Free chapter · Read without an account
Chapter 43
WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
YOTA
@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha
PAGE 43
Gidan su Fatima a cike yake da yan biki. Wasu daga cikin mutanen baƙi ne da suka zo daga wasu garuruwa domin halartar bikin.
Hayaniya da dariya sun cika gidan, yayin da mata ke ta gaisawa da juna, wasu kuma suna ta shirye-shiryen abin da za a yi na bikin.
Da suka shiga, Fatima ta fara gaisawa da mutanen da suka tarar a harabar gidan, Nihla ma tana binta a hankali tana gaidasu,
Cikin fara'a da dariya suke amsawa, wasu daga ciki suna zolayar Fatima.
Haka dai suka samu suka isa part din maman Fatima.
Fatima ta tura ƙofar falon, suka shiga.
Maman Fatima tana zaune a kan kujera tare da wasu mata biyu. Tana ganin Nihla fuskarta ta cika da fara'a, rungume Nihla tayi tana dariya, Nihla Kuma tana ƙoƙarin zamewa ta gaida ita.
Maman fatima tana da wayewa Sosai Bata da duhun kai, macece me faran faran da mutane.
Juyawa sukayi suka fara gaida sauran matan Dake ɗakin.
Fatima ta nunawa Nihla wata mata tace:
"Ga mama Dr.Nasir fa"
Murmushi Nihla tayi ta sake rissinawa tana gaida matar.
Amsawa tayi tana murmushi.
Daga ɗakin mama, dakin Fatima suka shiga, Fatima ta rufe ƙofar.
"Wallahi na gaji," ta faɗa tana cire mayafinta.
"Nihla tace bacci nake ji wallahi"
Ba tare da ɓata lokaci ba, suka shiga bandaki suka yi wanka, Nihla ce ta fara shiga bayan ta fito Fatima ta shiga. Suna fitowa, kowacce ta saka riga mai sauƙi, ganin lokacin la'asar yayi sai suka gabatar da sallar, suna idarwa kwanciya suka Yi akan gado, baccin da sukayi bashi da yawa, karfe biyar da Rabi na yamma suka Farka,cikin hanzari wanka kowacce ta sake yi.
Nan take suka fara shirya kayansu cikin wata Yar madaidaiciyar jaka
Ba su ɗauki manyan kaya ba. Kowacce ta zaɓi abubuwan da za ta buƙata kawai, cikin gaggawa suka gama shiryawa.
A falon Gidan suka samu ya Adam Fatima ta rokeshi akan ya taimaka ya Kaisu gurin makeup. Ba tare da ya mata maganar ya dauki key ɗin mota ya fita, su Kuma suka bi bayansa
A yau ne za a fara gudanar da Ladies Party, ɗaya daga cikin abubuwan da aka shirya kafin babba.
Allah ya taimakesu Basu samu mutane da yawa a wajen Mai makeup din ba Dan haka da wuri suka kammala komai
kamanninsu ya sauya sosai. Makeup ɗin ya fito da kyawun fuskokinsu cikin salo mai sauƙi da kyau, ba tare da an wuce gona da iriba.
Nihla ta saka baƙar riga mai kyau wadda aka yi mata ado da ɗan silver, sannan ta saka takalmin silver. A wuyanta akwai sarka silver, yayin da ta ɗauki ƙaramar silver clutch.
Fatima ma ta yi irin wannan salon tayi, amma da ɗan bambanci wajen ƙirar rigarta.
Lokacin da Fatima ta Kalli Nihla sai da furta Kalmar:
"Wow! Kinga irin kyan da kikayi kuwa" ai dole na ɗauki wannan kwalliyar na turawa irfan
Nihla dai sai aikin murmushi take, ita kanta tasan tayi kyau domin Bata taba yin makeup a rayuwarta ba. Wannan karo na Farko.
Me kwalliya ta musu hotunan da video domin ita kanta ta yaba da irin kyan da sukayi.
Ya Adam ya shukasu, yaƙi zuwa ya ɗaukesu, Dan haka Nihla ta Kira yaya Jafar tace masa yazo ya ɗaukesu. Ya Kaisu wajen event din, address din inda suke ta tura masa, be dauki lokaci ba sai gashi ya karaso. Fatima ta shiga gaba Nihla tana baya,
"Kunga fuskarku kuwa"
Jafar ya faɗa Yana dariya
"Yanda kuka San aljanu, wannan ko hanya na haɗu daku ai bazan ganeku ba"
Harara Nihla ta jefa masa gami da tura Baki gaba.
Fatima tayi dariya "wlh Yaya Jafar baka ga yadda mutane suke yabon irin kyan da mukayi ba."
Nihla tace "rabu dashi, nasan dai munfi wannan budurwar tasa kyau"
Haka Jafar yay ta tsokanarsu har suka je wajen event din.
Da suka isa wajen taron, wurin ya riga ya cika da Yan mata ƙawayen amarya da cousins ɗinta.
Fitilu masu haske sun ƙawata wurin, mata suna ta shiga suna fita, wasu suna ɗaukar hotuna, wasu kuma suna gaisawa da abokai da ƴan uwa.
Wasu daga cikin cousins din Fatima sun San Nihla, dan haka tana shiga wurin suka fara janta, domin ɗaukan hotuna, Nihla ta sake a cikinsu sosai.
Kiɗa ya fara tashi M/C ya fara Kiran kawaye amarya su fito su taka, Yan mata aka shiga filin rawa, Nihla tana gefe tana kallonsu tana dariya tana musu video da wayarta.
Wata cousin din Fatima Mai suna Laila CE, tazo ta ja hannun NIHLA suka shiga cikin rawar tare, tun tana Jin kunya da ɗari dari, har ta saki jiki ta tiƙi rawa son ranta.
Ba'a tashi daga partyn ba sai wajen karfe 11 na dare. Anty Laure ce ta ɗauko su Nihla a motarta, yayar Fatimace tana da Yara biyu mace da namiji, gidanta Dake Jan bulo suka nufa domin a chan zasu kwana.
A gajiye suka shiga Gidan, makeup din fuskarsu suka goge Sannan suka nemi wajen kwanciya, suna kwanciya bacci ya ɗaukesu saboda gajiya da zirga zirga.
Umsar ✍️
***