Free chapter · Read without an account

Chapter 3

by Amina Mustapha Abdullahi · Awara: Soyayyar Azima

tana futa dakin dake kusa da wadda ta futa ta shuga, ta rufe kofar ta zauna kan tabar da ke a dakin ita kade tafara raira kuka,

 cike da takaicin mahaifin nasu da bakin ciki, kuka take sosai babu me rarrashinta, daga dayan dakin inna najin gunjin kukanta amma me zata mata,

 babu abinda zata mata saide ta cigaba da musu addu'a su tasu kaddarar kennan,

"sallamu alaikum! 

sallamar wata budurwa da zatayi sa ar Azima ta shugo cikin gidan, Azima na daki tanajin sallamar safeeyar, amma bata da kwari futowa. 

sai kukan ta da taciga ba tanaji suna gaisawa da inna "inna ina azimar take Usman yacemin ta daho, 

"E" safeeya yanzunnan tashuga dakin su" cewar inna, 

"ohh to bari naje, safeeya tafada tana juyawa ta tura kofar dakinsu Azima ta shuga,

  "oh oh oh kinannan kina sana ar taki kennan kinzo kin kulle a daki sai faman kuka kamar wata mage, to me yafaru me akai miki?"

safeeya ta tanbaheta tana kalonta da son jin amsar da zata bata, dudda kasancewar ta son ta tsuniyar kizo bazata huce ta koki ba,

 zancen daya ne kan baba ko innnarsu anisa ( matar babansu) 

"har kin karaso safiya? naji ance kina nemana zamuyi magana me yafaru?" 

Azima tafada cikin muryarta data fara dashewa tana share hawahen da suka sulalo mata, "au bazaki fadan abinda ke damunki kennan ba?

 koda yake nasan akan baba ne kihi hakuri Azima adu' a ya kamata kinahiwa baba ba wai ki zauna kina kuka ba, 

tafada tana rike hannunta cike da tausaya musu sabida halin babansu ba boyahe ne a an guwar ba dan ko yanzu da tataho saida ta gansa a majalisarsu ana rigima dashi akan caca antaru a gurin sai zage zage suke,

"inajinki safeeya meke faruwa kike son magana dani?"

 dogon nufashi taja tana dahowa daga duniyar tunannin da tatafi Tayi murmushi cike da farin ciki ta ce, 

 "wani sabon Company aka bude shine sa'adatu tazo take gayamin masu kudine a gurin da taje, kinsan tana sayar da shinkafa da wake tace babu masu sayar da abinci a kusa da su, 

muma murinka hi nide shinkafa da miya zan runka hi, tunda kin iya danbu sosai kihi shida alala ko tuho zamuyi ciniki sosai,

 shine nace kema bari na gaya miki" dagowa Tayi tana kalon safeeyar cike da mamaki kafin ta girgiza kai ta ce,
  
"ai basai nahi magana ba safeeya ki riga da kinsan halina yanzuma kawai kin tare nine kin fada,

 kinga kwa basai na tsaya ina miki sharhi ba wannan da nake a unguwar muma dan yazama dole ne, 

"mwss ai nasan da hakan nazo nagaya miki Azima a wannan rayuwar da ake fama da itafa dole sai ka mike tsahe ka temaki kanka,

 ba wai katsaya sanhi ba Azima in mun zauna a gida ina zamu samu kudin dorawa da karatunmu,

 ke kankifa kinsan gaskiya kike kokarin dakileta dole sai mun mike tsahe, nikaina ba san sana ar nan da muke a bakin titi nake ba"

"hmm bazan iya ba safeeya in na nema ma, inna baba zata bawa ke zaki iya zuwa amma daga awara bazan kara komai ba, a ina Companyn yake?"

"nan challawa ne fa amma nasan tunda kika ce bazaki ba bazaki ba, bari na tafi kinga magariba Tayi, 

daman wannan maganar ce ta kahoni da bazan zo ba" tafada tana mikewa tsahe, murmushi Tayi ta ce,
 
  "uhm bazan de je ba saide kihi hakuri" banza safeeya Tayi mata tana futa tsakar gidan itama biyota Tayi suka futo tare, 

dede wata magidan ciyar mace tana shugowa da wata budurwa a bayanta, tana sallama 

amsawa sukai Azima na cewa "sannu da zuwa innaro, dagowa matar Tayi ta zuba mata wani kalo tanahin gaba ta bude dakin dake nesa da na inna ta shuga,

budurwar yarinyar ce ta karaso inda suke tana murmushi ta ce,

 "ohhh safeeya andena fushin an kaho mana ziyara ne?" kalonta Tayi ta dauke kai tana

 "ehi wlh kinsan bana fushi da yar uwata, Tayi gaba tana sai mun sake haduwa Azima,

 murmushi Azima Tayi ta juya zata shiga dakin inna taji Anisa nacewa "mwss aikin banza ace mutum ya koma muna fuki sai gulma kamar me, 

banza ta mata tana shugewa dakin inna tanajin Anisan na gaya mata bakakyan maganganu,

 "inna kaho kudin nahi maza maza naje na siyo garin rogo kawai sai muyi dan wake tunda an dade ba ahi ba" 

"yauwa kin kaho shawara daman dare yahi da ahi tuho"

inna tafada tana dauko jakar da take ajihe kudin ta ciro mata dubu daya da dari biyar ta ce,

"Azima karki dade dare yahi kinga sallah za ahi ki taho da manja akantin isiya na dari biyu magi mesta na dari. 

amsa Tayi tana zura hijab dinta ta ce "insha Allah inna"

 ta fuce tare da zura silifas dinta tana futa, cikin sauri take tafiya a lahin nasu ko ina ka huce majalisar maza ce suke hira da sana ar tasu wato gulma.

 saida Tayi yar tafiya kafin ta iso wani katon shagon awo da dan lahi, saida ta jira yazo kanta kamin ta mikame dubu da dari biyu cikin nutsuwarta tace

 "farin garin rogo zaka ban kuma sabuwar dauka, amsa yahi ya koma ya auno mata ya daho ya mika mata fuskarsa da murmushi ya ce,
 
 "Azima gari ya sauko dubu daya ne kuma kamar yadda kika ce sabuwar dauka ne ke nafara zubawa"

"aikam na gode, tafada tana amsar ledar garin da canjin ta juya ta bar gurin gaba Tayi,

 awani shagon masu saida kayan miya ta tsaya. manja ta bada aka bata da magi, sannan ta sai albasa da tumatir na canjin rogo ta juyo gida.

gabda zata isa gida akai kiran magriba, da sauri ta karasa gida babu kowa a tsakar gidan ajihe ledar Tayi a kitchen ta huce bayan gida.

ruwa ta kama ta dauro alwala ta huce dakin inna, tadda ita Tayi tana sallah itama sallaya ta shinfida tafara sallah, koda ta idar bata tsaya lazimi ba ta futo 
ta huce kitchen...........

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol