Free chapter · Read without an account

Chapter 32

by A'ISHATU OUMBHANAT · HAƊUWAR ƘADDARA

       💦HAƊUWAR ƘADDARA💦
              (Hatsari da Rai)  
        
             WRITTEN BY
     A’ISHATU(Oumbhanat✍️❤️‍🔥)

***

***

https://www.arewapen.com/u/aishatuoumbhanat42

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W\.A)*
THE STRONGER'S WRITER'S TEAM 🌟

    
      BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 

PAGE 32


            ~~~~~○○○○~~~~~

GIDAN ALHAJI UMAR SABO 


Ƴan ɗaurin aure suna dawowa aka fara taya murna da fatan alkhairi, Baba ɗakinsa ya shiga ya sa aka yi masa kiran Inno.


Bayan ta zo sun gaisa ya shiga faɗa mata ko mai dalla-dalla yanda za ta fahimta, ai sai ta saka kuka tana faɗin.

Amma wannan ɗan sanda anyi ja’irin yaro saboda Allah ba ƙaramin so yarinyar nan take masa ba, ko shi ya sa ma naga gabaɗaya ba ta da walwala ashe alhini take.” 

Sai kuma ta tsayar da kukan tana face majina da haɓar zani, su dai su Baba haƙuri kawai suke bata.


“To ni Karime da wanne ido suke so mu kalli yarinyar nan mu yi mata bayanin halin da ake cik, sauƙin ma an ɗaura auren da wani da tuni ya bar mata abin kunyai.”


“Abba ya girgiza kai yana faɗin “Dama so nake na fara faɗa miki kafin a kira Zainabu a faɗa mata halin da ake ciki.”

“Baiwar Allah ba, imaza ka kirata ta zo nan.”

Waya ya ɗauka ya kira Umma amma hayaniyar mutane ta hana aji me take faɗa ko ita ta ji abin da yake cewa, kashewa ya yi ya leƙo wajen ɗakin ya aika yaro ya kirata, ba jumawa sai ga ta ta iso, gaishe su ta yi ta nemi waje ta zauna.

“Zainabu dalilin da yasa na kira ki, amma dai ki saurari wannan maganar tukun” ya ƙarasa maganar yana kunna mata voice ɗin Hamza.


A matuƙar firgice ta ɗago tana kallonsa idonta cike da hawaye,

 “Innalillahi Wa’inna Ilaihiraju’un!!”
 Take furtawa hankali tashe, tuni idanunta sun cika da hawaye, ta ci gaba da magana cikin ruɗewa.

“ Wannan wanne irin tozarci ne, yanzu ita Nanan shi ke nan ba a ɗaura aurenta ba, ya yake so mu yi da ita.”

“Ki kwantar da hankalinki Zainabu an ɗaura auren Nanah a yau ɗin nan shi kuma yaron mahaifinsa ya nema masa auren Shafa’atu kuma an ɗaura shi ma.” Baba Aƙilu ya faɗa.

Mama da tun wucewar Umma ta bi bayanta a hankali, laɓewa ta yi a jikin bangon ɗakin tana sauraron duk abin da ake faɗa, ko da ta ji wannan magana ta Hamza ba ƙaramin daɗi ne ya cika ta ba kamar ta taka rawa, maganganun Umma suka ƙarawa farincikinta armashi, yau dai taga Zainabu da ƴarta a ƙasa, sai dai kalaman Baba Aƙilu ne suka wargaza duk wani farinciki da take ciki.

“Za ta yi aure a ranar da aka saka”
Kalaman Malam suka dawo mata kamar yanzu yake faɗa, wata irin zufar tashin hankali ce ta yanko mata, ‘sai yanzu ta fahimci me yake nufi, ashe tsugunne bata ƙare ba, ya zama dole ta bincika waye aka aurawa Nana muddin mutumin kirki ne sai ta ga bayan auren ko ta halin ƙaƙa’ zantukan da take ta yi a zuci kenan har ta shiga uwar ɗakinta.


Da mamaki Umma take duban Baba dan neman ƙarin bayani, gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi.

“Tabbas an ɗaura da ɗan abokina Ibrahim sai dai ba shi ne ya haife shi ba ɗan amininsa ne Alhaji Zakariyya, yanzu ki je ki turomin Nana da Shafa’atu.”

Farinciki da fargaba ne suka cika Umma tausayin ƴarta ya kamata, auren wanda ba ka so shi ma kuma ba ya sonka abu ne me matuƙar wahala amma in sha Allah za ta dage da addu'a Allah ya shiga al'amarin ya basu zaman lafiya.

Ko da ta isa ɗakin nasu suna zaune ana hira ƙawaye na tsokanarsu, Nana tana gefe jikinta a sanyaye sai dai kawai ta yi murmushi, a gabanta duk mazajen su Habiba suka kirasu suna sanar da su an ɗaura amma ita shiru Hamza be kirata ba.

Shigowar Umma ne ya katse hirar ta su ta kira Shafa’atu da Nana suka bi bayanta har ɗakin Baba, guri suka samu suka zauna suka gaida mutanen falon suna mamakin dalilin kiran.

“Khadija, Shafa’atu” Baba ya kirasu lokaci guda, suka amsa masa a tare.

“Ni waye a wajanku”

“Mahaifinmu ne.” suka ba shi amsa suna mamakin wannan tambaya.

To madalla, kun san ina da haƙƙin zaɓa muku mazajen aure a addinance amma ana baku zaɓi ne saboda kada daga baya azo ana nadamar haɗawa, to ina so ku yarda da ƙaddara kuma kusa a ranku babu wanda yake auren mace da ba tasa ba, ku yi haƙuri da duk wani abu da ya sameku kuma ku zauna da Mazajenku lafiya.”


Tun da ya fara magana jikin Nana yake wata irin rawa tana tunanin mene ya fari haka, yaushe aka ɗaurawa Shafa aure?

Khadija ki saurari wannan kafin ki ji abin da zan faɗa, tiryan-tiryan ta Fara sauraron maganar Hamza wadda take jinsa kamar ɗigar dalma a zuciyarta, wani irin ƙululu ya yi tsaye a maƙogoronta ya ƙi faɗawa.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraju’un!!³” ta faɗa afili hawaye na ɓallewa a kan kumatunta, ita kuwa Shafa buɗa bakinta sai cewa ta yi.

“Baba wannan asiri a ka yi masa, ka san kuwa irin son da yake wa Aunty Nana? to duk yanda aka yi tsakaninsu aka shiga narantse ku bincika komai .”

Murmushi Baba ya yi.
 
“Kwantar da hankalinki Shafa’atu, ai an ɗaura auren Nana da wani yaro Jafar ɗan abokina ne, ke kuma mahaifin Hamza ya karɓan masa aurenki kuma an ɗaura.”

Jaɓar Shafa ta zame ta zauna daga durƙushen da ta yi tana zaro idanu cikin firgici, kafin kuma ta ɗora hannun akai ta fasha da Ƙaƙƙarfan kuka.

“Na shiga ukuna Baba ka taimake ni ka raba auren nan narantse Aunty Nana yake so, na faɗa maka asiri aka yi masa, kar muje sai ya dawo hayyacinsa ya ce be sanni ba a shiga uku, ka taimaka Baba.”

Duk yanda ƴan ɗakin suke cikin wani hali sai da ta basu dariya, suka ɗan murmusa.

“Haba Shafa ki yi shiru mana ba ki ji bahaushe yana faɗin matar mutum kabarinsa ba, ki yi haƙuri mu karɓi ƙaddararmu in sha Allah ba za mu yi nadama ba.”
 
Shafa ta juyo tana kallon Nana da ke murmushi cikin mamaki tana faɗin.

“Kin san abinda kike faɗa kuwa, saurayinki fa Baba ya aura mun, ai da sun yi haƙuri an ɗaura aurenku sai a yi ta addu'a har abin ya karye.” 

“Ki yi shiru kawai.” Nana ta faɗa cikin dariya da ɓoye halin da take ciki.

Sannan ta juyo wajan su Baba ta fara magana a hankali.

“Baba na karɓi zaɓinka da hannu biyu in sha Allah zan yi iya ƙoƙarina ganin na yi wa mijina biyayya na gode Allah ya ƙara ni san kwana.”

Da ameen suka amsa cikin farin ciki kafin ya sallamesu su fita,Baba ya faɗawa Shafa’atu ta kira mahaifiyarta su zo tare, dan ita ma ta zo yi musu Allah ya sanya alkairi sai abu ya haɗa da yarta babu shiri.

NANAH

Kamar wadda iska za ta kayar haka take tafiya tana keta jama'a, da ƙyara ta isa ɗakin Umma ta shige can cikin uwar ɗakin ta faɗa kan gadon ta fashe da wani irin kuka me cin rai.


‘Ashe so yana zama ƙi? me ta yi masa da ta cancanci wannan tozarcin, wacce irin ƙiyayya ce wannan tabbas ba za ta manta ba har abada, Hamza ya kasheta, maganganun da take ta yi a zuciyarta kenan.


Miƙewa ta yi ta fara cire kayan jikinta tana jifa dasu, ta janyo hijabin Umma ta saka kafin ta ƙara komawa kan gadon ta ci gaba da kuka ta juma tana yi kafin Umma ta shigo tana shafa bayanta a hankali cikin sigar lallashi, tsawon lokaci kafin Umman ta fara magana.


“Ki yi haƙuri Nana na san abin da ciwo amma babu wanda ya isa ya tserewa ƙaddararsa, ki yi haƙuri ki jure in sha Allah ba za ki yi nadamar yi mana biyayya ba, ki sa a ranki hakan shi ne mafi alkairi, ni na san za ki ci ribar haƙurinki a gaba, Allah ya miki albarka ya sa albarka a cikin aurenki, maza ta shi ki gyara jikinki.”


Miƙewa ta yi ta shige bayi ta fara watsewa jikinta ruwan sanyi ko zai rage mata zafin zuciyarta, fitowa ta yi ta samu Umma a zaune ta ajiye mata wasu kayan.

“Umma ba zan saka wannan ba a kwashe a kaiwa Shafa duka.”


Umma ba ta yi magana ba ta ɗakko mata wata atamfa cikin wamda ta ɗinka musu ta bata ta saka, cikin nutsuwa ta gyara fuskarta da kwalliya ƴar kaɗan sanna ta fito daga ɗakin.

Zuwa wannan lokacin magana ta gama ba za gidan gabaɗaya masu alhini na yi masu tsegumi suna yi an dai rasa mene taƙamaiman zance, ga Shafa’atu sai kuka take, sai kallon tausayi ake yiwa Nana amma ta nuna kamar bata san ana yi ba.


GIDAN HAMZA 


Inna ta yi Jugum cikin jimami tun bayan dawowar su Baffa da aka faɗa mata komai, numfasawa ta yi tana kallon Baffa.

“Yanzu kam na yarda da abun da ake fada akan fasa auren Yaron nan da aka sha yi, dole akwai me hannu a cikin alamarin.”

Baffa ya yi Murmushin manya.
“Mata ke nan yanzu ke Halima mene na wannan maganar ko ma mene ai an riga da anɗaura aure ko, sai ku zauna ku tattauna yanda za a je gidansu yarinyar gobe ku ji yaushe za ta tare.”


Inna ta ji jina kai “ To Allah ya kaimu goben, sai ka kira shi ka faɗa masa canji da aka samu.”

“To, hakan ba laifi.”

HAMZA

Banda bugawa ba abinda zuciyarsa take, ga wani irin tsoro da yake ji a ransa ya rasa ko na mene ne, yana kwance a ɗakinsa kamar mara lafiya ya rasa abin yi, wayarsa ta yi ƙara Baffa ne ya ɗaga ya kara a kunnensa tsawon ƴan daƙiƙi Kafin ya ce.

“To Baffa ga ni nan zuwa.”

Ya zaun shiru ‘ ya san abin da ya yi ba daidai ba ne amma ya ze yi? ji yake ana tunzura shi akan dole ya aikata, kuma sai da ya yi ya ji ya dawo daidai amma a ƙasan zuciyarsa akwai wani irin ɗaci da ya kasa bayyanawa akan harshensa.

Miƙewa ya yi ya fito daga ɗakin ya nufi ɓangaren da su Baffan suke, da sallama ya shiga ya gaishe su, kafin Baffa ya fara magana.

