Free chapter · Read without an account

Chapter 13.

by Nasreel RL · Furen Zuciya. Flower of the heart.

🌸🌹🌺FUREN ZUCIYA.
 Flower of the heart.

   By Nasreel R.L.
      🤍A hausa love story…….

Chapter 13; 
Ghair Muaddal royal palace;
Located at the heart of Sarmul kuwa, district one, the Iconic Royal Palace of Ghair Muaddal stands. Wani mahaukacin gate ne zai sadaka da official district one bayan dogon titin shiga district din, ba normal gate bane dan tsawonshi kamar wani skyscraper yake, ga fadin gaske dan idanda ace mutane ne ke budeshi majiya karfi sai amsamu mutane wajen 50 a kowanne side domin a budeshi. 
Sturdy build ne da gate din kana gani kasan bana ginin yanzu bane, kallo daya zaka mishi kasan yadade da zama a wurin, badan tsufa ba saidan yanayin fadi dakuma karfen da akayi anfani dashi, kasan cewa gate din yaki ne da defence dan duk abun mutun kowani weapon zaiyi anfani dashi bai isa ya kada wannan gate dinba. Black gate ne and silver, ga wani design na Siberian tigers manya manya a jikinshi. Duk lokacin asuba ake bude gate din, sannan karfe sha biyu na dare ake rufeshi, sai ranar friday da ake rufeshi karfe 9 nadare basai sha biyu ba, dokar masarautace da babu wanda ke tsallaketa kowaye shi kuwa. Idan aka rufe gate dinnan babu shiga cikin masarautar babu kuma fita. 
Bayan ka wuce gate din har irin iskar dakake shaka zakaji ya chanza, wani siririyar iskace mai ni’ima sakamakon Frinkling trees dakuma dragon blood trees dasuke baja baja a titin dakuma cikin masarautar, bishiyu ne dasuke surace iska su cire chututtukan iska kaji iska kamar ba’a duniya kake shakarta ba, babu wani datti ko kura, ga rare scent flowers dake shuke a gurin wasu manya wasu kanana dake fitar da wani sihirtaccen kanshi. 
Dogon titi ne tsakanin gate dinnan da kofar shiga masarautar da yakai tafiya a mota na wajen 15minutes kafin kakai the Iconic snow Siberian tigers entrance. Kofar shiga masarautar ba kamar normal kofa takeba, Giant statue din siberian tigers ne guda biyu da saika daga kanka zakaga karshensu, dan kusan tsawonsu daya da trees dake surroundings din gurin, da gold akayi jikinsu gabadaya duk girmanshi, yanda suke a tsaye sun bude baki dogayen teeth dinsu kamar zasu kai hari.  
Zagaye dasu kuma dogon gini ne da duk abunka bazaka iya tsallakawa ba, baka ganin inda masarautar tafaro kota kare. A tsakiyar statue din siberian tigers din guda biyu karamin tudu ne medan fadi dake raba titi, babu securities ko daya a gurin, dan zakayi zaton ko babu tsaro ne saidai sam ba’a bukatan irin wannan securities din. Dan idan bakada izinin shiga masarautar baka isa ka tsallake wannan entrance dinba bare ka shiga, hakama fitarta baka isa ka fita babu izini ba. 
Dayake Mihrimah sunada permanent residence ID na Royal house yasa ba’a wani bata lokaci wajen bincikan su da motarsu ba. Suna tsayawa a wajen security protocol din wani Boxy gurine da mota take shiga ayi scanning dinta da mutanen ciki in seconds duk abunda ke ciki za’a ganshi kamar X-ray machine sannan a tantance kafin a bude ka wuce cikin gate din. 
Bayan ka shiga ciki wasu mahaukatan architecture zaka fara gani, sam ba irin normal gine gine bane, tsayawa fadan tsaruwa da abun mamakin cikin masarautar Ghair Muaddal ba abunda zai yuwu bane, dan saimu gama littafinnan tsaf akanshi kawai. 
A Royal residential area inda sarki da matarshi da yayanshi suke, Babban gurine sosai dayake cikin masarautar amma a tabaya a kuma katange. Shine gurin da a kasar babu inda yakeda maximun priority security kamarshi. 
Sauka daga motarsu Mihri tayi bayan an zo gurin shiga residential area din dan ba’a shiga da motar waje. Residence car suka hau sannan aka karasa dasu. daga gurin zuwa gate na residence din wajen 10 minutes drive ne. Sosai Mihrima kebin ko’ina da kallo. Kusan shekaranta daya rabonta da Royal house, komai ya chanza a ciki. dama haka Ghair Muaddal take, ko sati daya kayi baka zo guri ba ka dawo zakaga chanji dan basa wasa da renovation dakuma upgrade.
Wani ajiyar zuciya Mihri ta sauke kafin ta sauka daga resident car din a bakin entrance na residential area. Wasu gabza gabzan Securities ne fal gurin bazama ka iya irgasu ba suna zagaye tunkan ka hada ido dasu idanba mai taurin zuciya ba sai cikinka ya tsure saboda irin special horon da aka basu kafin su zama masu tsaron residential area. 
Ga fuskokinsu a rufe yake da mask idanunsu kawai kake gani da babu alamun rahama a ciki, ga mahaukatan weapons a jikinsu da saika rasa mema sukeyi amma kallo daya kasan idan daya ya sameka bazaka ko shura ba. sannan ga  wasu motion detection CCTV camera irin max security prison grade dinnan da basuda blind spot, duk kankantar abu sai sunyi detecting dinshi.  
Bude mata kofar shiga gate securities din sukayi tareda rusunawa da kaimata gaisuwa. Ansa su tayi ba yabo ba fallasa sannan ta shiga ciki tanajin kirjinta na waji dum, dum. Saidai wani bangaren na zuciyarta dadi ne ke mamayewa dan tadade tana son dawowa kodan sultana datake kamar uwa a gareta. 
Wani iri kuma tafara ji a jikinta tuna sultana, da yanda tayi tayi da ita ta zauna last year ta rufe kunnuwa taki zama. Sannan tunda tasa kafa ta fita bata dawo ba duk yanda sultana tayi da ita koda na yini daya ne amma ina taki. Saidai waya kawai. 
Buildings ne guda biyu manya manya sun tsaru da wani arnen vintage architecture kamar ba mutun ne yayisu ba, komai na jikinsu white ne, basuda banbanci ko’a girma saidai a yanayin yanda aka tsara exterior din dakuma irin flowers dake zagaye da kowannen cikinsu zaka gane wannene na Vael Sultan wannene na Sultana dan flowers dake zagaye da part din sultana Sunfi zama colourful and girly su pink ne dasu red, na sultan kuma duk kusan white ne haka babu colors sosai. 
Cikin part na Sultana komai cikinshi Golden ne da white, sai dan touch of pink dan nan da chan. Irin yanda gidan yake fully decorated in the Ghair Muaddal Royal style, komai daban yake da yadda aka saba. 
Wani sanyin iskar turaren wuta dana scented flowers mai ni’ima ne ya ratsa hancin Mihri da saida ta lumshe idanunta, Main palour na part din wanda shine Palour na saukan baki babu kowa a cikinshi mihri tabishi da kallo kawai memories na dawo mata. Golden chandelier daya kusan mamaye rabin palour din duk girmanshi dan set uku na sofas ne dukda duk sofas din iri dayane a design dakuma colors dinsu dayake creamy white amma kowanne set yana gurinshi daban, sai main set dayake a tsakiyar palourn wanda shi kanshi palour ne guda. 
Wucewa tayi daga nan ta hau elevator zuwa second floor, wani hadadden living area ne a harabar, sai kofofi wanda Mihri straight kofar dake tsakiya ta nufa. Knocking uku tayi a hankali sannan ta tsaya tanajin yanda idanunta sukeson chanzawa kwalla nason fitowa daga idanunta. 
Saida akai Wajen two minutes ba’ayi magana ko motsi ba sannan aka bude kofar wata matace irin middle aged dinnan ta tsaya tsaye a kofar jikinta sanye da kayan kuyangun Ghair Muaddal. Dan murmushi Mihri tayi mata aranta tana tunanin ina kuyangar Sultana Khairiyya take? Dan bata taba ganin wata kuyagar a dakin hutawar Sultana ba banda Khairiyya sai wannan dabata san face dinta ba yau. Mayar mata da murmushin tayi sannan ta rusina ta gaisheta irin gaisuwar masarauta tareda yimata iso ciki. 
Wani hadadden lounge ne jama’a aljannar duniya kawai ne cikin wannan gida, duk inda ka shiga yafi na bayanshi haduwa. Nanfa shi ake kira da aljannar duniya, dan irin na Ghair Muaddal ba irin na kowa bane idan nace zan tsaya fada muku haduwar wannan part din tundaga entrance har zuwa nan bazamu samu mu gama book dinnan bah. 
Kan high chair dayake a tsakiyar hadadden lounge din dake surrounded by other resting chairs irin na sarauta, wata middle aged woman ce zaune sanye da wani luxurious red and golden lace dake daukar haske yake daukar reflection a golden ceiling din palourn dayake kamar an zuba mini stars a jiki. Hannayenta dake kan hannayen sofar ta ajiyesu elegantly sanye suke da wasu azababbun gold bracelets stacked one on top of another masu wani irin unique design, gold na wuyanta ma kanshi abun kallo ne, shi bawai yacika girma bane saidai akwai cika ido ya kwanta tsaf akan slender neck dinta. 
Kafarta dake sanye da low heels red maidan duhu daya hadu sosai da color din kayanta, heels din take dagawa a hankali tana saukewa yana making wani paff, paff, paff sound. Face dinta masha Allah, Kallo daya kayi mata zakace batafi 30years ba ba ragi ba kari, ga wani sihirtaccen kyau da Allah ya mata irin kyannan ne mai bacci yan madaidaitan idanunta dasuke sihirtattun sleepy eyes a wani lumshe ta barsu. Irin kyannan ne da bakowa Allah ke baiwa ba acikin masu kyau, hancinta dogo siriri lips dinta are full masu dan fadi red dasu sunsha red lipstick. Ga gashin kanta data daureshi a baya wani unique golden shade daya kara haskaka glowy skin dinta. 
Da ganin irin zaman datayi kasan sarauta nabin jikinta ba kadan ba, irin yanda ta dauki kanta kasan akwai izza a jininta. Waro sleepy eyes dinta tayi zuwa kan Mihri data tsaya turus a bakin kofa kamar an kafeta a gurin idanunta sunyi ja wasu hawaye na kwararowa kamar an bude famfo. 
Da wani irin sauri Mihri ta nufa inda Sultana take tana sakin handbag dinta da wayarta a kasa ta fada kan sultana tana fashewa da wani miskilin kuka da sai yanzu tasan tana kuka dan har wani shasheka takeyi tana danna kanta a kan kirjin Sultana.
Sultana da ita kanta idanunta sunyi ja ganin yar nata yau finally ta kawo kanta da kanta ga kuma situation dinda tasan Mihri ta shiga na wannan zance mara dadi yasa itama ta rungume ta tana shafa kanta a hankali. Saida sukayi wajen 10minutes a haka sultana ta tabbatar kukan Mihri yayi haka sannan ta cike hannunta daga bayanta ta dago face din mihri data kasa dago ido ta kalleta tareda share mata hawayen face dinta. 
Cikin sassautar murya mai dadin sauraro dake cikeda natural Izza tace “My daugher yanzu ni kike kunya kuma? Don’t get me angry this early morning darling, dago ki kalleni da chan dakike soyayya da ɗana bakiji kunyata ba sai yanzu?”. 
Haba ai kamar ta taso mata da wani sabon kukan ta dago ta kalleta kawai ta sake fashewa da kukan murya a karye tace “Sultana Imad baya sona yanzu, mutuwa zanyi wlh ki yafe mun kinji?”.
Hade rai Suktana tayi cikin yar dakakkiyar murya tace “Kar nakara jin maganar wai zaki mutu ko wani abu, in yafe miki me? Kinmun wani abu ne? Sannan rabu da Imad kinji zamuyi maganinshi cikin ruwan sanyi karki damu. Kedin fa nina raineki ba wani ba nafi kowa saninki hatta mahaifiyar data haifeki bata sanki yanda nasanki ba. Dan haka kibar komai a hannuna yanzu share hawayenki kinji”. 
Saurin share hawayen tayi ta dago tana kallon Sultana dake mata wani irin kallon so da kauna dayasa taji rabin abunda ke damunta ya tafi. Duk sanda take tareda Sultana toh lallai duk damuwar datake ciki saita samu yanda tayi ta yaye matashi. 
Dan turo bakinta tayi a wani shagwabe ta kara rungume kafafun sultana dan a kasa kan carpet take zaune ta daura kanta a cinyar ta batareda ta dago idanunta ba tace “Sultana bakya fushi dani dan bankara zuwa bah tunda natafi? Amma da gaske yana sona har yanzu? Ya tambayeki ni tunda na tafi?”. 
Bude baki sultana tayi zata ansata akayi knocking kofa. Kuyangarta dake bakin kofar ta bude kofar batareda ta kalli Camera dake displaying wanda yake a wajen ba dake jikin kofa dan tariga tasan waye ke shigowa part na Sultana a wannan lokacin. 
Sallama yayi ciki ciki cikin wata sexy deep voice da saida Mihri taji voice din ta wani sosa mata wani spot a zuciyarta da batasan lokacin da ta dago kanta a guje ta kalli inda taji muryar da ko a gangarar mutuwa tajita zata gane muryar Imad dinta. 
dogo ne sosai dan duk tsawon kofar saida yadan duka kanshi sannan ya shigo. Sanye yake da white shirt button up yayi rolling hannun daya fitoda hadadden golden designer wrist watch dinshi, yana sanye da black trousers alaman daga aiki yake yacire suit din jikinshi ne. Dukda kayan ba’a matse yakeba amma zakaga alamun muscles dinshi, kana ganinshi bawai ya murde dinnan bane amma kuma kasan baya wasa da gym. 
Golden hair gareshi shima amma yayi cutting dinshi short, ga eyes dinshi da basuda girma sosai zagaye suke da dogayen eyelashes, eye balls dinsa are hazel color that makes him look so sexy and masculine. Bai tara saje ba akan sharp jawline dinshi, ga pink lips dinshi da sosai yakara ma face dinshi dimension hade da dogon masc nose dinshi. 
Idanunshi ne ya sauka akan….
(Author’s note: Guys😆 ga Imad ga Mihri fah. Yanzu wasan zai fara. Ya kuke ganin Imad zaiyi reacting idan yaga Mihri? Itama ya Mihri zatayi reacting? Nifa gani nakeyi a yanda mihri keji zata iya tashi ta rungumeshi shima🤣).

Mirals pov:
Batai wata wata ba a harzuke ta daga hannu zata zabga mata mari idanunta ya sauka akan badge din jikin uniform na Miral da aka rubuta Batch 1 a jiki. Sauke hannunta tayi sannan tace “kinyi sa’a wlh yau kikazo kuma kina cikin yan batch 1, da yau saikin gayama aya zakinta”. Tana gana fadan hakan kuma ta juya ta koma inda take.
Wani ajiyar zuciya Miral ta sauke dan harta sadakar dukanta zatayi sai kuma taga bata tabata bah. Kallon badge din dake kirjinta tayi an rubuta batch 1, ita batama lura dashi ba sai yanzu. Tabota taji anyi tayi saurin matsawa tareda kallon wanda ya tabotan irin kallon meye hakan nan. 
Wannan yarinyar ce mai blue eyes data dago mata hannu. Dan juyawa tayi tafara jin ranta na baci ta tsani ana shige mata. Ga har wani kama da Layla yarinyar keyi, sai taji ta kara tsanar yarinyar kawai. 
Cikin wata jolly voice yarinyar kanaji kodaga voice dinta kasan irin masu shegen surutun nan ne tace “sunana Aliona, i am from russia, nazo wannan kungiyar ne sati hudu dasuka wuce. Sannan inaso na zama friend dinki you are so beautiful kinsani koh? Wlh ban taba ganin mai kyau kamarki ba, Allah sarki dama mamana ta fada mun mutane masu kyau basa rayuwa mai tsawo, musamman masu kyau irin na sirens kinga kuma ke irin kyansu kikeda shi kamar ba mutun ba, ashe da gaske takeyi tunda kina cikin Batch 1. Kiyi hakuri kinji, a heaven sai mu zama kawaye best friends forever”.
Tafada hakan tana miko ma Miral karamin yatsarta alamun su kulla kawa. Kallonta kawai Miral ta tsaya yi ita tunda take a rayuwarta bata taba ganin mai surutu haka ba. Kawai daga haduwa tabata labarin rayuwarta gabadaya. Dan iskanci ma wai har tana tambayarta wai ko tasan tanada kyau itada face dinta. 
Abun ya bata haushi yakuma bata dariya at the same time saidai bata nuna ba. Abunda ya tsaya mata arai shine tace wai ita yar batch one ne shiyasa zata mutu da wuri, me batch 1 din ke nufi ne? Kodai ta tambayi yarinyar ne tunda ita tasani? Saidai kuma tasan tana tambayarta zatayi tunanin ta yarda suyi kawancen ne. Wata zuciyarce tace mata ai kawai ta bude baki ta tambaya komai daga baya ne akan ta zauna batasan komai dake faruwa ba dakuma abinda ke shirin faruwa. 
Cikin flat voice ba yabo ba fallasa tace “menene batch 1 din? Meyesa kuma zan mutu kafin ke dakika rigani zuwa?”. Dan dariya Aliona tayi saikuma ta kwashe da dariya kamar wata mahaukaciya. Kallonta kawai Miral keyi tadan hade face dan batason wulakanci, har ta mike Aliona tayi saurin rike hannunta tana tsayar da dariyar tace “sorry bestie bake nake ma dariya ba, kawai maganar naki ne bayani dariya, ke banda abinki ai dama dole ki rigani mutuwa a cikin wannan kungiyar, kin fini kyau sannan daga gani na girmeki nifa i am 19years old. Sunfison fresh blood”. 
Dan waro ido Miral tayi taji anyi maganar blood, dama tasan za’ayi hakan. Cigaba da magana Aliona tayi tace “Toh bari kiji, kinga wannan batch 1 din? Yana nufin kune a farko na wannan watan. Duk karshen wata suke diban wayanda sukafi kyau, basuda shekaru sosai, sai su tafi dasu babu wanda ya taba dawowa sai 3weeks ago da wacce aka tafi da ita a batch 1 na wancen watan ta dawo, ashe guduwa tayi”. 
Saida tadan nunfasa tareda gyara zamanta ta rage muryanta daga ita sai Miral tace “kinga yanda ta dawo? Babu kaya a jikinta kwata kwata, jikinta kamar anyi mata wanka da jini. Babu idanu a cikin idonta kamar an kwakulesu, ga cikinta an yankashi anyi yanka uku kayan cikinta sunyo waje ta rikesu. Bakinta da hancinta duk jini ke kwarara tazo muna lunch tana ihu tana so tafada mana wani abu takasa. Dakyar tasamu muryar ta tadan fito Tana fara magana kuwa bamu gane metake fada, sannan ba muryarta bane muryan wani ne kamar ba muryan mutane ba dake magana cikin wani yare dabamu gane ba. Tana fara maganar kuwa kawai wuta ta kama daga cikin jikinta a take ta kone kurmus ko hayaki wutar batayi bah, bakuma toka bayan ta gama konewar”. 
“A duk ranar karshen wata sukeyi, wanda zai kamar jibi kenan. da daddare suke zuwa daukar yan batch 1. Banda ita babu wanda ya taba dawowa sai wancen shekarar wanda sukenan sukaga wacce ta dawo ta wancen shekarar duk sun haukace suna cikin wani daki yanzu ba’a ganinsu, ance wacce ta dawo wancen shekarar da ita muka gani da yanda take da dukkanmu mun haukace muma”.  
(Tashin hankali). 

For more information ga WhatsApp number na ***.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol