Free chapter · Read without an account

Chapter 16

by Rukayyat · RIKON KA'KA



Comments ɗin ku shine ƙwarin guiwar writers rashin comments na kashe ma mutum jiki yaji kamar ba'a son abinda yake 

Ina miƙo saƙon gaisuwa da fatan alkairi zuwa ga Aunty Farhat ikon Allah hadari sa gabanki inda kike so aljannah mai masoya da yawa fara mai farar aniya sikari bakiyi farin banza ba damo sarkin haƙuri ƴar halak mai maida alkairi da alkairi walkiya harsa lungu da sako na birni da ƙauye gatan mara uwa ke mai uwar ma ke gatansa ce wallahi.

*************



Wani nauyi ya hau kanka yanzu tafiya ka daɗe ba naka bane domin yanzu kanada iyali." Cikin mamaki Sulaiman ya ɗago ya saka idanunsa cikin na Malam wanda shima shi yake kallo, sai kuma ya yi sauri ya yi ƙasa da nasa idon.


"Ehhhh yanzu kanada iyali na nema maka auren ƴar gidan Malam Dikko babbar ɗiyarsa Maryamu ina fatan ba zaka bani kunya ba domin na san na isa da kai wannan yasa na yanke hukunci ba tare da shawara da kai ba dai da mahaifiyarka, baza ka bani kunya ba Sulaiman?" Malam Ahmad ya yi maganar yana kallon Sulaiman da jiran abinda bakinsa zai furta

Sulaiman bai ce komi ba ya yi shiru, shi tunani ya ke dama ana aure babu soyayya ne shi dai ya ji ana cewa saurayi ya auri budurwarsa to kuma me za'ace ma nasa auren kenan yarinyar da in a ka ce ya siffanta kamaninta bai san ta ya zai fara ba to wai shi yanzu har ya yi girman da za'a yi masa aure babu izininsa ko neman yardasa to in ba iyaye ba waye zai yi masa haka ya karɓa ne.

" Ina fatan baza ka bani kunya ba?"

Maganar Malam ta katse tunaninsa, don tunda Malam ya ce ya aura masa Maryamu tunanisa ya tafi yawon wani ɗan lokaci natsuwarsa da kuzarinsa su ka fita da daga jikinsa suka tafi yawon wani lokaci wanda shi kansa bai san in su ka tafi ba kawai dai ya neme su ya rasa tsintar kansa ya yi da ce wa.

"Ehhh insha Allah amma yarinyar tana...." Sai kuma ya yi shiru bai ƙarasaba.

Malam ya fahimci abinda ya ke son faɗa shiyasa ya katse shi ya da katar da tunani sa ta hanyar ce wa


 " Dukanku biyayya kuka yi Allah zai baku ladar biyayya ita kanta Maryamu na san biyayya ta yi"

"Shikenan Malam in dai yarinyar ta yi maka kuma ta yi ma Inna shikenan"

"Maryamu na da hankali kaima zata yi maka na sani insha Allah"

"Ina fatan zaka min alƙawarin kulawa da ita a hankali zakaci ribar zama da ita."

"Insha Allah ba zaka sameni da musgunawa a gareta ba"

Ya yi maganar kansa na ƙasa.

Malam ya kalli Sulaiman don karantar yana yin sa,

 "Ka tashi ka shiga ɗakinka"


Babu gaddama ya miƙe ya fito a tsakiyar gida ya iske Inna kayan dake kusa da ita ya ɗauka iya na sawarsa ya bar sauran a gurin ya shiga ɗaki, kallon sa kawai ta ke yi tunani daban daban a kwakwalwarta sai kuma ta kauda tunanin ta yi masa addu'a da fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali don yan da ta ga yana yin shi tabbas yana cikin damuwa domin tun fitowar sa ɗakin Malam take kallon fuskarsa duk da tun da aka auren kullum addu'ar ta Allah yasa ma auren albarka ya kuma bama yaronta ikon kulawa da amanar da suka amsar masa.

"Assalamualaikum warahamatullah"

Maryamu jikinta duk tsoro ya gama rikita ta don tun lokacin bikinta bata sake jin wani tsoro ko fargaba ba sai yanzu jiki duk babu kwari kallo ɗaya zakama fuskarta kaga tsantsar tsoro da fargaba a cikin idonta baki na rawa murya na sarƙewa ta amsa sallamar.

 "Wa wa'alaikumussalam"

Tana ƙoƙarin miƙewa ta amsa kayan hannunsa ya kauce daga gurin da take sauran kaɗan ya hana ta faɗi ƙasa ko kallon ta bai yi ba ya wuce ya zauna a ɗaya gadon da ke ɗakin.
Ganin haka ya sa ta durkusa har ƙasa ta gaida shi.

