Free chapter · Read without an account
Chapter 12
da magariba sallah Tayi ta kwanta a cinyar inna, dan ta gaji ga kasala da ta rufeta, suna a zaune Usman ya shugo da leda a hannunsa ya ce,
"inna gashi inji yaya khamis, amsa Tayi tana.
"kai an gode Allah yayi albarka, ta bude siraine wanda yaji yaji da albasa, sai kamshi yake daga gani zehi dadi ta ce,
"kai Masha Allah mun gode Allah yabiyasa.
ta ajihe ledar a gefe "yauwa inna yace yaya Azima taje zasuhi magana, sauri yake,
"toke Azima kwarara jikinki kije kinji, yayan naki yana kiranki maza maza, inna tafada tana dago kanta baki ta tabe cike da shagwaba ta ce
"gaskiya inna bazani ba, bega banda lafiya ba ya hakura wataran munyi maganar"
"Aa Azima kiyi hakuri kije banda rashin kunya, shidin yayanki ne tashi kije, Allah yayi miki albarka tashi diyar arziki"
tashi Tayi rai bace ta zuri daya daga cikin sababin hijab din da sukazo dasu, Tayi waje,
tana kunkuni a kofar gida ta sameshi kan mashin dinsa, karasawa Tayi fuska hade, ganin tasanma ba rahama cikin makoshi ta ce,
"inna huni anyini lafiya?"
kalonta yayi na sakani kafin yadan tafe baki ya ce "ku a naku garin haka ake gaisuwa kennan?"
"aimu muta nan kano ansan mu da tarbiyya yaya me ka gani" tafada tana kalon sa da mamakin maganar da ya gaya mata
"amma kuma mu nana ba, gasu kuma ba ƙakye duk ƴan kanon, ke in banda kaddara me ze hadani dake yar mashayi dake"
dagowa Tayi ta kalesa tayi murmushi me yalwa, har jerarun fararan hakoran ta na bayyana ta ce,
" E, mu bakake ne kuma bamu da kyau, amma kuma kasanmu hasken musulunci da ilimi ke haskakamu,
yan kano muna nane kuma mahaddata, kaga kwa yaya ina alfahari da hakan,
kuma ina godiya da tunatarwa da kamin cewa yar mashayi ce ni, babu wani bawa da ya isa ya kaucewa kaddararsa.
ammfa awajan me ilimi ne ze yadda da haka" ta kuma murmushi ta ce.
"oh ba wannan ya kahoni ba, zaka iya fadar abinda yasa kake kirana, murmushi yahit yana dan sosa keyarsa ya ce,
"nazo na gaya miki ki sanni, ni bana sonki kuma bazan soki ba, karki kuskura ki yadda a aura miki ni, dan takaici na neze kashe ki.
zaki zama yar aiki nane wajan matata kin fahimta ko?" kai ta girgiza ta ce,
"dama inada hali da na hana hakan,dama inada karfi, dana kwaci kaina, daga makircin ka,
Haka zalika baka san wani abu ba, bazan taba sonka ba, sabida ni mijin da nake son aura ba irin ka ban.
Kai nan namiji ne ko? Gaba daya ba kai kama da namiji ba, kana zubin dan daudu, kake wannan feleke.
do min kwa kai din nani kayi kama da dan daudu, ni kuma bazan iya auran dan daudu ba,
a rasa waye macen waye namijin zanhi adu' ar zabin Allah ne kawai, sai anjima,
nama kuma da ka kahowa inna ba ma bukata, dudda hakan baze hana in maka Godiya ba, Allah yakara budi da arziki me amfani.
ta huce cikin gidan fuskarta dauke da murmushi, zuciyarta cike da kuna da zafi hade da takaicin abinda yaya khamis ya fada mata,
da kalo ya bita zuciyarsa na nana ta dan daudu, shine dan daudun sai yakali kansa ya kuma kalon kofar wani abu me kama da takaici da kuna na sukar zuciyarsa,
yanajin dolle ya koya mata hankali na hanyar cusa mata soyayyarsa, ze nuna mata tabbas yana da karfi da ikon, cusa mata soyayyarsa,
ya figi mashin dinshi ya bar gurin, zuciyarsa cike da tsanar Azima, fuskarsa kuma cike da yaudara da mugunta, game da ita hade kuma da soyayyar bogi wadda ze hukunta ta da ita.......
..........koda ta shiga ciki, daki tashuga ta kunshe kanta a hijjab ta runka kuka, da jin zafin duniyar wace irin rayuwa take.
saida Tayi me isarta kafin tatashi Tayi sallahr isha a sujjadar ta ta karshe, tafara rokon Allah cikin kuka da nema dauki da temako ga Allah a bisa wata kaddarar da take tunkarar ta,
"Ya Allah, Ya Rahman, Ya Rahim*
Ya Allah idan auren nan alheri ne a gare ni, a addini na da duniya ta, ka saukaka mini shi, ka sanya soyayya da rahama a tsakaninmu
Idan kuma ba alheri ba ne, kuma ba zai sa ni farin ciki ba, Ya Allah ka kawar da shi daga gare ni, ka kawar da ni daga gare shi,
ka zaba mini wanda ya fi shi alheri, wanda zai so ni saboda Kai.
Ya Allah Ka shiryar da mahaifina, Ka cire masa son abin da yake sha, Ka mayar da shi gida mazaunin salihai,
Ka sa idanunsa su ganta, Ka sa zuciyarsa ta ji tsoronka
Ya Allah ni yarinya ce, ba ni da karfi sai Karfinka, ka zama Gatana da Mafitar kowace damuwa ta.
tana kaiwa nan ta kuma fashewa da kuka, tanajin zuciyarta na sassauta haka ta idar da sallahr ta koma gefe tana karanta,
"la illaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimi, ya haiyu ya qayumu birahamatuka astagisu,
sutake ta karantawa tanajin zuciyarta na kara nutsuwa tana annan Usman ya kaho mata abinci taci, sannan ta kwanta da addu'o i a bakinta har bacci ya dauketa
....cikin dare wani sabon zazzabin ya rufeta, haka ta runka rawar sanyi ita kade, washe gari da zazzafan zazzabi ta tashi dan da kyar Tayi sallahr asubah.
hankalin inna yatashi, gannin yadda jikinta ya koma kamar garwashi, haka yaya ta bada shawarar a kaita asibiti kawai............
**********
*Abuja*
*maitama*
*private family residents*
........familyn fa matawalle yau suna cikin farin cikin, birthday dinda za suyi musamman hamshakai, ikram, Amma, leema, kairiya, ummu kursum,
gaba daya harabar shashan Hajiya Babba, anme wani irin decoration me ban sha awa da daukan hankali ajiki a rubuta da manyan baki,
HAPPY 19th BIRTHDAY
IKRAM, AMMA, LEEMA,
UMMU KULSUM & KHAIRIYA
19 - Pretty, Blessaid & Loved
gurin ya hadu iya haduwa, an kashe kudi ba wai, don ko wani event din al barka, su hammah arif and shahid anyi kokari haka kuma hammah mu'azam.
babu kowa a harabar sai daukar ido take, gidan yayi tsit kamar ba mutane aciki jiran karfe 4:00 ake fara zuba capacityn birthday....
(shin fans me ze faru wajan birthday dinnan, za ahi shi lafiya batare da, dada ko bah ko SIDI sunsani ba,
haka zalika mom da ajida husna zasu bari ayi, wannan birthday din babu me amsa muku wanna tan bayar sai👉✍️ku biyomu acikin shirin private family residents me taken (zuriyar matawalle)
......"mom da gaske birthday dinnan zaki bari ayi? baki gayawa dada da bah ba, me yasa mom a gabanki fa aka hana ajida koda photo na birthday why mom?"
murmushi mom dake hakima ce kan kujera sanhe cikin super atanfa Tayi ta girgiza kai ta ce,
" tun wani zamannin husna Since when did I tell Abbe to go and tell Dada to calm down? There will be NO birthday in this housai. Just sit and watch what will happen in this family today!"
murmushi Tayi tanajin jinawa mom, da sai yanzu takeji abun da ya makale mata a makoshi na hucewa
"wai me yake faruwa a gidannan naga su kairiya sai shuge da fuce suke, kuma kamar ana shuga da kaya bangaran hajiya Babba?"
wata hadadiyar kyakyawar budurwa ta fada, wanda kyanta ze iya sawa ka manta inda kake tana dauke da cat eyes masu girma da daukar hankali, duk wani da namji.
ga duri dede gwargwado, ajida kennan a kalla zatayi 22yhsr, karasa shugowa Tayi ta zauna ta ce,
"inajinku me ake, "kinga ajida babu ruwanki ki zuba ido ki gani mana" cewar didi husna
"gwanda a gaya mata ajida It is the children of this housai that are doing birthday, and even mah is supporting them, that's why you will hear noisai in the housai today"
"what mom ban gane ba aci..kin..gidannan ake birthday, i am not yuhu ba me i am sama dasu stop them a gohi bayansu no no i love dada this thing is happening"
mom ce cikin lallashi ta ce, "kinga ajida ki kwantar da hankalinki nayi magannin komai,
a fusace ta mike kamar zata tashi sama Tayi compound tana cewa "a ina din kikai magani ba a isa aci amanata ba ta fuce kamar tatashi sama..