Free chapter · Read without an account
Chapter Nineteen
by Sadiya Umar Turaki · IMAANI
Washe gari da safe Imaani tana cikin waya da Ammi after breakfast, Ammin tace, “Zan dawo next week In Sha Allah, kin shirya tafiyarki Abuja ko?”
Imaani tace, “Yeah na shirya zan tunama Hamma.”
“Good, you're also going with your PA, Rafeeq bazai zauna ba idan kunje, kinsan aikin dake gabanshi.”
Imaani ta jijjiga kanta, “Okay tohm babu matsala, apart from The Olive Room I'm also checking out Arcadia ko? I checked my calendar for next month naga schedule ɗin.”
Ammi tace, “Yeah, Hadiza ta turama PA ɗinki list of all the necessary details you'll need. Find time to go through it before then.” Hadiza ɗaya daga cikin assistants ɗin Ammi ce.
Sai sannan ta tuna bata san inda zata zauna ba idan taje, gidansu na can Abuja babu kowa sai securities da ɗaiɗaikun ma'aikata masu kula da gidan. “Ammi where would I be staying? A Maitama ko gidan Abiyy?”
“No bazaki zauna a Maitama ba tunda Rafeeq bazai daɗe daku ba, you'll stay at Abiyy’s in Asokoro.”
Imaani tace, “Okay.”
Ammi ta tuna jiya Imaani ta tura mata video bata gani ba dawuri shiyasa basuyi maganan ba. Although she has an idea about where it came from, because Abbu yayi briefing ɗinta akan zuwan baƙinshi na jiya. “Naga kin turamin video jiya, I saw it late shiyasa banyi responding ba.”
Kunya Imaani taji ta kasa ce mata komai.
Ammi tayi murmushi tace, “Inajinki baby.”
A hankali Imaani tace, “Um, dama Nurain ne ya kawo min jiya daya zo shine na nuna miki.”
Ammi tace, “That's good of him, Allah Ya amfana. I highly commend his approach da yayi tun dawuri, kinga that says much about his character and seriousness, da tarbiyar gidansu. I do hope zai ɗaure a haka.”
Imaani bata ce komai ba, bakin ya mutu yau da suke magana akan unchattered territory, wanda basu taɓa yi ba ada.
Ammi ta gane me ƴar tata ke ji bata ja zancen ba tayi dariya kawai kafin tayi mata wani maganan daban, sukayi sallama daga baya.
Around 1 after Zuhr Imaani ta gama shirinta cikin lavender day dress da cream kimono mai lavender flower prints akai daga HAFS ERA, tayi rolling kanta da cream veil ɗinda yazo dashi.
Ta jujjuya gaban mirror to determine the level of comfortability da takeji cikin kayan. Sanda su Siddiqa suka zo tayi mata recommending brand ɗin bayan ta ganta da wani beaded Abaya nasu dayayi mata kyau sosai.
Simple everyday jewellery ta sanya a hannayenta; wrist watch, bracelets, da zobuna from Zurella. Ta sanya black plumps from Givenchy sai anklets da toe rings from LeCalla.
Taje tayima Abbu sallama yace ta duba idan ƙannenta na buƙatan wani abu suma ta siyo musu. Ta fito daga side ɗinshi kenan taga ya tura mata kuɗi dayawa wanda zai isa harma ya rage. Toh kuɗin gasunan akwai su masha Allah, ko ita zata iya yimusu restocking komai daga asusunta amma Abbu baya wasa da responsibility ɗinshi akan ƴaƴanshi.
Ɗakin Asma'u wanda yake kusada nata tayi knocking tashiga. Zaune ta ganta a armchair tana kallo a Tab, ta ɗago kai ta dubeta.
Imaani tace, “Kina buƙatan wani abu ne zan fita yanzu Abbu yace na siyo supplies.”
Asma'u tace, “Yeah toiletries ɗina sunyi ƙasa, I'll send you a list yanzu.”
“Kiyimun specifying brands ɗinda kike amfani fa kafin kice bashi kikeso ba.”
“Eh zanyi, Adda please ki tayani picking up order na. I bought some khumrahs and oil perfumes toh ansamu matsala da delivery man shine tace nazo na amsa da kaina.”
Imaani tace, “Joyce bazata iya zuwa ta amso miki bane?”
Pleadingly Asma'u tace, “Dan Allah Adda, a wurin gidansu Naseemah workplace ɗin yarinyar yake.”
“How did you know I'm going to Naseemah's?” Imaani ta tambayeta suspiciously.
Asma'u tayi smirking tace, “I just guessed.”
Rolling eyes ɗinta Imaani tayi kafin tace, “Kiyi mata magana in 15 minutes zanzo na amsa, and send the exact address to Samuel.”
Asma'u tace mata tagode as Imaani was closing the door behind her. Ta shiga ɗakin Shukrah dake opposite nata ta duba bayinta taga me zata buƙata itama.
Bayan ta sauko ƙasa tayi ma Baaba sallama a Kitchen tafito waje.
A round driveway ɗinsu dake gaban porch ta haɗu da Cynthia ta buɗe mata ƙofar sabuwar motarta 2025 Land Rover Range Rover Sports SV in Carbon Bronze Satin colour, wanda Abbu yace za'a kawo musu rannan.
Interior ɗin motar is in deep burgundy-brown leather paired with black accents, na Asma'u kuma red color ne with black accents as she requested ayi customising mata.
Ta shiga motar ta kira Naseemah tace mata gata nan zuwa, ta tabbatar ta shirya dan tasan halinta. Imaani ta ajiye wayan kenan text ɗin Asma'u ya shigo, ce mata tayi ta yi directing mai turaren takai gidansu Naseemah kawai idan Imaani taje sai ta ansa. Imaani tayi mata reply da ba damuwa, hakan yama fi mata sauƙi.
Basu daɗe ba akan hanya suka isa unguwarsu Naseemah. Samuel ya tambayeta ko a waje zasu jira, Imaani tace su shiga ciki dan last time da suka sauke Naseemah bata shiga ta gaida iyayenta ba.
Samuel ya danna horn mai gadinsu ya leƙo kai, ganin sabuwar mota yasa ya ƙaraso yaga wanene. Samuel ya sauke window suka gaisa dashi tunda ba baƙon fuska bane kafin mai gadin ya koma ya buɗe musu.
A compound ya tsayar da motar Imaani ta sauka kafin ya juya kan motar ya jira fitowarta. Dama sunsan indai sukazo gidan toh ita kaɗai take shiga ta barsu a waje.
Bakinta ɗauke da sallama ta shiga ciki, mutanen da ke cikin faffaɗan parlour.n suka amsa mata, ƙamshin turaren wuta na tashi gunin ban sha'awa.
Muryar dattijuwar kakarsu taji tana faɗin, “Lale lale maraba, kinyi kyan gani ƴar nan. Jiya jiya nake cema mashiriciyar nan na kwana biyu ban sa ki a idona ba sai gaki yau a gabana ƙaraso mu gaisa.”
Murmushi Imaani tayi ta ƙarasa ta zauna a ƙasa kusada ita, ta rasa me yasa tsofaffi keson zama a ƙasa, hardly ka gansu akan kujera ko a ɗaki ne.
Inna ta miƙa mata hannu sukayi musabaha kafin Imaani ta gaisheta, tace, “Ya kika baro mutanen gidan yasu mahaifiyar taki?”
Imaani tace, “Suna lafiya Inna.” Ta juya ta gaida mahaifiyar Naseemah dake zaune a sofa, daga gani kallo sukeyi kafin shigowarta.
Mama ta ansata, tace, “Nan take zaune tare damu fa tana jiranki kafin ki kirata a waya ta tashi ta hau sama, ko me taje yi oho. Ga saƙo yanzunnan aka kawo akace a baki.” Ta miƙa ma Imaani ɗaya daga cikin plastic bags biyu dake kusa da ita.
Imaani ta amsa tace, “Thank you Mama, dama tace zata kawo nan sai in ansa kawai.”
Mama tace, “Ai turarukan Amina nada kyau sosai, nima yanzu ta kawo min wasu dana sa ta ƙaro min kafin wanda ke wurina su ƙare.”
Inna tace, “Au ko wannan yarinyar me shagon saida magunguna inda ake siyomin man zafi?”
Mama ta buɗe kwalbar farin khumrah immediately ƙamshi ya baɗe wurin, taɗan shafa kafin ta miƙa ma Inna ta gwada. “Ita fa Inna, ga ƙamshin bamai hawa kai bane babu ƙarfi sosai, yanada daɗin amfani.”
Inna ta buɗe ta shafa itama, tace, “Ai kuwa gashi, zanso naji yanda baƙin humrar ta yake.” Ta kalli Imaani, “Kawo hannunki nasa miki kema kiji yanda yake.”
Imaani ta miƙa hannuwanta Inna ta tsiyaya mata, ta shafa tanajin cool scent ɗin na tashi mai calming notes. Ai kuwa irin ƙamshin da takeji kenan so da dama tare da Asma'u. Ta duba jikin ledar taga Meenar Scents, at the back of her mind ta ajiye niyyar trying turaren Aminan tunda ita ma'abociyar son kamshi ne.
Sai sannan Naseemah ta sauko ƙasa sanye da two piece navy blue dress shirt with wide white pants, tana kallon Imaani sheepishly wacce ke banka mata harara tana gyara zaman farin veil ɗinta.
Inna tace, “Kedai kiyi ma kanki karatun ta natsu, ke kenan kullum bazar bazar ba natsuwa se kace kina tafiya ana mintsilinki.”
Mama tace, “Atoh Inna mutum bazai gama kintsawa ba a natse tun da wuri sai ya kama tsalle tsalle da ƙabli da ba'di idan lokaci ya ƙure. My friend zo kuwuce kafin ki cigaba da ɓata muku lokaci!”
Haɗa rai Naseemah tayi tana kallon Inna tace, “Banfa daɗe ba inajin sanda ta shigo ai bayi na shiga.” Inna ta fara mata tsiyar data saba yi, Naseemah tace, “Toh na fasa siyan tuffan, ki aiki Nazir ya siyo miki.”
Inna tace, “Ke kika sani, ai inda ya fiki kenan. Yaushe zan tsaya jiranki dama, ganin bai shigo ba har yanzu yasa nace ki siyomin inba haka ba zan tsaya nemanki ne. Naga wanda zaki kuma samu ya lallaɓa ubannaki.”
Imaani sai dariya take musu ƙawarta kuma ta haɗa gabas da yamma jin gorinda Inna ke mata.
Sallama Imaani tayi musu, Naseemah tayima Mama kaɗai sallama ta kama hanyan fita.
Muryar Inna na binsu a baya tace, “Ho ho zaki dawo gidan ki sameni ne, kuma sekin siyon tuffan ko nacema ubanki kar ya ƙara..”
Basuji ƙarashen zancen ba suka fito waje. Naseemah ta buɗe ido tana kallon gabanta tace, “Wow! Wannan hot cake ɗinfa daga ina ƙawata?”
Imaani ta harareta kafin ta amsa ta, “Daga sama ya faɗo.”
Cynthia na jinsu ta danne dariyarta ta buɗe musu backseat suka shiga.
Naseemah ta fara shafa jikin leathers ɗin motar, “Kan bala'i, this ride is it! Allahumma baarik Imaani, kice zamuyi cruising mai dalili a garinnan. Allah Ya soki Nazir baigani ba da kinsha surutu yau.”
Imaani ta buɗe wani compartment a console inda ake ajiye kaya ta sa turarukan Asma'u, tana murmushi tace, “Thank you so much, Abbu ya siya ma ni da Asma'u fa, ba'a daɗe da kawowa ba. Yau na fara hawa nawa ma.”
Naseemah ta jijjiga kai, “Gaskiya ne, Allah Yasa Daddy ya tausaya min ya canza min nawa nima. Na kusa jana'izarta idan bata sa anyi nawa ba.”
Dariya Imaani tayi, tace, “Kafin mu fara Master's aka canza miki naki fa which was 2 years ago, kuma kema kinsan rough driving ɗinki ke janyo miki.”
Naseemah tace, “At least I can drive to save my life unlike someone I know.”
“Ohommiki, just because I don't drive doesn't mean I can't.”
Suka cigaba da tsokanar juna har suka isa NNDC mall. Tare da Cynthia dake binsu a baya suka nufi cikin building ɗin. Wani ƙaton shagon skincare suka fara zuwa kowa ya ɗauki trolly suna hira suna ɗiban products.
Saida Imaani ta fara ɗaukan na ƙannenta bayan ta duba list ɗinda Asma'u ta turo mata sannan ta fara ɗiban nata.
After about 30 minutes suka gama da wannan shagon, Cynthia ta ɗaukar musu kayan suka fito sai suka shiga wani supermarket to shop for toiletries da kayan ciye-ciye.
Basu daɗe sosai ba suka gama suka fito, sannan Cynthia ta ɗebi kayan ta fara kaiwa mota.
Naseemah ta shafa cikinta, “Nifa nafara jin yunwa ya kike ji ne?”
Imaani ta girgiza kanta in exasperation, “Let's check out Bugatti upstairs. Akwai sabon meal ɗinsu da ya fito last week inaso nayi trying inji.”
Naseemah tace, “Let's go then, lokacin Asr yakusa ma.”
Suka hau can top floor inda Café ɗin yake, wurin akwai mutane babu laifi.
Indoors suka zaɓi zama because the air is a bit chilly outside since harmattan is already knocking. Wani table of four that's vacant by the wall, irin wurinda suke son zama kenan suka nufa sitting opposite each other.
Imaani ta sa musu order.n spicy stick honey wings for starters. Ba'a jima ba aka kawo musu. Cynthia na nan tsaye discreetly a gefe bayan ta kai kayan sayayyansu mota ta dawo.
For main meal seafood fried rice with fattoush salad sukaci, Naseemah tayi suggesting exotic escape for mocktail. Suna ci suna hira abinsu gunin ban sha'awa.
Imaani dai tunda suka shigo take jinta a takure kaman ana binta da kallo, wanda ba sabon abu bane a wurinta but this time ba irin curious looks ɗinnan bane, openly take ji ake kallonta.
Da suka gama Naseemah tace, “I'm going to the restroom bazan daɗe ba, wanna come with?”
Imaani tayi pulling wani disgusted face that made Naseemah laugh. Tasan irin ƙyamar da Imaani ke dashi, she rather hold her discomfort in until she's home than for her to visit a public toilet. Naseemah ta wuce da jakarta so that she can pay for the meal idan ta fito.
Text yashigo wayarta daga Nurain, with a soft smile ta buɗe ta karanta. Tambayanta yakeyi yaushe zata koya mishi overnight oats ɗin, yanaso yayi trying. Tayi mishi reply da yazo restaurant ɗinta gobe if he's free sai suyi tare.
Bai kai ga turo mata reply ba taji mutum tsaye a kanta, ɗaga kanta tayi taga idanunshi na kan wayarta yana bin chats ɗin da kallo.
Quickly tayi switching off screen ɗin, the ever-observant Cynthia ta fara takowa Imaani ta girgiza mata kai sai Cynthian ta dakata but was on alert.
Ya kalli Cynthia itama ta kalleshi sai yaja kujerar kusada Imaani ya zauna. Haɗa rai Imaani tayi kafin tayi magana yace, “Tun ɗazu nake jira ki gama sai yanzu, dama nace miki I'll see you soon. Saboda ke nayi postponing komawa Abuja sai na ganki kafin na tafi ganin baki fito ba tun Friday.”
Da mamaki Imaani ta kalli Sadiq jin me ya faɗa. At least bayida guts ɗin zuwa gidansu, which is the safest place she can be. Maybe ma yayi trying yaga bazai samu shigaba without an invitation shiyasa ya jira saida ta fito.
Imaani tace, “Me zanyi maka?”
Yayi countering da, “Waye kikace yazo ya sameki gobe? Me zaki mishi? Bakiji me na faɗa miki ba jiya?”
Da zafi zafi tace, “Who the hell do you think you are to be asking me these questions? Na sanka ne? Koda ace na sanka huruminka ne abinda nakeyi?”
Sadiq ya kalleta yana ɗan nazari, yaga alama territorial behaviour ɗinshi zai iya ja mishi idan baiyi hankali ba. Ya riga ya saba samun duk abinda yakeso at his will. Bai taɓa convincing mace ba balantana yayi chasing ɗinta so in his head Imaani tariga tazama nashi tun ranar da yaji tayi mishi.
Ya danne abinda yakeji, yace, “How have you been tun bayan haɗuwarmu? I've been calling to check up on you amma bakya ɗagawa, nasan duk cikin jan aji ne but please ki dinga ɗauka ina jin muryarki ko zanyi aiki dakyau.”
“Kai a tunaninka irin kiran da kake min deserves an answer? Wa yake kiran mutum non-stop kaman bayida aikin yi?”
Bai bari maganarta yayi mishi zafi sosai ba yace, “Duk ba wannan ba, nidai nace ki dinga ɗaukan calls ɗina if not zan iya yin abinda bakya so.”
Sai tayi shuru ganin kaman maganarta baya kaiwa ko ina a wurinshi, kira ya shigo wayarta daga Nurain. Tayi silencing ta ajiye because she's currently feeling too mad to answer his call.
Sadiq yace, “Shine ko? I would give him a proper warning to stay away from what is mine.”
Rai a ɓace zatayi magana wani call ɗin ya shigo, Sadiq yasa hannu ya ɗauke wayar ya amsa call ɗin yana tashi tsaye.
Itama ta miƙe tsaye tana jinshi, yace, “Ko wayene kai Imaani ba irin taka bace, I'll tell you once don't ever call her again. Kar kuma ka sake kazo wurinta gobe, so ɗaya nake warning-”
Bai ƙarasa magana ba Cynthia ta ƙwace wayar daga kunnenshi ta miƙa ma Imaani.
Imaani ta duba taga the call is still on tace ma Nurain, “I'll call you back, let me sort this out.”
Cynthia tace, “Should I show him out madame?”
“No thank you Cynthia-”
Firmly tace, “He seems to be on the verge of violence.”
Imaani ta kalleta, “I will handle him.”
Nodding kanta Cynthia tayi amma bata matsa ba, Imaani ta kalli Sadiq taga wani murmushi ne ma a fuskarshi, irin ta burgeshi ɗinnan.
Tace, “I don't know what motivated you to pull that move and I honestly don't care but if you do that again, zan nuna maka might ɗina tunda naga alama bakada hankali.”
At this point kowa a cikin Café ɗin yabar abinda yakeyi yana kallonsu. Sadiq bai bar murmushi ba yayi inclining kanshi, “Kaman na ɓata miki rai, amma banga laifina ba saboda na faɗa miki ke tawace kaɗai ba ta wani ba. But it's all in good time, I'll make you understand what I mean better.”
Imaani ta ɗaga murya tace, “Take your nonsensical words and get out of my life, bazan ƙara yima magana ba duk abinda kaga ya biyo baya kai kaso haka.”
Sai sannan Naseemah ta dawo, Sadiq ya kalleta yace, “Naseemah right?”
With confusion Naseemah tace, “Yes..?”
Yace, “Nayi upsetting friend ɗinki dukda ita taso hakan, but she'll understand me soon when she calms down.” Ya kalli Imaani yayi mata salute, “Until next time, take care.” Kafin ya juya ya kama hanyan fita.
Zuciyar Imaani na bugawa da sauri da sauri ta ɗauki jakarta tace, “We're leaving.”
Da sauri Naseemah tace, “Definitely, I've settled the bills.”
Imaani batayi loosing anymore composure ba tabi bayan Cynthia dake gaba suka fita tareda Naseemah.
Ba wanda yayi magana saida suka shiga motan, Cynthia tace, “Mr. Dadan-Garba must be informed about this.”
Imaani tace, “No you don't have to do that, just inform Hamma he'll handle everything. Nima zanyi mishi magana idan mun koma.”
Cynthia da Samuel suka kalli juna amma basuce komai ba. Abbu ne ya ɗaukesu aiki but in order to build trust with your principal, wato wanda suke tsaro, dole saida mutual confidentiality between them.
But in terms of threat, that confidentiality must be breached in order to secure the principal by all means necessary.
Naseemah tace, “What happened? I just left for like 5 minutes.”
Imaani da ta kasa samun natsuwa because that has literally never happened to her before ta girgiza kanta kawai while trying to calm herself down.
Anger is the most prominent feeling she's having right now and shock at how quickly everything escalated then fear because, well, why not?
Nurain ya faɗo ranta, ya zata fara mishi explaining komai?
Naseemah ta karkaɗa hannayenta a fuskar Imaani, “Faɗa min mana, waye wannan? Ya akai ma yasan sunana?”
Imaani tace, “Ni kaina nayi mamakin yanda yasan sunanki, shine Sadiq ɗinfa.”
Zaro ido Naseemah tayi, “What? Wannan ɗin? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Eh na yarda he is a self-entitled piece of shit. Taɓaki zaiyi naga ko me?”
Imaani tace, “Ya isa? Da ya jama kanshi fiyeda yadda yayi already. Wayana ya ɗauka ya amsa kiran Nurain.”
Naseemah ta tafa hannuwa, nan Imaani ta warware mata meya faru bayan tafiyar ta.
Naseemah tace, “Ƙawata me yake shirin faruwa dake ne? Rayuwarki shuru da amma yanzu da kika fara soyayya shikenan-”
Imaani ta katseta, “Kinga kar ki ƙara tadamin hankali ko Abbu banason yasan zancennan. I'll just tell Rafeeq ai ya taɓa ganinshi, yana wurin sanda muka fara haɗuwa da Sadiq.”
Naseemah tace, “Allah Yasa ayi ma tufkar hanci dan ni guy ɗinnan yabani tsoro. Kamata yayi muyi namu binciken akanshi saboda musan inda zamu fara kafin ku ƙara haɗuwa dashi.”
Imaani tace, “Abinda zanyi kenan, Cynthia I need everything you can find on him. His name is Sadiq Matawalle and he's called Hudhaifa, you also know what he looks like.”
Cynthia tace, “On it already, I'll submit what I find tomorrow morning.”
By then sunkai unguwarsu Naseemah, Imaani ta tuna mata saƙon Inna. Naseemah tace a rabu da ita kawai, ba gori Innar ke mata ba. Imaani bata saurareta ba tasa Samuel ya tsaya wurin mai saida fruits aka siya dayawa harda wanda zata kai gida.
Suka sauke Naseemah a ƙofar gidansu, Samuel ya tayata kwasan kayanta ciki bayan ƙawayen sunyi sallama da juna.
Da daddare bayan Imaani ta koma gida, after dinner tace ma Rafeeq tanason magana dashi. Yace mata zai nemeta after Isha' idan yadawo in batayi bacci ba.
Ina zata iya bacci yau? Haka ta zauna ta jirashi sai wurin 9:30 yadawo, ya kirata a waya ta sauko ƙasa yana jiranta.
Ta sauka ƙasan cikin shirin bacci, pink and grey cotton pyjama top and trousers with black head warmer. Rafeeq yana zaune yana danna waya a parlour shima cikin shirin bacci.
Imaani tace, “Hamma ko zamu shiga study room muyi maganan acan?”
Rafeeq yace, “Meya faru?”
Ta kalli stair case, sai ya gane batason wani ya sauko yajisu ne. Tashi yayi ya nufi can tabi bayanshi suka shiga ciki.
A dogon sofa dake gaban wani ƙaton bookshelf ya zauna itama ta zauna, tace, “Cynthia tayi maka magana ne?”
Yace, “Munfara but I was in a hurry sai tace zata turamin report gobe da safe.”
Imaani ta jijjiga kanta jin Cynthian tayi yanda tace bata faɗa ma Abbu ba. Nan tayi mishi bayani akan Sadiq tun daga rananda suka haɗu a bikin Muhibba, zuwa haɗuwarsu a Fifth Chucker, sai na yau da wayan da yake damunta dashi.
***
Get your premium Abayas, sprays, perfumes (designer or not), sunglasses and lots more from HAFS ERA via *** on WhatsApp or hafs_era on IG, you won't regret it!
Idan kinaso kirinƙa ƙamshi kaman Asma'u toh her amazing Khumrahs (Black and White) and oil perfumes are from MEENAR SCENTS via *** on WhatsApp or aminartou on IG