Free chapter · Read without an account
9. New Phone and The Engagement
by Zainab · TSAƘANINMU
TSAKANINMU
_Abuja, Nigeria._
Ranar Friday Ahmad ya tafi ɗauko Abba daga Nnamdi Azikiwe Int'l Airport saboda kwana biyu Abba baya nan yayi tafiya zuwa Qatar.
Tunda Abba yayi retire a matsayin permanent secretary anan Abuja yake son zama gida kawai ya huta tunda yayi aikin shi ya gama, amma kuma se suka nuna suna son cigaba da aiki dashi suna bashi consultancy work, yana advising ministries, agencies, yanzu har private companies yake yiwa consultancy.
Shigowar su main gate a gidan, Jawahir na tsaye tana jiran su already, tayi sauri taje wurin mahaifin ta ta buɗe mishi mota.
Hugging Abba tayi tana jin daɗi ya dawo daga tafiyar shi.
Shafa sumar kanta yayi lovingly yace "Na same ku lafiya, Jawahir?"
"Lafiya ƙalau, Abba. Kun dawo lafiya?"
"Alhamdulillah"
"Allah ya hutar da gajiya" tace, ya amsa da amin.
Yana riƙe da hannun ta suka shiga ciki, Ahmad yana bayan su yana kallon ƙanwar shi ina ma zata cigaba da zama haka babu ruwan ta da ba zasu dinga sa idanu akanta ba.
Se bayan Abba yaci abinci ya gama hutawa ya fito daga ciki riƙe da kwalin waya.
Jawahir na zaune a gefen shi a kujera guda ya bata kwalin waya. Amsa tayi da faɗaɗɗen murmushi akan fuskar ta tace "Abba iPhone 6s plus? Nawa?"
"Eh, naki ne, Jawahir"
Hannuwan shi biyu ta riƙe like hugging them to herself tana girgiza jikin ta tana faɗin "Abba nagode. Abba nagode sosai, Allah ya saka maka da alheri, nagode sosai Abba"
"Se kace wacce aka ba ɗan mutum"
Murmushi tayi tana ciro wayar daga kwalin ta. Anan ne Khalifa ya shigo goye da school bag a bayan shi ya dawo daga Hostel domin yayi kwana biyu kafin ya koma kuma gashi gobe za'a kai kuɗin auren Ahmad.
"Yaya Khalifa" tace tana nuna mishi wayar "Abba ya siya min iPhone 6s plus"
"Ma sha Allah" Khalifa ya faɗa da farin ciki ga farin cikin ta "Kin gode sosai. Abba Allah ya saka da alheri"
"An dawo hutun kwana biyun ne, Khalifa?"
"Eh, Abba. Sannu da dawowa"
"Yawwa, sannun mu"
Zama Khalifa yayi yace "Inda an fara Medicine a Baze ko Nile, da chan zanyi to avoid clinicals in National Hospital"
"Sai da Yayan ku yace ka taho States kayi karatun ka, ka nuna kafi son ka zauna Abuja"
"I hadn't known better, Abba"
"Yanzu kun kusa gamawa"
"Eh"
"Allah ya bada sa'a da nasara"
"Amin, Abba. Nagode"
"Gobe idan aka kai kuɗin Ahmad, saura kai"
Ɗan murmushi Khalifa yayi wanda be kai cikin ranshi ba yace "Abba aure se na gama karatu tukunna"
"Har shekara nawa kenan?"
"Ba yawa, Abba. Mun kusa. Nafi so se na gama har housemanship da NYSC na fara residency"
"Allah ya bada sa'a, Khalifa"
"Amin, Abba. Nagode" ya sake faɗa
Kallon Jawahir yayi da gaba ɗaya hankalin ta na kan sabuwar wayar ta har ta dauko tsohuwar ta iphone 6s wanda Hamdan ya siya musu tare da Gumsu lokacin da akayi launching nata, ta cire sim card ta maida a wancan.
"Abba wayar nan da ka siya fa Yaya ba ze ji daɗi ba"
"Ita tace a siya mata fa" Abba ya faɗa wa Khalifa
"Zata sha faɗa"
Ɗago idanu Jawahir tayi da murmushi tace "Abba ni nace a siya min? In dai haka za'a ce zan maida maka kar Yaya yayi faɗa"
"Har kin mance ke kika ce a siya miki?" Abba yace
Shiru tayi tana tunanin yaushe tace a siya mata. Se chan kanta yayi clicking "Lah! Abba lokacin da wasa nake fa"
Dariya Khalifa yayi yace "Kene dai da Abban ki. Nima faɗa mishi zanyi kene kike ta pressuring Abba a baki plus"
"Zan ce ba haka bane ba fa"
Murmushi suka yi tace "Abba kar kace mishi ni nace a siya Please. Kace ka gani ya baka sha'awa shine kace a ba Jawahir"
"Yanda kika ce ayi, haka za'a yi"
Tashi Khalifa yayi yana dariya yace "Abba da ɗiyar shi dai!"
"And his only daughter" ta faɗa da jan faɗa
Kwaikwayon ta Khalifa yayi ya wuce zuwa ɗakin shi domin ya samu ya huta.
***
Ƙarfe goma na safe duk kowa ya shirya da abokanan Abba da ƴan uwa an tafi nema wa Ahmad aure.
Dama tun kafin ranar, mahaifin yarinyar yace ba sai ankawo komai ba ko goro ya isa.
Goro aka bada da kuɗi dubu talatin na neman aure. Aka kuma yanka sadaki dubu hamsin. Anan aka bada sadakin ya rage musu ɗaura aure kawai a sheda Maryam ta zama matar Ahmad.
A chan gidan su Jawahir, mutanen arziki sun zo musu, cousins nasu ne da distant cousins nasu da aunts din su duk sun taho, harda wata good friend na Maman su that has been loyal to their mother even after her demise saboda lokaci zuwa lokaci tana tahowa duba su.
Da mazan zasu dawo gida bayan an gama nema, aka haɗo su da cartons of 5 alive da boxes na cupcakes.
Bayan sun dawo ne, ƙawar maman su, Aunty A'isha, se da ta ja musu kunne dukan su banda Rashid.
"Ba ku tahowa kuna gaida Aunty'n ku ko? Har dai kai Khalifa" ta nuna Khalifa da yatsan ta "Na mance yaushe rabon da ka taho inda nake. Kuma ko na taho nan ɗin ba ganin ka nake ba. Shi Rashid da yake likita and we all know how busy doctors are, amma haka yake squeezing time yana zuwa muna gaisawa dashi"
"Aunty A'isha kin san Hostel nake zama"
"Eh, ai yanzu zaka fara. Daɗin abun se da ɗa na ya zama likita tukunna ka fara"
Dariya suka yi , Khalifa yace "Kiyi haƙuri Aunty A'isha zamu taho in sha Allah"
"Naji bayanin ka amma ban san wane bayani shi ango Ahmad ze bayar ba"
Sunkuye kai Ahmad yayi yana murmushi "Aunty A'isha kin san exams za'a fara a jami'o'i shiyasa"
"Kowa dai da nashi dalili, to bari inji na ƴa ta Jawahir" Aunty A'isha tace tana maida kallon ta ga Jawahir dake kusa da ita sosai
Dariya suka ƙara yi Jawahir na manne da ita tace "Ko shekaran jiya fa nazo Aunty A'isha. Su kace kina wurin aiki"
"Ai kinsan ina wurin aiki kika taho. Next time ki taho lokacin da kika san ina nan"
"Insha Allah Aunty A'isha duk zamu taho mu gaida ki" Rashid ya faɗa
"Toh Rashid! Allah ya nuna mana lafiya"
"Amin Aunty A'isha"
Tashi Aunty A'isha tayi zata wuce tace "Dama nace bari nazo na muku Allah ya sanya alheri"
"Mun gode Aunty. Allah ya bada lada ta zumunci"
"Amin Rashid" ta amsa ta sake ce, tana nuna Ahmad "Yaron nan fa nasan lokacin da yake baby. Yanzu Ahmad ya girma har ya ɗauko maganar aure"
Dariya suka yi dukkansu harda ita.
"To ku yiwa Abban ku Allah ya sanya alheri, naga kaman da akwai mutane a wurin shi"
Tashi Ahmad yayi daga kujera yace "A'a Aunty A'isha, bari a kira shi"
"A'a ka kyale shi, Ahmad. Ai na gan ku kuma ya isa"
"Aunty A'isha dan Allah bari a mishi sallama" Rashid yasa baki.
Gyaɗa kanta tayi ta zauna shi kuma Ahmad yaje kiran Abba.
Tare suka shigo dashi a parlour. Gaisawa tayi da Abba tana mishi Allah yasa albarka ga neman auren da akayi na Ahmad. Godiya yayi mata sosai yana me farin cikin tsayuwar ta akan yaran shi har yanzu da babu ƙawar ta.
Bayan sun gama magana ta tashi zata tafi. Jawahir ce ta kawo mata su 5 alive da cupcakes da gidan matar da Ahmad ze aura suka kawo.
Godiya tayi musu kuma gaba ɗayansu har motar ta suke suna mata godiya da Allah ya tsare hanya. Har ta bar gidan, da murmushi ɗauke akan fuskar ta. Silently tayi wa Maman su addu'a jaddada rahama a gare ta.
Da marece lokacin Nigeria, Hamdan ya kira gida video call yayi magana dasu gabaɗaya on this great occasion.
Gaida babban Yayan nasu suka yi, each one of them se da ya tambaye shi aikin shi ko ya karatu.
"Ahmad, ka girma ko?" inji Hamdan as a way of acknowledging that Ahmad is engaged to be married
Kallon shi suka yi gabaɗaya suka yi dariya.
"Yanzu Khalifa ne kan layi" ya ƙara faɗa
"A'a, Yaya" Khalifa yace yasa yatsan sa ɗaya ya nuna daga tsakiyar kan Jawahir yace "Itace gaba"
"Wace?" tayi saurin cewa "I'll finish university before I get married, so yes, kaine gaba"
"Idan gardama kuke yi, ku bari ayi muku tare"
Ahmad yayi dariya yace "Dama abinda suke so kenan"
"You gotta count me out, Yaya Ahmad" inji Khalifa
"Jawahir bata ce komai ba. Kar ka mance" Rashid yace
Dariya suka yi dukkan su tace "Nima ayi counting nawa out, Yaya"
"To an cire ki"
Madina tayi appearing a video call ɗin ɗauke da murmushin ta "Ya kuke dukkan ku, ƙannen Yaya Hamdan"
Murmushi na kan fuskar su suka amsa mata in unison.
"Congratulations, Ahmad. Allah yasa albarka"
"Amin, nagode sosai Aunty"
"Kasan damu za'a yi biki idan muka zo Eid ba zamu koma ba se anyi"
"Really, Aunty?" Jawahir tayi sauri tace
"Yes, yes, my baby"
"It'll be a beautiful wedding then. Thought it'll be boring"
"Not at all. Da wedding vibes din mu ma zamu taho"
Dariya suka yi suka cigaba da hirar su se da sha biyu ta buga Eastern time tukunna suka yi musu sallama zasu yi mowing backyard nasu kuma suyi gyaran gida tunda dukan su aiki suke basu zama se weekends ne suke samun lokacin zama a gida.