Free chapter · Read without an account
12. The Family
by Zainab · TSAƘANINMU
TSAKANINMU
Bayan sun dawo masallaci aka zauna a parlour.
Maza a tray ɗaya suka ci abinci harda Abba, matan ma haka, hannun kowa a cikin tray no difference.
Shi de Hamdan yana gama cin abinci, ya sha kunun gyaɗar da matar Rashid ta taho musu dashi.
Cupcakes da Jawahir tayi suka fara ci kowa se praising nata yake. Zuciyar ta ta cika da farin ciki sosai, tana sanin it was Yaya Hamdan that brought her passion to life.
Su na nan duk zaune, aka kira wayar Jawahir me cupcakes ya zo amsa.
Me hidimar su tace wa yana kitchen ɗin ta ta ɗauka ta kai mishi.
Koda ta fito ta ga the same guy da yazo kwanakin baya har yana cewa ita me yin kayan fa.
Box na Cupcakes ɗin shi ta bashi ya ajiye a gaban seat na motar shi, Camry.
"Ko dai kene me yin kayan?" ya tambaya handmaiden saboda shi dai yaga ba ita ya gani a jawahirmusawa handle a Instagram ba amma kuma yanzu sau biyu tana kawo mishi saƙon shi.
"A'a, bani bace ba"
"Kije ki cewa wacce tayi kayan, ina so zan gan ta"
Wani kallo handmaiden ta mishi shi kuma ya tsare ta da idanun shi yace "Ina jira"
Wucewa ciki tayi ta samu Jawahir cikin familyn ta. Kowa na ganin ta yayi shiru yana sauraren abinda zata ce.
"Wanda ya amsa saƙon shi yace ina me haɗa kayan yana son ganin ta"
Hamdan yana jin abinda tace amma ko ɗago kanshi be yi ba ya cigaba da abinda yake.
Ahmad yace "Ki je kice ba zata zo ba"
"Kai kuwa dai Ahmad! So kake ka korar mata customers ne? Consumer is a king fa, no ba za'a yi haka ba. Kasan ko abinda ze faɗa mata can't be conveyed by another person ko yaga kayan ta sun mishi sha'awa sosai he'd want to help or something, no pls, ba'a yin haka" Aunty Madina ta faɗa
Tsaye handmaiden tayi tana jiran amsar da zasu bada saboda taga suna magana akwai masu kawo dalilin kar Jawahir ta tafi.
"5minutes, kika ga ɓata miki lokaci ze yi ki dawo" inji Khalifa
"Ba kuma kai ke so ta kawo miji tayi aure ba. Idan bata kula su ba ta yaya za'a yi auren?" inji Rashid
"Wanda yake son ta da aure, gamu duk nan ya taho ya fara mana magana tukuna kafin ya isa gare ta" Ahmad ya amsa
Tashi Jawahir tayi ta tafi wurin mutumin ta bar su suna magana. Koda ta fito, har ya tafiyar shi.
Dawowa ciki tayi, Aunty Madina tace "Har kun gama maganar?"
"Koda naje har ya tafi"
"Oh" Aunty Madina tace
"Kinga Aunty? Dama ba da gaske yake ba"
Murmushi Aunty Madina tayi suka cigaba da hira kaman me.
Lokacin Sallah Isha yayi, gaba ɗayan su suka tafi suka yo alwala. A compound aka shimfiɗa manyan carpet guda biyu. Na gaba shine na maza, na baya kuma na mata.
Abba ne yaja su Sallah Isha, bayan an gama Isha yaja su Tarawih.
Ƙarfe tara da rabi suka gama Sallah. Bayan sun gama ne suka dawo cikin gida suka cigaba da labaran su na rayuwa.
Shi dai Rashid ba don yaso ba ya tashi suka wuce gida ƙarfe goma da ƴan mintuna.
Gumsu itama har tayi bacci suna gama sallah Tarawih.
Ɗaga kai Jawahir tayi taga har ƙarfe goma da minti talatin da biyar tayi. Itama ta fara jin bacci amma bata tashi ba. Wayar ta ta jawo tana dannawa akai akai.
Hamdan tun ɗazu yaga wayar da aka kira ta amma ya mance yayi magana a kanta se yanzu da ya ƙara gani.
"Kin chanja waya ne, Jawahir?"
Kallon Abba ta fara yi tukunna ta kalla Ahmad.
"Menene kike kallo na, ni na saya ne?"
"A'a" ta amsa Ahmad ta kalla Hamdan "Yaya , Abba ne ya siya min"
"Abba kuma?" Hamdan ya faɗa tare da kallon Abba sannan ya maida duban shi a wurin ta "Kina son waya me yasa baki faɗa min ba?"
"Yaya dama....." ta fara, Aunty Madina na kallon ta ɗauke da murmushi akan fuskar ta.
Shiru tayi bata da abin faɗa. "Yaya dama menene?" Hamdan yace
"Bani na saya dan kaina ba, cewa aka yi na sayo" Abba yayi defending kanshi ai kuwa suka yiwa Jawahir dariya itama tace "Dama Yaya da wasa nace Abba ya siya min wayar idan ya tafi Qatar....da wasa fa Yaya, se gashi ranar da ya dawo ya bani wayar yace gashi ya siyo min"
"Abba kana dai jin abinda yarinyar nan ke ƙulla maka a wurin Yayan ta" Khalifa ya faɗa
"Ka bar ni da ita. Akwai wani lokaci" Abba yace cikin wasa
"Yaya nidai kayi haƙuri. Ba zan ƙara ba"
"Da kina so da ki faɗa min Abba be wahalar da kuɗin shi ba"
"Iyye! Jawahir ta Yayan ta" Ahmad ya zolaye ta
Kallon shi tayi sau ɗaya bata kara ba su kuma suna murmushi.
Tsakanin su suka cigaba da hira , Abba da Hamdan kuma suna magana entirely different from irin hiran da su Aunty Madina suke.
Ba su Hamdan suka tashi wucewa ba se getting to 12 AM.
Dukkaninsu suka fito sukayi musu rakiya har motar Yaya Hamdan. Se bayan sun wuce ne su ma suka dawo kowa yayi retiring zuwa ɗakin shi.