“Hakika yau Hamza ka kunyata ni kuma ka zubar mana da ƙima, abin da ka yi baka kyauta ba, ka kunyata bawan Allah a cikin jama'a, to mun godewa Allah yarinya ba ta rasa miji ba an ɗaura mata aure a take a wajan.”


Wani dummm ya ji maganar Baffa a tsakaiyar kansa, sai dai duk yanda ya so ya buɗe baki ya yi magana ya kasa kamar wanda aka liƙewa bakin, muryar Baffa ya ƙara ji.

“Kuma ka saurare ni, ni ba mutumin banza ba ne, dan haka na karɓa maka auren ƙanwarta Shafa’atu, Wallahi³ idan har ka sake wani abu ya faru ka rabu da yarinyar nan ba'a bisa doron shari'a ba to ka nemi wani uban ba ni ba.”


“Ya hayyu ya ƙayyumu!, ya faɗa cikin tashin hankali, ya rasa takamaiman tunanin da zai fara amma dole ya amsa ko ya ƙi ko yaso.


       ~~~~~●●●●●~~~~~~



GIDAN ALHAJI ZAKARIYYA 

MAMMA 

Tana shiga sashenta ta faɗawa ƴan uwanta har da auren Jafar aka ɗaura yau ɗin, abin ya zo da mamaki nan fa murna ta Ƙaru aka shiga hada-hada.

“Bari zuwa gobe sai mu zauna a tsara yanda al'amarin zai kasance tun daga kan lefe da wajan zama tinda abu ya zo a ƙurarren lokaci.” Hajiya Amina matar Yayan Mamma Alhaji Mahmud ta faɗa.

“Toh shi ke nan Allah ya kaimu.”



HAJIYA ZINATU 

Cikin tashin hankali ta isa part ɗinta, wayarta ta ɗauka ta kira yallaɓai, ringing huɗu ya ɗaga,

Yallaɓai akawai matsala fa, yanzu Alhaji yake sanar da mu ya ɗaurawa jafar aure.”

Daga can ɓangaren yallaɓai ya mike tsaye cikin ruɗani.

“Me kike fada haka Zinatu.”

“Da gaske nake yallaɓai.”

“Tabbas Alhaji Zakariyya ya shammace ni, amma duk da haka bata ɓaci ba zan san abin yi.” Yana gama magana ya kashe wayar.


Hajiya Zinatu ta ci gaba da zarya daga nan zuwa can, tana tunanin mafita ga jafar ya tona mata asiri, kuma ta san dole Alhaji sai ya bi ba’asin maganar yanzu ya za ta yi?

‘To ko dai rashin lafiya za ki ƙirƙira saboda a manta da maganar?’ zuciyarta ta bata shawara, “shegen yaron ma ko ta yaya bakinsa ya buɗe bayan boka ya faɗan ba zai taɓa faɗa ba?” Ta furta a fili tananjan tsaki.
  
           ~~~~~~~●●●●○~~~~~~~



JAZY


Tafiya yake yana rangaji kamar zai kife a ƙasa saboda jirin da yake kwasarsa, wajan machine ɗin sa ya nufa ya kunna a guje ya kwasa ya fice daga unguwar ya nufi gidan harƙalla, Allah ne ya kare amma a irin yanayin da yake ciki komai zai iya faruwa.

Wani irin baƙi zuciyarsa ta yi masa ya kasa tunanin komai so yake ya samu wani abu da zai gusar da ƙuncinsa na tsawon lokaci, yana isa ya yi parking ya faɗa cikin gidan , in da yake ajiye kayansa ya nufa ya kwashi wasu ƙwayoyi marasa a dadi ya watsa a bakinsa ya bisu da ruwa, kafin ya ɗakko wani babban ƙullin wiwi ya kunna ya fara zuƙa yana feso hayaƙi ta baki ta hanci ya runtse idanunsa.

Wasu irin abubuwa ne suke wucewa ta tunaninsa rayuwarsa a baya ta shiga dawo masa daki-daki…


SHEKARU GOMA SHA BIYAR BAYA

OUMBHANAT✍️❤️‍🔥


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol