Free chapter · Read without an account
LOKACI CHAPTER 37
***
⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION
Under Team Yota's Amazing Pen's.
FULANI ❣️
***
PAGE 3️⃣ 7️⃣
Tana zaune a falo cikin nutsuwa, dilka ce a jikinta, wayarta a hannunta tana duba saƙonni, duk yawanci na fatan alkhairi ne da ake mata, ana gama bikin Zahra ita ma aka shiga cikin hidimar bikinta, duk wanda ya ganta a yanzu ya san tana cikin farin da kwanciyar hankali, wanda ba kowa bane sila face mijinta da zata aura.
Tun bayan abincin taron da ta yi masa ya mayar da kiranta kamar me, kusan babu ranar da ba zai kira ta ba, wani lokacin haka kawai zaice ya kirata ya gaisheta ne, a hankali sabo ya shiga tsakininsu ba tare da ta sani ba, ba za ta manta ranar ba tana zaune a ɗaki wayarsa ta shigo wayarta.
"Assalamu alaikum"
Ta yi masa sallama.
"Wa'alaikumus salam Khairi ya kike?"
"Lafiya lau, Alhamdullah kai fa?"
"Lafiya ƙalau"
Daga nan suka yi shiru na ɗan lokaci, ita a nata ɓangaren tana mamakin dalilin shirunsa dan ta san ba haka yake mata ba, shine ya katse shirun nasu.
"Ummul khairi"
Ya kira cikakken sunanta.
Da ɗan mamaki ta amsa masa.
"Yanzu dai gashi kina ta murna, Za'ayi bikin Bestyn Best friend ɗinki, ke yaushe ne za'a yi naki auren?"
Tambayar da ta sakata yin shiru, farin cikin da ke kan fuskarta a take ya gushe, ta sauke idanunta ƙasa kamar yana gabanta, tambayar tasa ta dawo mata da wani tsohon rauni da ta daɗe da binne sa, ta jima shiru kafin ta daure ta ce masa.
"Faisal ni babu lissafin aure a yanzu a tare dani, dan na haƙura da shi gaba ɗaya a rayuwata"
Shiru ne ya ratsa wayar, yana zaune a office ɗinsa, bai san sanda ya gyara zamansa ba, idanunsa suna kan wayar dan a handsfree ya saka ta, bai san komai a kanta ba, kamar dai yanzu bai san dalilin da ya sa ta yanke wannan hukuncin ba, amman yanda ta yi maganar, ya isa ya fahimtar da shi cewa akwai wani abu mai nauyi a bayan furuncin nata, yasan haka kawai mutum ba zai taɓa yin wannan furucin ba, yaji wani irin rauni a cikin muryarta, wanda shine dalilin da ya sa ya ji bai kamata ya ƙara mata wata tambayar akan wadda ya yi mata ba.
"Khairi"
Ya kira sunanta a hankali.
"Naa...am"
Ta amsa masa muryarta na rawa.
"Kin san wani abu?"
Ba ta iya amsa masa ba, sai numfashin da take saukewa, shima bai jira cewarta ba ya ɗora da bayaninsa.
"Bansan me ya faru da ke a baya ba, ban kuma san dalilin da ya sa kika yanke shawarar cewa ba za ki sake yin aure ba. Ina son ki saurare ni, Khairiyya ina sonki, ina son ki zama matata Khairiyya, ba wasa nake miki dagaske ina sonki, ba wai har kar bussiness ce ta kawo ni wajenki ba, a'a soyayyarki ce Khairi"
Kamar anyi ruwa an ɗauke hawayen idonta ya tsaya, tayi ƙoƙarin magana amman ta kasa ce masa komai.
"Ban taɓa yin aure ba Khairiyya, ina fatan ki kasance matar da zan fara sabuwar rayuwa a tare da ita, ba ke ba alƙawari na yi wa kaina, duk macen da zan aura zan yi iya ƙoƙarin wajen ganin na sakata farin ciki, ba za ki taɓa danasanin aurena ba Khairiyya!"
Wani ɗan murmushi ya yi kafin ya ƙara da cewa.
"Mommyna za ta yi farin ciki sosai, ina fatan zaki bani dama Khairiyya"
A hankali ta sauke numfashi, dan mamaki ne ya hanata ce masa komai, ba ta yi tsammanin Faisal zai fito da irin wannan maganar a tsakaninsu ba, shiyasa duk ta daburce ta rasa abin da za ta ce masa.
"Faisal!"
"Khair"
"Ka bar wannan wasan aurena uku kai kuma baka taɓa yin aure ba, tayaya kake tunanin hakan zai yuyu abu ne da ba zai yaɓa yuyu ba, dan Allah ka bari"
"Ban damu da ko aure nawa kika yi ba, Khairiyya ke nake so ba auren da kika yi ba. Idan har baki yarda ba zan zo muyi magana, dagaske nake miki aurenki zanyi cikin lokaci ƙalilan Khairiyya"
Rasa abin ce masa ta yi har suka yi sallama. Bayan sunyi sallama akan cinyarta ta ajiye wayar, shiru ta yi maganganun Faisal na ta mamaituwa a cikin kunnenta, kafin ya ajiye wayar.
"*Ina sonki Khairi! Ina son ki zama matata*"
Hannunta ta kai ta shafa goshinta, kafin ta miƙa'e daga inda take zaune, a fili ta furta.
"Ya rabb!"
Tun daga wannan ranar Faisal ya sakota a gaba da naci da magiya, har abokinsa ya turo mata, ƙarshe kuma momynsa ta kirata da kanta, tun daga lokacin ta dage da addu'a da neman zaɓin Allah, a gefe ɗaya kuma suka yi magana da Aunty Maryam, dan haka ta basa dama ya fito, wata ɗaya kacal aka saka bikin nasu, wani irin shirin ake kamar wannan shine aurenta na fari, ba wai na huɗu ba, gashi abun babu wuya har sun shiga cikin satin bikinta...
★★★
*AUWAL*
Tun bayan rabuwarsa da Khairiyya, bai daina shaye-shayensa ba, a maimakon ya gyara rayuwarsa sai ƙara zurfafa da ya yi a cikin halin da ya jima a cikinsa, Umma ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin ya dawo cikin hayyacinsa, amman abun yaci tura, tayi nasihar, ta yi faɗan amman duk abun yaƙi yiyuwa.
Rashin Khairiyya a tare da shi sai ya zama kamar wani zararre, dan tun bayan dawowarsa hayyacinsa da ya tabbatar ya sake ta, shikenan komai nasa ya ƙara taɓarɓarewa, sai da Umma ta yi dagaske yaƙi zuwa gidansu, daga ƙarshe dai ta yanke shawarar yi masa wani auren, da fatan hakan zai sa ya manta da Khairiyya ya fara sabuwar rayuwa.
Sai dai auren bai kai ko wata ɗaya ba ya watse, a cikin sati biyu kawai gidan ya zama kamar filin dambe, ya yi tunanin kowacce mace irin Khairiyya ce ashe ba haka abin yake ba, idan ya faɗa mata magana mara daɗi guda ɗaya, sai ta faɗa masa goma, idan ya zageta sai ta rama zagin fiye da wanda ya yi mata, haka idan ya daketa duk abin da hannunta ya kai kai zata ɗauka ta buga masa, wanda faɗansu na ƙarshe ne ya sa ta tattara kayanta ta koma gidansu, dukanta ya yi ta ɗauki wuƙa ta yanke sa, tsoron halin da ya shiga ne ya sa ta gudu gidansu, daga ƙarshe dai a haka auren ya watse.
A hankali ya koma kamar wani mahaukaci saboda shaye-shaye, ko yaushe cikin maye yake, sai dai duk da halin da yake ciki baya hanasa tunanin Khairiyya, bai san tana da haƙuri ba sai da ya sake aure, a hankali ya tuna yanda take shiru duk zagin da zai mata ba za ta taɓa ramawa ba, haka kuma bata taɓa kai hannunta da sunan ta rama dukan da yake mata ba, ta na iya ƙoƙarinta wajen kaucewa faɗa da shi, haka kuma tana kula da shi duk da irin halin da yake nuna mata.
Yana zaune da wiwi a hannunsa ya buɗe hotonta a wayarsa tana murmushi, ya na kallon hoton yana busa hayaƙi, dogon numfashi ya ja ya kira sunanta kamar zata amsa masa.
"Masoyiya Khairiyya!"
Ya furta sunan nata a hankali kamar yanda ya saba. A karo na farko da ya fara jin girman asarar da ya yi, ba wai kawai ya rasa mata bane, a'a ya rasa macen da ta kasance garkuwa a garesa, a da yana sassauta shaye-shaye saboda ita, amman yanzu yin abunsa yake babu wanda zai ce masa dan me.
Fitowarsa daga gida kenan ya haɗu da wani abokinsa, ƙanwar abokin nasa suna mutunci da Khairiyya, bayan sun gaisa yake tambayarsa.
"Ashe bikin tsohuwar matarka ake?"
Kaman an tsayar da komai a wajen Auwal ya ɗago da sauri yana kallonsa, kamar bai ji daidai ba.
"Me ka ce?"
Abokin nasa ya sake maimaita masa.
"Nace ashe bikin Khairiyya ake, jiya Sadiya taje bikin ai, yau ma ta tafi, gobe ne ɗaurin aure nima za ni in sha Allah"
Da farko kamar ya rasa abin cewa, saboda wani abu da yaji ya mamaye zuciyarsa, sai can kuma ya karkata bakinsa.
"Wanne ne me ƙarar kwanan ne zai auri matata?"
Ya tambayesa idonsa har yayi jajir.
"Ban sani ba, amman dai ance me kuɗine"
Sachet ɗin magani ya zaro a aljihunsa kore ya ɓalli guda huɗu ya saka a bakinsa, wata koriyar ƙwaya ce da suke mata laƙani da Roti.
"Ehh bara naje dan kan uwar*su su bani matata"
Ya yi maganar ya na yin gaba.
Zuwa lokacin da ya ƙarasa gidansu Khairiyya baya wani ganewa sosai duniyar ta fara juya masa, cikin wata iriyar tafarsar zuciya ya ƙarasa gidan, ya kuma ci alwashin dole sai sun dawo masa da matarsa.
★
Gidan cike ana ta hada hadar biki, a lokacin za'a tafi yi mata jere, duk da mijinta ya ce baya buƙatar komai daga garesu, amman haka yayanta suka ce a'a dan auren gata suka shirya mata, suna son wanke mata zuciya, kuma sunyi nasara.
Get gidan a buɗe yake dan haka bai sha wahala ba wajen shiga, dayawa matan da suka gansa, hanya suke bashi dan ya na tafiya yana haɗa hanya, duk da ƙwayar ta fara aiki a kansa yasan part ɗin Ummu dan haka can ya nufa kai tsaye, mutanen da ya gani a tsaye ya sha gaban su.
"Ya ne ina Khairiyya"
Ya yi tambayar cikin kaushin murya, ya na kallonsu, juyawa suka yi suna kallonsu, ɗaya daga cikinsu ta ce.
"Wanene kai bawan Allah?"
Ta yi tambayar a ɗan tsorace ta na ja da baya, saboda yanda ta ga yanayinsa.
"Ni mijinta ne kuje ku fito min da matata, mu tafi gida"
Ganin duk sunyi shiru ne ya sa a fusace ya ce.
"Ku je ku faɗa mata na zo, Auwal ne ta zo mu tafi, zan ga ɗan iskan da zai ɗaura wa matata aure"
Kafin kace me labarin har yaje kunnen Ummu, saboda yanda ya fara tara jama'a ana kallonsa, duk wanda ya gansa yasan baya cikin hayyacinsa.
Khairiyya tana zaune a falon Ummu tare da Aunty Maryam, suna duba abu a wayarta, kamar daga sama suka ji hayaniya a ƙofar part ɗin Ummu.
"Khairiyya, kina ina ki fito mu tafi, wai ya ne me yasa ba zaki fito ba"
Muryar Auwal ta ratsa parlown kamar yana ciki.
Da wani irin sauri ta ɗago kanta, dan murya ce da ba za ta taɓa mantawa da ita ba, duk tsayin shekarun kuwa da zata ɗauka ba ta ji ba.
"Auwal?"
Aunty Maryam ce ta kalleta cikin son kwantar mata da hankali ta ce.
"Ki kwantar da hankalinki kar ki tsorata babu abin da ya isa ya yi miki"
Amman ina tuni hankalinta ya tashi, jikinta babu inda baya rawa, kakkarwar da hannunta ya ke ne yasa wayarta suɓucewa a ƙasa.
"Me ya kawo sa Aunty"
Ta yi maganar cikin tashin hankali.
"Ki zauna anan kar ki fito bara naje"
Ta faɗa ta na nufar hanyar barin wajen.
Yana tsaye a ƙofar part ɗin Aunty Maryam ta buɗe ƙofar, yana tsaye ya nata tangaɗi, yana kallon mutanen da suka taru suna kallonsa. Ita dai Aunty Maryam gani ta yi ma kamar ya haukace, dan haka ta kame fuskarta sosai, ba tare da tsoro ko shakka ba ta tsaya a gabansa.
"Malam lafiya"
Ta tambayesa tana tsare sa da idanunta.
"Matata nazo ku bani mu tafi"
Kallon baka da hankali ta yi masa.
"Kai a wa kenan, ko bayan shaye_shayen ka haukace? Yaushe ta zama matarka ko bayan ka saketa ta gama idda aka ɗaura muku aure bamu sani ba?"
"Ban sake ta ba, dan haka dole a bani matata mu tafi"
"Ku tafi ina?"
Ummu ta katsesa a hasale.
"Gidanmu"
Ya bata amsa kai tsaye yana kallon cikin idonta, da na sa idon da ya jirkice.
"Saboda baka da kunya ko kuma dan kaga bamu ɗauki mataki akan ka ba, shine za ka zo kayi mana hauka a gida?"
Cikin ɗaga murya ya maida kallonsa kan Aunty Maryam da ta yi maganar.
"Ba ruwanki da abin da ya faru tsakanina da ita, ku kira min matata mu tafi"
A lokacin ne ta fito da baby hijab, akan doguwar rigar jikinta, ta na ganinsa ta tsaya cak, ba tare da ta ƙarasa inda yake ba, shima ido ya zuba mata ya na kallonta.
"Masoyiya Khairiyya!"
Kasa amsawa ta yi, saboda yanda gabanta yake faɗuwa.
Taku biyu ya yi zuwa gare ta, ta koma bayan Aunty Maryam ta tsaya.
"Ki shirya mu tafi, na zo ɗaukar ki ne"
Cike da takaici ta fito daga bayan Aunty Maryam, tana girgiza kanta, idanunta har sun cika da hawaye.
"Me ya kawo gidanmu? Me kuma kake nema a wajena?"
"Ke"
Ya bata amsa yana ƙara matsota, Aunty Maryam da ta fara fusata da abin da yake, ba ta san sanda ta saka hannunta ta hankaɗasa baya ba.
"Ko a mafarki ba na fatan sake ganinka, bare kasancewa a tare da kai Auwal"
Ta faɗa cikin rawar murya.
"Saboda wani ɗan iska da za ki aura?"
"Koma dai menene ka tafi kabar nan"
Kusan haukace musu ya yi a gidan, gashi babu namiji duk mazan gidan basa nan.
★
A ɓangaren Faisal ya na ta kiran wayarta ba'a ɗaga ba, sai can aka ɗaga, Autarsu ce ta ɗaga ko gaisawa basuyi ba, ta yi masa bayanin abin da yake faruwa, bai san sanda ya miƙe tsaye ba, dan ya san labarinsa a bakin Khairiyya, kamar ma ta fi jin tsoronsa akan duk mazan da ta aura, da sauri ya ɗauki mukullin motarsa, cikin gaggawa ya fice da ga office ɗin.
Zuwa lokacin rikicin ya yi ƙamari, dan har ta kai ga Aunty Maryam ta ɗaga hannu ta maresa a karo na biyu.
Lokacin da ya zo ganin get ɗin gidan a buɗe sai ya shigo ciki bayan ya fito daga motar, wayar Auta ya kira ta zo ta shigar da shi har parlown gidan da ake rikicin, kallo ɗaya ya masa ya ƙarasa gaban Khairiyya.
"Faisal"
Ta kira sunansa hawaye na zubo mata.
"Is okay Khairiyya i'm here"
Kallo ɗaya yawa Auwal ya ciro wayarsa ya yi, waya dan bai ga amfanin yin magana da shi ba. Dan tabbas idan ya ce zai yi magana za'ayi ɓatacciya da shi, babu jimawa ya ajiye wayar.
Sai a lokacin ya tsugunna ya gaida Ummu da Aunty Maryam.
Magana ya yi da Aunty Maryam, ita kuma duk ta sallami mutanen parlown, ban da Auwal da ke zaune a ƙasa. Kujera ya samu ya zauna, yana kaɗa ƙafarsa, Khairiyya ya ke ta faman rarrashi cikin kwantar da murya ganin duk yanda ta yi wani iri.
Ko 1 hour ba'a yi jiniyar ƴan sanda ta cika unguwar, wayar Faisal ce ta fara ƙara ta shi ya yi ya fita babu jimawa suka dawo da police guda uku cikin parlown, kallo ɗaya sukawa Auwal, da ya nuna musu a kwance, ya ɓingire kamar mai bacci sai sumbatu yake.
"Me ya faru haka abokina"
Ɗaya daga cikinsu ya tambayi Faisal, da alamun sanayya.
"Wallahi tsohon mijin matata ne, ya riga ya sake ta, kasan kuma gobe ne ɗaurin aurenmu, ya dawo kuma yana wata magana wai bai saketa ba, duk ya tsorata ta"
Yayi maganar cike da damuwa yana miƙa masa wayar Aunty Maryam, inda gashinan inda yake sakinta a gidansu da bakinsa, ba su jima suna tattaunawa da su ba akan case ɗin, suka tafi da shi office ɗin su.
Hannunta yana cikin na Aunty Maryam kanta a kafaɗarta, tana ta sauke numfashi saboda kukan da ta ci ta ƙoshi.
A gabanta ya tsugunna.
"Ki kwantar da hankalinki, na yi miki alƙawarin hanyar da kika bi, ba zai ƙara bin ta ba, daga yau ko da tsautsayi ba za ki ƙara saka shi a idonki ba, zan wakilce ki har a gama case ɗin, ya na dawowa hayyacinsa za'a muku tsakani, Please ki cire damuwa a ranki kinje Khairi"
Kallonsa take hawaye na zubo mata, haka Aunty Maryam cike da jin daɗi take kallon Faisal ɗin, ganin babu ruwansa da wanzuwar ta a wajen rarrashin matarsa kawai yake.
"Nagode sosai Faisal"
Murmushi ya yi mata, sannan yayi wa Aunty Maryam sallama, ita kuma ya yi mata alamar zai kirata.
Rarrashinta Ummu da Aunty Maryam suka yi tayi, a lokacin Alhajinsu ya shigo shima, ƙara masa bayani abin da ya faru a kayi, amman jin cewa case ɗin na hannun Faisal sai ya barsa, dan yasan zai yi abin da ya dace.
Washe gari ƙarfe sha ɗaya aka ɗaura auren Khairiyya da mijinta Faisal.
Sosai zuciyar Ummu ta cika da farin cikin sake ganin auren ƴar tata, inda ita kuma tun da a ka ɗaura take kuka, bata kuma bar bakinta ya huta da addu'a da fatan Allah ya sa gidanta kenan ba, Allah kuma ya sa daga wannan auren shikenan ƙadaddararta ta ƙare.
A daren a ka kaita gidan mijinta, sai muce Khairiyya Allah ya baki zaman lafiya a gidan aurenki....
FULANI
***