Free chapter · Read without an account

Chapter 9.

by Nasreel RL · Furen Zuciya. Flower of the heart.

🌸🌹🌺FUREN ZUCIYA.
 Flower of the heart.

   By Nasreel R.L.
      🤍A hausa love story…….
Chapter 9:

Bangaren Miral: washe gari;
Jin kamar motsin mutane akanta ne yasa ta bude idanunta da still bacci ne akansu ta dago hannunta tareda murzasu a hankali, warosu tayi takalli inda take jin motsin, wasu yan mata ne guda biyu sanye da uniform na masu aiki kowacce dauke da kayan gyara a hannunta sun tsaya suna dan rada a tsakaninsu basuma ga alaman ta tashiba, kana gani kasan shawara sukeyi ko su tasheta kosu barta. 

Mikewa tayi daga kwancen datake tana kallon living room din reality na dukanta dan ita sam ta manta ma wai a gidansu take. Tsaye taso ta mike taji yanason gagaranta dan a kasa ta kwana ga jikinta yafara sabawa da kwanan lallausar katifa saitaji kamar anyi mata duka. 

Saurin juyowa sukayi suka kalleta a tare kafin cikin dan girmamawa su durkusa su gaisheta. Mamaki ne ya kamata dan ita tunda take bazatace ga lokacinda wani ya taba gaisheta ba, kodan basusan waye ita dakuma matsayinta a gidan bane? Dan ita bazatace ta gane fuskokinsu ba dan haka dole bayan tabar gidan ne sukazo. 

Wani irin awkwardness ne taji tama rasa me zatace musu, ga wata bakar yunwa dake dukan yan hanjin cikinta kawai ta gyada musu kai, cikin muryarta dake cike da bacci saidai zakinta bai raguba tace “karfe nawa please?”. Kusan a tare suka ansa “12am ma’am”. Zaro idanu tayi mamaki na cikata ya akayi har 12 yau bata tashi ba?. 

Thank you tace musu sannan ta nufi kasa tana kallon yanda abayar jikinta dasuke tin jiya dasafe a jikinta sukayi wani squeezing kamar tayi dambe a da tiger. Gyara mayafin kanta tayi daidai lokacin tana sauka kan stairs din. Fita tayi daga part din ta kitchen ta nufi part din masu aikin gidan tana mamakin yanda komai na gidan yake yanda ta barshi shekara da shekaru. 

Kitchen na part din masu aikin dake shine a farko idan ka shiga part din ta shiga babu kowa a ciki kamar yanda tayi tunani ta bude freezer ta dauko sausages da milk carton ta fito dashi. Pan ta dauko ta kunna electric gas din ta dauko eggs biyu ta soya sannan ta saka sausages din ta soya ta juye akan plate ta zuba milk din a cup sannan ta mayar. 

Anan kitchen din ta zauna taci a hankali dan tasan bazata samu kowa anan part din yanzu ba kowa yatafi aikinshi sai wajen 2 suke dawowa. Tas ta chinye dukda sausages din kanana ne saitasa wajen 6 amma taji cikinta ya cika fam. Sosai taji jikinta yafara dawowa daidai saidai bata bar kitchen dinba tunani takeyi idan tabar nan din ina zata? In kuma tace zata shiga cikin palourn masu aikin ba karamin aikinsu bane sumata tijara, bakuma tason komawa main part dan sam batason haduwanta da kowa dake ciki. 

Tuna cewa bataga luggage dinta bane yasa tayi saurin mikewa ta fita daa part din zuwa main part. A laundry and storage room dayake a kasa tayi sa’a bata haduda kowa ba tasamu Mai kula da dakin a ciki. Gaisheta tayi matar yar dattijuwa ce ta ansa mata ba yabo ba fallasa tana kare mata kallo alaman taga kamarta da yan gidan saidai bata taba ganinta ba ta tambayeta metake bukata. Fada mata kalar akwatinta tayi dakuma cewa jiya aka shigodasu tareda kayansu Hanat matar tace mata ai Ummi tasa ankai shi dakin hanat. 

Sosai taji ranta sam babu dadi amma saita danne tayi ma matar smiling tareda cemata tagode ta fice daga room din. Sam batason abunda zai hadata da Hanat dan batamasan ko ta tashi ba yanzu idan taje ta kwankwasa mata kofa ta tasheta wayasan abunda zatayi mata. Idan kuma tace bazata ba dole bazata iya zama ba wanka ba chanjin kaya ba. Ji tayi kamar ta kama kai tasa ihu, tarasa meke mata dadi a duniya. 

Ganin babu wani anfani da tunane tunanen zai mata ne yasa kawai ta nufa stairs ta hau sama part dinsu Hanat. A living room ta tsaya sam tarasa meyasa amma jikinta ya kasa karasawa da ita gurin dakin Hanat din, kodan jikin nata na tsoron abunda zai biyo baya ne oho. 

Karar bude kofa ne ya dawo da ita daga tunanin data shiga, dakin Layla da ada zata kirashi da dakinta shine aka bude. Layla ce ta fito jikinta sanye da wata blue off shoulder dress data kama chest da slim waist dinta da wani white maxi skirt dayakai har kasa kafarta sanye da white loafers kanta daure da wani turkish scarf daya bar bayan a bude brown wavy hair dinta ya sauko har baya, hannunta rike da wata designer Blue handbag. 

Daura Almond blue eyes dinta Layla tayi akan Miral da itama ita take kallo kafin ta sakin mata wani pure smile tafara takowa a hankali kamar bazata taka kasa ba zuwa inda Miral take. 

Kamar an daskareta a gurin haka Miral taji, idanunta sun kafe akan face na Layla dayasha make up she looks so pretty and elegant, saikuma idanunta ya sauka akan nata kayan dayake kamar tayi burgima akansu. 

Wani shame ne ya rufeta, bata taba sanin tanada ego da pride ba saiyau, ji tayi dama ace kasa ta bude ta shanye ta yau akan irin kallon da Layla take mata tun daga sama har kasa, zata iya rantsewa taga alamar tausayi akan idanun Layla koda kuwa na split second ne wanda hakan ya kara sata jin wani kunya wai yau ita Layla zatayi ma wannan kallon?, bayan duk halin data shiga a sakamakon ita Laylan ne ta shigeshi?.

Kusa da ita Laylan ta tsaya bayan tagama kare mata kallo tawani tabe baki tace “Miral kenan, kinga yanda rayuwa ta juya mana koh? Dama nasaba gaya miki a baya sam bakida wayau, shiyasa a gidannan ake miki abunda ake miki, amma kika share magana ta, gashi yanzu rashin wayonki ya maidaki kaskantacciya, kazama kuma mara galihu, nikuma Layla danake a da ni za’a cema mara galihu gani yanzu yakika ganni? Inada komai a duniya, familynki sun zama nawa, iyayenki sun zama nawa, dakinki yazama nawa, friends dinda kikeson yi bakiyi ba suma sunzama friends dina”. 

Tadanja nunfashi tasa idanunta cikin na Miral dake cike da hawaye tana kallonta sannan tacigaba “Kina tunanin ba’asan menayi bane kokuwa? No, kowa yasan baki aikata abunda kika aikata ba, amma me? Bai hana ayi miki abunda akayi miki ba. Kinsan meyasa?”, 

tayi wani shu’umin murmushi sannan tace “ saboda ba’a sonki, an tsane ki, iyayenki sun tsane ki, duniya ta tsane ki, nima kuma mutun daya dakika taba zama close to na tsane ki tun ranar dana fara ganinki, amma me? Inada wayau, bakamarki ba, na danne tsanar daneke miki har saida na cinma burina. Ke din Miral tabo ce akan doron kasa, ko shaidan akwai masu sonshi dan ana mishi bauta, amma ke Miral, bakida abunso a jikinki ko zuciyarki daidai da gwayan zarra, bakida anfani a duniya, bayan wannan fuskar taki mai kama dana aljanu, sannan ni Layla namiki alkawarin saina lalata ta”. 

Tana gama fadin hakan kuma tabi gefen Miral dake kame a gurin ta wuce ta samu two sitter sofa ta zauna tareda fiddo wayarta tafara daddanawa kafarta daya kan daya. 

Kasa motsawa Miral tayi gabadaya kwakwalwarta ta kulle, Abu daya ta iyayi a gurin shine ta dago idanunta ta kalli inda taji idanuwa akanta Hanat tagani gefen Solail idanunsu akanta Hanat dawani shu’umin murmushi akan face dinta alamun abunda taji takuma gani yayi mata dadi, Solail kuwa ko’a jikinta kawai kallon Miral din takeyi kamar taga wata dabba datake tsantsami. 

Takowa Hanat tayi daidai inda Miral take ta tsaya ta kalleta kawai ta wani kwashe da dariya ta nufi Layla dake zaune kan sofa tan fadin “Kai Layla, wannan cin mutunci haka? Ai basai kin fadawa wannan Jakar mai kwakwalwar kifi wannan maganar hakaba, inaga ma har yanzu bata gane wani abunda kika fada ba, kinsan jahilar karatun nata da saura, banmasan ya akayi Su mommy sukayi wasting kudin school fees aka kaita school ba”. 

Kamar abun yaba Solail dariya ta zagaya ta chan nesa da Miral tana fadin “Kusamu ku fitarda wannan kazamar crazy girl dinnan daga part dinnan please, ugh, ni gaskiya daga nan part din daddy zan koma bazan iya zama inda take zama ba, banson infection, wayasan maza nawa sukayi wasa da ita cikin shekarun nan?”. Tafada tana tabe baki. 

Dariya suka kwashe dashi dukkansu ukun kafin su mike su nufi kasa alamun wani gurin zasu saboda outfits dinsu. 

Miral da saida tayi wani 10minutes a gurin kwata kwata brain dinta ta dauke wuta kafin tawani sulale kasa ta rike kanta dake wani sarawa kamar ana buga mata guduma a tsakiyar kan. Duk abunda suka fada sai dawo mata yakeyi tana ganin fuskokinsu kamar yanzu abun ke kara faruwa, yana gamawa kamar an sashi a loop saiya dawo farko. Wani ihu ta saki tana jin kanta kamar ya rotse saboda karar ihun datayi. 

Babu abunda yayi mata ciwo sai fadar Layla cewa ansan batayi komai ba. Kenan dama Mommy da Daddy sunsan batayi komai ba? Sunsan sharri Umm layla tayi mata tareda Laylan. Fuskan Daddy ranar daya koreta daga gidan kawai take tunawa. Yanda wani azababben fushi ya rufe face dinshi, irin dukan dakuma maruka dayayi mata kamar yasamu gardi da harsaida ya gotar mata da Ć™ashin jaw dinta ya kauce daga gurin zamanshi. 

Memoryn data kulleshi a cikin brain dinta tasa kwado ta rufe tun daga ranar daya faru bata kara barin kanta ta tuna maiya faru ba. Ranar graduation na Layla da Solail, bayan graduation dinner nasu an dawo gida Solail tafara aman jini kafin ta suma. Rushing zuwa asibiti akayi aka kaita dakyar aka ceto rayuwarta bayan anyi test akace wai poisoning dinta akayi, sannan kuma poison din bazai wuce 30minutes a jikinta ba. 

Sosai daddy yafara bincike a ranar dan zaizama dole bayan tadawo gida ne akayi poisoning dinta and bataci komai ba sai watermelon slices da Umm Layla ta yankama Miral amma bata shaba ta ajiyeshi a dining. Sosai zargin daddy yakoma kan Umm Layla, saidai kuka kawai takeyi takasa koda magana ne yasa aka Sa Layla yin magana. 

Itama Laylan kuka taringa yi dakyar aka samu ta bude baki tafara magana. Hakuri taringa ba Miral tana ce mata bazata iya boyewa ba tana kuka sannan tafara ba Daddy labarin cewa taga Miral na zuba wani gari akan Watermelon din amma batasha ba ta tashi ta tafi tabarshi a gurin. A cewarta tun jiya da daddare dasuka kwana tare take cemata saita kashe Solail, amma tace idan ta fada zata kasheta itama, sannan ta dade tana cewa zata kashe Solail kawai dai bata zata da gaske takeyi bane. 

Basu ko barta ta karyata sharrin da Layla tayi mataba Suka tambaya Umm Layla ko gaskiya ne dama tana fadan zata kashe Solail wanda Umm Layla ta tabbatar da hakan gaskiya ne. 

Tun daga nan kuwa ita har yanzu takasa ma tuna menene yafaru da ita bayan jin wannan maganar, dan tasan tazauna cin watermelon dinnan kenan Layla ta kirata dan haka ta tashi ta tafi tabar Umm Layla dake wajen bata tafi ba, dawowanta kenan taga Solail nasha dan haka ta juya ta tafi dan tasan ba bata abunta Solail zatayi ba. 

Abunda kawai take tunawa shine irin dukan da Daddy yayi mata dakuma maganganun Mommy wanda har tsine mata tayi a ranar, sannan suka sa aka wurgar da ita a wajen district din wanda idanba dan Police sun dauketa zuwa station sannan aka kira Daddy wanda yace shiba yarshi bace sannan yace a yanke mata hukuncin kisa dakyar Ummi tasamu aka bata yarinyar tabar kasar da ita. 

Wani tunani ne ya fado mata, ai akwai CCTV camera a gidan tako ina, dan haka da an duba CCTV ai za’a ga waye yayi, wanda tanada tabbacin an duba bayan ta tafi, a hakan ne za’asan ba ita tayi ba. Saidai kuma ga Layla lafiya lau a cikin gidan kamar itama anan aka haifeta bawai yar mai musu aiki bace. 

Duk wani bakin ciki da shame da emotion datakeji slowly taji yana komawa bacin rai da anger. Dama suna sane babu abunda tayi ake mata wannan cin mutuncin? Duk bala’in data shiga a rayuwa a dalilin wannan abu da azabtarwa datasha a hannun mutane mabanbanta dama kowa yasan batada laifi? 

Wani abu taji kamar dutse ya tokare mata makoshinta, zuciyarta tafarfasa kawai takeyi, jitayi ayau idanba ta tashi ta rama abunda akayi mataba zata iya mutuwa. Bakuma takan kowa zata faraba saita kan Layla. Mikewa tayi kanta na kara sara mata saidai ina bama tashi takeyi ba. 

Kwalban drink ta dauka ta sauka stairs din a dining ta tarar dasu suna cin abinci suna dan hira Layla ce a farko sai Hanat, Solail kuma a opposite dinsu ta zauna. Basu ma lura da itaba tana zuwa daidai inda suke Layla na dagowa ta kalleta batayi wata wata ba ta rotsa kwalbar a goshinta. 

Wani ihu Gabadayansu su ukun sukayi Layla ta dafe goshinta datakejin jini na bulbulawa kamar an kunna famfo dan bada wasa Miral tayi bugun ba, haba wani ihun ta kara saki dayafi wancen tama kasa mikewa. 

Ai Miral jitayi fah wannan bai ishe taba kawai ta saki kwalbar ta dunkule hannu tafara kaimata duka hannu bibbiyu tako ina bataji bata gani. Irin ihun da Layla keyi kasan dukan na shiga yanda ya kamata, Miral kuwa kamar Wanda Tasha wani energy drink ai ko nunfasawa batayi. 

Su Hanat da Solail da sunma rasa nayi itadai Solail dama batayi niyyan shiga ba dan yanda taga idanun Miral sun juya ga yarinyar dukda batada wani kiba amma tanada tsawo yanda take hadawa harda kafa tana kaima Layla duka wlh bazata shiga ba ita tasan batada karfi dama. 

Itako Hanat tsoro ne kawai ya hanata shiga dan kawai tuna azabtarwar datayi ma Miral kusan kullun dasuke riyad yasa takasa motsawa dan tsoronta taje cetar kawarta a hada da ita dan yanda Miral tayi kamar ta haukace ga idanunta sunyi ja jawur sun juya. 

Ihun Layla na ya sauko da Mommy da Ummi da gudu basu taba tunanin zasuzo su tarar da Miral na dukan Layla kamar wata sabuwar kamu ba. 

For more information ga WhatsApp number na ***.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol