Free chapter 路 Read without an account

28

by Gidan Iko 路 GARWASHI






 *GARWASHIl*
                       
                     
    *Hadiza Bara'u Gidan iko*


............Kayan da aka Tara min na hidimar biki su suka nuna min matsayin dake gareni wurin yarima Gibson ba Dan kadan bane ba Kuma son wasa Yake min ba Ni da kaina naji da ace Babu wani kudiri a Raina Babu abinda zai Hana na karbi kaunar yarima Gibson don ba kowace mace bace tayi wannan sa ar ta zuwa Duniya don mijin ta ya sota Haka ba to Amma mun Dade da yin hannun Riga da Ra ayo yin juna Ni da Gibson

Amaka kuwa tafi kowa murna don tana ganin nafi kowane mace Dace musamman kayan da taga yarima Gibson yayi min Wanda ko a Gidan sarautar sai fa irin sarautar su igwai ake ganin wannan kabakin Arziki
.
Hadimai biyar mah ta turo min Wanda zasu Rika yi min hidima inda Kuma aka SHIGA hidimar biki gadan gadan inda naso mu samu kebewa da yarima Gibson Amma hidima Bata Bari ba

Na Kira Umar na fada mishi halin da nake ciki duk da a waya ne sai da na Gane firgitar da yayi Amma ya Soma nuna min girman iyaye da yi musu biyayya wajibi ne. Ko da Bai fito fili ya fada min ba nagane cikin tashin hankali yake don shi ya Riga Ni datse wayar duk da Ni na kiranshi abinda Kuma Bai taba yi min ba koni na kirashi sai in na katse 

Wannan abin shi ya Kuma tabbatar min da lallai Umar baiji dadin labarin Nan ba tunda gashi muryar shi bata boye min yadda ya karbi zancen ba. Sai naji gaba Daya hankali na yayi masifar tashi babu Kuma abinda nake so irin na ganni a gaban Umar inji abinda Yake damuwar shi Sai kuma zuciya ta tace min to sake Kiran shi mana ki tambaye shi?

Na kuwa sake Kira amma Bai daga ba sai da na jera mishi Kira yafi Akirga Bai dauka ba Kuma Bai maido min Kiran ba . Hankali na ya Kara tashi na Rasa abinda ke min Dadi na sake jaraba Kiran na kumayi sa ar samun shi har ya dauka

"Ka gafarce Ni Umar idan magana ta ta Bata maka Rai Ni ma na kasa sanin abinda zanyi don Allah ka fada min abinda zanyi.

"Aminatu ki sani ko da yiwa iyaye wajibi biyayya ne to Banda sabawa Ubangiji banji Dadi ba da wani ne Zaki Aura ba Ni ba Amma Kuma na yarda da kaddara in ke din ba matata bace babu yadda zanyi Amma kuma ina tsoron auren ki da Wanda ba musulmi ba don matukar ya Aure ki Kika koma karkashin ikon sa to gaki can ya mayar dake addinin shi don bana Jin zai yarda kina musulunci shi Yana kirista da ace dai shine musulmi to kema Haka Zaki kasance. Shawarar da Zan Baki ki fada mishi ko ke wacece idan ya yarda kowa yayi addinin shi to sai ki Aure shi idan Kuma bai yarda ba to ki Nemo mafita don ko ya yarda kiyi musulunci matukar shi din Bai musulunta ba to matsala ce babba idan kuka haifi Yara don duka Ya'yan ku shi zasu bi ba zai taba Bari suyi naki addinin ba kinga kenan Ashe kece babbar wadda zatayi Asara

Na gamsu kwarai da wannan maganar don Haka nace mishi yadda duk yace min hakan zanyi inda Kuma yace to na shawarci Gibson idan ya yarda kowa yayi addinin sa to muyi a Rubuce Kuma Suma yaran da zamu Haifa Suma mu sama musu matsaya guda Daya Tak akan addinin da zasuyi. Da Haka muka Rabu


Tuni na Gama kudurewa a Raina komai zai faru sai dai ya faru maganar Umar ta Kara tada min hankali Akan Wai yaran mu ma sai mun zaba musu addini yo Ni yaushe ma Zan tsaya Auren wani Gibson? Ai ko ya yarda nayi addini na ba Zan Aure shi ba musulunci kawai zai SHIGA na Aure shi shima don in Rabu da su Amaka lafiya abinda Kuma nasani ne zaiyi wahalar Gibson ya musulunta


Sai magaruba Gibson ya shigo inda na Gama sallar magaruba Ina Kuma sanye da hijabi na inda Kuma na karanto tarin mamaki Mai yawa a kan fuskar shi na gani na sanye da hijabi. 
Ya cika fall da mamaki Yana kallon tsakiyar idanu na har dai ya furta cewa me nakeyi da hijabi Haka ko zafi banaji?

Kai tsaye na bashi amsa da cewa salla nayi. Ya zaro ido Yana fadin meye? Na Kuma maimaita mishi abinda na fada 
Sai naga yayi murmushi Yana fadin baya son irin wannan zolayar shi fa duk abinda da ya shafi musulunci baya son shi wannan hijabin ma Kar na Kuma saka shi don kyamar shi Yake

Wani Abu naji ya tsiri zuciya ta Jin ya Fadi baya son musulunci kuma Yana kyamar hijabina

Na dube shi fuska ta babu sassauci na fito da tasbaha ta irin counter din nan wadda ake sakalawa a Dan yatsa na nuna mishi Ina fadin ba fa zolayar shi nake ba dama Ina jiran ya Zo ne don na ji Ra ayin shi idan zai iya Auren musulma idan kuwa ba zai iya ba sai mu hakura kawai

Ya zauna Yana kamo Ni zuwa jikin shi Wai zamuyi magana nayi saurin zare jikina daga gareshi

Ya dubeni Yana fadin baya fa son wannan wasan na canja mishi wani ni Kuma na fada mishi gaskiya ce nake fada mishi na Kuma nuna mishi inda na gama salla yanzu

Yayi min kallon da ya tabbatar min da ya Soma yarda da abinda na fada mishi kafin ya samu abin cewa Kuma na fito da Alkur ani Ina nuna mishi na Kuma kunna mishi waya ta Kira ar ta karade dakin inda ya Mike cike da tashin hankali Yana kallo na 

Ya Dade Yana kallo na kafin ya koma ya zauna Yana fadin. Nayi matukar mamaki da Kika zamo Haka gaskiya Justina Amma kuwa su mama sun San hakan? Nayi maza na kada kaina Alamar Basu sani ba shima don Naga yadda ya damu da sona ne kuma shima don dama Zan bashi shawara idan ya yarda da Auren mu a Haka NE yayi addinin shi nayi nawa ko Kuma idan zai yarda ya musulunta...........

Yayi saurin kada min Kai Alamar ba zai musulunta ba don in har yayi hakan to iyayen shi zasu kashe shi Amma ya yarda muyi auren kowa yayi addinin shi....
Nayi maza na tare shi da cewa to yaran da zamu Haifa fa? Su Kuma wane addinin zasuyi? Ya bani amsa da cewa nashi nayi maza nace ban yarda ba sai dai suyi musulunci shima yace Bai yarda ba sai dai mu bar yaran su zaba da kansu Wanda suka ga ya burgesu ko suka fahimci shine gaskiya sai suyi Kuma babu cusa akida babu canja musu Ra ayi nace na yarda Amma muje wurin igwai ayi komai a gaban su Kuma su zamo shaida don Kar daga baya yazo ya tada alkawarin...........


Kar ku Bari ayi tafiyar nan Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran



Gidan iko shine sunana kecewa saduwar ALHERI馃枻馃グ

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol