Free chapter · Read without an account
Chapter 29
💦HAƊUWAR ƘADDARA💦
(Hatsari da Rai)
Story and writing by ✍️
AISHA (Oumbhanat)✍️❤️🔥
***
***
https://www.arewapen.com/u/aishatuoumbhanat42
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W\.A)*
THE STRONGER'S WRITER'S TEAM 🌟
~●~●~●~●~●~●~
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
PAGE 29
~~~~○○○○○~~~~~~
NANAH
Jugum-jugum suke tafiya ba me magana daga can dai Amira ta kasa haƙuri ta kalli Nana cikin sanyin jiki ta ce.
“Gaskiya Aunty Nana kin iya ganganci, banda jawa kai masifa uban me ya kai ki mai da masa raddi a haka ma dube shi ƙato balle kuma ɗan daba.”
“Nima banda kartawa babu abun da cikina yake tsorona daya azo da daddare a farke mana ciki mu shiga uku.”
Wannan magana ta Habiba ta ƙarasa tsinke ɗan zaren nutsuwar da Nana ta fara samu ganin sun yi nesa da shi ba tare da ya biyo su ba.
Ji Aunty Habiba da jawo masifa ɗan Allah ku rabu da ni na ji da abun da yake damuna, duk yanda kuke ganin hatsarin mutumin nan ni na san fiye da haka wallahi.” Nana ta fada cikin sanyin murya.
A haka dai suka ƙarasa gida ba wadda ta faɗi abun da ya faru har dare ya yi kowa ya nemi makwanci.
Dare ya tsala amma Nana ta kasa barci sai juyi take, gabaɗaya jin ta take yi a tsorace bata san dalili ba amma gabanta sai faɗuwa yake.
Wayar ta dake ƙarƙashin filo ta zaro dan duba lokaci ƙarfe 03:34am na dare, miƙewa ta yi ta fita ta ɗauro alwala ta hau darduma ta fara jero nafila da roƙon Allah ya tabbatar da alkairi a cikin rayuwarta.
—----------–—————
MAMA
02:43am
Gabaɗaya wannan dare ta yi sa ne cikin tunanin abun da suka tattauna a wajan Malam, zagaye ɗakinta kawai take cikin neman mafita.
Ita fa bata son Zainabu da ƴaƴanta musamman Nana da tafi tsana sama da sauran ba tare da wani dalili ba sai son zuciya.
Tunani take taya za ta ɗauki warin takalmi ba tare da an gane ba? ‘Sai dai ki ɗauke duka idan yaso sai ki jefar da ɗaya ki kai masa ɗayan’ wani sashe na zuciyarta ya bata amsa.
Jinjina kai ta yi cikin gaisuwa da shawarar da ta yanke.
~~~~~~~~●●●●●~~~~~~~~
ZINATU
Waya ce maƙale a kunneta tana zarya a ɗakinta, cikin ƙasa da murya take magana.
“Yallaɓai karka damu komai yana tafiya akan tsari, ina tabbatar maka ba za a samu matsala ba.”
Ta yi shiru tsawon lokaci, “To ba damuwa duk yanda ake ciki zan nemeka,amma dan Allah yallaɓai a cika mun alƙawari.”
Wayar ta sauke ta ƙura mata ido, ta faɗa cikin dogon tunani akan abun da ya kamata ta yi.
~~~~~~●●●●●~~~~~
POLICE STATION
HAMZA
Tunda ya samu saƙon nan tun a hanya ya kira Inspector Jabir akan su ɗebi yara a je wajan yana hanya.
Bayan sun kamo masu laifin a cell aka zuba su duk da yawansu sannan ya shiga office ɗinsa yana sauke numfashi dan kuwa sun sha wahala.
Ruwa ya ɗauka a fridge ya sha kafin ya fito ya saka aka fara ɗaukar statement din kowa.
Kujera aka saka masa a gaban cell ɗin ya zauna yana kallonsu cikin nazari kafin ya fara tambayarsu.
“Mene ne musabbabin rigimar.”
Shiru suka yi suna kallonsa kamar nama a gaban Kura.
Murmushi ya yi kafin ya ce.
“Da alama kuna son daɗewa a prison.”
Sannan ya miƙe ya bar wajan.
Yana tafiya suka kaure da wani faɗan dan dama rigimar bata mutu ba.
“Yallaɓai suna faɗa fa.” faɗin corporal Bala.
“A raba musu cell.” ya faɗa yana kwantawa a kan kujera ko zai samu bacci.
~~~~~~■■■■~~~~
JAZY
Dare ya yi sosai lokacin da ya dawo har an kulle gidansu dan haka ya canza akalar shi zuwa gidan harƙalla.
A zaune ya tadda su sun yi jigum, da kallo ya bisu ganin yanda wasu suka ji ciwo sosai.
Dressing ya fara yi musu Jagwa yana taya shi goge jini, saboda dama idan irin haka ta faru shi yake zama likitansu, sai da ya gama tsaf kafin ya ce suje su kwanta.
“Kamalu wannan karon ba zan ƙyale duk wani me hannu a cikin wannan abun ba.”
Tunda Jagwa ya ji ya ambace shi da asalin sunansa ya san ransa a matuƙar ɓace yake.
“Allah ya huci zuciyar shugaba.” ya faɗa yana rusunawa.
Wayarsa ya zaro ya danna kira amma har ta gama ringing ba'a ɗaga ba, murmushi ya yi yana girgiza kai, kafin ya zame a kan kujerar ya kwanta.
~~~~~~●●●●~~~~~
NANAH
Sai da aka yi sallar asuba kafin Nana ta kwanta bacci.
Ƙarfe bakwai ta farka, wanka ta shiga ta yi kafin ta shirya dan yau zata shiga school.
Bayan ta kammala ta je gaishe da su Umma da Mama faran-fara ta amsa tana mata a dawo lafiya.
Da wuri ta samu abin hawa ta wuce, yau Amina ta rigata zuwa.
Amarya sai yaushe za ki ɗauki hutu ne.”Amina ta tambaya.
“Sai nan da sati biyu.”
“Ah ki ce so kike rana ta koɗar mana da ke.”
“Ai farare irinku rana take koɗarwa ba mu baƙake ba.”
Suka nemi wajan zama bayan sun zauna Amina ta lura da yanda Nana ta yi shiru ta zubawa waje guda ido.
“Nana me yake damunki ne naga yanayinki duk ya sauya.”
“Ba komai Amina me kika gani?” Nana ta faɗa da ɗan guntun murmushi.
Yar dariya Amina ta yi wadda bata da muhalli a wajan.
“Nanah ke nan ni fa ba yarinya ba ce, ki faɗa min idan da hali na baki shawara idan kuma na addu'a ne sai na taya ki.”
Nana ta sauke numfashi tabbas tana buƙatar abokin shawara bayan su Amira a take ta kwashe duk abin da ya faru ta faɗawa Amina.
Amina ta jinjina kai cikin alhini
“Lallai kam dole ki shiga tashin hankali masamman ma irin mutumin da rigima ta haɗaku, amma ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu abin da zai miki kuma shawarar da zan baki ko da kun sake haɗuwa kada ki nuna kin san shi ma bare har wani abu ya ƙara haɗaku.”
Nana ta girgiza kai cikin gaisuwa da maganar Amina.
~~~~~~~●●●●●●~~~~~
Yau da aka tashi akwai ƙarancin abun hawa dan haka suke a tsaye a ƙofar makarantar suna jiran tsammani.
Wata irin ƙura haɗe da ƙarar machines ta turnike wajan da suke a tsaye tsawon lokaci kafin ƙurar ta lafa haka ma ƙarar.
“Haba bawan Allah meye haka za ka zo ka ɓata mana jiki dan Allah amma dai kasan hakan ba daidai bane k…..?”
Maganar Amina ta maƙale a kan harshenta ba tare da ta ƙarasa fitowa ba, sakamakon mugun ganin da tayi a gabanta rarumo hannun Nana ta yi ta riƙe ƙam jikinta na makyarkyata saboda tana da tsoro.
Jazy ne tsaye a gabansu fuskarnan a haɗe murtuk, sanye yake da wata ɓakar armless da gajeran wando iya gwiwa me uban aljihu rututu wuyansa sanye da sarƙa sai sheƙi take a hasken rana, wani ƙwamemen takalmi ne a ƙafarsa sau ciki ya manne idonsa da wani baƙin sunglasses, zagaye da shi yaransa ne su huɗu sun saka shi a tsakiya suna muzurai.
Wata siririyar wuƙa ya janyo daga ƙasan rigarsa samfurin gayawa jini na wuce sai ƙyalli take alamar sabunta.
Baya Nana taja da sauri ita ma nata jikin na ɗaukar rawa, matsowa ya yi kusa da ita kamar zai haɗe jikinsu, wuƙar ya kai kan fuskarta yana yawo da ita cikin wani irin killer smile ya fara magana murya a dashe.
“A yanzun nan idan naga dama sai dai a ɗauki gawar ki anan? amma ba zan yi haka ba, kin san me ya sa?”
tsuru ta yi tana kallonsa jikinta na ɓari dan gani take yi a ko wanne lokaci zai iya yankarta, sai haɗiyar yawun tsoro take.
“Saboda ina sonki” ya faɗi maganar da murya can kasan maƙoshinsa, hade da sakin wani kalar murmushi da ya fito tare da sautin bugun zuciyarta.
Durƙushewa ta yi a ƙasa cikin rashin sanin abin yi dan a lokacin babu abun da take ji sai amon muryarsa ‘saboda ina sonki’ toshe kunnenta ta yi dan ta daina jin maganarsa.
Be daina murmushin ba ya bita ƙasan shi ma ya ɗago hannu kamar zai kai fuskarta sai kuma ya janye yana dunƙulesa ya cije bakinsa.
Miƙewa tsaye ya yi yana ci gaba da kallonta
Ki faɗawa wancan me baƙaken kayan ya sa a ran shi faɗa da aljani ba riba duk wanda ya shiga teku to ya tabbatar ya iya iyo idan ba haka ba ya nutse a ciki, mun fara takun saƙa ke nan.
Yana gama magana ya juya ya hau machine ɗin yaransa na dafe masa baya, yabar Nana cikin ruɗani.
~~~~~~~~~~~~~~~~
MAMA
“Allah shi gafarta Malam ga takalmin na kawo.” amsa ya yi yana yin ƴan surkullensa da faɗin wasu maganganu kafin ya barbaɗe shi da wani garin magani sannan ya miƙo mata, hannun dama ta kai za ta karɓa.
“Kull kar ki sake ki taɓa shi da hannun dama idan ba haka ba komai zai lalace, kin ga yadda kowa baya son kallon bayan takalmi saboda ƙazantarsa, to haka shima zai tsane ta muddin ta saka takalmin nan a ƙafarta, dan haka ki tabbatar ta saka idan ba haka ba duk abin da ya biyo baya ke kika jawo kanki..”
“Za ta saka ma, amma kuma ai na ji kace zata yi aure a ranar?.”
“Tabbas za ta yi aure amma duk bincikenmu Mun kasa gane komai sai duhu tana da tauraruwa me tsananin haske al'amarinta a ɓoye yake.”
“In dai buƙata ta biya ai shi ke nan, idan ya tsaneta ko an yi auren ai bata da kwanciyar hankali.”
Sallama ta yi masa ta kamo hanyar gida dan yau ita kaɗai tazo saboda Rakiya bata nan.
~~~~~~●●●●~~~~~
HAMZA
Sai da gari ya waye kafin ya nufo gida bacci ne a idonsa ga tarin gajiya dan haka yana dawowa be nemi komai ba sai wajan kwanciya, sam be kula da addu'ar kwanciya bacci ba ya kwanta a take kuwa bacci ya kwashesa.
Samira da ke kallonsa ta taka tsallen murna sai kuma ta yi saurin toshe bakinta dan hana fitowar ihu, fita ta yi daga ɗakin cikin farinciki ta kira Mom ɗinta.
“Wallahi Mommy ya kwanta jiya har na karaya da ya fita aikin dare amma sai ga shi da safen nan da alama a gajiya yake dan ko abinci be nema ba ya kwanta.”
Daga can ɓangaren Mom ta ce “Ai ina faɗa miki mu bi komai a sannu yanzu ba gashi haƙarmu za ta cimma gaci ba.”
Ai wallahi ko da baƙin aljani suke tsafi bata isa ta shigo gidan nan ba ramin Kura Ai sai ƴaƴanta.” Suka ƙarashe da sakin shewa.
~~~~~●●●~~~~~
Alhaji Haruna Jaji
Yana sauka daga jirgi dama driver da securities na jiransa, mota ya shiga suka tafi a gaban rantsattsan gidansa driver ya yi hon me gadi ya buɗe masu suka sulala ciki.
Da gudu Rauda ta fito ta taresa cikin farinciki, rungumeta ya yi cikin matsanancin son da yake mata suka rankaya cikin falon.
Mommy na zaune da littafin azkar a hannunta tana karantawa shogowarsu ya sa ta ajiye ta mike ba yabo ba fallasa tana masa barka da dawowa.
Shima fuska a ɗaure ya amsa mata kafin ya haye sama yarda ta dafe masa baya, ita ma Mommyn bin bayansu ta yi ta je ta haɗa masa ruwan wanka.
Bayan ya gama kitsawa ya sakko ƙasan suka ci abinci sai hira yake shi da ƴarsa.
“Daddy ina son fara aiki fa.” Rauda ta fada tana kai lomar abinci bakinta.
“Ok Darling Wanne irin aiki kike so a ƙasar nan?, ko a ina ne ki faɗa min.”
“Daddy duk sanda na yanke shawara zan faɗa maka.”
Jinjina kai ya yi kafin ya sako mata tambayar da ta girgiza ta…✍️
OUMBHANAT✍️❤️🔥