Free chapter · Read without an account
Chapter 11
........... wannan batun, ba karamin tada hankalin Azima yayi ba, haka zalika shikanshi khamis din yatada hankalin baze auri Azima ba.
shi yana da tasa kyakkyawar budurwar baze iya auranta ba, rikici de yaso faruwa a familyn gani nin haka yasa baffa sawa a hada taron gaggawa zuwa karfe 2:00 na Rana.......
kowa yana zaune ya halarci kiran baffa da hardo, kowa so yake yaji me zece, amma kuma khamis be iso ba.
ita kanta inna zainaba tazo gurin, Azima na gefe Tayi kasa da kanta hankalinta tashe bazata iya yiwa su baffa da hardo musu ba,
dolle ne a gareta Tayi biyayya gasu, tunda inzata mutu baba baze ce a fasa ba, shi dadi ma zeji.
itama kuma baza taso mahaifinta yatada rigima akan umarnin su baffa ba......"sallamu alaikum"
sallamar khamis ta shigo dakin, kyakkyawan bafulatani ke nan ƙin kowa in wanda yarasa,
ba wata mace da zata ce batayin khamis ga kyau ga daukar wanka, fari jajir dashi sumar nan ta fulani a gyare.
ga rufin asirinsa dede gwargwado, dole ai aso Azima ta auri khamis, zama yahi suka ga gaisa san nan baffa yafara magana
"munduba abinda yadace wa zuriyarmu gabaki daya, Amma kuma munji wani rikici yana faruwa tsakannin fadimatu da kai khamis me yake faruwa ne?"
shin kana son fadimatu koko muna sauraran ka" kasa yahi da kansa ransa babu dadi, shi baze iya yiwa su baffa musu a gabansu ba.
kuma shi bayason Azima ace kaf dangi a rasa dawa za a hadashi saida wannan bakar yarinyar,
kuma saboda shi aka raina shi Allah ya gani yanada budurwar da yake so a kd. Amma ba yadda zeyi
"khamisu kai ake saurara shin kanason fadimatu, yar uwarka ko Aa, ba wanda za ayiwa dole?"
dagowa idannnunsa su danyi ja, ya hadihe wani yahu me daci ya ce,
"baffa zabin kuce Azima me zesa nace banayi tunda ku riga da kun zaban zan muku biyayya,
nasan baza kutaba zaban abinda ze cutar dani ba, ina godiya da wannan hadi da kukayi"
murmushi hardo da baffa sukai cikin jin dadi hardo yace, "Allah yahi maka albarka khamisu kaima ya baka zuriya masu himaka biyayya kamar yadda kamana,
kefa fadimatu ya kinason yayan naki ko A'a, ba wanda zamuyiwa dole acikin ku"
kasa ta kuma yi da kanta wani irin zafi na mamahe jikinta daci nawayiwa bakinta maraba,
kanta na mata wata irin sarawa, cikin kankannin lokaci jikinta yafara rawa karkar kamar me zazzabi cikin rawar murya da inda inda ta ce,
"bani da ta cewa baffa, inde ku ya muku shike nan ni me yimuku biyayya ce akan abinda kuka zabarmin a matsahin a bokin rayuwata.
inde kun amince nima hakanne a gurina"
"Allah yayi muku albarka ya sasanta tsakannin ku kutashi kuje za muyake lokacin da yadace ke zamu hadu da mahaifinki akan batun,
Wata gauruwar ajiyar zuciya inna ta sauke, da gaba daya hankalin ta yatashi, tana tsoron kan tariyi ya mai maita kansa.
Dudda tasan Azima me biyayya ce, gasu baffa ma haka ne a gurin su, sunji dadin amsar da ta bada.
"baffa inada magana" khamis yafada kansa a kasa
"muna jinka fadi abinda kake so ko ma mehe za muyi maka shi,
Hardo yafada yana kalon khamis din da yayi kasa da kansa
kai ya kuma sunkuyarwa yana jinjina girman Maganar da ze fada
"baffa za a iya himin alfarma bayan bikina da Azima, in auri wadda nake so na hadasu tare"
"au kaida kana da wadda kake so? babu matsala ai shi namiji na mata hudune, saide fa zakayi adalci a tsakanninsu.
duba da ita wacan kana sonta ba kamar fadimatu ba inde zakayi adalci a tsakanninsu falulahil hamdi"
"insha Allahu baffa zanhi adalci a tsakanninsu, ai Azima yar uwata ce"
kai baffa ya girgiza ya ce, "haka akeso babu matsala sai kusasanta da Aziman zuwa kafin su koma,
ita budurwar taka yar inace mehe sunnanta?"
"baffa yar kd ce, kuma yar babban gida ce ɗiya ga Alhaji isuhu k/mashi ce sunnanta zulaihat"
kai duk suka girgiza kafin hardo ya ce, "lalle diyar gidan mutunci ce, Allah yasanya alheri ya kalli su inna, da inna zainaba, da gwago, da innar aisha, da sauran mazan da suke gurin ya ce,
"to kunji hukuncin da muka yanke, kuma yara sunyi biyayya, sun amsa zuwa sati nagaba, zamu tatauna mu yake hukuncin da yadace,
da lokacin biki za ku iya tafiya amma ke mairama da ke yaya ku tsaya zamuyi magana"
cike da ladabi suka ce to duk suka tashi suka futa, ita kuma Azima ta huce dakin da suka sauka ta fara raira kuka gwannin ban tausayi.
duk rashin samarinta da dadewar da Tayi baTayi aure bane ya jaho haka,
harda za a bada sadakarta, kuma ga namijin dake da budurwa, itada ta tsani kishiya kai wannan wace irin kaddara ce ke kokarin tin karota.
ita tasani ya khamis basonta yake, ba ita ma basonsa take ba, dudu nawa take da har mutane suke kalon ta dade babu aure.
shekara 18 abinda a yanzu sai ka ga mace yar shekara28 babu aure, amma ita me shekara 18 an adda beta.
koda yake dole yan mabera suce tada batayi aure ba, duba da ko A'isha 16 da rabi take ita gata a 18 kuka take sosai tana me tausayawa kanta....
saida inna Tayi wajan awa kafin ta shugo, cike da farin ciki a fuskarta turus Tayi tana kalon Azima wadda keta rawar dari alamun sanyi,
sosai na damunta "Azima lafiya kike meke damunki?"
inna tafada ta na karasawa wajan da Azima take taba jikinta Tayi taji zafi rau, zafinma sosai cikin rudu inna ta ce,
"Azima wai meke damun kine zazzabine fa a jikinki"
"inna dan Allah ki rufene sanyi nakeji, ki rufeni, sanyi, sanyi sosai" tafada cikin rawar murya da karkarwa har hakorata na haduwa garaf garaf.
alamun zazzabin na damunta sosai, zama inna Tayi kusa da ita jiki a sanyahe,
"Azima zazzabi ke damunki, ke nan yaufa lafiya kalau muka tashi meke faruwa?"
shiru Azima Tayi dan bazata iya magana ba, "shike nan bari na kiraho Usman ya siyo miki magani kisha,
ko na tambayi yaya ko za a samu, ta tashi cikin sauri tabar dakin.
koda ta futa bata samu magani a wajan yaya ba, sai futa Tayi tabawa Usman ya siyo ya kaho mata ta koma dakin,
tana nan a kwance ta samu guri ta zauna ta ce,
"Azima tashi kisha magani, jikinki yayi zafi sosai,mikewa Tayi sabida bata son hayaniya ta amsa da pure watern dake gefe tasha,
sannan ta koma ta kwanta bacci ya dauke ta.
bata farka ba sai 5 jikin yayi sauki ba lefi, saide dacin baki da kuma cihon kai tashi Tayi, tana ya mutsa fuska tana kalon dakin, inna bata nan,
amma tanajin hayaniyarsu, sama sama, dakin gwagon A'isha, tashi Tayi ta futo ta huce bahi alwala ta dauro ta huce daki ta tada sallah.
saida ta rama azzahar san nan Tayi la asar, tana zaune a sallaya inna ta shugo mata da abinci
"yajikin naki Azima?"
"jiki alhamdullulah inna kamar kinsan yunwa nakeji, Amma kuma bakina babu dadi"
murmushi inna Tayi tana dafa ta tare da zama kusa da ita ta ce, "ze daho dede azima yanzu ga abincin kici, sai kije ki gaida gwagon A'isha,
"to inna" tafada tana amsar abincin tafara ci saida ta kammala taje ta wanke hannunta, ta huce dakin gwago ta gaida ta.
San nan taja ta shashan hardo, ta gaida matansa, ta huce na baffa, duk kokari take, duk ta gaida su ta juyo batare da ta zauna ba,
ta daho dakinsu dan ita jitake Sokoton ya futa aranta, gwanda sukoma gida ko taji dadi,
nan din duk haushin kowa ta keji, zama Tayi tana jiran ayi magariba ta kuma kwanciya tanajin bangara hardo sunajin salbes.
tanaji in tana cikin farin ciki, amma sai taji yau labarin baya mata dadi,
kodan ya kunshi rayuwa makamancin nata, saitaji kamar marubuciyar da ita take, haka tadan shingida ranta bace tana sauraran shirin badan taso ba,