Free chapter · Read without an account

14. The Wedding

by Zainab · TSAƘANINMU

TSAKANINMU

Bayan Sallah da kwana huɗu aka kai lefen Ahmad, set uku. Dama already tun lokacin da aka kai kuɗin auren aka sa bayan Sallah da sati ɗaya za'a fara biki. 

A chan ɓangaren gidansu matar da ze aura, Maryam, Henna party za'a fara yi as one of the wedding events. 

A gidansu Maryam aka yi Henna party, harda su Madina da Hafsa, Jawahir da Gumsu duk sun tafi da wasu ƴan uwansu dake nan Abuja. 

Tun last zuwan su shekara shida da suka wuce ba'a ƙara yiwa Gumsu lalle ba se a Henna party na Ahmad da Maryam. 

An yi mata lalle a hannu ba me yawa ba, yayi mata kyau a hannu se kallo take. 

Bayan an gama biki gabadayan su suka wuce gidan Abba. Gumsu taje ta nunawa Abba lallen ta ga hasken nan da gare ta saboda weather na USA. 

Kuma ta nunawa duka uncles nata, da suka koma gida haka tayi ta nuna wa mahaifin ta tana tambayar shi ko yayi kyau. 

"It looks beautiful, Dad?"

Kallon hannuwan ta Hamdan yayi ya riƙe yace "Yes, Gumsu"

"You then have to get me a henna artist back home in the States"

Dariya Madina tayi "You this girl!"

"I'm really serious"

"I'll get a henna artist for you in the States. Don't mind your Maama"

"Yeah, I know you'll definitely"

"Yes, definitely" tace ta bashi knuckles nata suka haɗe tukuna ta wuce ɗakin ta. 


A ranar da za'a yi dinner, a Transcorp Hilton za'a yi. An yi decoration me kyau kowane table da nashi flower. Kiɗa yana tashi ahankali se vibe na biki kake ji a cikin hall. 

There was different kind of food, drinks and desserts. Everything was so high end and luxurious. 

The groom, Ahmad, was dressed in a white shadda in babbar riga that tailor did his best on and a zanna bukar traditional cap that fit his head perfectly. The bride, Maryam, was dressed in a white flowy gown with embroidery and they look absolutely perfect together.

The groomsmen were dressed in a blue sky shadda with babbar riga and the bridesmaids were dressed in a fitted sky blue gown with their pink gogoro on.

Sauran mutane kuma se suka sa duk kayan da suke so. 

Madina, Hafsah, Jawahir da Gumsu kayan su iri ɗaya maroon lace da gogoro, harda Gumsu an yiwa gogoro tace hoton da aka mata ma cikin kayan, zata sa Dad nata yayi mata babban hoto dashi a ajiye a living room nasu. 

It was a very beautiful event , everything looks perfect, modern and beautiful. 

Ranar Assabar ma haka gidansu Jawahir ya cika sosai da mutane na yinin biki. Mutane ne kala-kala kowa da irin nashi gayu me kyau. 

Abinci daban daban kama daga na gargajiya da na zamani da drinks su ma haka, kunun zaƙi ne da kunun aya da zobo duka anyi.

Ƙarfe biyu na rana aka sa za'a ɗaura aure.

Jawahir ta gayyaci Ashraf zuwa ɗaurin auren amma ba tace ya taho dinner ba.

Kiran wayar ta yayi, wayar na hannun Gumsu tayi sauri taje kai mata. 

"Someone's calling you" Gumsu ta faɗa tana stressing idanun ta wurin karanta sunan da yayi appearing kan screen wayar Jawahir. 

"Ashraf? Yes, Ashraf is calling you" ta faɗa ta miƙa wa Jawahir wayar. 

Jawahir tace "Baki gani ne?"

"What?" Gumsu says

"Aren't you seeing?" Jawahir ta ƙara cewa da turanci ta amsa kiran Ashraf ta ɗaura a kunnen ta

"Nope. I just ....I couldn't see the name clearly" 

Nodding kai Jawahir tayi tana kallon ta tace "Yes, Ashraf?"

"Na manta inda na ajiye invitation card da kika bani. Ina ma ne ake ɗaura auren?"

"A National Mosque ne"

"Okay, I'll surely attend"

"Thank you, Ashraf. Bye"

Cire wayar tayi a kunnen ta se Gumsu tace "Who's Ashraf? Your boyfriend?" 

"Boyfriend? No. He's my friend" Jawahir tayi saurin faɗa bata son Gumsu ta ƙara mata wata tambayar indai akan sunan Ashraf ne.

"Ohh!" Gumsu tayi se kuma bata ƙara cewa komai ba ta wuce daga wurin Jawahir.



Duk hidimar bikin nan da ake, Aunty A'isha na tare dasu kuma ba zasu taɓa mance alhairan ta ba da kuma yanda take loyal to her dead friend ba. 

Ƙarfe biyu aka ɗaura auren Ahmad Tahir Musawa da Maryam Khalid akan sadaki Naira dubu hamsin. Mutane manya masu muƙami na Nigeria ne suka halarci bikin saboda Abba shima babban mutum ne a gari.

Ƙarfe biyar na yamma akayi wankin ango a nan gidan Abba. 

Ahmad harda kukan shi saboda mahaifiyyar su da yake ta tunawa. 

An mishi watsin kuɗi da kayayyaki a wurin daga ƴan uwa da abokan arzikin su. 

Ƙarfe tara kuma ya ƙara shiri na zuwa sabon gidanshi. Maryam aka kawo ta nan gidansu Abba ya haɗe su su biyu yana musu nasiha da tunatarwa akan haƙurin dake cikin zamantakewar aure. 

Bayan haka, aka tafi kai amarya ɗakin ta. 

Gidan kuma already an watse sosai se wanda ba garin suke ba gobe zasu tafi.



              ***


 
Bayan bikin Ahmad da sati ɗaya, Hamdan ya tambaye Abba ko Jawahir zata iya zuwa inda suke a Jabi tayi koda kwana biyu ne ganin sun kusa komawa States. 

Abba be hana ba, shi kuma abinda yasa Hamdan ya tambaya saboda yaga Abba baya so Jawahir tayi nesa dashi ko kaɗan, abinda ma ya hana mata zama gabaɗaya tare dasu a States. And he respected that saboda yasan itace ke kama da mahaifiyyar su sosai yafi so ya ganta a kusa dashi ko yana samun solace ga irin rashin da yayi. 

A ranar, tare dashi suka wuce gidan shi dake Jabi. 

Dama Hamdan ya faɗa musu da Jawahir ze taho tayi kwana biyu idan Abba ya yarda, so Gumsu na ganin ta tayi sauri ta fito daga ciki tayi hugging nata suka shiga cikin gida tare.

Da dare ma dukan su suka fito a compound suna yin hirar su. Iskan green trees na kaɗawa ana jin sanyi sanyi. Haske a ko ina kaman ba dare ba. 

"When are you coming to visit us in the States?" 

Gumsu tayi tambayar wa Jawahir.

Kallon Hamdan Jawahir tayi tace "Yaya bata jin Hausa har yanzu?"

Kallon Jawahir Gumsu ke yi , a confused look. 

Madina tace "Gata fa kina gani kina jin ta. Se kamar zata ji amma haka nan bata ganewa"

"Ki koya mata kafin mu wuce" inji Hamdan 

Murmushi Jawahir tayi tace "Amma kuna yin Hausa a gida ina mamaki har yanzu bata jin Hausa"

"Tana jin wasu kalmomi kuma tana ganewa amma fa kaɗan kuma kaɗan sosai, ta maida ne shine babbar matsala. Wasu kuma ko ganewa bata yi bale ayi maganar maida maganar" Madina tayi wa Jawahir bayani ta kuma ƙara cewa “Ba abinda ma take ganewa wannan yarinyar”

"Aunty ki zo mu koya mata to"

"Se kace kema wata Hausa kika iya" Hamdan ya faɗa 

"Ni ce ban iya Hausa ba, Yaya?"

"Exactly, baki iya ba. Yaran garin nan mafi yawan su basu iya Hausa ba , ba ke kaɗai ce ba"

"Haka malamin mu fa yace ranar"

"Eh, haka ne"

"What're you talking about?" Gumsu tace taji an bar ta ita kaɗai 

"You didn't pick anything from what we said?"

"Of course, I know you guys are talking about me. And about Hausa"

Jawahir tace "We want to teach you how to speak our language"

"I'd love that. I like this amazing language and always stunned when Dad or mom speaks it, so I'd love that"

"Da kina so da kin maida hankali" Madina ta amsa 

"I actually said Barka da sallah to Jawahir's father on Eid. You can ask him"

Madina ta sake ce "Anyone can say Barka da sallah, my baby. Even the one who has never been to Hausa land"

"Okay you don't want to commend me? I understand" Gumsu tace da fushi 

"I'll teach you Hausa in the most simplest form I know"

High five tayi wa mahaifin ta tana murmushi.

"I'll compete with Mom on this very Hausa issue. Will be ahead of her when it comes to speaking it"

"You must be kidding, Gumsu" 

"Trust me, aunt. In a few years, I'll be the one to teach her"

Madina murmushi take tana kallon Hamdan irin kallon nan na "ji abinda ƴar ka ke faɗa"

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol