Free chapter · Read without an account
Chapter 15
by Hauwa Salihu · MATAR SALMAN
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
*đź’«MATAR SALMAN đź’«*
*➡️PART ONE*
*PAGE 15*
Maman Sakina ne ta je ta sami Mama a ɓangaren ta shiga bata hakuri, itama hankalinta ya tashi sosai.
Mama ta goge hawaye tana kallonta tace ”Rabi na rasa inda zan saka raina inji daɗi wallahi.”
Mmn Sakina tace "Amina matsalar da Rumaisa ke ciki fa kamar asiri ne fa, in kin lura lokaci guda ta fara abubuwanan.
Mama tace "Nima abinda nake tunani kenan Rabi domin lokaci guda Rumaisa ta sauya zuwa wannan mummunan halayyar.”
Mmn Sakina ta danyi shiru sai kuma tace "Amina ance zato zunubi amma inaga abinnan kamar a gidan nan aka mata fa.”
Mama ta tabe baki tace "Kin rigani a baki na riga ki a zuci ne Rabi, nifa tunda akayi babu daɗi akan maganar auren Rumaisa da Salman, naga Shatu ta goma gefe tayi shiru, hankalina bai kwanta ba. Amma Allah mun tuba.”
Mmn sakina ta ɗan waiga bayanta sannan tace "Da dadewa na jiyo hirarta da Sadiya tana cewa, indai ta yi amfani dashi shikenan bukatarmu ta biya, zakiga abun mamaki, dani suke zancan..... wlh Amina a lokacin ban kawo tunanin komai ba nama dauka ko Raihana ce don a kwanakin da ta dawo kamaru Raihana ta yi ta zuwa kiji sunata kus kus a daki na dauka ko itace, amma fa da naga halinda Rumaisa ta shiga sai na fara tunanin ko dai ita suka baiwa wani abun.”
Mama tace "Ba mamaki zai yiwu ai Rabi, don kina ganin Rumaisa kamar wayayyiya wlh muguwar wawiyace yarda da mutane take da wuri, sai su dauki abu su bata tayi amfani dashi ba tareda tunanin komi ba.
Maman Sakina tace ”To Allah dai ya kyauta, amma Amina Innarsu Salman abar tsoroce wlh ni kaina da kika ganni da kyar na sami lfy ni da yarana a gidan nan. Sai da na tafi kauyenmu gun wani kakanmu na nemo mana taimako sannan muka sami lfy.
Abinda za'ayi in Rumaisa ta warware gobe muje kawai koma me yake damunta insha Allah zamu dace, kuma ba malamin tsubbu bane irin mutanen nan ne da aljanu suka budewa ido wlh baya duba adduo'i kawai yake badawa sai rubutun sha kuma, da tofi sannan yasan magungunan gargajiya sosai.”
Mama ta danyi shiru sannan tace ”To ba matsala Rabi sai muje ai, Allah ya kaimu rai da lafiya goben.”
Mmn Sakina tace "Amin, to yanzu ki kwanta ni zan koma sai da safen.”
Sukayi sallama, ni dai ina ta sharar baccina ko a jikina. Da safe Mama tuni ta shirya tsaf ta dauki makullan mota ta fita sai gidansu Ya Salman. Abin mamaki ta sameshi kwance a Palo har da karin ruwa aka masa. Cikin mamaki ta karasa gabanshi tace ”Salman me ya sameka?”
Cikin karfin hali da jarunta irin tashi yace ”Goggo zazzabine kawai fa, shine na kira abokina Doctor James kawai naga dare yayi kuma banson in daga muku hankali, shine ya saka min drip din.”
Mama ta girgiza kai tace "Sannu Allah ya baka lfy, nasan duk sanadin Rumaisa ne ka shiga cikin wnn hali Salman, ni kaina ikon Allah ne kawai yasa na wayi gari haka.” Tana faɗin haka ta zauna tana dafe kai sai hawaye.
Ya girgiza kai da sauri yace "Goggo karki zubarma Rumaisa hawaye don Allah.”
Ta goge hawayen tace ”Salman ya zanyi ne da raina, duk inda na saka kaina babu daɗi, Rumaisa ta daga mana hankali, gaka nan kwance har da drip, ni ban taɓa jin ko ciwon kai kayi complain ba.”
Runtse ido kawai yayi, shi kaɗai yasan zafin da yakeji a zuciyarsa amma ya daure yace ”Goggo Amina kidaina saka damuwa a ranki, kuma nima ai naji sauki sosai, kinga drip din kawai nake jiran ya kare na cire na tafi nayi breakfast ko Inna ma basu sani ba.”
Mama tace "Allah ya baka lfy Salman.”
Yace "Amin ina zakije dama?”
Tace "Ai zama bai ganni ba Salman, zamuje mu nemawa Rumaisa taimako akan wannan matsalar.”
Yace ”Amma Goggo menene kike ganin kamar yake damunta?”
Tace ”Ban sani ba Salman amma wadan nan abubuwa ba a banza takeyinsu ba. dole in tashi tsaye wurin ne ma mana magani.”
Shiru ya danyi sannan yace "Goggo da dai kinci gaba da mata addu'a sai kiga koma meyene Allah zai yaye mata.”
Ta yi ɗan murmushi ta ce ”Hakane Salman addu'a kam kullum a cikin ta muke sai dai kasan Allah ma yace tashi in taimakeka koh?”
Shiru yayi mata kawai ganin kamar hankalinsa bai kama ba yasa tace "Karka damu Salman ba gun malaman tsubbu zanje ba, ko kadan bazan yarda na kauce ba ka kwantar da hankalinka.”
Ya gyaɗa kai Cikeda gamsuwa yace ”Shikenan Goggo na fahimceki Allah yasa a dace kuma.”
Mama ta ce "Yawwa Amin Ya Allah.”
Suna cikin hala Doctor James ya shigo da sallama suka gaisa da Mama da ta mike ta kalli Salman tace ”Yawwa Salman tunda naji kace Salim ma zaizo ga nan makullin motarda Rumaisa ta kawo a maida wa maishi kawai bama bukata.”
Ta ajiye makullin a gabansa sannan ta fita.
Ina tashi na koma sashin Mama nayi wanka na shirya don Maman Sakina tace akwai inda zamuje. A raina nace ”Allah ma yasa gidan Babana zata kaini in huta da matsalarta itada da Ya Salman.”
A palon Abba na sami Mama nima na zauna na gaisheshi.
Nasiha ya dinga min sosai har da ayoyi ya dinga ja min, nikuwa ina karasa masa a zuciyata. Mama kam shiru kawai ta yi har Abba ya gama sannan muka tafi.
A baya na zauna Mama ke tukin motar Mmn Sakina a gefenta,
Suna hirarsu har muka isa don kauyen ba nitsa sosai.
Gaskia har na manta rayuwar kauye.don haka komai sai ya dinga bani dariya.
Gidan da mukaje babban gidane na wani malami don harda almajirai muka tarar a waje suna karatu don haka muka wuce cikin gidan. Aka kawo mana tuwon dawa miyar kuka da yaji man shanu, gaskia nikam zagewa nayi naci. Mama kam sun kasa ci sai masara aka gasa musu sukaci.
Har sai bayan azahar Malam ya turo muje.
Sosai suka dinga hira da Maman Sakina ya na tambayarta labarin birni. Sannan daga bisani ta yi masa bayanin komai da ke tafe damu.
Nan ya kalleni na wasu seconds ya danyi shiru sannan yace "Zai iya yiwuwa asirin ne don gaskia bata da aljannu. amma akwai maganar sakaci da addini ma.”
Ya kalleni yace "Rumaisa kafin hakan ta faru kin taba yin wani mugun mafarki?”
Shiru na danyi sannan nace "eh nasha yinsu.”
Yace "Kamar me kike gani a mafarkin?”
Na ce "Eh to na taba yin mafarkin wata mata ta sokamin wuka a ciki, sannan ina mafarki maciji ya sareni ko kare ya cijeni.”
Ya gyada kai haka yaci gaba da min tambayoyi ina bashi amsa daga karshe yace ”Allah ya sawwaka yanzu zan baku adduo'i da zakuyi sannan za'ayi amfani da ganyen magarya insha Allah indai asiri ne to kome karfinsa bi'iznillah zai karye. Amma fa adduo'in da yawa kuma sai kun jajirce kuma akwai na tofawa a ruwa tasha ta kuma shafawa kullum har tsawon wata guda babu fashi, daga nan fa zakuga sauyi in Allah ya yarda, kuma ku godewa Allah abun bai gama shiga jikinta sosai ba, karyeshi bazai yi wuya ba, Allah dai ya bamu sa'a.”
Mama ta gyada kai cike da gamsuwa tace "Amin Baba, kuma in Allah ya yarda Baba zamuyi kuma mun gode matuka.”
Yace "Babu komai sai dai kuma ina mai bata shawara ta rike ibada hannu bibbiyu adduo'in safe da yamma kar ya wuceta sannan duk abinda zatayi ta fara da addu'a.”
Mama ta kalleni tace ”Kina dai ji koh? Tom.”
Kai na daga mata don ni tuni na gaji da zaman maganar tasu ma haushi yake bani. Sun jima suna tattaunawa, sannan daga bisani ya bamu komai a rubuce da bayani dalla dalla.”
Sai kusan magrib muka dawo.
Mama kam ba alamun wasa a fuskarta duk wayoyina ta kwace ta kashesu sannan tace a dakinta zan koma kwana.
Da kanta ta dinga min tofi a ruwa ta ban na shanye a gabanta. Sannan da asuba ta tasheni bayan mun idar da sallah ta sakani gaba sai nayi azkar din safe na karanta Qur'ani izu biyu don rabawa mana tayi tace ko wani Safiya zamu dinga karanta izu biyu.
Ranar Monday misalin karfe shidda da rabi na gama shirin tfy mkrnta nayi breakfast duk abin nan idanunta na kaina har na gama ta karbi jakata ta dudduba sosai sannan ta kalleni tace ”To jirani inzo in kaiki.”
Ta shiga ciki ta dauko hijabinta da key din motarta muka fita. A waje muka hadu da Ya Salim da Ya Salman suna shirin shiga cikin gidan su kuma, nan suka gaisheda Mama nikam idona na kan Ya Salman yayi matukar kyau cikin kakinsa kamar na rumgumeshi nakeji wallahi.
Shiko baima san ma inayi ba, don haka na danyi gyaran murya nace "Yaya ina kwana?”
Ba tare da ya kalleni ba yace "lfy lou.”
Nayi murmushi nace ”Ya jiki kuma?”
Banza ya min don haka na kalli Ya Salim nace "Yaya jiya bamu ko gaisa ba kazo lfy ya kabarsu Ummie?”
Yace "kowa lfy lou.”
Sannan ya kalli Mama yace "Goggo ina zakuje?”
Mama tace makaranta zan kai ta dama.”
Salim yace ”Haba Goggo gamu nan, ai ki bari muje na kaita ki koma gida ki huta.”
Ta girgiza kai tace "a'a Salim gabadaya ni yanzu na ajiye komai zan kula da shiga da fitan Rumaisa har sai ta karasa makarantar nan sannan ta fito da miji ayi mata aure na huta.”
Salman yace ”Goggo ki bar komi a hannunmu kekam kije gida, na miki alkawarin zamu saka ido akan duk wani shige da ficenta a garin nan.”
Mama ta sauke ajiyar zuciya tace ”To shikenan Salman kuma don Allah karku saurarawa Rumaisa in har ta aikata ba daidai ba ku hukuntata.”
Kallona yayi nima yaga idona akansa amma muna hada ido ko tsoro banji ba na maka mishi harara na É—auke kaina. Mama gida ta koma.
Ya Salim ya kalleni yace ”Ɗan jiramu bari muje mu gaida su Abba sai muzo mu tafi.”
Bata rai nayi na turo baki nace ”Ni gaskia nayi letting.”
Ya Salman kam tuni yayi shigewarsa ciki fuskar nan a daure.
Ya Salim yace ”Ki jiramu nace ba dadewa zamuyi ba.”
Ya shiga ciki shima na bisu da harara.Basu jima ba suka fito muka tafi.
Ya salim a hanya shima fada ya dinga yi min. Ni dai gani nake kamar kowa ya tsaneni yanzu. Har muka isa Ya Salman kam baice komai ba.
*
Haka sukaci gaba da sanya ido a dukkan lamurana na fuskanci matsi da takura sosai a lokacin.
Ahmad ya nemeni a waya har ya gaji kawai ya sameni a school rannan anan ya nuna bacin ransa akan wai Ya Salman da Ya Salim sunje sun maida mishi motarsa kuma sun masa kashedi akaina.
Nima na gaya mishi yadda suka takura min a gida kwanan nan amma nace ya kwantar da hankalinsa so nake a gama exams ne nasan yanda zan bullo musu, ai dai in na bar musu garin ba shikenan ba, don wallahi gudu zanyi, haka na lallabashi ya tafi.
Salima da kawayenta ya kasance duk inda muka hadu sai sun zageni suce min karuwa saboda Ahmad ya kasa rabuwa dani alhalin ba aurensa zanyi ba. Ni dai bance musu komai ba don ba ta kansu nake ba. Allah Allah kawai nake muyi exams mu gama, ina shawaran garin da zan tafi, don kudi kam inada shi ko haya zan iya kamawa inyi zamana, inaga ma ko Lagos kawai zan gudu abuna.
Mama kuwa ta dage da adduo'in nan ba wasa, Ni har na gaji da shan tofi da sauran abubuwan shafe shafe da take bani especially ganyen magaryan nan duk randa ta shafa min sai jikina yayi kaikayi kamar nayi hauka, don ma dare dare ne mukeyinshi shi. Ina dai shan azaba kawai. Amma kuma hankalina ya É—an soma dawowa da nitsuwata tunda har ina zama inyi karatun exams dina.
*
Sai wani sabon al'amari kuma tunda muka fara exams nakejin kaina na ciwo kadan kadan addu'a kawai nake kar ya hanani jarrabawata don wani lokaci haka kawai sai inji kan nan ya wani sara har naji hankalina yana barin jikina sai a hankali nake dawowa dai dai kuma.
Anan naje nayiwa Doctor Hakim complain kasancewarsa General Doctor, ya rubuta min magunguna, kuma na sha amma shiru kakeji, ciwon kai sai abinda yayi gaba, wani lokacin har idona bana iya budesu da kyau.
Allah ya karbi addu'ata randa muka gama exams ina fita hall kawai na yanki jiki na fadi ji nake duniyar na juyawa dani. Jin dalibai nake sama sama sun kewayeni suna me ya sameta ko ta suma ne? a zo a kaita clinic.
Daga haka nidai ban kuma sanin inda nake ba har tsawon kwana huÉ—u. Sannan na fara gane wayanda suke kaina.
Mama na gani sai Fa'iza da Sakina. A hankali na bude baki ina jin kaina na min nauyi nace "Sis yaushe kuka dawo?”
Sai naga fuskokinsu cike da mamaki suna kallona Mama ta rike hannuna tace "Rumaisa kina nufin kin ganemu?”
Nace ”Mama na ganeku mana ai nasan lokacin da na fadi dazu ne aka kawoni nan kuma a ka sanar daku a gida koh, kawai ina fita hall jiri ya ɗaukeni.....
Ta girgiza kai tana murmushi tace ”Rumaisa yau kwananki huɗu anan baki san inda hankalinki yake ba, ba kya gane kowa.”
Na mike da sauri don mamaki, sai naji kaina na juyawa kuma, da sauri na koma na kwanta ina runtse ido
Da sauri Mamama ta rike ni tace "kwanta kwanta bari na kira Doctor. Sakina ku kula da ita ina zuwa.”
Mama ta fita anan su Fa'iza suka shiga yi mun sannu. Doctor Hakim ne ya shigo. Nan ya kalleni yayi murmushi yace "Rumaisa ya jiki?”
Nace ”Da sauki Doctor.”
Ya gyada kai sannan yace. "yanzu me kk ji?”
Nace ”ciwon kai kadan kadan sai jiri kuma ina jin tsigar jikina na tashi.”
Anan ya gwada min bp sannan ya kalli Mama yace "Mama kinga jininta ya fara sauka ma yanzu dai Alhamdulillah, abinda za'ayi a sama mata abinci taci tasha magungunanta mugani zuwa anjima zan dawo in sake dubata, InshaaAllah ba wani abu.”
Mama tace "To Doctor mun gode sosai.”
Yayi murmushi yace ”Babu komai Mama Allah ya bata lfy.”
Mama ta ce amin. Anan ya fita.
Mama tasa min abinci na danci nasha magunguna na kwanta anan bacci yayi awon gaba dani. Har yamma na tashi naga Ya Salman da Ya Salim da Abba sun shigo suka min sannu da jiki. Naji sauki sosai Ahmad ma yazo don su Ya Salman na fita ya shigo cikin shigan manyan kaya kamar bashi ba. Ya gaisheda Mama da ladabi sannan ya kalleni yace "Queen ya kika karaji?”
Ba tareda na kalleshi ba nace ”Da sauki waya fada maka banda lafiya?”
Yace "Juliet ce.”
Daga nan shiru na masa. Har ya kari zamansa sannan ya tashi bandir din dubu dubu ya fitar ya ajiye a gefena sannan ya kalli mama yana sunkuy da kai kamar na Allah yace "Mama Allah ya bata lfy na tafi.”
Mama tace "kuma har da dawainiya haka? To mun gode Allah ya saka da alkhairi, a gaida gida.”
Ni dai ban kuma ko kallonsa ba har ya fice.
Mama ta kalleni tace ”Wai waaye wannan din kuma?”
Nace "Ahmad ne......
Ai ko kan na karasa naga Mama ta kura min ido ido cike da mamaki tace "Au shine Ahmad din, ɗan gwamnan?”
Shiru nayi, itama bata sake ce min komi ba.
Sati na daya aka sallamoni.
Amma gabadaya na kasa sakewa duk da su Fa'iza na nan amma wnn karon basu gane min ba, daga wannan lokacin nayi wani sanyi wanda har yanzu ban sake komawa Rumaisa na na farko ba.
Banda aiki yi sai kuka, nadama mara adadi ya shigeni, na rasa inda zan saka kaina naji daÉ—i a duniyar nan!
Sunyi rarrashin duniya sun gaji haka ma Mama.
Ranar da daddare bacci ya gagareni don tsabar bakin cikin rayuwa, nayita juye juye na gaji na tashi na tafi dakin Mama banyi mamakin ganinta akan sallaya ta idar da sallolinta tana karatun Qur'an ba. Kusa da ita na zauna dan haka ta sami aya ta tsaya sannan ta rufe Qur'ani ta kalleni tace "wai ke Rumaisa har yanzu bazaki bar wannan kuka ba? Da kyar fa jininki aka samu ya sauka bayan athsma kina son sakawa kanki hawan jini karfi da yaji, kina 'yar karama dake amma kina son ki dorawa kanki damuwa. To bari kiji in dai da tsawon rai to baki fara komai ba a rayuwarki tunda ba kiyi aure ba baki haihu ba, abinda yake gabanki yafi na baya yawa don haka gara ki rage damuwa ki barwa Allah lamarinki domin babu abinda ya gagareshi.”
Hawaye na zubowa nace "Mama wlh abubuwanda ya faru dani yasa naji komai na rayuwa ya fitan min a rai Mama ni kunyan kowa nakeji a gidan nan musamman Ya Salman da Abba, wallahi bansan me ya hau kaina ba nima.”
Na karasa maganar cikin matsanancin kuka. Jawoni tayi jikinta tace "ya isa haka nan kukan, haka ke kuma taki kaddarar baki isa ki tsallakeba, kuma ki daina dawoda hannun agogo baya ki bar wannan maganar don ya wuce sai dai a kiyaye gaba, kuma kinga sakaci da addini shi ya ja miki, da ace kin rike addininki hannun bibbiyu wani abun ko zai sameki sai kiga yazo da sauki.”
Na gyada kai ina goge hawayena nace "Mama ina zargin wani abu gameda wani maganin da Inna ta bani, domin tunda na fara amfani dashi na soma jin yanayina na canzawa na fara jin ciwon kai, sannan daga baya kuma marata.......
Anan na bata labarin yadda na fama da yadda mukayi da Inna da Sadiya akan wannan maganin.
Shiru tayi ta zuban ido sannan daga bisani tace "Rumaisa duk bakinda ya furta baya sonka, daga baya ko ya dawo yana sonka karyace, ki kula da wannan a rayuwa. Su kuma su suka sani da mahaliccinsu, yanzu dai da fatan kin hankalta, kuma in Allah ya kaimu rai da lfy gobe kije ki gaida Abba da Salman ki nuna musu nadamarki.”
Na daga mata kai.
Daga nan na koma daki na shiga toilet na dauro alwala nazo na hau sallayata nima.
Da safe har 10:00am na tashi don haka na fada wanka bayan na fito na shirya tsaf.
A Palo na sami Mama da Fa'iza da Sakina suna breakfast sai hirarsu suke.
Suna ganina Fa'iza tace "Queen an fito knn?”
Harara na sakar mata nace "Nace bana son sunan nan ko?”
Tace "Ai ko baki so dashi zan kiraki tunda haka naji 'yan makarantarku ke kiranki duk wanda suka je dubaki a asibity, ohh kinga mutane kuwa lalle ke me jama'a ce.”
Sakina tayi dariya tace "Ranki ya dade Queen of beauty.”
Fa'iza tace "amma fa na BUK.”
Shiru na musu na ficewata cikin gida, ɓangaren Abba na shiga kasancewar yau Sunday yana nan, muka gaisa anan na shiga bashi hakuri.
Murmushi yayi yace ”Ni kuma me kika min Rumaisa? Ai babu komai Allah dai ya kara shirya mana.”
Kaina na sunkuyar, yace in tashi inje, daga nan dakin Mmn Sakina na shiga na gaisheta itama,
Sannan na tafi dakin Inna na sameta da Sadiya suna hirarsu harda dariya.
Suna ganina naga yanayin fuskarsu ya sauya a take Sadiya tace min ”Lafiya kika shigo mana babu sallama?”
Fuskata a daure nace "Ai baza zaki ji sallamata ba kina dariya shewa kamar ba musulma ba.”
Dariya ta kuma yi race "au dariya da shewa ma laifine kenan?”
Tsaki nayi nace "Ni ba wurinki nazo ba.”
Na kalli Inna wacce naga gabadaya ta zuba min ido taji me zance. Na mika mata robar maganin data bani nace "Inna maganin da kika bani naji dadinsa kwarai da gaske, don nayi amfani dashi yadda ya dace, kuma yayi aiki yadda aka tsara, ga nan robar na dawo miki na kuma gode sosai Allah ya biyaki abun kika min.”
Gabadaya sai naga mamaki ya bayyana a fuskarsu. Yayinda tuni hawaye ya ciko idona na ajiye robar na juya na fita.
Gidansu ya Salman na tafi shima na sameshi ya shirya zai fita aiki. Sallamata tasa shi juyowa muka hada ido da sauri na sauke idona kasa duk sai naji kunya kamar na nitse.
Tunda ya amsa sallamar bai kuma ce min komai ba.
Na daure nace ”Yaya ina kwana?”
Bai amsa ba kuma baida niyar amsawa.
Durkusawa nayi har kasa a gabanshi nace ”Don Allah Yaya kayi hakuri ka yafe min laifin da na maka wlh ba laifina bane na wayi gari kawai na tsinci kaina a cikin mummunan yanayinda nima bansan yanda akayi ba, duk abinda ya faru kasan ba halina bane Yaya.....
Na kasa karasa maganar kuka yaci karfina.
Ido ya zuba min kawai, don shi kadai yasan me yakeji a ransa gamedani.
Ya dai daure yace ”Shikenan na yafe miki amma.....don Allah ki daina zuwa inda nake don ban son ganinki sam sam!”
Na girgiza kai ina kuka nace ”Yaya idan kamin haka baka min adalci ba...... don Allah ka daure ka manta da abinda.......”
Cikin tsawa yace ”Ke!....ki tashi ki tafi nace bana son ganinki......”
Cikin kuka nace "Yaya wlh bazan iya wannan horon ba gara ka min wan......”
Yace "Ok tunda bazaki tafi ba ni bari in bar miki gidan.”
Ya tashi da sauri a zuciye nima na tashi na fita ina kuka na bar mishi gidan, shikenan burinsu ya cika sun saka Ya Salman ya tsaneni!
Tun daga nan fa komai ya birkice tsakanina da Ya Salman don gabadaya baya ko son jin muryata a sanadin hakan har ya daina zuwa kofan Mama, nikuma ji nake kaunarshi na karuwa a zuciyata kowane dakika Ya Allah!
Kafin mu gama hutu tuni har an anzo anyi maganar auren Fa'iza da Sakina hakama ya Salim anje an masa tambaya don so ake a hada gabadaya ayi shi a karshen wannan shekara wato December, dama an É—aga ne saboda Ya Salman da Ya Salim su karasa gininsu, To yanzu sun gama. Abie kuma ya ware musu kudi masu tsoka saboda hidimar bikinsu, ga kuma business da ya dorasu sunayi a gefe, dalilin da yasa ma kenan ya shiga ya fita har saida aka dawoda Ya Salman aiki a Kano.
Sai dai zakusha mamaki nasani domin Ya Salman yace shi bai gama shiryawa ba tukunna ba yanzu zaiyi auren ba. Abba suka sakoshi a gaba akan ya fada musu meye matsalarshi?Yace ba komai kawai shi ba yanzu zaiyi auren ba.
Su Abie suka kirani nima suka tambayeni ko dai akwai wani abu da ya hada mu ne?
Nace nide babu, in ma akwai to banda masaniya. Anyi juyin duniya dashi ya fadi mecece matsalarshi amma ya kafe kan ra'ayinshi wanda a karshe Abie yace wa Abba su barshi a hankali zasu shawo kanshi, domin sun kuma fahimtar gabaÉ—aya Salman ya sauya.
Inna kam babu wanda ya kaisu farin ciki domin komai na tafiya yadda malaminsu ya tsara musu a nasu tunanin fa kenan.
Nikam nayi kuka har na gode Allah Mama ta ce in yi hakuri kawai mu barwa Allah komai.
Gaskia wannan karon hutun baiyi dadi ba har aka bude makaranta su Fa'iza suka koma ni kuma naci gaba da zuwa ina dawowa ganin na nitsu hankalina ya dawo jikina yasa Mama ta barmin motarta da kaina nake zuwa in dawo kuma Alhamdulillah na daina kula kowa dama ni ba wani kawayene dani ba kunsani, don haka in naje abinda ya kaini kawai nakeyi in mun gama lectures na dawo gida, anan ma ba na fita daga kofar Mama, na daina kula harkar kowa.
Ya salman tuni na watsar da lamuransa don na gane ba son aurena yake ba, shiyasa yake wani cewa be shirya ba.
Ahmad kam ba yanda baiyi dani ba mu koma kamar da amma naki na saurareshi don haka ma nace mishi in har da gaske yana sona to ya bar shaye shayen nan yazo muyi maganar aure don ni aure zanyi.
Tunda mukayi haka dashi bai kuma nema na ba, haka ma Fahad muka rabu daga randa nace ni aure zan yi.
Yanzu Doctor Hakim ne kawai ya rage yana ta bina akan na amince ya turo magabatansa nace mishi sai nayi tunani.
Watarana na dawo makaranta sai na shiga cikin gida ɓangaren su Inna don in duba jikin Zainab don tana zazzabi duk kwanan nan Mamana tace min. A tsakar gida naga wata budurwa wacce kusan zamuyi sa'a fara sol kyakkyawa doguwa ga gashi kam har gadon baya, da ga gani ba tambaya 'yar kamaruce don tana shigen yanayi da Inna.
Muna hada ido sai naga ta harareni ta shiga palon Inna hannunta daukeda kulan abinci da plate.
Murmushi nayi na wuce dakin Mmn Sakina ina mamakin ita kuma wacece, bayan na gaisheda Mmn Sakina na tambayeta jikin Zainab don tana bacci.
Tace "Jiki kam da sauki sosai Rumaisa yau kun tashi da wuri”
Nace "Eh munyi test ne.”
Muka danyi shiru nace "Mama wacece na wuceta a tsakar gida?”
Tace "Inaga Latifa ce ai 'yar Yayan Inna, ta miki magana ne?”
Nace "a'a kawai naga ta na min wani irin kallon banza ne, kamar mun taba haduwa hakan nan kuma ni ko aurensu Sadiya ma ban ganta ba.”
Mama ta tabe baki tace "Ai wnn haka takewa kowa, gogaggiyar 'yar duniya ce daga gani don in kinga rashin kunya da takeyi a gidan nan sai kin rike baki, gara ma da baki shigowa nan ɗin, don tuni Sadiya ta gama gaya mata komai akan kowa, wai naji Inna na cewa itace Salman zai aura, amma sam batada respect Allah dai ya kyauta ya kuma shirya mana.”
Dan murmushi nayi cikin karfin hali nace "Amin Mama bari in isa side dinmu, ayi ma Zainab sannu in ta tashi Allah ya sawwaka.”
Tace ”To Rumaisa zataji na gode, kice Mamanki zan shigo anjima.”
Na tashi na fita ina amsa mata da to kawai, don hankalina sam baya jikina, A tsakar gida na sami Inna tana aikace aikacenta.
Na gaisheta ta amsa hade da fadin ”kira min Sadiya a palo Rumaisa.
Nace "To.”
Tun kan na shiga palon naji kamshin turaren Ya Salman wannan ya bani tabbacin ya na palon kenan.
Na daure na shiga da sallama wata tsiririyar murya naji ta amsa min. Na shiga nan da nan naji kirjina ya soma bugawa.
Ya salman yana zaune ita kuma tana zaune kusa dashi ko É—an kwali babu akanta ta zuba gashi har tsakiyar bayanta.
Abinci yakeci ita kuma tana mishi hira da fulatanci kamar mai rada ta wani kwantar da murya tsabar iya kisisina kamar zata shige mishi jikinshi.
Nayi matukar kokari nayi controlling din kaina na kauda ido na akansu na wuce dakin ciki labule na daga na kalli Sadiya dake shirya Abdul nace ”Sadiya Inna na kiranki."
Duk da ma nagane ba aiken gaske Inna ta min ba kawai tana so inje inga Ya Salman da wata ce.
Don koda na fita sai naga fuskarta cike da fara'a tace min kin kirata?
Nima murmushi nayi nace ”Eh Inna tana zuwa ma.”
Tace ”To nagode.” ta faɗa tana bina da ido.
Nikam nan na wuce kofar Mama. Amma duk yadda na so na daure abun ya gagara don haka kawai kuka na shiga yi ni kadai nasan me nakeji a zuciyata a wannan lokacin. A haka Mama ta sameni tace "Yau kuma meye faru?”
Nace "Mama Ya Salman da gaske ya daina sona ya sami wata, Inna ta samo mishi mata a garinsu.”
Shiru tayi ta rasa me zata ce min can ta numfasa tace "Kinga Lathifa kenan?
Na dago ina kallon Mama nace "Mama dama kema kinsan tazo ne?”
Ta ce min ”Na sani Shatun ce ma da kanta take sanarda ni ta zaɓawa Salman matarda zau aura, gata tazo, kuma ta kara ja min kunne akan alakarki da Salman don bata so.
Don haka abinda nake so dake ki kara hakuri komai zai wuce kinji?”
Na share hawaye nace ”Haka Inna tace miki Mama? To shikenan inshaa Allah daga yau na daina zubda hawaye akan Ya Salman kuma na hkr dashi ni zan bawa Doctor Hakim dama ya turo magabatansa kawai.”
Tace "Rumaisa karfa ki biyewa zuciyanki kije ki auri wanda bashi kike so ba, ki sake tunani, shin kin shirya auren Hakim? kin yarda zaki zauna dashi a kowace irin yanayi?
Sannan aure fa idan kinyishi ki tabbatar kinyi kenan mutu ka raba ba wai zuwa zakiyi ki dawo ba. Saboda haka kar ranki ya baci kije kima kanki zaben tumun dare.”
Nace "Ko kadan Mama Hakim ya dade yana bina tun farkon zuwata jami'a kuma duk abinda ya faru dani ya sani amma bai taba nuna min kyama ba dai dai da second daya kuma tunda muke dashi maganarsa dayace bai wuce in yarda in aureshi ba don haka inaga yanzu lokaci yayi da zan bashi wannan damar.”
Jikin Mama yayi sanyi na lura sai kawai ta ce "To shikenan idan har hakan ta kasance bazanyi bakin ciki ba sai dai in sanya albarka. sai dai Allah yasa su Yaya su fahimcemu, don har gobe so suke su daidaita maganar ki da Salman.”
Nace "Karki damu Mama zasu fahimcemu InshaaAllahu.”
Daga nan fa na dage na fara cusawa kaina tsanar Ya Salman. Tuni nayi wa Doctor Hakim albishir daya turo magabatansa kuma banson auren ya wuce nan da wata daya tunda yace ya shirya to nima na shirya É—in.
*RUMAISA SALMAN BY MAMAN KAUTHAR*