Shiru ya yi na wani lokaci sannan ya amsa bata sake cewa komi ba ta koma ta zauna a kan gadon da ta ke zaune kafin ya shigo tunda ya kwanta hatta abinci bai nema ba da sake sake ya yi bacci itama hakan ne a ɓarayin ta

Ranar haka suka kwana babu wanda ya ƙara magana cikin su.

Washe gari da safe Petel ta shigo gidan sanye ta ke da blue ɗin kayan saƙi na fulani sababbi ne fill Usmanou ya kawo mata su da ya je Rugar Ruma aka aiko shi ya bata daga gurin Baffa Datti, tana shiga ɗakin Maryamu ta fara shiga kamar yan da ta saba sai ta ga Sulaiman kwance yana bacci Maryamu bata cikin ɗakin tana kewaye da sauri ta fito cikin ɗakin ta koma da gudu zata fita sauri ta ke ta je ta faɗa ma Dikko ta ga wani yana bacci a ɗakin Addah Inna ta fito ɗaki ta ga fitowar ta daga ɗakin.


"Ke Petel zo nan" 


Inna Hafsatu ta ce wadda fitowar ta kenan dama taga Petel ɗin tana sauri zata fita ko waigowa ba ta yi ba da gudu ta ruga zata fita kenan har taje ƙofar gida ta yi karo da mutum da sauri ta ɗago kai domin ganin waye Bassam ne tsaye sai kuma Malam Ahmad da ya iso yanzu tana ganin Malam Ahmad ta kauce taba Bassam guri da sauri ta ƙarasa wurin Malam Ahmad ta ce "Baba Malam wani ya shiga ɗakin Addah ga shi can yana kwance ku je ku fito da shi kada Baffa ya ji zai yi ma Addah faɗa kuma Addah tsoro ta ke ji bata son faɗa can kuma ta fara kuka, Maryamu na kewaye ta ji yo maganar da sauri ba don ta gama abinda ta ke ba ta fito daga kewayen amma ta ƙasa ƙarasowa wurin saboda ta manta mayafinta a ɗaki bazata iya zuwa gaban Malam Ahmad a haka ba.

Inna Hafsatu ta ƙaraso wurin shi kan shi Bassam da ke tsaye a gefe so ya ke Malam ya bada umarni ya je bukkar ya ga wani tsagera ne har ya iya shiga cikin bukkarsu ya kwanta a cikin ta ba tare da sun san shi ba.

Malam ya riƙe hannunta ya ce "Petel ɗiyata waye kika gani a ɗakin?


"Wani ne ke bacci ya juya baya banga fuskarsa ba"


"ya isa mijinta ne ba matsala ba ne muje ciki ki zauna"

"A'a wallahi Nanne ta ce ba'a zama ɗaki ɗaya da maza"

Bassam kansa ya kasa ɗauka wai waye mijin wa ake magana kuma ina Addah Maryamu ɗin, Inna ta kama hannunta ta ce 


 "To muje in baki abun kari sai ki je ki faɗa ma Nanne amma ki daina kukan"

Wuce wa suka yi Inna ta shiga ɗaki da Petel Bassam ya biyo su a baya don yana son jin ƙarin bayani suna zama "Wai baki ganni banne ko kimin barka da dawowa" Bassam ya yi maganar yana kallon ta yan da take shash'shekar kuka, shiru ta yi ba ta bashi amsa ba.

"Inna wai waye mijin Maryamu ɗin da Malam ke ce wa?"

"Waye in banda ɗan uwanka"


"Kai yaushe a ka yi haka bani da labari" 

Ya yi tambayar yana ƙure Inna da ido alamar yana jiran amsar ta ne.

"Ka je ka tambayi malam shi sai ya faɗa maka ni bana da amsa"

"To ai nasan ba soyayya suke ba Inna tab gaskiya kar ayi min aure irin wannan"

 Ya kai ƙarshen maganar yana kwanciya ita dai Petel ba ta ce komi ba sai share hawaye take yi.

 "To kasa ni kai ma dawowa ta gaba ka dawo ka iske matarka"


"Haba Inna shekarata ashirin da wani abu fa har yanzu ni yaro ne fa kawai don kun yi ma Alhaji Sulaiman aure ya amsa, ba lallai ba ne ku yi ma Alhaji Bassam ya zauna ba" 


Yana dariya har da riƙe ciki don shi maganar auren duk a alamara ya ɗauketa.

Kasa jure zama Petel ta yi ta miƙe zata fita "To ke kuma ina za ki je?"

Juyawa ta yi ta kalli Bassam sai kuma ta yi banza da shi ta wu ce, ita abunne ya haɗe mata biyu wai shege da hauka ga tunanin namiji a ɗakin Addah ga haushin Bassam ya tafi bai tafi da ita ba rigimar ta dawo sabuwa ta wuce ta fita, kamar an jefota ta shiga gida ta iske Usmanou da Baffa a gurin garken shanu da wowarsu kenan da ga ƴan bokale sun je wata ta'aziyya matar wani abokin Baffa ta rasu, da gudu ta ƙarasa gurin da suke "Baffa wallahi ba laifin Addah bane ita bama ta cikin ɗakin shi kaɗai ne ke bacci a ciki" 

Malam Dikko ya kalleta alamar ita wannan lafiya kuwa, ta ƙarasa kusa da Usmanou ta riƙe hannunsa ta ce "Hamma ka ce Baffa ka da yama Addah Maryamu faɗa" 
Baffa kallonta kawai ya ke bai san a kan me ta ke magana ba Nanne ce ta ƙara so wurin ta ce "Muje bukka!"

 Petel ta bi bayanta suka wuce suna shiga ɗakin Nanne ta zaunar da ita a saman gado ita ma ta zauna ta riƙe hannunta "Waye kika gani a ɗakin Maryamu ɗin?"

"Yaya Sulaiman ne na gidan Inna Hafsatu"

"To ai mijinta ne Bintou anan zai ringa kwana dama ba an yi auren su ba"

"To kenan Baffa ba zai mata faɗa ba?"

"Ehhhh ba zai yi ba albarka ma zai sa ka mata, yi ma mijinta biyayya shine abin da zai sa mu yi farin ciki" 

"To shikenan tun da ba zai mata faɗa ba"

Komawa ta yi ta kwanta Nanne ta miƙe ta fita, tana kwance ta ji an yi sallama Yaya Usmanou suna gaisawa da wanda ya shigo, kunnanta ya tabbatar mata da wanda ya yi sallamar maganar Nanne ta ji tana ce wa "Ahhh angode sosai Allah ya saka da alkairi"

Tsaraba ce da su Sulaiman suka yi da zasu dawo shine aka kawo ma su Nanne nasu.

"Bassam ya ce babu komi Inna ta ce Bintou ta zo yanzu"

Kiran Nanne ya katseta daga baccin da ya ke son ɗaukarta, "Petel ki zo ana kiran ki!
Turo baki ta yi sannan ta fito daga cikin bukkar tana murza ido tunda ta fito Bassam ke kallonta yana murmushi komi na Bintou burgeshi ya ke, tana ƙarasawa ta je gaban shi "Ga ni Nanne"
"Ki je Inna Hafsatu na kiran ki"
Ko kallon Bassam bata yi ba ta wuce don har yanzu haushin shi ta ke ji, dariya ya yi yama su Nanne da Baffa sallama ya fita.

Lokacin da ya fito har ta kusa shiga gidansu da gudu ya ƙarasa ya riƙe hannunta "Wai fushin mai kike yi?"
Tana ƙoƙarin kwace hannunta "Ni mun ɓata da kai babu ruwana da kai kuma ka sake min hannu " Cikin fulatanci Petel ta ke maganar tana tura baki gaba "Amma dai Bintou kin san ban san abinda kika ce ba ko?" Bassam ya yi maganar yana riƙe da hannunta.


Ƙara tura baki gaba ta yi ta amshe hannunta ta shige cikin gidan Bassam zuciyarsa wani zafi ta ke masa yau Bintou tana fushi da shi ya rasa mai yasa zuciyarsa ke masa haka da sauri ya bi bayanta ya shiga gidan, tana shiga ita kuwa ɗakin Inna ta shiga.

 "Gani Inna" 

"Wa ya ce ina neman ki?"


"Bassam ne" 


"A'a wasa ya ke miki amma tunda kin shigo taimaka ki wanke min wannan dutsen ki niƙamin kayan miya zaki iya ai ko"

"Ehhhhh" 


Shine kawai abinda ta ce tana ƙoƙarin ɗaukar ƙaramin dutsen da ake niƙa da shi da sauri ya iso gurin ya ɗauka ya ce "Inna yaushe zata iya ɗaukar wannan dutsen ai saita karye"

"Zan iya bani"


Inna tana kallon Bassam duk abinda ya ke ga damuwa a fuskarsa ƙara'ra, "Ka barta zata iya" Bassam ya a ji ye dutsen ya koma gefe ɗaya ya zauna yana kallon Petel ita kuma tana zuba ma dutsen ruwa a in da ya ke tana wankewa, tana gamawa Inna ta amsa ta wanke babban dutsen da kanta wanda da shi ne zata niƙa kayan miyan, farfasa kayan miyan ta fara sannan ta ba Petel sauran bayan ta kusa gamawa don so ta ke ta ɗauke wannan fushin da ta ke daga fuskarta, "Ɗauka ki saka a dutsen ki ƙara daka su yau miya mai daɗi zaki yi mana zan ci girkin ƴan matan Nanne" ta washe baki alamar an faranta mata rai yau za'a bata girki abinda bata taɓa yi ba tun da take,

 "Ai Addah ce ƴan matan Nanne ni kuma ƴar autar Nanne" 

"In ji wa" 

Suka ji an ce daga ƙofar ɗakin Maryamu duka kallon su gurin ya kai Maryamu ce tsaye tana ƙoƙarin saka takalmi gurin da suke ta ƙaraso ta duƙusa ta gaida Inna cikin girmamawa "Barka da safiya" da fara'a a fuskar Inna ta amsa "Barkanmu dai Maryamu" Amsar aikin da Petel ta ke yi Maryamu taci gaba da yi har yanzu Bassam Bai tashi a gurin ba idonsa na kan Petel duk fushinta ya dame shi sai kuma ya miƙe ya shiga ɗakin shi ya zauna a ɗan ƙaramin gadon shi na kara yana kallon ƙofa tsintar kansa ya yi yana hawaye duk da ba kuka ya ke ba amma hawaye ke zubowa daga idanunsa.

"Kai Bassam kukan mai kake yi?" Da sauri ya goge hawayen idanunsa Inna ta yi saurin ƙarasawa gurin da ya ke "Mai ke damunka" Shiru ya yi bai ce komi ba "Bassam na ce Mai ke damunka"
"Babu komi" Shiru duka su biyun suka yi babu wanda ya ke magana 

"Addah gida zan ta fi bacci zan yi kin ji anjima zan dawo" Abinda kunnan shi ya ji yo kenan Petel ta ce, "Inna don Allah ki rarrasheta ta daina fushi taƙimin magana" "Wacece"

"Bintou na tunda na dawo bata sake min magana ba har bukkarsu na shiga taƙi kulani" 
"Yaushe Petel ta zama Bintoun ka ban sa ni ba"

Kafin ya ba Inna amsa sai kuma ya fara wasu hawayen, ganin hakan yasa Inna ta ƙasa ce wa komi ba wai don bata da abinda zata ce ba sai don kawai rashin ce wa komin a wannan lokacin shine ya fi a zuciyarta ta ke saƙawa da kwancewa aguguwa da dama suna yawo a zuciyrta ta kasa barin tunani guda ɗaya

"Shikenan bari in turo ta ka bata haƙurin tunda kai ne ka mata laifin ba ni ba"

Tana faɗar haka ta miƙe ta fito sanda ta fito har Petel ta kai bakin kofa "Petel Petel " Da sauri ta waigo ki zo Bassam na kira"

"Ni mun ɓata da shi"
" To ai shikenan tun da kin ɓata da autan Inna Hafsatu dole yau in haɗa masa kaya ya dawo gidanku"

Da gudu ta dawo wurin "Da gaske zaki dawo da shi gidanmu gurin Baffa su ringa tafiya kiwo da Usmanou"

"Ehhhhh zan baku shi ga baki ɗaya"

"To bari in je in ta ya shi haɗa kayansa mu tafi"

Da hanzari a karo na farko ta shiga ɗakin yana zaune yanda Inna ta barshi awurin tana shiga sai kuma ta tsaya tana murguɗa baki da sauri ya miƙe ya je gurinta ya durkusa ya riƙe hannunta yana hawaye "Bintou ita fa a duk sanda ya ce Bintou mantawa ta ke da sunanta ne don ita Petel ta fi ganewa, "Bintou har yanzu fushi kike dani" sai a lokacin ta kalleshi yana durkushe "Ba kai ne ka tafi ka barni ba"
"Bazan sake ba Bintou ki daina fushin" Riƙe ƙugu ta yi tana kallon yanda ya ke hawaye, ita ma sai ta fashe da kuka da sauri ya miƙe "Bintou na yi miki wani abu ne ki yi shiru kar a ɗauka wani abu na yi miki don Allah Bintou ki yi shiru" 

Rungume Bassam ta yi ta zagaya da hannunta a bayan shi ta riƙe shi sosai kamar za'a kwace shi kasa riƙeta ya yi jikinsa sai rawa ya ke ƙafarsa ta yi masa nauyi ƙaron farko a rayuwarsa da ya ke jin bugun zuciyarsa na nunkuwa fiye da yanda ya ke tunanin zuciyar ɗan adam na bugawa kukan Petel na shiga cikin jikin shi sosai har yana niyar fitar dashi cikin hayyacin shi gaba ɗaya kukan juya masa kansa ya ke. "Bazaki sakeni ba Bintou ki daina kukan" ya faɗa a murya mara fita sosai, ƙara riƙe shi ta yi ta ci gaba da kuka, hannunsa yasa ya ɓanɓareta daga riƙon da ta yi masa, sai a lokacin ta ɗago ido ta kalleshi.



 "Ka daina kukan Yaya Bassam"

"To ki dai na fushin da kike"

"Zaka sake tafiya ka barni?"

"A'a Bintou ke mace ce bazan iya tafi da ke ba amma bazan ƙara tafiya ban faɗa miki ba"

 Shiru ta yi na wani lokaci sannan ta ɗan tura baki gaba.

 "Shikenan zaka dinga yi min tsarawa?"

 Cikin tsantsar yarintar da ke ɗawainiya da ita take maganar.

"Yanzu ma nayo miki"

"Da yawa kayi min?"

"Ehhhh kamar girmanki"

"To ai ni ƙarama ce sai dai kamar Nanne ko Addah"

Dariya Bassam ya ke sosai yanda ta ke maganar sai ƙara basa dariya ya ke "Shikenan zan kawo miki har gida tunda kin daina fushin dani"

Juyawa ta yi da gudu ta fito ya biyo ta a baya yana dariya, fitowar ta ya yi dai-dai da shigowar Malam Ahmad ya ganta ta fito ɗakin Bassam ga shi ya biyota a baya yana dariya kamar bai gansu ba ya yi zai jige ɗakinsa don ya san wata shiriritar ce domin Bassam kaɗai ke biyema Petel.

"Ina kwana Baba Malam" Petel ta ce juyawa ya yi ya ganta a durƙushe kan gwuiwarta tana gaida shi, "Lafiya lau Petel" yana faɗin haka ya shige ɗakinsa.

Bayan sallar La'asar sun dawo masallaci da Malam Dikko da Malam Ahmad tafe suke suna firan yana yin gari,

 "Ah dama gurunka zan je zan ga ka a tafe" 

Cikin fulatanci akayi maganar.

Maganar da suka ji ne suka juya gaba ki ɗayan su, Malam Dikko ne ya yi fara'a ganin mai maganar, cikin harshen fulatanci ya mayar masa da maganar, "Buba kai ne ta fe da yamma haka?"

"Ehhhh wallahi ni ne"

"To mu ƙarasa ƙofar gida Bismillah" 

Zaune suke a cikin harabar da bukkarsu take Petel ta fito ta same su ta durkusa har ƙasa ta gaida Malam Buba "Ina wuni" ya amsa da fara'a "Lafiya lau Surbajo" Petel har da jin kunya ta miƙe ta shige kewaye.

Malam Buba "Ya mu kaji da ƙarin haƙuri wallahi na so in shigo a yi addu'ar bakwai da ni wani uzuri ya riƙe ni"

"Haƙuri Alhamdulillah ai nayi rashi lamunde akwai haƙuri duk cikin matana ta fi su haƙuri"

"Yanzu ka ga sauran biyun ga sunan kullum cikin rikici suke yanzu haka da na fito rigimar suke yi na baro musu gidan."

"Allah ya kyauta ya jikanta."

"Ameen ya Allah Ɗikko". Malam Buba har magriba suna tare don a tare suka je masallaci sai bayan magriba sannan ya ce zai wuce Malam Dikko ya je domin yi masa rakiya.


 "Ni ko Malam Dikko an yi ma wannan yarinyar miji ne?"


Malam Dikko ya ji tambayar kamar bazata 

"Wace yarinya kake magana?"

"Yarinyar wajenka mana ƴar budurwar da ta wuce mu ɗazu"

"Ai Petel yarinya ce duka shekararta Tara kuma kaga ƙaramin jiki gareta" 

"Ai da za'a bani da na maye gurbin marigayiya da ita?"

"Uhmmmm" A jiyar zuciya kawai Malam Dikko ya yi 

 "Allah kuwa ai yarana duk suna kamarta nike aurar da su" 

Malam Buba ya yi maganar yana ɗan wani murmushi shi a dole mai kunya.

"Allah yasa mu da ce"

"Ameen ya Allah amma kayi tunani akan maganar ko yaushe a shirye nike."


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol