Free chapter · Read without an account
Chapter 10.
🌸🌹🌺FUREN ZUCIYA.
Flower of the heart.
By Nasreel R.L.
🤍A hausa love story…….
Chapter 10;
Securities Mommy ta kira ko 2 minutes basuyi ba suka shigo lokacin ko ihun Layla an dena ji. Saida sukayi da gaske suka samu suka riketa lokacin Layla tagama sumewa face dinta yayi luhu luhu yayi ja kamar an kumbura ta fuskar duk jini.
Dawo da hannayen Miral bayanta sukayi suka riketa har a lokacin tana kokarin kwace kanta saidai ina, takasa. Durkusar da ita sukayi kan knees dinta sai a lokacin Mommy takaraso inda take batayi wata wata ba ta dauketa da wani mahaukacin mari da saida taji jini a bakinta.
A wani hankali ta dago ta sa rinannun idanunta kan na Mommy tayi mata wani irin kallo da saida Mommy tasha jini jikinta ganin kallon datayi mata. Ayau ta tabbatar sunkai Miral bango dan miral bata taba koda wasa ta kalleta da nufin wani abuba barinma ana mata hukunci, kullun kanta a sunkuye yake yau itace tayi mata wannan kallon datama kasa gane menene yake nufi.
Ganin Miral batada niyyan sauke idanunta ne yasa Mommy ta cire idanunta daga kan na Miral ta kalli securities din a sanyaye tace “Ku fita da ita ku rufe mun ita a store room na bayan garage, kar a bari ta fita kar a bata ko ruwa ko abinci”.
Ansawa sukayi kafin su dago Miral zasu jata waje ta cije ta kara kallon Mommy ido cikin ido a wata irin murya dake nuna ranta na tafasa tace “zan baki shawara tun yau kisa a kashe ni a gidannan ku huta, dan nayi miki alkawarin hardai na rayu, hardai da nunfashi na a doron kasa sai kun dandana abunda na dandana, saina rama duk abunda kuka yimun sau dubu makuwa,” tafada tana kallon su Hanat da Ummi da Solail daya bayan daya sannan ta kafe idanunta akan Ummi tace “idan har kin kawoni nan ne danki cutar dani kema bazan kyale kiba, saukinku kawai ku kasheni, dan Wallahi sai kunyi nadamar barina darai dakukayi”.
Wani irin sakin baki Mommy tayi tana kallon Miral yau taga abun mamaki. Sosai kuma abun ya daga mata hankali dan a ganinta Miral ta haukace ne yasa take musu irin maganganun nan, saidai kuma tuna waye su din yasa ta kwantar da hankalinta, makiyansu ma dasuka taka Miral basu iya tabasu ba bare kuma wata yarinya guda daya? Tasan kawai bacin rai ne yasa ta fadin hakan, ita bama zata iya cewa ga ranar da Miral tashiga baci raiba sai yau, dan yarinyar akwai hakuri sosai dako mayarda magana batayi.
Ummi kuwa sosai tasha jinin jikinta, gabadaya tunaninta kawai ya akayi Miral tagano plan dinta? Tabe baki tayi aranta tana fadin me yarinya daya zatayi musu? In tasani ko batasani ba duk daya aikin gama ya gama. Matsalarta kawai yanda zata lallashi Mommy tabarta ta dauki Miral din gobe ta fitar da ita zuwa inda sukayi zata ajiyeta.
Family doctor Mommy ta kira dan duba Layla, sunma kasa tabata dan gabadaya fuskar tata babu kyan gani yayi chaba chaba da jini kamar a boxing ring.
A bangaren Miral kuwa wani store room ne na ajiye karafuna da parts na mota kasan shi duk bakin mai gashi babu window suka wurgata ciki suka rufe kofar ko tafin hannunta bata iya gani saboda duhu. Wani tafasa zuciyarta keyi jitayi har yanzu bata fitarda abunda ke zuciyarta ba.
Wani ihun ta saki tana fitarda wani kuka mai tsuma zuciya tana tuna rayuwar data shiga a sakamakon wayanda zata kira familynta. Meta musu suka tsaneta haka? Tun daga haihuwa babu wanda yataba nuna mata so da kauna banda Grandma dinta. Takuma tabbatar itadin yarsu ce bare tace koba yarsu bace. itadin haifaffiyar familyn Zahir ce kama bata karya.
jiri taji yafara dibanta sai a lokacin taji irin warin bakin mai dake dukan hancinta. Saurin dafe kanta tayi saidai ina jirin wani karuwa ma yakeyi, idanunta wani fari fari yafara nuna mata dukda babu wata kufar haske a dakin kafin luu ta sume.
Babu dadewa aka bude store room din wasu gardawan maza sanye da bakaken kaya fuskokinsu sanye da mask baka ganin komai a jikinsu su wajen 3 dayansu ya sabo Miral a kafada
yafito da ita suka nufa wajen gidan. Securities dake gadin hanyar gabadayansu babu ko daya a gurin sa, sai wani dake kwance cikin jini rike da kirjinshi kana ganinshi kasan babu rai a jikinshi.
Cikin wata bakar mota katuwa kamar school bus suka sata suka shige tareda jan motar a haukace gate din shiga gidan already a bude yake suma securities na gurin gate din a kwance cikin jini tsakiyar goshinsu a fashe da bullet.
[toh fah.. guys suwa kuke tunanin sun dauki Miral, su iya shigowa har cikin gidan Zahir su dauki mutun suma securities kisan gilla bakuma a sanma sun shigo ba? Akwai kura fah yanzu labari zai fara, kafin nan bari mudan leka wani yanki na labarin].
Bangaren Mihrimah;
District 2; Ghazi family: Ghazi estate;
Duk cikin districts din bayan royal palace babu inda ke standing out kamar district 2 a kasar baki daya. Irin gine ginen sun fita daban dana ko’ina a cikin sauran districts din. Tsaron district dinma yanda kasan wani shugaban kasa ne a ciki duk waji lungu da sako tsaro ne baka isa kayi wani motsi a ciki ba batareda survelliance ba.
Cikin main estate na District din wanda yake a tsakiyar district din sanna yafi kowanne haduwa da tsaruwa a part din farko Wata Kyakyawar budurwa ce zaune kan tsakiyan bed na wani hadadden vintage style bedroom ta waro manya manyan lulu idonta masu dauke da brown eyeballs zagaye da dogayen coiled lashes akan matar dake gefenta.
Wani irin cute kyau gareta kamar barbie, slim round shape face dinta na dauke da wannan big eyes din da su kake fara gani a face dinta they look so sparkly and lively. Hancinta irin small nose dinnan ne mara fadi saidai yanada dan tsawo kadan, reddish pink lips dinta kuma basuda girma sosai but they are full and looks so supple.
Black curly hair dinta a sake har tsakiyar bayanta yayi framing face dinta, tanada golden skin da sai gyalli yakeyi yana glowing kana gani kasan yar hutu ce. Dukda a zaune take zaka gane cewa batada wani tsawo sosai.
Matar dake gefenta dasuke dan kama saidai ba sosai ba amma manya manyan idanun nasu iri daya ne kawai dai na yarinyar sunfi nata girma dakuma kyau hadeda daukar ido ta kure yarinyar da ido kana gani kaga bacin rai a cikinsu, a kufule tace “Mihrimah, wallahi bazan maimaita kaina ba, nagaji da excuses dinki. Ki hada kayanki gobe zaki koma Royal house, sultana kusan every week saita kirani jin lafiyarki. Kuma kinsan akwai engagement din Imad akanki koh?”.
Sauke idanunta tayi daga kan Ummi sam batason abunda zai shiga tsakaninsu amma wannan abu da Ummin ke suggesting ba abune datake ganin zata iyaba. Silent ajiyar zuciya ta sauke sannan ta mike a sanyaye ta kalli Ummi tace “Ummi zanyi tunani akai”. Tana fadan hakan ta mike da sauri ta bar dakin.
kofar fita ta tarar da sistern ta Deniz wanda tadan fita tsawo da kadan kamar su daya banbancinsu kawai idanun ne da ita Deniz nata idanun basukai girman na Mihri ba, sannan nata idanun a kafe suke irin wayanda kasan sunsan duniya dinnan. Dan smiling Deniz tayima Mihri cikin siririyar voice dinta cikeda aji tace “lil sis, me kuma ya hada kida mom yau?”.
Shiru kawai tayi mata bata amsa taba dan tasan tana bude baki kuka zata fara, bakuma tason Deniz taga kukanta dan haka kawai ta girgiza mata kai tabi gefenta ta wuce. Dan kallonta na yan seconds Deniz tayi kafin itama ta girgiza nata kan ta bude kofar dakin Mom ta shiga.
Straight room dinta ta nufa dake hadeda living room, room dinta na opposite na Deniz. Komai a dakin pink ne. barbie inspired bedroom ne daya gaji da haduwa. Kayan jikinta daya kasance white jeans ne dakuma pink tshirt free da aka rubuta “cool girls dream” a jiki ta zare tabari daga ita sai jeans dakuma vest ta wurga kanta a king sized bed dinta mai daukeda pink pillows da bedsheet ta janyo Quilt ta rufe jikinta harda kanta ruf a ciki.
Maida kukan datakeji tayi gabadaya abubuwa sunyi mata yawa.
Jin kamar anyi mosti a dakin ne yasa tayi saurin juyawa zuwa inda taji sound din. Da mamakinta Tahira tagani a tsaye akan dressing mirror tana skincare kamar batamasan da mutun a dakin ba. Rolling eyes dinta Mihri tayi ta juya ta kwantar da kanta. Saida wajen 5minutes suka wuce takara juyowa taga har lokacin Tahira bata gamaba yasa ta saki wani tsaki tace “wai ke Tahira bakya gajiya da wannan shafe shafen ne? Kuma ma ki rasa inda zakiyi sai kinzo gidanmu kuma har cikin daki na?”.
Juyo da kanta Tahira tayi masha Allah she looks divine. Kyakyawa ce ajin farko Almond eyes dinta dasuke yan madaidaita masu daukar ido ta saka ma Mihri tana kallonta irin yane dinnan.
Mikewa zaune Mihrima tayi ta dauki wani pink heartshaped pillow daya ta rungume a kirjinta ta zura ma Tahira ido. Itama Tahira ita take kallo ganin yanda face na Mihri gabadaya babu annuri kana ganinta kasan damuwa take ciki yasa ta ajiye toner datake shirin shafawa ta dauki wipes ta goge hannunta ta nufo gadon ta zauna.
Dan matse bakinta Mihri tayi tana sakin ajiyar zuciya. Tahira dataga Mihri batayi alamun zata fara magana ba yasa ta tambayeta meke damunta. Kin fada Mihri tayi a cewarta babu abunda ke damunta, dakyar Tahira tasamu tace zata fada mata amma ba anan ba.
Ok kawai Tahira ta ansa mata sannan tace su tashi subar gidan mana. Mihri sam batada niyyar fita amma kuma sanin yakamata ta fitar da abunda ke zuciyarta dababu wanda zata iya fadawa banda Tahira yasa kawai ta mike ta shiga toilet.
Cikin ten minutes tayi wanka ta fito ta shafa body oils dinta ta nufi walk in closet ta dauko wata pink abaya mai wani mahaukacin design dakaganashi kasan an kashe mishi kudi dakuma time saboda intricate design na flowers din daya mamaye kasan abayar dakuma hannun. Saurin shiryawa tayi cikinsu sannan ta daure kanta ta baya in a bun ta daura mayafin abayan a dan baya gaban gashinta a bude. Heels ta zura loubottin black sannan ta dauki wata custom design handbag ta dauki silver bracelet ta zura a hannunta ta fito.
Kwalli kawai ta iya sawa da pink lipstick sai pink blush sannan ta dauki lip gloss ta saka a cikin bag dinta ta nufi waje bayan ta dauki wayarta.
Koda ta fito bata samu tahira a dakin ba dan haka ta nufi waje. A outdoor parking space ta sameta cikin wata red Mercedes benz SLR McLaren. Kofar gaba ta bude ta shiga basuce ma juna komai ba Tahira taja motar a guje suka fice.
Cikin Anguwar entertainment quarters na Sarmul kuwa suka shiga. Ba kowa keda access da gurin ba sai familynka sun kai abunda sukakai kafin na ka samu access da cikin gurin. Sannan still a ciki akwai guraren da sai yaran cikin district 2 zuwa 4 ne kadai ke samun shiga ciki. Sannan akwai wani artificial lake and waterfall dasuke kira da Sarm-lake wanda yaran district 2 ne kadai ke shiganshi.
Nan tahira ta nufa dasu a kofar shiga ta sauko Mihrimah ta sauko tahira taba security guard daya key din motarta dan akai mata parking lot.
Kusan babu kowa a ciki sosai hakan yayima Mihrimah dadi dan dama batason haduwa da kowa musamman ma cousins dinta da yawanci basa rabo da nan din.
Gurin ya hadu iya haduwa kamar wata aljannar duniya. Iya tsaruwa gurin ya tsaru ga wani breathtaking waterfall dayake amayo ruwa da karfin gaske kanajin karar dayakeyi ga iskar gurin so refreshing.
Gurin zama suka zauna daga dan lungu waiter tazo Tahira tayi musu ordern cheesecake dayake favorite na Mihrimah dakuma lemonade. Babu dadewa waitern tadawo tareda serving dinsu. A hankali Mihrimah ta dauki dessert fork din tafara cin Cheesecake din tana kallon ruwan dake kwarara gabadaya hankalinta ya tafi batamaji kiran da Tahira kemata ba har saida ta tabo ta.
Da sauri ta juyo da idanunta ta kalli tahira dake mata wani irin kallo tace “wani irin kallo ne wannan?”, tana hade gira. Girgiza kai kawai tahira tayi sannan cikin sassauta murya tace “Mihri kifada mun abunda ke damunki, damuwar nan na shirin miki illa idan har kika cigaba da kunsheta a cikin zuciyarki. Gabadaya kin chanza ki kalle kifa mihri, kalli abunda kika zamo kin rame bakya iya komai. Komai ya tsaya miki kin dena zuwa school, kin dena dariya kwata kwata bakida energy. Haba, akan namiji? Akan Imad?haba”.
Binta da ido kawai Mihrimah keyi tanajin wani zafi a zuciyarta. Ita kanta tasan halin da ta shiga ciki saidai jin sunan Imad da yanda Tahira ke kiranshi kwata kwata batajin dadin hakanba. “Babu ruwan Imad, ba saboda shi na shiga halin dana shiga ba”.
Wani karamin murmushi Tahira tayi alamar bata yarda ba. Ta dauki lemonade dinta tayi sipping a hankali. Mihrimah ganin Tahira ta juya ta dau wayarta tafara daddanawa yasa taji babu dadi a ranta. Sam batason tana bata mata rai duk duniya batada wata kamarta, batada friends duk friends dinta sun daidaice, cikin cousins dinta ma banda Tahiran babu wanda suke wai close dukdai suna gaisawa amma basa zama su fadawa juna matsalolinsu.
Sauke idanunta tayi tanajin yanda kwalla keson fitowa amma ta taresu, cikin wata murya a karye tace “Tahira Ummi takasa fahimta ta, tace dole nakoma Royal house gobe. Kinkuma san dole na tafi kafin ta hadani da grandpa. Bazan iya cigaba da zama a royal house ba. Inason Sultana har cikin zuciya ta, amma Bazan iya Rayuwa a guri daya da Imad bah…” ta fashe da kuka tana fadin “Tahira mutuwa zanyi bansan meke damuna ba, inaji a jiki na bazan cigaba da rayuwa ba. Nakasa komawa school bana gane komai, bana iya bacci bana samun kwanciyar hankali”.
Tahira kanta jitayi kanar zatayi kuka saidai ta danne bata taba ganin Mihrimah a irin wannan halinba, cikin muryar rarrashi tace “Mihri wai ko kin tuna ke kika yi sanadiyyar rabuwarku? Saida na fada miki lokacin wannan ba solution bane, karki rabu dashi amma kika ki. Yanzu ba wannan ba, na tabbatar har yanzu Imad na sonki, ki koma Gurin sultana, ki manta da baya ki gina sabon rayuwa dashi”.
Wani dariyar takaici ne ya fito daga makwogwaron Mihrimah, cikeda takaici tace “Tahira ko kin manta ni dakaina na fada mishi mu rabu? Kin manta rokona daya rinka yi nayi kunnin uwar shegu nayi blocking dinshi nabar Royal palace din gabadaya? Kin manta wata nawa yana bina na fada mishi abunda yayi kafin ya hakura?”.
Sauke idanunta tahira tayi dan ita batamasan mezata ce ba. Share hawayen face dinta Mihrimah tayi sannan tace “Idan har nakoma Royal house Ummi anfani dani zatayi dan su cinma burinsu, dan haka babu anfanin rabuwa dashi danayi tun farko”.
Tsaki Tahira tayi sannan a wani kufule tace “Kefa Mihri wlh bansan matsalar kiba. Toh sai me idan Sunyi anfani dake suncin ma Burinsu? Basai ki barsu da Sulieman dinba, daidai yake da ita Deniz din ki barta ta aureshin mana kina tunanin zasu iya cutar dashi ne kokuma su saka shi yin abunda baiyi niyya ba? Kuma ma ai ba cutar dashi zasuyi ba ita Ummi kawai sotake yarta ta Auri Vael Rahem na Ghair Muaddal, wanda kowacce uwa a cikin Ghair Muaddal kema yarta fata. Dan haka kibar wannan maganar kawai tunda kina son Imad dinki kuma na tabbata har yanzu yana sonki kawai ki cire komai a zuciyarki ki gyara rayuwarku”.
Gyada kai kawai Mihri tayi daidai lokacin kiran Ummi ya shigo wayarta. Mamaki ne ya kamata mekuma zatayi ma Ummi yanzu. Har saida takusa katsewa sannan ta dauka tasa a speaker, a wani hargitse taji muryan Ummi tana fadin “kin gama damu Mihrimah, burinki ya cika. An soke maganar aurenki da Imad yanzu wata kazamar yarinyar District 4 zai aura, yanzu saiki zuba ruwa a kasa ki shanye”.
For more information, ga WhatsApp number na ***.