kana ya huce Kai tsaye inda deo suke tsaye da constable
“Detective Inspector Daniel” “Inspector Deo” Cewar Daniel ya fada ayayinda yake gyara tsayuwar suka yi musabaha kowanne fuskar sa da annuri “Give me everything you've got,”
cewar Daniel cike da tarin nutsuwa, nan deo ya fara basa bayanan da suka haɗa ciki harda na guards lokacin da suka kira police, yadda aka gano gawar da kuma bayanin farko da Jiddah ta bayar Daniel ya saurara ba tare da katse sa ba “Where is the woman who found the body?” “ She is setting inside” Daniel nodded hade da sake kallan gdn, “anyi Mata tambayoyi ne?” “Initial questions only” deo ya Gaya,“Alright We'll speak to her again later For now, keep her separate from the other witnesses”
Deo ya gyada kai “Understood” kai tsaye Daniel cikin gdn ya shiga yana kai duba ga masu daukar bayanai nan wani officer daya fito daga kitchen ya nufo sa da cewa “we have recovered a two mobile phone from d scene” “ whose phone?” Ya tnby, Jami in ya dubi jiddah dake zaune tare da matan kafin yace “ d one is for her but the other na mata shiyar ne” jiddah ta ɗago kai nan take “ was it found near d body” ya faɗa yana nuna wayar jiddahn yace “ nooo…Sr min sameta me a kitchen” Daniel ya girgiza kai kafin ya sake cewa “ bagged nd recorded?” “ exactly Sr” ta Kai duba ga wayar ta dake hannu officer lkc kankani taji kirjinta ya mata nauyi bata da wani abu zargi amma me zasu bincika aciki….??
A compound kuwa Fitilun suna nan ayanda suke mark da jaxon sunyi tsaye suna kai kawo tsakanin jami’an kafin mark yace “reports sun fara cika gdn wanna lamarin ya daure mun kai ba iya matar gdn ba munkan mu zasu zarge mu ba zasu gyale mu ba cikin Binciken su” jaxon ya sauke ajiyar numfashi kafin yace “ nasan daga nan zuwa safiya lbr ya sauya salo se yanzu naji dama bamu kira police ba” mark ya Masa wani kallo kafin yace “ lefin waye ai duk laifin kane alalle ka dage aiga irin ta nan ba..” yay saurin yin shiru ganin wani officer yayi inda suke yace yana duban su “ me kuke tattaunawa kuma?” Cike da gabble Jaxon ya soma mgn “ nothing yallaɓai” “ in yallaɓai ya fito zaku fadi yanda akai” jaxon ya zare ido yana duban mark “ yallaɓai iya gske mu kenan ba musan wani abu ba bayan wanna” officer din ya huce ya bar su nan suna ta maganganun.
Da gari ya fara wayewa, sannu ahnkl labarin ya fara fita daga cikin gidan zuwa wajen gdn, gdjen dake da kusanci dasu suka soma fahintar abinda ke faruwa har zuwa wanna lkcn Motocin police suna nan tsaye a wajen babban gidan, Wasu daga cikin ma'aikatan dake aiki a gdn sun fara fitowa, amma officers suka hana su shiga wuraren da aka killace, wata mota ce tsaye nesa da gate din gdn daga nan wata ta biyo bayan ta, in few minutes Masu daukar hoto suka fito suka shiga tnby jami'an dake tsaye bakin gate din
“ what’s happening here? Is it true someone has died inside the house?” “Is the owner involved?” tnbyoyin da suke yi kenan amma officers suka cigaba da dakatar dasu daga shiga, cikin mintinan da basu huce talatin ba ƴan jaridu daga sassa daban daban sukai wa gdn tsinke sede har zuwa lkc police didn’t allow Dem to reach inside, tana tsaye gaban bayan labulen parlon tana kallan tarin Mutanen dake wajen gate, wanda awannan karon ba wai police take tsoro ba tana tsoron abinda duniya zata fara zargi akan tane….