Free chapter 路 Read without an account

27

by Gidan Iko 路 GARWASHI

*GARWASHI*


    *Hadiza Bara'u Gidan iko*


...........Wata firgita hade da Rudani suka sauko min duk a lokaci Daya inda jikina ya dauki kyarma na sake duban yarima Gibson don tabbatar da ba idona bane Yake min gizon ganin shi da wuka da nayi ba

Na sake bin hannun shi da kallo inda na Kuma ganin shi Rike da siririyar wukar Nan sai kyalli take abinda ban sani ba shine me Yake nufi da nufoni da wuka?

Tamkar ya SHIGA zuciya ta ya Karanto abinda zuciyar tawa take sakawa sai ji nayi Yana fadin

"Kikace ba Kya Sona sai wani kike so? Ya fada idon shi akaina Kuma suffar shi ta juye tamkar ba shi ba Kuma Yana magana ne cikin fita hayyaci tamkar dai shima Yana da irin cuta ta ta shafar aljanu

Tsoro Mai tsanani yayi masifar kamani don yanzu na Soma fahimtar abinda Yake nufi da nufoni da wuka
Bakina ya kasa motsi bare na sake maimaita mishi abinda na fada mishi a Asibiti

"Ki sake fada min ba Kya Sona wani kike so don Zan nuna Miki Ni da ke bamu da sauran amfani a Nan Duniya tunda munzo ne Kawai don mu barwa yan baya tarihi Ni da ke don Zan kashe kaina Kuma na karshe ki tunda ba zamu Amfani juna ba 

Jikina ya dauki Rawa don yadda nake ganin ya sauya min daga yarima zuwa wani Abu Mai Kama da Naman daji Kuma abin tsoro 
Shirun da nayi ya fusata shi ya daka min tsawa Yana fadin ba Zaki fada min abinda Kika fada min ba? Ya sake fada Yana Nuna ni da tsinin wukar Ni Kuma tsoro yayi matukar kamani inda bakina ya Soma Rawa Ina Fadin Ina son ka !  

Ya janye wukar daga nuna nin da yakeyi Yana fadin banji abinda kikace ba?
Na sake maimaita Ina son shi yayi murmushi Yana fadin to kin yarda Zaki Aure Ni? Nan ma na sake daga kaina Alamar Eh. Ya saki wukar ta Fadi a kasa ya Ruko hannuna Yana Rungumo Ni inda Naga idaniyar shi na fitar da HAWAYE inda naji tausayin shi ya kamani ganin ba da wasa Yake sona ba har Yana neman zaucewa da aikawa kisa Kuma bana Jin a acikin hayyacin shi yayi hakan lallai so gaskiyar Mai yin shi Kuma lallai ne Mai yin so baya ji baya gani

Sai ya zamo dukkan kulawa da lafiyar yarima Gibson an danka min ita akaran kaina hatta da magungunan shi suna hannu na da Kuma lokutan da ake Shan su na hardace 

Kwanan su Amaka da Maazi Nkem Biyu sukayi nufin komawa gida inda zasu barni nayiwa yarima Gibson Zaman dakin da banyi mishi a farko ba

Da zasu tafi ne Amaka ta kebe Dani tana Rike da kunne na fuskar ta murtuke take kallo na tana fadin

"Allah yasa ki dawo min Legos babu ciki a tare dake kiga Rashin mutuncin da Zan Tata Miki Wallahi ko Kuma ki sake tada mishi makaryatan aljanun ki ke dasu sai kwankwatse ku Wallahi ta fada tana sakar min Rankwashi me shegen zafi shima Maazi Nkem yayi min nashi fadan inda ya sanar Dani matukar aka samun matsala a wannan karon shima zai saka Bakin bindiga ya harbeni don ba zai mutu ta silar Bakin cikin da nake shayar dashi Wanda ke barazana ga Rayuwar shi

Da Haka suka tafi suka barni Ina tunanin ta inda Zan kamo wannan Al amarin nawa Wanda na Gama tabbatar da kaddara tace hakan 

Saukin da na samu na farmakin da nake tsoro daga yarima Gibson shine saboda bashi da lafiya Amma kulawa Kam Ina iyakar iyawa ta don dai na samu na kubce don ko ba Zan taba iya abinda ake maganar nayi ba 


Sati Daya daidai da tafiyar su Amaka yarima Gibson ya warware ya koma kamar baiyi ciwo ba inda Yake sabunta tarairaya inda na Gane abinda yake nufi har dai yazo ya furta da Bakin shi Ni Kuma na fada mishi gaskiya na tsani wannan Al adar ba Kuma Zan taba yarda hakan ta faru a kaina ba matukar ba Aure akayi ba


Da Yake mutum ne Mai sanyin Hali Kuma da gaske Yake son sai ya yarda muka ci gaba da Zama a Haka sai dai ya Rungume Ni ko ya subace Ni iyakar shi kenan daga hakan baya wucewa don ya kiyaye abinda bana so


Kullum cikin amsa wayar Amaka nake ta na tambayar yadda muka kwana muka tashi Amma dai sai dai nace Mata muns lafiya

Abinda ban sani ba shine yarima Gibson ya samu sarki igwai ya fada mishi Yana son ayi bikin mu kawai ba sai an Bari na Sami ciki  ba inda igwai ya Gane son da yarima Yake min ba nawasa bane inda ya so ya nuna Rashin amincewar shi Amma Kuma yana tsoron tashin ciwon yarima Gibson inda ya amsa ba don ya so Haka ba sai ma sharadin da ya gindaya mishi na in aka samu matsala ban haihu ba to Dole ne ya sake Ni su zaba mishi wata matar ya Aura ya Kuma amsa da cewar ya yarda 

Ban San abinda ake ciki ba Ashe har maganar ta Riski su Amaka da Maazi Nkem Suma sun yarda da hakan don suna ganin Ina dab ba Basu kunya  don Haka sai aka SHIGA Shirin biki ba tare da nasan abinda ake ciki ba

Sai da ya Rage saura kwana bakwai inda shima kayan Auren ne aka zube min don za a fara Al adun biki inda Kuma Amaka da Maazi Nkem suka iso da Shirin Aure na inda Kuma hankali na yayi dubu sai da ya tashi don matukar Aure ya tabbata tsakanin mu da yarima Gibson na Gama SHIGA garari don tabbas babu Ni babu musuluncin da nakewa kulafuci don Haka sai kawai na yanke shawarar da nake ganin itace mafita ta ba Zan Auri yarima Gibson ba bani kamar inayi Allah ya sani bana Ra ayi sai dai su Amaka da Maazi Nkem suyi hakuri shima yarima Gibson sai dai yayi hakuri Ni din yadda na Zama musulma bani da mijin da ya wuce musulmi Kuma Aure irin na musulunci don Haka Zan bawa yarima Gibson zabi idan zai iya musulunta to Zan Aure shi idan kuwa ba zai iya musulunta ba to Zan fito in fada mishi gaskiyar ko ni wacece...............


Kar ku Bari ayi tafiyar nan Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran



Gidan iko shine sunana kecewa saduwar ALHERI馃グ馃拑馃徔

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol