Free chapter · Read without an account

012

by SultyWrites · NI DA YA NABIL

_ NI DA YAYA NABEEL _


  _YOUNG WRITER✍️



* 012 *




" Wa annan tambayoyin duk ni kaɗai love". Ya fada yana dan Murmushin ƙarfin hali, kafin ya ce, "Ba sunan ta fauza ba, ta ɓatar da sunan ta ne Saboda a tunanin ta zaki faɗa min kuma kina fada zan gane ta shiyasa ta ce miki fauza, sunan ta Fatima Musa sunan smasher kuma ya samo asali ne a dalilin kaifin basirarta shiyasa ake kiranta da smasher. Na san smasher itama yar nigeria ce amma a nan tayi karatu, da a qarqashina take amma wasu halayya data ɗauko min yasa na canja mata team na cire ta daga tawaga ta, ashe tana riqe dani shiyasa ta haɗa kai da maqiyi na. Batun yadda akayi na san sunzo wurinki kuma wanna bashi ya kamata ki tambaya saboda kin san waye mijinki".

Jin yayi shuru ya sata cewa, "Baka gama amsa min tambayoyi na ba fa" 

"Me kikeci na baka na zuba ai zan fada miki ko dan ki ɗau darasi. Abokina ne ko nace amini na, tare mukayi karatu dashi a nan kasar, dan nigeria ne shi ma dan har muka gama karatu muka fara aiki bani da wani amini bayan shi, shaquwar dake tsakanin mu ta wuce tunanin ki, dan duk sauran abokan mu haushin sa suke ji saboda a ganin su shine yake hanani kula kowa, lokacin da aka fara mun qarin girma a wurin aiki lokacin ya fara ja baya dani nan kuma munafukai suka samu hanyar shiga tsakanin mu.

An sha faɗa min Al'ameen na mun bi ta da qulli ban taba daukan maganar da wani muhimmanci ba, duk da kuwa canja min da Al ameen ɗin yayi na damuna amma in na tambayeshi sai yace bakomai yanayin aiki ne, a haka aka cigaba da kawo mun maganganu kan Al'ameen kaza, Al'ameen kaza, yana bin diddigi na, hassada yake min waye² irin dai wadannan maganganun. Sai dai a duk lokacin da suka ambaci hassada murmushi kawai nakeyi domin nasan duk in da hassada take nasara na nan dan abokan tafiya ne in nasara na nan kuma dole hassada ta biyo baya, in hassada na nan to dole akwai nasara a wurin. Amma duk da haka ban taba nunawa Al'ameen komai ba, haka aka cigaba da min karin girma cikin lokaci kankani na yiwa abokan aikina fintinkau ke har ma na sama dani saboda jajircewa ta a aiki na, kasancewar son aikin a jijina yake.

 A lokacin ne kuma Al'ameen ya fito fili ya nuna shi cikakken makiyina ne I was very shocked dan abun ya tabani sosai, kasancewar sa mutum mafi kusanci dani kuma har lokacin inajin Al'ameen a raina, saidai shi kuma a lokacin ya fara amfani da wasu sirrika na da ya sani dan ya durkusar dani amma kamar taki yake zubamin, sunana ya fita sosai qasashe da dama sun fara neman qulla alaqa da Russia saboda ni. 

Al'ameen bai fita a raina ba sai a wani aiki da aka bani, na sha wahala kwarai kafin na samo bakin zare shi kuma a lokacin Allah ya ara masa dama ya wargaza min shirina, naji haushi kwarai da gaske kasancewar yana karkashina ne a lokacin sai na canja masa team nan kuma ya shiga aiko da saqonni marassa dadi iri ² bai kuma gajiya ba da son ganin bayan farin cikina har yau din nan da nake faɗa Miki, duk kuma wanna abun da ya faru cikin shirin sa ne, whl Assum Al'ameen ya koyamin darasin rayuwa wanda har na mutu bazan taɓa mantawa ba. Dalilin da yasa suke neman rayukan Ku kuwa saboda ku na Matsayin mata na ne dole ku ne rauni na idan wani abu ya same ku zan shiga tashin hankali, farin ciki zai qaura mun wanna shine dalili.

Su Arthur kuma nasa su daukeki ne tare da miki barazana da bindiga saboda akwai wa'anda aka sa su biyo ku, ta hakan ne kawai baza suyi tunanin ni nasa a daukeki ba amma kuma kika bata komai a cikin kasuwar nan saboda maganar da kika wa smasher, dan dama sun tari nan ne da shirin su saboda sun san dole ta nan zaku fito".

Dafe kirjin Asum tayi tana sauke numfashi kafin tace, "Wato ya Nabeel duniya abun tsoro dan adam abun tsoro, kaii jama'a Shiyasa fa akace makashinka na tare da Kai, kuma masoyin Ka wani lokacin ya kan juye ya koma maqiyin ka, amma ya Nabeel kayi kuskure daka nisanta su dakai domin maqiya maqale masu ake ko ba komai zaka san takun su. Kaga cire Al'ameen da kayi daga karkashin Ka shi ya bashi daman kafa nasa yankin har ya samu damar yaqarka, haka smasher ma hakan ne ya bata damar zuwa ta hada kai dashi dukda bansan abinda tayi ma ba ita".

"Hmmm smasher cewa tayi tana so na, ni kuma na nuna Mata bana ra'ayin ta amma bata hakura ba, ta dinga salon yau daban na gobe daban, abubuwa dai marassa daɗi, na taka Mata birki na kuma nisanta ta dani, sannan kema ina so in gargade ki karki yadda da kowa, domin mutum mugun icce ne ka masa dare ya ma rana, Ka janyo shi inuwa ya turaka rana, kiji tsoron dan adam Assum ki san ya zakiyi mu'amala da mutane karki yadda Ku zama so close da mutum".

 "Whl ko baka gargadeni ba ya Nabeel wannan labarin kawai yasa jikina yayi sanyi". Shuru ne ya ratsa dakin can tace, "Muje Ka rakani in ga Jumayma tunda ni naji sauki". Da mamaki ya ɗago yana kallon ta, he couldn't believe asum ke cewa zataje ganin kishiyar ta Jumayma, daƙyar ya shanye mamakinsa yace, "Baza ki bari zuwa anji....".

Katse shi tayi a shagwaɓe tace, "Ah ah ni dai hamma please mana". Dankwalin ta ya dauko ya miqa mata sannan ya taimaka mata ta sauko daga gadon, hannun ta cikin nasa suka fice.

 Dakin da jumayma take suka shiga tana zaune tare da wata cousin dinta dake aure anan kasar itama, ga wurin da aka harbeta nan a kafada manne da bandage, ba laifi jikin da sauki. Gaishe da matar Assum tayi ba tare data Kula kallon banzan da Jumayma ke jifanta dashi ba tace, "Jumayma ya karfin jikin?".

 A kufule tace, "Na warke rass tunda nasan ai ba haka kikaso ki ganni ba so kikayi kizo ki tarar dani tsakanin rai da mutuwa dan ki ji dadin kanainaye min miji, munafuka kawai". Ta faɗa tana hayayyaqo mata. Ƙasa Assum tayi da kanta tana mai jin zafin Kiran Nabeel da Jumayma tayi matsayin mijinta dan ita in suna tare mantawa take da cewa yana da wata matar ma, amma saboda shi ta daure duk da yadda take fama da masifaffen kishinsa ta danne tace ya kawota ta ganta dan yaji dadi.

 Riqo hannunta da yayi ne ya sata dawowa daga duniyar tunanin data tafi, baice komai ba ya jata suka fice daga dakin. Suna komawa dakinta cikin ɓacin rai yace, "Karki kara zuwa Inda take, ki rabu da ita tunda bata san ya kamata ba". Kallon daya ta masa ta fahimci yaji haushin abinda Jumayman ta yi mata ne kuma taji dadin yadda ya nuna bacin ran sa akan hakan, dan ta tabbatar da soyayyar da yake fada yana yi mata yanzu.

 Langwabar da Kai tayi tare da faɗin, "Eyyerh ya Nabeel maybe zafin ciwo ne fa dan Allah ka mata uzuri".

"Zauna ina zuwa". Ya fada yana kokarin fita, saurin shan gabansa tayi, "Dan Allah karka koma wajenta, karka mata fada". Cikin wani irin yanayi yake kallon ta, ya harde hannuwan sa a kirji, dan shi yanzu abun Assum ya daina bashi mamaki ya fara bashi tsoro anya bata samu matsala a Kanta ba kuwa yarinyar da ta gwammace ta yafewa kishiya mijin tsabar zafin kishi saboda kawai yayi waya da ita a gabanta amma yanzu itace take kare ta. Wani girmanta da qimarta ne yaji ya cika masa zuciya, ya kai hannu ya kamo fuskarta yana murmushi yace, "Kwantar da hankalin ki, ba wurinta zani ba zanje na karba miki sallama ne mu wuce gida".

" To Jumayma fa ?".

"Ya allah, wuce ki zauna ina zuwa". Ya fada ba tare daya bata amsa ba.

Komawa tayi ta zauna tana sake sake har saida ya shigo ya sanar mata an sallame su. Zata haɗa musu kayayyakin su yace ta barshi za'a zo a tattare. Haka suka fito hannun su cikin na juna, sojojin dake zagaye da hospital din suka take musu baya tare da bude musu mota, Saida Assum ta shiga sannan ya zagaya ya shiga, driver yaja suka fice daga hospital din.

 Ko da suka isa gidan ma gani tayi an kara matakan tsaro sosai. A daya motar dake bayan tasu taga Jumayma da cousin dinta ta sun fito ashe tare aka sallame su. Fuuu jumayma ta wuce su ta shige ciki kamar wata kububuwa, satar kallon Nabeel tayi taga hankalin sa ma baya kansu yana magana ne da wani jami'in su, tsayawa tayi jiransa saida ya gama sannan yaja hannun ta suka shige, zai nufi bangaren sa da ita tayi saurin faɗin, "Ya Nabeel barin je dakina nayi wanka". Ba musu ya saketa ta wuce dakin nata, komai tsaf² a gyare kamar da wanda ke rayuwa a ciki. Wanka kawai tayi ta kwanta bacci ya ɗauke ta dan har lokacin bata jin karfin jikin ta sosai.

Lokacin data farka har dare yayi, fita tayi ta samu Nabeel a dining sai juya abincin yake a plate amma ya kasa ci kana ganin sa kaga wanda damuwa ta kawo kai cikin rayuwarsa, yana ganin ta ya saki murmushi tare da bude mata hannun sa, karasawa tayi ta shige jikin sa tare da zama kan cinyar sa. Jan hancin ta yayi tare da faɗin, "Yau kinsha bacci fa, tun ɗazu nake duba ki naga ko kin tashi".

"Wash Allah, ni kam da jan hanci yana kara masa tsayi da yanzu nawa sai an yanke shi ya Nabil ka takurawa hancin nan". Murmushi yayi kawai yana kureta da ido. "Umm ya na ganka kai kadai? Ina Jumayma?". Abincin ya dibo a spoon ba tare da yayi magana ba ya nufi bakin ta, bude bakin tayi ya sa mata, da kansa ya dinga feeding dinta saida ta koshi sannan ta karbi spoon din shi ma ta shiga feeding din sa. Bayan sun gama ta wuce dakin ta.

Saida ya gama komai ya kwanta sannan ya ɗauki waya ya shiga Kira Assum ɗin sai dai har ta katse bata daga ba, sake kira yayi sai a lokacin ta ɗaga, "Sai kin sake fiddo ni ne?". Ya faɗa ƙasa ƙasa.

 Da mamaki tace, "Jumayman fa?". Shuru yayi kamar baiji ta ba, ta sake cewa, "Amma ya Nabeel in banyi kuskure ba kamar yau kwanan Jumaymah ne ita ya kamata ka kira ai, kar mu zama masu son kai".

"Okay thom nagode da tunatarwa yanzu zan kirata, ai mantawa nayi". Ya fada tare da kashewa.

 Wayar tabi da kallo tare da runtse idanunta wasu zafafan hawaye suka sauko mata, ina san ka mijina, ina so mu kasance tare har a aljannah ba zanso Ka kasance marar adalci b.... kuka ne yaci karfin ta ta shiga raira shi kamar wadda aka lakaɗawa duka. Ji tayi an dafa ta, a firgice ta ɗago dan batayi tunanin zuwan kowa dakin ta ba a wanna lokacin. Nabeel ta gani tsaye yana kallon ta, murmushi tayi ta shiga goge hawayen ta wasu na sake zubowa. Gefenta ya zauna ya buga tagumi yana kallonta, kame kame ta shiga yi, "Ya yaa..ya Nabeel me kake anan kuma ?".

"Meysa kike kuka bayan ke kikace in kirata?".

"Kuka kuma? ah ah ni ba kuka nake ba". Hawayen ya dangwalo tare da nuna mata, sai kuwa wani kukan ya sake taho mata, ta kifa kanta Kan cinyar sa ta cigaba da yi. Bai hanata ba ya shiga shafa bayanta saida yaga ta fara galabaita sannan ya dago ta ya rungume yana fadin, "Kukan nan ya isa haka love in dai ba so kike nima nayi kukan ba, bana son hawayen kin nan dan Allah ki bari karki wahalar min da kanki" 

" Amma yaaaa.....". Shiiiiiiiiiiii ya daura yatsansa Kan lips dinta, "Jumaymah ita tace in fara kwanakin daga kanki saboda bata da lpy, kafin na koma dakin ta ta sake samun karfin jikinta". Kallon sa take da alamun rashin yarda, hakan yasa ya zaro wayar sa ya Kira Jumaymah cikin muryar bacci ta daga, "Hello babe".

 "Naam sweetheart ba dai har kinyi bacci ba kefa nake jira". Ya faɗa yana kallon Assum data sunkuyar da kanta. " Eyyerh Kayi hakuri Babe ai na fadama ka fara yin kwanakin farkon wurin Assum tunda kaga ni banajin dadi zuwa lokacin da zaka dawo dakina kuma na dan Kara warwarewa".

 "Okay Thom Allah ya baki lpy sweetheart, have a sweet dreams of me"  Ya fada tare da datse Kiran ya zubawa Asum ɗin Ido. Kunya ne ya kamata ganin ya fada mata abu ta nuna masa rashin yardarta, kamar yasan mai take tunani kuwa yace, "Ada nayi kuskure amma yanzu ina kokarin kamanta wanna adalcin, ina tsoron Allah ya kamani da laifin tauyewa daya hakkinta dake kaina, asum bazan miki karya ba saboda kawai ina son kwana wajen ki".

 Ƙasa² tace, "Kayi hakuri to". Hancin ta yaja tare da faɗin, "Ban hakura ba".  Shagwabe fuska tayi tare da faɗin, "To me kake so nayi ka hakura" .

"A canja min suna daga ya Nabeel ɗin nan". Shuru tayi yace, "To shikenan barin cigaba da fishina".

"Ah ah Thom Beul habiby".

"OMG sunan yayi an babynah zo mu kwanta kar gari ya waye muna surutu". Ya karashe yana gyara kwanciyar sa tare da Mata masauki a kirjinsa yaja duvet ya rufe su .

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol