Free chapter · Read without an account

Chapter 40

by Umma mustapha · WA ZAI FUSKANCE NI??

WA ZAI FUSKANCE NI?
BOOK 1
Umma Mustapha

YOTA

PAGE 40

Irfan da ya fita daga gidan. Wani garden me kyau ya shiga, a tsaye yake ya juya bayansa, hannayensa suna cikin aljihu. Har yanzu yana fama da bacin rai. Maganganun Jabir suna ta yawo a cikin zuciyarsa.
Idan har Jabir gaskiya ya faɗa, Nihla ba ta sonsa, to ya zai yi? Duk wahalar da gwagwarmayar da ya sha a baya sun tashi a banza kenan.
Ya ture tunanin daga zuciyarsa. Dole ya nemi ganin Nihla, domin akwai abubuwan da yake so su tattauna. Yana son sanin dalilin da ya sa take masa haka.
Wajen motarsa ya koma ya buɗe, ya ɗauko kwalin sigari. Ya daɗe yana kallon sigarin, tsaki ya ja, sannan ya yi jifa da kwalin, har yana kai wa tayar motar duka.
Ya rasa yadda zai yi. A ƙarshe, cikin motar ya koma, ya ja ta, ya tafi gida.

Nihla tana zaune a gaban wani ƙaramin akwati, tana shirya kayanta a ciki.
Bikin gidan su Fatima za ta tafi. Ta gama shirya komai. Turarukan da ke kan mudubi ta ɗauko, ta zuba su a jaka. Duk wani abu da za ta buƙata ta gama saka shi a cikin akwati.
Saboda Fatima ta ce mata gobe da safe za ta zo ta ɗauke ta su tafi gidan ƙunshi. Daga Gidan ƙunshi, za ta wuce gidan su Fatima, ba za ta dawo ba har sai an kammala bikin. Shi ya sa ta shirya komai tun daren yau.
Da ta gama shirya kayan, ta mike ta gabatar da sallar Isha'i. Ba ta samu yin ta a kan lokaci ba. Tana idarwa ta fita falo.
Dukkansu kowa yana zaune.
Kusa da Jafar Nihla ta zauna. 
"Daddawar ɗaka an fito! Naga kin koyo sabon salo yanzu, ɗan zaman da kike yi a falon ma kin daina."
Nihla ta ɗan kalle shi, sannan ta ce, "Kai, Yaya Aminu! Jiya ne fa kawai ban zauna ba."
Aminu ya ɗaga gira.
"ah Karya kike yarinya."
kafin ta furta komai,i Yaya Babba ya shigo falon.
Nan take kowa ya gyara zamansa. Wasu suka risina suna gaishe shi, wasu kuma suka koma cikin nutsuwa.
Nihla kuwa ta sauke idonta, kamar wadda ta yiwa sarki karya. Wayar Aminu ce a hannunta, tana buga game, gaba ɗaya hankalinta yana kan game din da take Yi.
Aliyu ne ya fito daga ɗaki. Hannunsa riƙe da wata kwalbar turare, yana kallonta cikin mamaki kamar wanda ya samu abin da bai yi tsammani ba.
"Wannan turaren waye?" ya tambaya, yana kallon sauran ƙannensa.
Cikin gaggawa Hafiz ya ce,
"Nawa ne."
Aliyu ya tsaya cak. Ya gyara tsayuwarsa, sannan ya ɗago kwalbar yana kallon Hafiz da wani irin kallo.
"A gidan uban wa ka samu wannan turaren?" ya tambaya. "Waye ya ba ka shi? Kasan kuɗin turaren nan kuwa?"
Hafiz ya yi shiru.
Aliyu ya ci gaba da cewa, "Akalla zai kai 280k. Ka min bayanin inda ka samu."
Da jin haka, Nihla ta ji wani abu ya tsirga mata a zuciya.
Tun da Aliyu ya fara tambaya, wani irin tashin hankali da fargaba ya dirar mata. Ta yi saurin kallon Hafiz, sannan ta mayar da idanunta ƙasa, tana ƙoƙarin kada a gane irin yanayin da ta shiga.
Hafiz, ganin lamarin zai kwabe da shi, ya yi saurin cewa,
"Auta ce ta ba ni kyauta fa."
Nan take shiru ya mamaye falon.
Gaba ɗaya kowa ya mayar da idonsa kan Nihla, alamar amsarta ake jira. Har Yaya Babba ya tattara hankalinsa, ya mayar da kallonsa kanta.
Nihla ta ji zuciyarta tana bugawa da ƙarfi. Sai da ta haɗiye wani yawu sosai, sannan ta ɗaga kai cikin sanyin murya ta ce,
"Fatima ce ta ba ni. Saurayinta ya kai mata kyautar guda uku lokacin muna makaranta. Shi kuma ya dawo daga Dubai, ya kai mata ziyara, ya ba ta tsaraba. Shi ne ta ba ni guda ɗaya a ciki."
Ta ɗan dakata, sannan ta ƙara da cewa,
"Ni kuma na ba Hafiz. Wallahi ban san yana da tsada haka ba."
Kowa ya sauke ajiyar zuciya.
Har Yaya Babba, wanda tun farko fuskarsa ta nuna shakku, sai ya sassauta ya koma cikin nutsuwa.
Hajiya Mama kuwa ta kalli Aliyu da mamaki.
"Yanzu Aliyu, turare za a ce dubu ɗari biyu da tamanin? Kuɗin wata saniya ne fa!"
Da jin haka, dariya ta ɓarke a falon.
Dukkansu suka yi dariya, banda Nihla. Dan har yanzu zuciyarta tana bugawa da sauri, domin ta san irin tambayoyin da zasu iya tasowa idan wani ya ƙara bincika maganar.
Aliyu ya girgiza kai, sannan ya ce,
"Wallahi Hajiya, na san wannan turaren. Lokacin da Abbie yana da rai, an taɓa kawo masa kyautar irinsa. Kuma har da kuɗin turaren a jiki."
Ya ɗan kalli kwalbar, sannan ya ƙara da cewa,
"Manyan masu kuɗi ne da gwamnoni suke amfani da shi."
Hafiz ya zaro ido.
"Da na san yana da tsada haka, ai kasuwa za mu kai shi! Ko dubu ɗari biyu ma aka ba mu, karba zamu yi."
Sai ya kalli Nihla, yana murmushi.
"Ko ba haka ba, Nihla?"
Nihla ta kalle shi. Duk da har yanzu akwai fargaba a zuciyarta, sai ta tilastawa kanta yin murmushi, sannan ta gyada kai.
Jafar, wanda yake zaune kusa da Nihla, bai ce komai ba. Kawai kallonta yake yi cikin nutsuwa, amma a cikin zuciyarsa ya san cewa akwai wani abu da ba ta faɗa musu ba.
Ya san Nihla ƙarya take yi.
Domin akwai ranar da ya taɓa shiga ɗakinta Zai tari ruwan zafi a toilet dinta, kawai ya ga wasu kwalaben turare a kan mudubi. Ba kwalabe ne na yau da kullum ba; dukkansu turare ne masu tsada.
Yanzu kuma Nihla ta ce wannan ɗaya Fatima ce ta ba ta.
Jafar ya ɗan ƙara kallonta.
"Idan wannan Fatima ce ta ba ta, sauran ragowar turaren fa?" ya tambayi kansa a zuciyarsa.
A hankali ya runtse idanunsa, sannan ya mayar da kallonsa gefe, kamar bai lura da komai ba.
Amma a zuciyarsa wata tambaya ta fara tasowa.
Me Nihla take ɓoyewa?
Akwai wani abu da ba ta son kowa ya sani.
Kuma Jafar ya fara jin cewa wannan turaren wanine ya Bata Amma ba Fatima ba...
Umsar ✍️ 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol