Free chapter · Read without an account

10. The Nigerian Cuisine

by Zainab · TSAƘANINMU

TSAKANINMU

_United States of America._

_Bethesda, Maryland._


Yau being Sunday, jiya Saturday suka yi mowing harda gardening. 

Gumsu loves gardening. Suna da Spring onions, tomatoes da lettuce a garden nasu. Kuma ita ta shuka with a little help from Madina. 

Basu suka yi breakfast ba se ƙarfe tara kowa yana gida. 

Bayan sun gama breakfast nasu da wasu ƴan mintuna, Madina ta koma kitchen ta fara aikin dafa musu fried rice for lunch, Gumsu na taimaka mata here and there da wasu abubuwa da labarai kuma. 

Bayan ta gama, suka yi setting dining table a tare da Gumsu. 

Sauran abincin da ya rage, kuma dama tayi harda dinner, ta zuba sauran a cikin food flask.

At 1 PM suka yi lunch ɗin su. Hamdan da Madina suna taɓa hira akan aikin su. Chan kuma se ya tuna da wacce ta taho neman ta on Friday, yace "A woman three houses away from ours came rang our bell on Friday. Said she's looking for you...wanna talk to you"

"Three houses?" tace tare da ajiye spoon ɗin ta tana tunanin ko wace. 

"Yes"

"I think....." Madina says thoughtfully "it was Olivia"

"Maybe she'll come back anytime soon"

"Yeah, maybe"

Shiru suka yi babu wanda ya ƙara cewa komai se bayan sun gama. Hamdan yace wa Madina "Thank you for the lunch, Love"

Nodding kanta kawai tayi ita kuma Gumsu ta tashi ta wuce living room ta kunna TV a Channel na Disney tana kallon 'Girl Meets World.' 

Ƙafafuwan ta duk suna kan couch ta maida hankalinta sosai ga abinda take kallo. Mata ne ake nunawa da maza from 12-14yr old. Theme song na show ɗin yana playing softly a background. 

Hamdan ne ya biyo ta wurin, quietness ɗin ya fara jan hankalin shi se ya kalla Gumsu ya lura da yanda ta maida hankalinta sosai akan kallon da take.

Dawowa yayi ya zauna kusa da ita. Yana kallon ta yana kallon abinda take kallo. 

Ya ɗan fara gane abinda ake yi a show ɗin yace "Kina son wannan yaron a cikin show ɗinnan?" Hamdan ya faɗa yana kallon yaron da aka nuna a cikin TV se kuma ya kalla Gumsu da take murmushi tana kallon yaron.

Shiru yayi be ƙara cewa komai ba ya cigaba da kallon saboda yaga hankalinta na kan su. 

Bayan an wuce wurin yaron, ta kalla mahaifin ta briefly tace "Dad, you were saying something?"

"Nace kina son wannan yaron da ake nunawa a show ɗin?"

Ɓata fuska tayi tana kallon shi, girar ta tayi squeezing. "What?" ta faɗa. Bata gane abinda yake cewa ba saboda basu taɓa magana irin haka ba kuma be taɓa mata Hausa ta irin wannan maganar ba.

Ƙara maimaita kanshi yayi tace "No, I don't understand"

"Hausar ne baki gane ba?" Hamdan ya faɗa yana kallon ta cikin ganewa. Su fa suna mata magana da Hausa amma har yanzu ƙwaƙwalwar ta baya ɗauka 

"Yeah, I don't understand"

"I meant, do you like that Fred guy?"

Rolling idanun ta tayi ko kallon shi bata ƙara yi ba ta cigaba da kallon ta. Murmushi Hamdan yayi yana me cigaba da kallon tare da ita be matsa mata akan tambayar ba. 

Lura yake yanda take yin murmushi idan aka nuna macen da namijin cikin show ɗin suna magana kamar abubuwan da suke faɗa yana birge ta. 

"You like this Fred" Hamdan ya ƙara commenting 

"Dadddd" Gumsu tace feeling embarrassed

Share yanda take embarrassed yayi ya sake ce "Do you have a crush? Anyone you like?"

"No Dad!" tace 

"Trust me, even Mom won't know about it. It'll be a secret between me and you and this living room"

Kallon shi Gumsu tayi tace "Nooo"

Murmushi Hamdan yayi ya tashi ya wuce. 

Ɗaga murya Gumsu tayi domin yaji abinda zata faɗa tace "You're so annoying Dad"

Murmushi ya sake yi be juyo ba be ce mata komai ba ya wuce.



              ***



Later in the day, ƙarfe 7.30 PM, Madina ta kawo food flask da ta zuba fried rice na ɗazu. 

Food flask ɗin ya buɗe da niyyar shi ze yi serving nasu, se yaga irin abincin ɗazu. 

Cire hannun shi yayi a food flask ya kalla Madina. 

"What's this, Madina?"

Bakin ta ta matse ta kalla food flask ɗin sannan ta kalle shi tace "Dinner, of course"

"You don't mean it" yace, ranshi na ƙoƙarin ɓaci "Dama da akwai Lahadin da muka ci dinner irin na lunch?"

"Naga abincin yayi yawa ku....."

"Ban gane kinga abincin yayi yawa ba? Idan abinci yayi yawa ba za'a iya ajiye wa a freezer ba gobe ayi microwaving nashi ba?"

Shiru Madina tayi tana kallon yatsun hannuwan ta. Gumsu su biyu take kallo se kuma itama ta saukar da kanta ƙasa tana kallon plates da spoons dake kan dining table. 

Tashi tsaye Hamdan yayi, cikin faɗa da ɓacin rai kaman in a very calm manner yace "You did this deliberately saboda kin san bana cin abincin da na ci a lunch a matsayin dinner. Shekara goma sha bakwai muna tare dake kin sani kuma da gangan kika yi wannan"

"I thought....."

"You thought nothing, Madina. We're making things easy for ourselves, muka yarda muka amince bamu da dinner a gidan nan on weekdays saboda aikin mu da irin aikin ki. But we agreed that you'll make tuwo and any kind of soup for us on Sunday for dinner. Isn't this our agreement?"

"Yes" Madina ta amsa ahankali 

"Then why are breaking it? it's a decision we made, the two of us. It's not as if I'm the only one that made it"

Shiru tayi ba tace komai ba. 

Juyawa yayi ya wucewar shi saboda shi baya iya cin abinci ɗaya ga lunch da kuma dinner. 

Kallon bayan shi tayi har ya ɓace mata. 

"Don't mind him" Gumsu tells her and Madina smiles. 

Serving fried rice din tayi wa kanta ta fara ci. Madina tace "Ba zaki jira tuwon ba?"

"No" she says "I don't mind. Will probably be asleep by the time you're done, so...." she shrugs her shoulders 

Kitchen Madina ta koma domin haɗa tuwon da ake son aci. 

Tuwon semolina ta ɗaura ta ɗaura miyar taushe. 

Koda takwas da rabi tayi ta gama tuwon semolina. Ƙarfe tara da ƴan mintuna kuma ta gama miyar taushe. 

Serving nasu tayi su biyu in the same plate ta same shi a ɗakin su. 

Tana shiga ɗakin tun kafin ta ajiye plates na abincin su tace "I'm sorry, Hamdan"

Plates din ya amsa daga gare ta and he offered a smile to her yayi squeezing hannun ta gently suka zauna suka ci abincin su.

Bayan sun gama cin abinci tayi shirin bacci ta zauna a couch shi kuma yana zaune a carpet na ɗakin suka fara magana. 

"Tomorrow is going to be hectic, Hamdan"

"A Monday after all"

"Yawwa, Kuma da laifin ka"

"Me nayi, Madina?"

"Ka sani yin tuwo ƙarfe takwas"

Murmushi ya fara yi yace "I'm sorry"

"Not accepted"

"Why?"

"My heart just refused to accept it"

"I'll have to use my other tactics then"

"Of course yes" tace mishi tana kallon shi bata murmushi 

Daga wurin da yake ya tashi ya dawo ya zauna kusa da ita, beside her. 

"I'm sorry, Love"

"Not accepted" ta faɗa tare da folding hannuwan ta a kirjin ta 

Hannun shi ya kai a jikin ta yana ƙoƙarin cire folding da tayi. Ƙin sakin hannuwan ta tayi ta riƙe su da kyau. Yatsun shi ya kai wurin cikin ta ya fara tickling cikin ta. Dariya ta fara yi sosai ta cire hannuwan ta unconcerned. Dariyar ta na cika bedroom ɗin su, quiet atmosphere na ɗakin ya chanja into something warm and lovely.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol