Free chapter · Read without an account

Chapter 16

by Hauwa Salihu · MATAR SALMAN

*đź’«MATAR SALMANđź’«*


*➡PART ONE*
*PAGE 16*



Nan da nan maganar aurena da Doctor Hakim kamar wasa sai gashi magana tayi karfi, don a cikin satin nan yace zai turo magabatansa. Sai dai kafin nan da Mama ta fadawa Abba cike da mamaki yace "Amina ko dai akwai abinda ya faru tsakanin Salman da Rumaisa ne wanda mu bamu sani ba? Kinsan fa ruwa bata tsami banza yaran nan su suka shirya kansu suka fada mana ko, amma gashi yanzu matsala ta faru a tsakaninmu duk mun tambayesu sunki su bamu cikakken bayani bare mu shiga al'amarin mu gyara gashi yanzu Rumaisa zata turo wani daban akan maganar aurenta, gaskia ya kamata dai mu san abunyi don baza mu zuba ido ba, bari na kira Kasim yazo dai tukunna, ku dakatar da shi Doctorn don Allah.”
Mama tace "To Yaya duk yadda kukayi dayane, Allah ya kai mu.”

Daga nan ta mashi sallama ta dawo side dinta ta sameni na gama shiryawa cikin atamfa Riga da siket nasha daurin dankwali na zuba sarka da 'yan kunne har da warwaro da zobuna na dauko jakata da tayi matching da takalmina, nasha gyale kuwa don ko Matar Shugaban Kasa a yau dinnan zan iya jerawa da ita tsaf.

Mama kallo na take tace "Rumaisa yau kuma makarantan kikewa kwalliya haka? A'a to sai dai kisa hijabi indai zakiyi driving. Dariya nayi nace "kyai Mama wai har kin manta nace miki zanje ne bikin wata 'yar makarantanmu?”

Tace "Aikam na manta yaushe zan zauna rike shiririta ga abubuwa da yawa nan a gabana.”

Murmushi nayi sannan na suri makullin motarta nace "Bazan ma shiga makaranta ba daga gidan bikin dai zan dawo gida kawai.”

Tace "Ki dai kula da kanki Allah kuna ya tsare banda dare.”
Na ce "amin Mama, inshallah.”

Na fita cikin sa'a kuwa saiga Ya Salman cikin kakinsa ya sunkuya yana gyara takalminsa.
Yana dagowa mukayi ido hudu, na riga shi kauda kaina sakamakon zuba min ido da yayi kamar mai shirin fadin wani abu, gabaɗaya ya kasa ɗauke idan sa a kaina, nikuwa jin kaina nayi ya kumbura a zuciyata har fadi nake ”Ni ɗin ta wasa ce?”
Ba tare da na sake kallonshi ba nace ”Yaya ina kwana?”

Kamar ba zai amsa ba daga bisani kuma yace. ”Lafiya lou.”

Ni dai tuni na shiga mota na tayar ina wani jijji da kaina, da gangan na fizgi motar da gudu kamar zan tashi sama cikeda kwarewa na bar layin.
Ya kuwa bi motar da kallo har ya ɓace. Nima saida na hau titi sannam na rage gudu.

Nan naji wayata na kira na lalubota na duba sai naga Raihana ce.
Na dauka nace ”Hello Hajiya.”

Tace ”Hajiya Rumaisa kina duniyar nan.....Ni dai don Allah kizo sai nemanki nake.”

Na ce ”Tohh lafiya dai kike ta nemana?”

Tace "Lfy lau karkiji komai don Allah kizo kayane fa masu zafi daga Sokoto nayi muku odarsu keda Sakina da Fa'iza amma kuma sai naji labari mara dadi akan maganarku da Yaya......

Na katseta da fadin ”Kinga bari nazo ina tuki ne.”
Na kashe sannan naci gaba da tukina. Gidanta na fara zuwa ina isa na sami Sadiya da Lathifa a Palo ana zuba hira da fulatanci cikin nishadi sai dariya suketa kwasa, na lura Sadiya tasu tazo daya da wannan Lathifar, to ba dole ba, yarinya ance budurwa ce amma ido a tsastsaye.

Ina ganin su nan da nan fara'ar da ke kan fuskata na nemeshi na rasa.
Sukam kallona suke tamkar basu sanni ba.
Raihana ta rike baki tace "Lallai Rumaisa irin wannan ado haka ina zuwa?”

Na ce "wlh biki ƴar makarantan mu ne zanje.”
Tace "To ki zauna mana, kin wani tsaya kamar bakuwa.”

Na ce "a'a, akan hanya nake, kuma naga kinada manyan baki ni zan tafi sai watarana.”

Sadiya tace "Ko dai mu baku wuri ne Hajjaju?”

Kallon banza na mata na ce "Kuyi zamanku.”

Tayi wani makirin murmushi tace "Au ga fa Lathifa Rumaisa baku gaisa ba, itace matar da Ya Salman zai aura.”

Na kalli Lathifa sai kuma nayi murmushi nace ”Allah sanya alkhairi, kinsan da yake ita batajin hausa ni kuma banajin fulatanci shiyasa ban mata maganaba......”

Raihana ta katseni da fadin ”Kinga zo muje ciki Malam ne yake son magana dake dama, waiko akan kanwarsa da ke department dinku ne ko yaya ne muje dai.....”

Taja hannuna muka tafi ɓangaren Malam ɗin ba kowa, a Palo muka zauna tace "Rumaisa me faru tsakaninki da ya Salman?”

Nace "Ba komai Raihana
. 
Tace "a'a wlh ban yarda ba haba Rumaisa me yasa zakuyi haka kuna fa son juna da Yaya sosai don Allah ku maida soyayyar ku, kinga wlh kayan mata na muku oda nidai daga Sokoto, naki ma yafi yawa don so nake ki rikita Yaya sosai amma kawai sai naji Sadiya na cewa wai ai kun bata waye waye yanzu Lathifa zai aura? Nifa kinsan Inna basa sakani cikin sangarsu tunda na daina biye musu.”

Nayi murmushi nace ”Ba komai, haka Allah yaso don ni a halin yanzu ma har na ba wani dama ya turo magabatansa, to kinga Yaya kuma ga Lathifar sa don haka yanzu abinda ya rage kawai ki mana addu'an fatan alheri.”

Tsaki taja tace"wlh daga ke har yaya kuna shirin TAFKA KUSKURE babba a rayuwarku don wlh aurenku shine alheri karku yarda a rabaku.”

A zuciyata nace daga baya kenan, sai kuma na kalleta nace ”Ai wannan ya wuce tunda ni na sami wani mijin, shi kuma ga matarsa nan kuma itama, 'yar'uwarku ce.”

Tayi tsaki tace ”ƴar'uwarmu ce amma basu dace ba don wlh Lathifa da kike gani 'yar duniyace cikakkiya wlh gaba daya ta gagari iyayenta amma shine kika ga Inna da kwashe kwashe ta kwasota wai Yaya ya aureta sai kace asiri akama Inna ? In ba haka me Yaya zaiyi da wannan 'yar iskar?”

Na tabe baki nace ”Hmm ke kika ga hakan ai, sukam basu gani ba, kinga ni tfy ta zan yi sauri nakeyi.”

Jikinta a mace tace ”Rumaisa shikenan tunda kinki ki bani hadin kai, amma fa ki sani bazan bar wannan maganar haka ba domin wlh sai na wargaza dukkan shirin Inna da Sadiya in Allah ya yarda.”

Nace "Ni dai ba ruwana ki bar zancan nan anan in kina son kanki da lafiya.” Daga nan na mata sallama.

Gidan biki na wuce inata tunanin maganganuna da Raihana, harga Allah ina son Yaya Salman amma abun yafi karfina dole in koyawa zuciyata hakuri da sonsa, ko ba komai in samu nitsuwa a zuciyata.


A cikin satin Abie yazo Kano nan Abba ya gaya masa komai dake faruwa, gaskia abin ya damesu sosai, sai dai sun kasa ganewa Salman kwata kwata, sun sake zaunar dashi amma yaki yarda ya fada musu matsalarsa, kawai yaji ya tsaneni ne bazai iya aurena ba.

Mama kam cewa ta yi kawai suyi hakuri su barshi haka Allah yaso, wani baya auren matar wani.

Duk yadda suka so su gyara alamarin ya gagara haka suka hakura, ba don ransu ya so ba, Abie yace kawai zai jira zuwan yan uwan Doctor Hakim domin azo ayi maganar aurenmu, shi kuma Salman sai ya nemo matar da zai aura don basa son bukukuwan ya wuce ending of this year, ya dai amsa musu da to kawai, amma shi kudin hidimar biki da Abie ya basu ma sabuwar mota yayi order.

Inna kam ba wanda ya kai ta jin dadi ita da Sadiya domin sunci nasarar rabani da Salman, gaskia wannan karon aikin malaminsu yayi kyau akaina ni da Salman,
sai dai a yanzu matsalarta bai wuce, yadda zasu cusa masa son Lathifa ba, sai kuma matsalar ta na biyu taga Sadiya ta koma gidan Jafar amma abin ya gagara duk shige shigen duniya sun gama amma ko labarin Jafar babu, tunda ya saki Sadiya bai kuma waiwayarta ba har yau gashi yaronsa ya girma har ana shirin yayeshi amma baisan ubansa ba. Wannan abun yana damun Inna sosai.

Yayinda Sadiya kam tuni ta fita harkar wani Jafar zuwan Lathifa yasa idonta ya kara budewa, don yawonsu suke, ta dinga zuga Sadiya akan kar ta koma gidan Jafar kawai ta yaye Abdul ta sami wani bazawari mai kudi zai fiye mata wannan wahalar. Don haka yanzu kominsu daya da Lathifa sun mannawa Inna hauka, alhalin ita tana ta kokarin ganin Sadiyar ta koma dakinta, Lathifa kuma Salman ya aureta, amma su suna harkokinsu don tsabar RASHIN NAZARI irin na Sadiya.


A satinda Doctor Hakim yace zai turo magabatansa sai muka ji shiru kuma, na kira wayarsa ma a kashe.
GabaÉ—aya hankalina ya tashi ga Abie yana jira suzo don ya samu ya wuce Abuja a yau É—in. Amma shiru shiru har bayan isha sannan sukazo, har naji sanyi a raina don dazun har kuka nayi.
Anan na fara trying na layin Doctor Hakim amma har yanzu a rufe.

Mama ta shigo ta sameni tace ”Yanzu kam hankali ya kwanta koh tunda kinji labarin bakin sun iso.”

Dariya kawai nayi na sunkuyar da kaina, tace "To sai ki samu kiyi bacci don mu tashi da wuri ai.”
Nace ”To mama.”

Na kwanta kenan sai ga kiran Hakim da sauri na dauka ina murmushi nace ”Doctor ina ka shiga tunda safe wayarka switch off?”

Yace "wlh ayyuka ne suka min yawa a asibityn yau, nayi tiyata.”

Nace "Ayya shiyasa mana naji muryarka a sanyaye nasan ka dibo gajiya kam sorry dear.”

Shiru yayi jin shirun yayi yawa kuma yasa nace "A'a lfy doctor?”

Yace "Da sauki dai Rumaisa, amma akwai matsala akan maganar aurenmu?”

Da sauri na tashi zaune kirjina na bugawa nace "Me ya faru Doctor wayanda ka turo sunzo fa har sun tafi.”

Yace "Eh sun je sai dai basu daidaita da su Uncles naki ba, domin sun nemi su gana ne da dangin mahaifinki sai dai kuma ba wata cikakkiyar bayani da aka musu akan waye ne mahaifin naki kuma a'ina yake."

Nikam tuni na fara kuka, hakuri ya shiga bani yace. "Rumaisa ban San me yasa suka min haka ba ni a ganina ba ruwansu da waye mahaifinki ko danginsa tunda yanzu ma a cikin danginki suka sameki kuma su Kawun ma sun isa su daura miki aure ba sai an tsaya wani bincike ba.”

Na girgiza kai cikin matsanancin kuka nace "Banga laifinsu ba ko kadan don wlh nima ina son sanin waye mahaifin nawa Doctor.”

Na karashe maganar da kuka shiru yayi sai kuma yace "Rumaisa kiyi hakuri ki bar kukan nan hankalina yana kara tashi, insha Allah zamu daidaita komai kuma kema kiyi kokari ki tambayi Mama labarin mahaifinki, idan har bata saurareki ba wannan karon ni zan tayaki mu binciko duk inda yake kinji?”

Nace "A'a ka bari kawai Doctor kar ka shiga maganar nan domin za'a iya samun matsala Mama tayi fushi dani.”

Yace ”To kisani Rumaisa ya zama wajibi ne a gareki yanzu ki nemi sanin waye mahaifinki.......

Na katse wayar naci gaba da kukana.
Ranar banyi bacci ba cikin dare koda Mama ta zo don ta tasheni sai ta sameni akan sallayata ina sallah don haka takoma.
Washe gari su Abba suka kiramu a palonsa anan fa Abie ya bayyana mata yadda sukayi da yan'uwan Doctor Hakim.

Shiru ta yi sannan daga bisani tace "To Yaya ni ban ma san me ma zance ba anan, kawai abar su Allah ya kawowa Rumaisa wani mijin shikenan.”

Abba ya katseta da fadin "Amina yana da kyau ki fada mana waye mahaifin Rumaisa mu nemoshi ko danginsa, domin nasan ko itama tana son sanin waye mahaifinta musamman yanzu da maganar aurenta ya fara samun matsala irin haka, gaba zamu duba, harga Allah wannan yana cikin dalilin da yasa nida Kasim muka fi son ace Salman ya aureta asirinmu a rufe, yanzu meye amfanin wannan?”

Bacin rai sosai ya bayyana a fuskar Mama ta ce "Yaya har yanzu kuma baku yarda dani ba, lokacinda naso kusan komi kin saurarata kukayi, yanzu kuma ni bana son tuna abinda ya faru a baya, Rumaisa dai tana da uba tabbas, amma nima bansan inda yake ba, in sunga zasu iya barin ayi auren haka fine, in kuma sunce sai sunsan waye mahaifinta to ni dai ban shirya amsa wannan tambayar ba, kawai su hakura da juna Allah ya kawo mata wani mijin, kuma ni Yaya a ganina ai kun isa ku zamewa Rumaisa dangin uwa dana uba koda kuwa Rumaisa er tsintuwace, don haka ni bana bukatar a sake kawo min zancen waye mahaifin Rumaisa, suje can da dalilinsu mara tushe, Allah haɗa kowa da rabonsa.”

Nikam tsananta kukana nayi na ce "Mama don Allah ki taimakeni nima ina son sanin waye mahaifin nawa.”

Ta girgiza kai kawai tana kallona cikeda takaici.

Juyin duniya Mama ta kafe kan ra'ayinta, dama ita dama haka take da kafiya, Abie kam tuni ransa ya baci ya kama yima Mama fada akan wannan hali nata na kafiya da taurin kai.
Nikam sai kuka na sani.

Inna ce ta fado mana a palon babu ko kunya ta kallemu gabadaya sai kuma tace da Abie "Kasim ka daina bata ranka a banza, duk naji tattaunawarku, Amina kuma bazata taɓa gaya muku komai ba gameda wannan ƴar ta ta ba, domin tasan ba ta hanya mai kyau ta sami yarinyar nan ba, duk mun sani anan ko ba haka ba?”

Ba tare da ta tsaya jin karin bayani ba nima ta kalleni tace ”Rumaisa bari na fada maki ko hankalinki ze kwanta kinji?”

Ta ci gaba da fadin ”Sunan mahaifin ki IBRAHIM, wanda a shekarun baya da suka gabata shine ya saurayin da hure wa mahaifiyarki kunne ta dinga bijire ma Yayyunta har ta kai ta kawo ya dauketa suka gudu suka shiga duniya, daga nan bamu sake sanin inda take, sai bayan wasu shekaru kawai ta dawo tare da ke kina yar shekara biyu alokacin, kuma Yayyunta sunce matukar zata zauna dasu to sai dai ta maidaki wajen ubanki domin su bazasu zauna da ita da tarin abun kunya ayita zaginsu ba a dangi, 
Shine fa akan haka ta daddage ba kunya ba tsoron Allah ta zuba masu rashin mutunci babu abinda ta rage bata faÉ—a musu ba, daga karshe ta fice wanda bamu sake sanin inda kuke ba sai daga baya muka gane tana wani kauye domin tana yawan shiga cikin gari acewarta tana kasuwanci amma babu.........

Abba ya katseta a fusace da fadin "Ya isa Shatu wai ke ina ruwanki ne?”

Mama tayi murmushi mai ciwo tace "Ai kawai ka barta ta karasa Yaya.”
Ta kalli Inna tace ”Ki karasa bada labarin ki Shatu.”

Inna ta yi murmushi ta kalleni tace ”Rumaisa......

Mikewa nayi sannan na kalleta nace ”Wani gari yake Innah?”

Ta buÉ—a hannu tace ”Nima bansani ba tambayi Uwarki.” 
Da sauri na bar palon ina kuka matsananci.
Na tafi na barsu, kan kace meye wannan na haɗa kayana na fita da sauri zan koma palon Abba in tambayi Mama garinda Ubana yake, sai muka hadu da Ya Salman a tsakar gidan ya kalleni da mamaki yace “Ke kuma ina zakije haka.”

Haushi ya cikani a fusace nace "Zan tafi neman mahaifina ne ko zaka hana?”

Cike da mamaki yace ”Ke kina cikin hayyacinki kuwa aina zaki je ki nemeshi? kin san shine dama?”

Na girgiza kai nace ”Ko ban sanshi ba zan bi duniya har sai na gano inda yake, domin ya isheni gorin da ake min.....

Jin muna haka da Ya Salman ya saka du su Abba suka fito har Inna, Abba da Abie ne suka shiga bani hakuri. Ni dai na dage yau bazan zauna ba zan tafi neman Ubana, domin ya isheni gorin da ake min.”

Inna ta yi dariya hade da shewa tace "Jeki abinki Rumaisa Allah ya bada sa'a kinji?”

Abba ya harzuko yace ”Shatu wai ke wace irice? Ana kokarin daidaita abu tun dazu amma sai kara hura wuta kike, kece fa kika fusata yarinyar nan ana bin komai a hankali, to wlh karki kuma sa bakinki bana so don na lura baki son zaman lfy.”

Ya kalli Mama yace ”Amina rike Rumaisa Ku je ciki kuyi hakuri don Allah maganar ya isa hakan nan, Ni nasan yadda za'a bullo ma lamarin InshaaAllahu.”

Mama ta girgiza tace "Yaya ai babu amfani in tsaida Rumaisa taje kawai, matarka ta rigada ta hargitsa komai ta tayarwa Rumaisa hankali ta yanda bazata taba saurarona ba don haka zamanta anan baida amfani taje .......

Sannan ta kalleni tace "Rumaisa ki je ba komai na yafe miki, kuma yadda Shatu ta gaya miki hakane, mahaifinki cikakken sunanshi *IBRAHIM AHMAD GALADIMA* Cikakken ɗan Adamawa ne a garin Yola, kina zuwa asalin Yola Town kikace familyn GALADIMA to babu wanda bai sani ba, ina miki fatan alkhairi Allah ya tsareki kuma a duk inda kike a fadin duniya!”

Ta karasa maganar tana kuka sosai ta wuce ɓangaren ta Ya Salman ya bita da kallo sannan ya kalli Innama.

Inna ta tabe baki tace ”Hmm ayi dai mugani.....”

Na kalli Ya Salman wanda na saka a raina shine gani na karshe, don ni bazan kuma dawowa ba na tafi kenan. Hawayene masu zafi suka zubo min, nayi saurin kauda idona daga kallon nashi, na kalli su, Abba kawai sai na juya da niyyar tafiyata Abie da Abba sukace in dawo kar in je ko'ina.

Hawayen idona tuni ya kafe nace "Kuyi hakuri Kawu karkuce naki jin maganar ku amma zan tafi tunda Mama ta bani izni kumin fatan alkhairi.”

Da sauri na fita Salman ma da sauri ya juya zai bi bayana wata uban tsawa inna ta daka mishi wai ya dawo Abba ya kalleta sai kuma ya kalli Salman yace ”Salman ka bita kuma ka dawoda ita karka kuskura ta bar garin nan Umarni na baka!”

Ni dai tuni na fice na barsu bansan ya suka kare ba.

Saida na tafi Atm nabi layin cire kudi daza su isheni don a wancan lokaci babu wani pos, gashi karshen watane anyi salary shiyasa ATM akwai layi. ƙarfe shabiyu ina tasha na kuwa ci sa'a na sami motar Adamawa saura mutum daya na biya kudi na bada address dina da number din Mamana saboda halin tafiya. Nayi addu'a yayinda nake shirin shiga mota...........

Sai ji nayi an riko hannuna ta baya.
Ina juyawa naga Ya Salman ne. Ya zuban ido nikam tuni na kwace hannuna raina ya mugun ɓaci a wannan lokacin.
Girgiza min kai yayi yace "Rumaisa babu inda zakije kawai kizo mu koma gida.”

Nace "wlh bazan koma ba, don banga dalilin da zai maidani gidanku ba mahaifiyarka da 'yar uwarka sun sakoni a gaba da zagi da gori don banda asali to zanje in samo asalin nawa kuma bazan dawo gidanku ba.”

Shiru yayi kamar bazai yi magana ba yace "Ni dai nace kizo mu tafi ba wai ki daga min murya attention din mutane ya dawo kanmu ba.”

Aikuwa nace babu gidanda zan koma wasa gaske kuwa saida naso tara masa mutane a tasha, don ma driver din babban mutum ne, shima saida ya shiga maganar duk tunanin kowa Ya Salman mijinane.

Shidai yana rike da hannuna yace bazan shiga mota ba yayinda ni kuma nace sai na shiga yace ”Rumaisa kinsan zan iya daukarki ko?”

Driver dinne ya dinga bani hkr yace in bi mijina har da Ć´ar guntun nasiharsa ya fito min da kayana. Ya Salman ya É—auka ya mayar mota ya dawo wurina. Kuka na kama yi nace "Ashe da kai ake hada baki ake kuntata mana ni da mahaifiyata a gidanku......

Kalle kalle ya shigayi kamin na ankara ji nayi cak! ya É—auke ni kamar wata er baby, kafin kiftawar ido har ya ajiyeni a mota ya kulle, kukan takaici da bakinciki nayitayi ina jan Allah ya isa, shi dai bai kuma tankani ba ya tada motar kawai muka bar pack din.


Muna isa gida ko kayana ban sauke ba na fita na nufi bangaren Mama. Ina shiga na sameta a kwance tana bacci. Ban kula ba na karasa gabanta na fara tashinta ina ”Mama ba kince kin yarje min in tafi ba? kinga har na tafi amma Ya Salman yaje ya dawo dani don Allah Mama kice ya barni in tafi wlh in naje zan dawo ko don ke da makaranta da na kusa gamawa wallahi zan dawo."

Ganin bata ko motsa ba yasa naji zuciyata ta buga da karfi na mike a tsorace.
Na juya ya salman ne ya shigo da kayana, a rikice nace ”Kazo kaga me ya sami Mama bata motsi?”

Ya ajiye kayan sannan ya karasa gaban ta shima ya duka gaban gadonta yana taÉ“a wuyanta sannan a sanyaye yace "Bacci takeyi bayan tafiyar ki ne ta suma, aka kira Doctor, yace jininta ya hau a barta ta huta.” 

Hawayene ya zubo min nace "Ka gani ko? Duk abin nan da yake faruwa dani saboda kai ne! Don Allah don Annabi ka daina shiga harkana ko na sami salama gun Inna.”

Bai ce komi ba kawai ya juya ya fita abinsa, bayanshi nabi a Palon Mama naga Mmn sakina ta shigo tana zaune bayan Ya Salman ya tafine ta ajiyeni ta dinga min magana hade da rarrashina tana in hakura da maganar tafiyar nan tunda Mamana bataso.

Gefe na koma na zauna naci kukana har na koshi sannan na hakura.

Gaskia a kwanakin mun fuskanci kuncin rayuwa nida Mama a gidan, Inna dai ba abinda ya canza a halinta duk da ba shiga cikin gidan ɓangarensu muke ba sosai amma duk sadda muka shiga sai ta dinga mana habaici, tana jifar mu da bakaken maganganu.

*
Sadiya da Lathifa dai sai harkokinsu suke. Sadiya ta kara wayewa tuni ta yaye Abdul haka suke barinshi gun Inna suyi ficewarsu yawo, yaro yayita kuka Inna tayita fama.
Lathifa ta tara samari sosai ma su kudi, manyan alhazawa, kunsan Kanawa da son farar mace gata kuma kalar tubarkallah son kowa, gashi ta iya salon karuwanci sosai. Don haka sai kashe mata kudi ake. Sadiya ma ba laifi ta É—an sami zawarawa daidai kalarta tunda ita dai batada wannan kyan na Lathifar, don haka suna ta shagalinsu.
Duk abun nan basu san Ya Salman ya zuba musu ido ne kawai yana jiran dubunsu ya cika. Inna tana son tayi complain kuma bata son aji kansu, amma harga Allah lamarin Lathifa ya fara isarta itakam, to an kawota ne fa domin taja hankalin Salman ya aureta, amma yarinya daga zuwa birni taga alhazawa ta fita harkar Salman.

Ranar da abun ya ishi Ya Salman, Wai sunje bikine amma sukaki dawowa har shadayan dare sun bar Inna da Abdul sai faman kuka yake mata, saida Ya Salman ya karbeshi suka je waje har yayi bacci sannan ya dawo dashi ya kwantar baice ma Inna komi ba, ya koma wajen ya ci gaba da zaman jiran dawowarsu Sadiya. Can kuwa karfe sha daya ya wuce kadan, wata dalleliyar mota jeep ta zo dab da kofar gida ta yi parking abun mamaki sai yaga Sadiya ta fito taci ado a matse cikin riga da siket babu mayafin kirki.
Ba ta ma ganshi ba ta wuce gida aikuwa da sauri yabi bayan ta Lathifa kam ba ta ma fita daga motar ba kasancewar motar saurayinta ne ta tsaya suyi sallama.
Yaya Salman kuwa a tsakar gida ya tadda Sadiya fuskar a murtuke ya fisgota hade da sharara mata mari yace ”Daga gidan ubanwa kuke?”

A tsorace Sadiya tayi baya zata gudu ganin yana shirin kwance belt daga kugunsa, ya damkota sai kuwa ta fara bashi hakuri "Yaya don Allah kayi hakuri wallahi na raka Lathifa ne biki......

A fusace ya sake É—auke ta da mari yace "Gidan bikin uban wa? Kuma da iznin waye kuka fita gidan nan kuka dawo karfe shadaya?"

Da sauri ta ce "Yaya Inna ce tace muje......

Inna dake zaune a kan kujerar dake tsakar gida take kallonsu cikin takaici da bakin ciki tace "Yanzu don bakida kunya karya zaki shirya min ina jin ki Sadiya, ba nace karku fita shine da kukaga na shiga wanka kuka yi ficewarku kuka barni da yaro ya bi ya fitineni da kuka don tsabar rashin hankali da rashin tausayi irin naki ba? To Salman ya kasheki ma yau in yaga dama.”

Sadiya ta fara kuka tace "Inna wallahi kin manta ne .......”

Ba ta karasa ba Ya Salman ya daka mata tsawa yayinda ya karasa cire belt ya shiga dukanta ta ko ina, ta shiga ihu tana ”Wayyo Allah Inna Yaya zai karyani...... Yaya na tuba wlh na tuba don Allah kayi hakuri......

Inna ta kauda fuska tace "Ai gwara ya karyaki din inyi jinya da irin yawon tsiya da kika tsiri yi.”

Ya salman kam bayaji baya gani sauke mata belt kawai yake. Ihunta ya tashi Abba wanda tun shigowarsa bayan isha ya tambayi Inna su Sadiya tace suna can dakin ciki.
Da sauri Abba ya rike Salman yana cewa ”Kai Salman meye haka, me ta maka da zafi haka kake dukanta?”

Sadiya jikinta duk ya faffashe tuni ta yi bayan Abba tana kuka.

Cikin tsananin bacin rai Ya Salman ya shiga gayawa Abba duk abubuwanda su Sadiya keyi.
Abba ma ransa ya baci sosai ya kalli Inna yace "Kinga abinda nake fada miki tuntuni ko? To wlh ni bazan bari Sadiya ta janyo min abun kunya ba don haka na baku wata daya taje ta daidaita da daya daga cikin maneman nata a daura musu aure kowa ya huta sai kuje ku gama shawarar ku.”

Ya kalli Ya Salman yace "Ina ita kuma Lathifar?”

Ya Salman yace "Ta na waje zaune a motar wani kato, yanzu karfe sha biyun dare.”

Yana fadin haka yayi wajen a fusace ransa na kuna. A kofar gida suka hadu zata shigo, ita ko gyalen ma babu, tana tafe tana kallon waya bai tsaya wata wata ba kawai ya kife ta da mari unexpected, bata gama fahimtar me ake ciki ba, ya shiga sauke mata belt a tsakiyar baya itama, a rikice kuwa tayi cikin gida tana ihu don bata san duka ba a gidansu.
Da gudu ta isa tsakar gida ta rirrike Inna tana kuka.

Jefar da belt din yayi yana huci Abba yace ”Kayi min dai dai Salman kuma na gode maka Allah ya maka albarka tafi kaje ka kwanta abinka.”

Tare suka fita da Abba shi ya tafi gidansu Abba kuma ya rufe get ya koma bangaren shi ya kwanta.

Inna da 'yan dakinta kwana sukayi basuyi bacci ba, sun kwana zazzaɓi, Allah yaso akwai paracetamol. Lathifa tuni ta hada kayanta wai ita bazata iya zama ana dukanta kamar jaka ba don tsabar mugunta a hakan ne za'a ce shine zai aureta watarana yaje ya kasheta a banza? ita kam bazata iya ba. Haka tayita fadar bakaken maganganu.

Sadiya dai sai ido, Asuban fari Lathifa tayu tafiyarta ko Abba bai sani ba don yana masallaci, juyin duniya Inna ta yi da ita ta hkr amma taki fir! Haka Inna tanaji tana gani ta tafi, bakin ciki fal zuciyarta, dama duk wanda yace tukunyar wani bazai tafasa ba, nashi ko zafi bazaiyi ba.

*
Ni dai bansan me suke ciki ba, tunda ba shiga harkarsu nake ba, a bakin Mmn Sakina muke jin labarin nida Mama, tabe baki nayi nace "hmm kadan ma Inna ta gani ai.”

A lokacin muka fara shirye shiryen exams kai ya fara daukan zafi da karatu, Banda lokacin kowa yanzu sai na karatuna da ibada, ko ina gida ma bana fita a daki nake wuni abina.
Mama kuma yanzu ta fi maida hankali a harkar kasuwancinta sosai don haka bata da lokacin kowa itama.

Kwatsam ranar ba saiga Ahmad har gida yazo ba, rabona dashi tun lokacin da na mashi nasiha akan shaye shaye nace mishi in ya daina ya turo magabatansa muyi aure......
Kawai yaro ya shigo wai ana sallama dani.
Inata mamaki na fita ina ganin shine na koma gida na gayawa Mama tukunna tace in shigo dashi Palonta mu zauna.
Don haka naje nai mishi iznin isowa bayan na kawo mishi drinks da ruwa mai sanyi. Na koma na zauna.
Ya kalleni yace ”My Queen sai gani babu notice, to tunda muka rabu zuciyata ta kasa hkr dake shine na dawo kawai don bazan cuci kaina ba, naji yadda kukayi da mutanen Dr Hakeem, amma ina son ki sani wannan makircin matarsa Dr Surayya ce (Ƴayarshi) itace ta dinga zuga mahaifiyar Dr Hakeem akan sai an san waye mahaifinki........koda ya ke ni bashi ya kawoni ba, My Queen na dawo ne fa.......” Yayi kasa da murya yana kallona.

Babu alamun fara'a a fuskata nace "Ina fatan dai baka manta yanda mukayi da kai ba a baya koh?”

Yayi murmushi yace ”My Queen ki kalleni mana, bakiga na canza ba wai?”

Sai a sannan na ɗan kalleshi nace ”Na gani amma........”

Ya tari numfashina da fadin ”Kinga yanzu na daina shan kome kuma bana zuwa casu wlh yanzu na zama mutumin kirki kuma wannan karon banzo da wasa ko da yaudara ba nazo ne da niyyar aurenki in har kika ban dama ko gobe za'a daura mana aure na shirya Rumaisa.”

Shiru kawai na masa ina nazari, ya kwantar da murya yace "Queen na baki dama kiyi tunani, wlh ina son ki zan iya yin komai akan ki, kema kuma nasan kinsani.”

Gyaɗa kai nayi nace ”Shikenan Ahmad zan yi shawara kuma zan tuntubeka InshaaAllahu.”

Ya saki murmushi hade da min salute yace ”Daz my Queen.”

Anan muka taba hira kaÉ—an, lallai na yarda Ahmad ya canza kam sosai ma.
Da yazo tafiya kudi ya zube min ga kuma shopping niki niki a manyan ledoji kunsan mutumin naku ai, na rakashi har waje a bakin motarsa muka tsaya hira kuma har Ya Salman ya dawo daga aiki ya samemu. ya fito a sabuwar motarsa yana sanyeda kakinsa ido muka hada dashi nayi saurin kauda kaina na haÉ—e fuskata.

Shikam tsabar takaici ji yake kamar ya zo ya shako Ahmad. Wato iskancin kuma har a kofar gida yanzu kam.

Sai kawai naga ya nufo inda muke cikin tafiyar jarumta da nuna isa duk yabi yayi kicin kicin da fuskarsa.
Ni dai na kauda kaina amma zuciyata nata tsinkewa. Gabana ya karaso yana fuskantata kai tsaye yace ”Wuce gida!”

Cike da mamaki na kalleshi na bude baki zan yi magana Ahmad ya tari numfashina da fadin "No My Queen kije kawai sai na kara zuwa kinji, kuma Please ki kula da kanki bye!”
Yana faÉ—in haka ya shiga motarsa yaja ya tafi, Ahmad yana burgeni saboda yadda yake rayuwarsa ba girman kai kamar ba É—an Governor ba, haka yake shiga ko'ina ba ruwansa da security.

Wani mugun kallo Yaya Salman ya bishi dashi....

Nikam kallonshi shima bayan ya gama raka Ahmad da ido ya juyo nima ya tsare ni da manyan idanunsa masu kwarjini.

Baxan juri kallonsa ba don haka na juya na tafi gida abuna, kuma abun mamaki sai ya bini a baya har ɓangaren din Mama, nace to ko nima belt zai ciro ya dokeni?......…..



*RUMAISA SALMAN BY MAMAN KAUTHAR*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol