Free chapter · Read without an account

Chapter 14

by Amina Mustapha Abdullahi · Awara: Soyayyar Azima

tuni mutane sun nutsu suna jiran shugowarsu, mc ne ya fara da cewa

 " ummu kursum matawalle" 

tare da kunna sparkles, 

ummu kursum ce ta baytayna cikin white gown meken tsiya, da kyau fuskarta taci make-up ta saki gashinta kowa jikake yana woow.

 sabida takai ace woow din zama Tayi a kujerar da take tata kafin mc yace 

"ikram matawalle,

 itama bayana Tayi cikin white gown kamar ummu kursum, Tayi kyau ba karya sabida kaf cikinsu tafisu kyau.

 amma kalar fatar sidi gareta dudda duk farare ne itama zama Tayi sai "kairiya itama cikin tata white gown din ta bayana duk masha Allah sannan 

"leema kai Masha Allah duk a halin matawalle kyawawa ne, masu kama daya kuma jini daya, duk sunhi kyau saita karshe.

 uwar gida kuma aminiyarsu yar uwarsu "Amma hamza Ibrahim matawalle.

 itama cikin tata shigar white gown ta bayyana Tayi balakin kyau da kwarjini, zama Tayi waka na tashi gwannin burgewa sai zuba annuri suke,

 kota ina camera man ke daukar photo kawahe aka bawa dama suka zo suka fara zuba ruwan nerori,

 dalla dalla rafa rafa kai ya Allah ka mana arziki dan nikam Ameena m Abdullahi da nake gefe naga ruwan kudi,

 kamar a zubar wai da sunnan ana kebra a gari, hmm bukatar aminiyar kursum yahi tazo Tayi jawabi.

 pretty ce tataso cikin shigar alfarma ta hayo gurin ta amshi mic tafara jawabi kamar haka 
   
"Today is all about YOU! Kowa na ciki da waje ya san cika ne, kika cika wani aho!

I got you a special gift, and I hope you like it. It's something to remind you of how special you are. 

Cheers to another year of blessings, success, and happiness! May all your dreams come true.
    Happy Birthday again! "

tana kaiwa nan ta futo da wani anbulan a jakarta ta ajihe, tare da wani dan kwali cike da coculet ta juya ta koma,

 murmushi kursum Tayi tana kalon pretty,

bukatar kawar ikram akai liya tazo Tayi nata, ta sowa Tayi cikin tata haduwar ta karaso kan step din tafara jawabi,

Gift from me, enjoy! 
More years, more fun! 

ta ajihe nata me uban yawa ta juya kasan cewar miskila ce, kawar amma aka bukata bintu itama cikin nata dodalewar tazo Tayi jawabi,

 haka kowa saida yazo yayi, ana haka saiga ajida tazo da tawagar ta ta zuba kyau,

 kamar itace me birthdayn ta amshi mic tafara jawabi cikin kwararan turancinta,

Cousin duties fulfilled! Ga kudi, ki sanya a dadi, ki yi shopping, ki more, ki shakuwa! 

Wanda ya ce cousin ba sa yin kyauta? Allah ya kara miki yawan rana, blessings, da success! May all your dreams come true!

   Cheers to the birthday girl!"

duk saida sukai mamakin zuwan ajida, haka suka basar ta ajihe musu mukulin mota tabar gurin cikin isa da takama,

 birthday yayi birthday anyi photo iya photo, kuma yayi trading iya trading, suyi photo da kawayansu.

sai gasu hammah arif da mu azm da shahid, sun iso cikin ankon boyal Black sunhi kyau, sosai.

suka hau step sukai godiya ga Allah, bayani sukai, sannan suka ajihe kyauta me tsoka,

 birthday yayi nisa yayin da photos da videos suke yaho a duniya, bakaramin flowers ya kaho ba, ko ina ka shuga shine,

Dan ba inda ba asan ZURIYAR MATAWALLE ba, da kuma tsatsan dukiyar da suke da ita. Birthday ya cigaba da tafiya cikin jin dadi,

suna cikin farin ciki bakin kowa a washe da fara a, yau sunyi birthday, 

kamar ance kairiya ta dago taga wani kyakyawan bafulatani tsoho yana shugowa da sanda a hannu sa,

 ba yansa ma gidanta guda 3 duk suna shugowa, cikin tashin hankali ta dafe kirji kafin Tayi wani yunkuri taji,

 muryar tsoho me ran karfe, me kwarjini da dattaku me ilimi da kirki Alhaji Ibrahim matawalle cikin mic yana magana

 "yahi kyau" 

"Yayi kyau!!!

"Yayi kyau!!!

"Yayi kyau!!!

Abinda ke musu yaho akai, haka sukaji, kamilaliyar Muryar, kamar saukar aradu, kansu ya dau wani irin dumm sabida furgici.

cikin rudu da tashin hankalin da basu taba shiga ba suka dago suka hada baki tare da dafe kirji wajan cewa, 
"DADA!

 DADA! 

BAH! 

ABBi! 

ABBE!........

(wata sabuwa kubiyomu dajin me ze faru, wajan birthday din nan da zuwan dada bah abbe gurin birthday).

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol