Free chapter · Read without an account

Chapter 20

by Rukayyat · RIKON KA'KA

Tunda suka isa Sulaiman suka bar Maryamu a gida da kansu suka shiga kasuwa suka sayi abinda ya dace duk da ya kasance ba ranar kasuwa bace amma haka suka yo siyayya saura kuma suka bari sai ranar kasuwa tunda suka dawo suka shirya wa Maryamu ɗaki ya yi kyau sosai Bassam kuwa ɗakin zaure ne suka gyara nan ya aje duk wani abu nasa.

Tun bayan tafiyar su Bassam bai sake lafiya ba kullum cikin kuka ya ke ga ciwo ya kwantar da shi ko ranar kasuwa ta zo Sulaiman ne kawai ke shiga kasuwa amma banda Bassam Maryamu kullum cikin kulawa da shi take kullum maganar shi ɗaya ita ce ta taya shi da addu'a ya auri Petel domin mutuwa zai yi in a ka raba shi da Petel.

********

Batsari

Tun ranar da su Bassam suka tafi duk wani walwala da farin cikin Petel ya ƙaurace a fuskarta yanzu gidan Inna Hafsatu ma bata zuwa domin kusan kullum sai dai Inna Hafsatu ta aiko mata da abun kari ko wani abu mai daɗi har cikin bukkarsu in kuma wani abun ne da kyar take yarda ta je gidan, kowa ya kasa gane kanta, yau dai Baffa yana zaune tun da gari ya fara haske ya fito yana a zaune a gefen bukka yana gyara abincin dabbobi ta shigo ta dawo daga makarantar Allo tun bayan asuba ta fita sai lokacin a ka ta shi ta dawo tana zuwa ta gaida Baffa ta wu ce bukka kallo Baffa ya dinga bin ta da shi zuciyarsa na saƙa masa aguguwa da dama tunda ta shiga bukka Nanne ta fara mata faɗa a kan ta hana kanta zaman lafiya dama in ba rigima ba ina Fulani ina kaɗo Malam Dikko yana gamawa ya fita ya samu Malam Ahmad su ka ɗan yi fira ko hakan zai rage masa damuwar dake damunsa sun daɗe suna magana sannan suka rabu.

****** 

Rugar Ruma zaune suke a tabarmin kaba dukansu manyan mutane wanda suka san darajar gemu da furfura babu yaro a ciki ɗaya daga cikinsu ne ya ce "Muna fatan za'a duba buƙatarmu a karo na biyu"
Baffa Datti ya yi shiru domin maganarsu ta gama ɗaure masa jiki hakan yasa kawai ya tsinci kansa da sakin murmushin da bai san na meye ba sun daɗe suna magana sannan suka rabu tunda suka tafi mutanan rugar suka shiga shigowa ana ganin wannan kayan aure mai yawa haka na waye sauran manya maza dake da nauyi da alhakin aurar da yaran ƙauyenne su ka ce tabbas basu taɓa ganin kayan aure masu yawan wannan ba anya ba cinikin yarinya zasu yi ba Baffa Datti ne ya ce a basu sati ɗayan da suka ce su gama bincike in a kwai matsala sai a mayar da kayan amma shi jikinsa duk ya yi sanyi da lamarin tun daga bayanin da iyayen yaron suka yi a wurin kawo kayan yasa ya ji yana tunani da shakku amma zai yi bincike.

*********

Anguwar Magaji 

Inna Hafsatu ce ke kaiwa da komowa cikin farin ciki hankalinta kwance babu abinda ke damu ranta sai damuwar da ba'a rasa ba girki take yanda ka san tana girka abinda muta ne ɗari zasu ci shigowar Malam Ahmad yasa ta yi murmushi shima dariya ya yi yana mamakin ƙarfin halin Inna Hafsatu ƙarfi da yaji ta zama hankaka maida ɗan wani naka bai ce mata komi ba ya shige ɗaki babu ɓata lokaci tabi bayansa tana shiga ta ce,

"Abinci ne a rabama Almajiran bayan layi"  

Malam ya ce "Uhmmm ai kin kyauta kamar wacce aka biyama kujerar makkah dariya ta yi tana fita a cikin ɗakin ta koma wurin girkinta ganin tana da sauran aiki, shi dai Malam dariya kawai take bashi.

*************
Abuja 

Yau dai jikin Bassam ya tsananta sosai wannan yasa Sulaiman ya yanke shawarar dawo da shi gida domin tsoro ya ke ya mutu Maryamu ta dage sai ta biyo su amma Sulaiman ya ce bai amince ba haka ta haƙura da kanta ta haɗa ma Bassam kayan shi da na Sulaiman suka kamo hanyar dawowa a cikin mota ya fara suma jikinsa ya yi zafi sosai halin da yake ciki ya ɗagama Sulaiman hankali jama'a ne suka taimaka masa wurin kula da Bassam shi kuma yana masa addu'a har ya dawo hayyacinsa sun ɗauki lokaci a hanya sannan suka iso Batsari.

Inna tana zaune tana alwalar la'asar ta ji sallamar Sulaiman tana ɗagowa idonta ya yi arba da Bassam wanda kallon shi ya ɗauke mata maganar da take son furtawa tunaninta da natsuwarta suka nemi ƙaura cewa daga rayuwarta cikin wata ruɗewa da kiɗima ta kwalama Malam wanda ke kwance a ɗaki da alama wani abun yake tun da ya dawo masallaci da ya shiga da sauri ya fito waje! yana ƙoƙarin yi ma Inna magana idonsa ya sauka a kan Sulaiman da ke riƙe da Bassam yana ƙoƙarin shigewa da shi cikin gida da hanzari ya ƙarasa ya taimakawa Sulaiman ɗin suka shiga da shi cikin ɗakinsa suka kwantar da shi Malam ne ya kalli Sulaiman ya tambayi meke damun Bassam babu ɓata lokaci ya sanar musu tun da suka isa garin Bassam kwana ɗaya ya yi da lafiya Malam ya jinjina maganar komawa ya yi cikin ɗaki ya barsu a wurin ya ɗan jima bai fitoba sai ga shi riƙe da wani kwarya ruwa ne a ciki ya kawo aka ɗaga Bassam a ka basa Malam ya yi umarnin a fito a basa wuri babu gaddama duka suka fito daga ɗakin Sulaiman ya shiga ɗakinsa sannan fito ya yi wanka ya wuce masallaci domin yin sallar da ta wuce shi. 

Bayan ya dawo masallaci ne ya haɗu da Malam Dikko a hanya har ƙasa ya duƙa ya gaidasa Malam ya yi mamakin ganinsa sosai to duka yanzu ko wata ɗaya sun yi da tafiya ne da zai ga Sulaiman "Allah yasa lafiya dai ko?" Ya yi tambayar yana kallon Sulaiman da har lokacin yana a durƙushe.

"Bassam ne babu lafiya tunda muka je ganin abun na ƙara gaba shiyasa na dawo da shi gida"

"Subhanallah ya jikin nasa da sauƙi ko?"

"Ɗazu dai har suma ya yi"

Cikin razana Baffa ya kalli Sulaiman kallon abin ya kai haka kenan 

"Allah ya basa lafiya mai ɗorewa insha Allah zan shigo a gaidamin da shi"

A haka suka yi sallama suka rabu Sulaiman ya wuce Baffa shima ya wuce wurin da zai je.

Tun da Baffa da Sulaiman suka rabu babu abinda Baffa ya ke fa ce tunani duk Nanne ce ta haddasa wannan bala'in a cikin ƙaramin lokaci ta canja rayuwar yara sun koma wasu marasa kuzari a haka ya yanke ma kansa hukuncin matakin da zai ɗauka.

Bassam bai farka ba sai wurin magriba Inna na zaune kusa da shi duk ya rame kamar ba Bassam ɗinta ba ɗan gayu kyakkyawa mai kazar kazar ya koma wani iri, tausayi da faduwar gaba suka zo mata a lokaci ɗaya cikin sanyin murya ya ce "Maryamu kin ga abinda nike faɗa maki ko yanzu ba iya Petel ke min gizo ba har da Inna"

"Bassam ba gizo nike ma ba ni ce Inna ce"

"Ban yarda ba kullum haka Petel ke zuwa tana min kuka yanzu kuma Inna har magana ta faramin a gizo"

Inna ta fara zubar da hawayen da ke fuskanta ta kamo Bassam ta ɗago shi domin ya sake tabbatar da cewa ita ɗin ce ba gizo ta ke masa ba, sai da ya tabbatar Inna ce da sauri ya riƙe hannunta da hannuwansa da zafin su ya yi saurin gigita Inna, "Inna an yi auren Petel ɗin?"

"Bassam ka dawo cikin hankalinka"

Cikin hanzari ta saki hannun Bassam ta fita da sauri ta ɗago wani jiƙon Ararraɓi da Tazargaje da ta jiƙa tun ɗazu kafin ya farka da hanzari ta dawo ta shiga bashi yana amsa da ƙyar yana rufe idanu.

Bayan an fito masallaci da magriba Malam ya duba Malam Dikko domin akwai maganar da yake so su yi amma bai samu ganinsa ba hakan ya haƙura, sai bayan sallar isha'i sannan suka haɗu, nan Malam ke sanar da Malam Dikko Bassam na nan gida Sulaiman ya dawo dashi.


 Malam Dikko ya ce ya sani ai sun haɗu da Sulaiman ɗin tun ɗazu ya sanar da shi nan Malam Dikko ya nemi da gobe da safe yana son Malam Ahmad ya masa rakiya wata anguwa in Allah ya kaimu a haka suka rabu, kowa ya shiga gida.


************* 

Rugar Ruma 


Gari ya waye kowa na hada hadar sa matasa na wurin garken shanaye mata masu wanki na yi masu shirin ɗaura abincin ƙarin safe na yi kowa da aikin da yake yi Mani ne tafe san ye yake da riga tazarce.


 Cikin bukkar Baffa Datti ya shiga da sallama, ya samesa zaune yana lazimi cikin girmamawa ya ɗago ya amsa sallamar, Mani yana zaune a ƙasa a kan tabarmar kaba Baffa Datti yana zaune a kan buzu cikin girmamawa Mani ya gaisa da Baffa Datti bayan sun gaisa ya sanar dashi maganar da ya masa a kan Bature.

 Ya samu Bature ya masa magana amma ya sanar da shi yana son wata yarinya Goshi ɗiyar yayar mahaifiyarsa ce Baffa Datti ya yi murna sosai ya musu fatan alkairi suna cikin magana ne sallamar Malam Dikko da Malam Ahmad da wasu mutune guda biyu wanda kallo ɗaya zaka musu ka gane manyan muta ne Baffa Datti ya basu izinin shiga.

 Bayan sun shigo suka zauna duka suka gaida Baffa Datti domin bashi girmansa tunda dukansu ya girmesu ɗaya daga cikin muta nan ya ce "Sai kuma ka ga mun dawo ba tare da an neme mu ba, kamar yanda kuka ce da muka kawo kaya"

 Baffa Datti ya ce "Kwarai kuwa" Malam Ahmad yama Baffa Datti bayanin halin da Bassam ya ke ciki bayan ya gama Malam Dikko ya ce "Na yan ke wani hukunci ba tare da shawara ba amma ina neman afuwa Baffa"

"Ni dama na riga na ba Bassam auren Petel a ɓangarena amma a ɓangarenka in kana ganin Bature ɗan wajen Mani a shirye yake to kawai a yi auren in kuma ba'a shirye yake ba to a tsaida maganar auren Bassam da Petel"

Nan Baffa Datti ya ke sanar dasu yanzu haka zuwan da Mani ya yi abinda ya kawo shi kenan.

 Nan take ya sanar dasu yanda suka yi da Mani daga Malam Ahmad har Malam Dikko wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyarsu babu ɓata lokaci a ka saka ranar auren Bassam da Petel wata ɗaya, Malam Dikko ya saka sharaɗi a kan auren yama Malam Ahmad baya nin Petel yarinya ce bai niyyar aurar da ita yanzu ba sai ta yi shekaru goma sha biyu don haka shi raino ya ba Bassam babu wani abu da zai shiga tsakaninsu sai ta cika shekaru goma sha biyu Malam Ahmad ya amince a haka suka baro rugar zuciyar kowa cikin farin ciki.


******
Anguwar Magaji 


Bayan sun dawo Malam Dikko har cikin gida ya shiga ya ma Bassam ya jiki sannan ya koma bukka ya sanar da Nanne ta shiga ta gaida Bassam yana kwance gida baya lafiya Petel tana kwance tana jin an yi maganar Bassam ta miƙe ta ce zata bi Nanne amma Baffa ya hana dole ta haƙura.


Malam Ahmad na zaune shi da Inna Hafsatu yana bata labarin yanda suka yi da Baffa Datti sai farin ciki take nan ta ke sanar ma Malam wallahi tun lokacin da Nanne ta sanar da maganar auren Petel ko bacci bata iyawa kullum cikin roƙon Allah ta ke a kan yasa Petel ce matar Bassam kuma auren ya zo da alkairi tabbas ta yi farin ciki sosai ko ba komi burinta na ganin Bassam da Petel a matsayin ma'aurata zai cika duk ba ta damu da wani sharaɗin da a ka saka na sai Petel ta cika shekaru goma sha biyu ba sannan Bassam zai kasance ta ba ita ba, damuwarta kawai a yi auren dama ai ita kanta tasan Petel ta yi yarinya amma ita a hakan ma ita ce da godiya suna cikin tattaunawa ne Nanne ta shigo ɗauke da sallama a bakinta.

 Inna Hafsatu cikin farin ciki ta amsa sannan ta nuna ma Nanne wurin zama, Nanne ta gaida Malam Ahmad ya amsa sannan ya tashi ya fita ya basu wuri Nanne bayan sun gaisa tama Inna Hafsatu ya mai jiki, Inna Hafsatu ta shiga da ita ɗakin Bassam yana bacci ta duba shi tabbas a wannan lokacin yaron ya ba Nanne tausayi , bayan ta gaida Bassam zata dawo gida Inna Hafsatu sai godiya take ma Nanne ita dai Nanne bata fahimci komai ba haka dai take amsawa, bayan ta dawo gida da aguguwa da yawa saƙe cikin zuciyarta


Zaune take a ɗakin Bassam tun bayan tafiyar Nanne sai tsara yanda zata masa albishir take duk yanda ta yi sai taga kamar bai yi ba amma ji take kamar ta tada shi a baccin kawai ta sanar da shi taga yana yin shi, wani farin ciki zai yi amma haka ta haƙura tana zaune har ya tashi daga bacci Inna Hafsatu ko tambayar ƙarfin jikinsa bata yi ba ta fara yi masa albishir da maganar da Malam Ahmad ya sanar mata kamar wanda aka zungura haka ya tashi duk da irin ramar da yayi wanda a fuska kawai sai ya baka tausayi zaka rantse ya shekara a kwance cikin muryan ciwo ya ce "Inna mafarki nike ko gaske?" 

"Kaci gidanku Bassam dama ina maka wasa ne?"

"Inna Petel zata zama matar Bassam?"

Dukan su babu wanda ya bama wani amsa kowa tambaya yake maido ma ɗan uwan sa an rasa wanda zai fara amsa tambayar wani a cikin su wani irin farin ciki ya rufe Bassam duk da zafin ciwo haka ya rungume Inna yana kukan farin ciki ita kuma tana shafa kansa ta ce "Auta na zai zama angon Petel" cikin barkwanci ta yi maganar wanda hakan yasa ya ɗaura kansa a cinyarta yana ƙara son gasgata abinda zuciyarsa ke tabbatar masa da cewa daga kunnuwansa ne suka kai sakon cikinta.

Suna cikin wannan farin cikin ne suka ji Sallamar Sulaiman wanda tun da ya fita da safe ya kasa samun kwanciyar hankali hakan yasa ya dawo domin ganin jikin Bassam bayan ya zauna ya huta ne Inna ta sanar da shi 
abin farin cikin da ya same su ya yi farin ciki sosai, ranar dai tunda Inna Hafsatu ta kai ma Bassam ruwa ya yi wanka ta samu yaci abinci sosai saboda Inna ce wa take in har ya bari Petel ta ganshi a haka to tabbas zata iya ce wa ta fasa saboda kwata kwata ya canja duk da tunda ya tashi a ranar kuma ya ɗan samu ƙarfin jiki yake son ganin sanyin Idanunsa amma Inna ta hana ta ce ya bari da kanta zata je ta kawo ta ya ganta.

Kwanan Sulaiman biyu ya koma domin yana ƙoƙarin buɗe wani shagon saida hatsi ana aikawa da shi wasu garuruwan ba dole sai ya je ba yana son fara samun ma'aikata sun yi shawarar da Bassam tun kafin ya kwanta ciwo da ku ɗin shi da na Bassam da ke hannunsa zasu haɗa domin buɗe wurin a cikin garin Abuja wanda da taimakon wasu abokan kasuwancinsu ne suka ƙarfafa masa guiwa wanda tun kafin ya koma ya sanar da Malam ƙudirinsa kuma ya amince yasa masa albarka sannan ya masa addu'ar neman tsari duk da dama Bassam da Sulaiman ba daga baya ba tunda tarbiyyar da aka ɗaurasu a kai kenan tun suna yara Alqur'ani ya riga yabi jini da tsoƙa ɓargo da fata na jikinsu.

Yau ya kasance sati ɗaya da maganar auren Bassam da Petel har yanzu kuma Baffa bai sanar ma Nanne ba sai yau suka zaune ya buƙaci da yana son magana da ita bayan ta zo ya sanar da ita komi Nanne yanda ka san zata hau bori tsabar baƙin ciki harda kuka wai ita duk an saida mata yara shikenan babu yanda za'a yi ta rayu da yaranta har ƙarshen rayuwarta babu irin maganar da bata yi ba amma haka Baffa ya dinga lallaishinta domin naji daɗi ne gari kuma tabbas shi ya ji daɗin yanda rayuwar Maryamu take gudana a gidan Sulaiman wanda haɗa su a ka yi ba tare da ya nema ba balle kuma Petel da ta zama wani ɓangare na rayuwar Bassam.


Duk fitinar Nanne haka ta yi ta ta gama da kudurce kudurce a zuciyarta, a ɓangaren Petel kuwa bata san me a ke ciki ba haka kuma Baffa ya ce in tana son ya bari ta bi Bassam in zai koma to kada ta je gidan, ba don ta so ba haka ta haƙura da zuwa ganin Bassam, a ɓangaren Inna Hafsatu kuwa kayan aure take haɗawa yanda ka san ita ce uwar amaryar a hankali kuma jikin Bassam na ƙara samun sauƙi duk zuciyarsa da gangar jikinsa tana wurin mahaɗin rayuwarsa Petel.
Kallon aguguwan ya ke kamar almara wai da gaske auren Petel a ka ba shi 
Gashi duk kuɗinsa da yake wurin Inna Hafsatu ya ce ta yi abinda ya da ce duk da Malam Ahmad ya ce ba'a son komi na Bassam da kan sa zai yi ma yaron shi aure.

Har yanzu Nanne taƙi saukowa Baffa har Rugar Ruma ya je sanar da Baffa Datti hakan yasa yau da kansa Baffa Datti ya zo har gida yama Nanne faɗa ya mata nuni da rayuwar farin cikin da Maryamu ke ciki Nanne ta yi kuka sosai kamar ranta zai bar gangar jikinta haka ta haƙura. 

Ana ta shirye shiryen bikin Petel da Bassam Baffa da Usmanou suna ta haɗa kayan da ya dace komi na siyayya sun yi ma Petel, yau ya rage sauran sati ɗaya bikin Bassam da Petel kuma a yau Malam Ahmad ya bashi damar zuwa ya ga Petel babu shamaki kamar yanda ya saba haka ya shiga cikin gidan na su tana cikin bukka zaune a saman gadon kara ya shiga suka gaisa da Nanne Petel ta rugo da gudu ta faɗa jikin Bassam tana masa oyoyo ko bari ya yi magana ba ta yi ba ta fara bashi labarin gyaran da Nanne ke mata kuma sannan Baffa ya ce tare da ni zaka koma ka kaini wurin Adda duk surutun Petel Bassam jinta kawai ya ke yana murnushi ganin surutun ya yi yawa yasa Nanne katseta ta hanyar aikenta zuwa ɗauko ma Bassam badarar shanun da ta a je a cikin madafa bayan ta dawo ta miƙa masa ta cigaba da tambayar wai Nanne ta ce Aure za'a yi mana irin na Adda da Yaya Sulaiman zaka ringa tafiya dani in da zaka je a haka suka ci gaba da fira Nanne ta fita ta basu wuri Patel na ta faman shirme.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya yau ya kasance sauran kwana biyu auren Bassam da Petel, an kai kayan auren Petel na gani na faɗa duk wani wanda ya gani sai sambarka domin Malam yasa an haɗa kaya sosai wanda duk wanda ya gani sai ya yi sambarka.

*********

Rugar Ƴan Bokale 


Tunda labarin auren Petel ya zo gare shi kuma ya ji sauran ƴan kwanaki ya ke ƙoƙarin kammala aikin da ya fara Allon ƙarfen da ya daɗe da ƙonawa ya ɗauko ya ciro ruwan wani magani a wata kwarya ya haɗa ya wanke wannan Allon da shi bayan ya gama yasa ɗaya daga cikin matansa ta kawo masa babbar ƙwaryar nonon da yasa a ka gama tatsewa bayan ya gama komi ne ya ɗauki komi ya maida a muhallinsa.


******

Anguwar Magaji 

Yau Maryam da Sulaiman suka shigo Batsari tun da ta zo tana gidansu sai tsokanar Petel Amarya ta ke ita kuwa ko a jikinta, sai dare sannan ta koma gida tana shiga ta iske Bassam ta fara tsokanar shi duk yanda ya so ɗanne wa amma haka ya biyewa Maryamu saboda ya san ita ba mai yawan magana ba ce kamar yanda ya yi tsammani bata jima ba ta shiga ɗaki ta barshi ya koma ɗakinsa ya kwanta.




Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol