Free chapter · Read without an account

Chapter 44

by Umma mustapha · WA ZAI FUSKANCE NI??

WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha

YOTA 

@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha

PAGE 44
Ba su farka ba sai ƙarfe goma na safe.
Nihla da Fatima sun ji daɗin kwana a gidan Anty Lauren sosai. Gidan ya kasance cikin nutsuwa, babu hayaniya ko cunkoso, sabanin gidan biki da aka sanshi da hayaniya. Hakan ya ba su damar samun isasshen hutu.
Bayan sun tashi, suka yi wanka suka shirya, suka fito suka yi breakfast tare da Anty Lauren.
Bayan sun gama cin abincin, Anty Lauren ta kalle su.
"Ni zan tafi gidan Mama yanzu."
Fatima ta amsa,
"To, Anty. Zan biyo ki, ina so na je na ɗauko kayanmu gaba ɗaya."
Sai ta juya ta kalli Nihla.
"Ki shirya mu tafi?"
Nihla ta girgiza kai.
"A'a, ni ba zan je ba, ki he ki dawo"
Fatima ta ɗan yi dariya.
"shikenan ai"
murmushi tayi
Ba tare da wata magana ba, Anty Lauren da Fatima suka shirya suka fice daga gidan.
Nihla kuwa ta tattara kwanukan da suka yi amfani da su ta kai su kitchen. A can ta tarar da mai aikin Anty Lauren tana wanke-wanke.
Ta gaishe da ita, sannan ta juya ta koma ɗakin da suka kwana.
Gado ta hau ta kwanta, sannan ta ɗauki wayarta.
Ba tare da ta yi dogon tunani ba, ta fara Kiran wayar Irfan.
Kiran yana shiga aka ɗaga, kamar dama yana jiran kiranta.
"Hello, Yan matana."
Jin muryarsa kaɗai ya sa Nihla ta saki Murmushi 
"Hello, Yaya Irfan."
"Wai sai yaushe za a daina kirana da Yaya?"
Dariya ta yi.
"Ba ka son Yaya?"
"Ni bana so."
"To me kake so in riƙa kiranka da shi?"
"Ki samo min suna mai daɗi."
Nihla ta sake yin dariya.
"To, kada ka damu. Zan samo maka sunan da ya dace da kai."
"Ina kika shiga jiya? Kika share ni ko?"
"Wallahi mun shiga busy. Kuma ba mu dawo gidan ba sai bayan ƙarfe goma sha ɗaya."
"Ai Fatima ta bani labarin irin rawar da kika tika," ya faɗa yana tsokanarta.
Nihla ta yi saurin ƙaryatawa.
"Ni fa ban yi rawa ba."
"Kin yi mana. Har video aka turo min fa."
Nan take Nihla ta yi tsit. Ta kasa samun amsar da za ta ba shi.
Irfan ya fashe da dariya.
"Na kama ki ko?"
"Hmm..."
Ya sake dariya kafin ya tambaye ta,
"Amma ina kike haka? Na ji shiru, babu hayaniyar mutane."
"Muna gidan Anty Lauren. Can muka kwana."
"Kuna hutawarku kenan, ƴan mata."
Nihla ta yi murmushi.
"Wane event za ku yi yau?"
"Hennah Party."
"Madalla. Zan zo kafin ku fita, saboda nii ya kamata na fara ganin kwalliyarki."
Nihla ta yi murmushi kawai.
Hirarsu ta ci gaba na ɗan lokaci cikin raha da tsokana, kafin daga bisani suka yi sallama.
Bayan ta ajiye wayar, Nihla ta sake komawa bacci.
Lokacin da Fatima ta dawo, ta tarar da ita tana barci. Ba ta tashe ta ba; sai ta koma falo ta zauna tana hira da mai aikin Anty Lauren.
Da ƙarfe huɗu na yamma, Anty Lauren ta dawo. Tare ta taho da me kwalliya.
Tana shigowa tace kowa ya tashi ya shirya
Nihla da Fatima suka tashi suka yi wanka, NIHLA aka fara yiwa, kafin a gama mata Irfan ya Kira yace gashi a kofar Gidan Anty laure.
Fatima ce ta fita ta tarbe shi, ta shigo da shi falon baƙi, sannan ta kawo masa kayan ciye-ciye, ruwa da lemo.
An gama mata kwalliyar tayi kyau sosai,
Mayafinta ta yafa a jikinta, sannan ta nufi ƙofar da za ta sadata da falon da baƙi.
Da sallama ta shiga, Irfan ya ɗaga kansa.
Idonsa ya sauka kanta.
"Masha Allah..."
Ya furta a hankali.
"Allah ya yi halitta."
Nihla ta karaso ta nemi kujera wadda take facing ɗinsa ta zauna.
Cikin sanyin murya ta gaida shi.
"Yaya Irfan."
Sai dai gaba ɗaya hankalin Irfan ya tafi kanta.
Yau kam Nihla ta yi masa wani irin kyau da ya sa ya kasa ɓoye mamakinsa.
A zuciyarsa ya ce, Duk ranar da Allah ya mallaka min Nihla a matsayin mata, ban san irin godiyar da zan yi masa ba.
Sai ya gyara zamansa ya ce,
"Yan matana, kin yi kyau sosai."
Nihla ta yi murmushi.
"Na gode."
"Amma akwai matsala ɗaya."
Nihla ta kalle shi.
"Matsala?"
"Eh. Rigar ta kama jikinki, sannan ga shi ƙaramin mayafi kika saka. A gaskiya hijabi ya kamata ki saka."
Cikin shagwaɓa har da ɗan buga ƙafa ta ce,
"kai Yaya Irfan Mayafin fa yana da girma."
Irfan ya yi murmushi yana girgiza kai.
"Irin wannan shagwaɓa haka, kar ki sa na kasa gane hanyar gida fa."
Nihla ta yi dariya, sannan ta ɗaga gefen mayafinta ta rufe fuskarta.
Bayan ɗan lokaci ta sauka daga kan kujerar, ta dauki cup, ta zuba masa lemo ta Mika masa.
Irfan ya miƙa hannu ya karɓa.
"Thanks."
Nihla ta koma ta zauna, suka ci gaba da hirarsu.
Hira ce mai sauƙi, cike da dariya da tsokana, har lokaci ya ja.
Cup din dake hannunsa ya ajiye ya kira sunanta.
"Hafsat!"
Amsawa tayi gami da zama serious.
Duk lokacin da Irfan ya kira ainihin sunanta, Hafsat, tasan akwai wata magana mai muhimmanci da yake son yi mata.
Ta gyara zamanta ta ba shi cikakken hankalinta.
"Na'am?"
"Magana za mu yi. Amma ban ce ki yi min kuka ba, please. Ki fahimce ni."
Nihla ta yi shiru tana wasa da adon da ke jikin mayafinta.
Irfan ya ci gaba,
"Tambayar da ba kya so ita ce zan sake maimaita miki. Please, Nihla, ki tausaya min mana."
Ya sauke numfashi.
"Ina son zuwa gidanku in gabatar da kaina. Dan Allah, ki fahimce ni. Ni ba na son a cika tsawaita soyayya ba. Kwata-kwata bana son a daɗe ana soyayya ba tare da an san inda za ta dosa ba."
Nihla ta yi ajiyar zuciya.
Ta ɗan yi shiru kafin ta fara magana.
"Yaya irfan ya kamata Ka fahimceni, Ina da dalilin da yasa bana son kazo gidanmu."
"Dalilin nake son Jin" ya katseta
Yaya babbah yace bazanyi Aure yanzu ba,karatu zanyi, Ina Jin tsoron yazo ya ganmu tare da Kai Zai ga kamar ban girmama maganarsa ba. Kuma bana son ya fada maka maganar da ranka Zai baci ko ya koreka. Dan Allah Ka fahimci dalilina
Irfan ya yi shiru yana kallonta.
Ya fahimci cewa tsoronta na gaske ne. Ba wai tana neman hanyar guje masa ba ce, Sannan tana kokarin bawa kowanne bangare hakkinsa. Tana kokarin ganin ta kiyaye maganar yayanta, a gefe Guda Kuma Bata son abin da Zai Bata ran masoyinta.
"Amma magana ta gaskiya, Irfan ba zai iya jira har sai Nihla ta kammala karatunta ba. Yana matuƙar son ta, kuma burinsa shi ne ya mayar da ita matarsa cikin halastacciyar hanya. Duk da haka, ya san cewa dole ne ya bi komai a hankali."
"Zanje na samu Yaya babba muyi magana dashi"
Dagowa tayi da sauri tana kallonsa.
Wani lokacin lamarin Irfan Yana Bata mamaki, yanzu Nan ta gama bashi bayanin komai, Amma Yana CE mata zaije ya samu Yaya babba, kodai tsokanar ta yake
"Baki CE komai ba"
"Ai na rasa amsar da zan baka ne". "kawai kice min kin Amince"
Murmushi kawai tayi domin Bata dauki maganar tasa serious ba.
"Ai Nasan baza Ka iya tunkararsa ba"
"Saboda me"
"Kowa shakkar yake"
Murmushi yayi ya girgiza, be che komai ba
Amma Zai Bata mamaki kuwa,
Ya fuskanci ƙalubale da dama a rayuwarsa, kuma sau da yawa ya fito da nasara. Don haka, bai ga dalilin da zai sa ya kasa fuskantar Yaya Babba ba.
Be sake mata magana ba, suka ci gaban da wata Hirar ta daban. Suna tare har su Fatima suka kammala shirinsu, shi ya dauke su ya Kaisu wajen da zasuyi hennah party, anty Laure Kuma ta dauki me kwalliya ta mayar da ita...
Umsar ✍️ 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol