Free chapter · Read without an account

Chapter 47

by Umma mustapha · WA ZAI FUSKANCE NI??

WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha

YOTA

@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha

PAGE 47

Yau ya rage saura sati daya su Nihla su koma makaranta, dan haka ta fara shirye-shiryen tafiya.

Bayan sallar Isha, tana kwance akan doguwar kujera, wayarta a hannunta tana dannawa. Hajiya kuwa tana zaune akan carpet, carbi a hannunta.

Sai ga Yaya Babba ya yi sallama ya shigo. Sai da ya rusuna ya gaida Hajiya, sannan ya nemi kujerar da ya saba zama ya zauna. Nihla ta zame daga kan kujerar da sauri tana gaishe shi. Ya amsa kadaran kadaham.

Kallon Hajiya ya yi ya ce mata, "Ina sauran yaran?"

"Na aike su gidan Naja," Hajiya ta amsa.

Be sake magana ba. Naja ta kasance kanwar mahaifiyarsu Yaya Babba, amma sam jininsa be haɗu da ita ba. Tun Nihla tana yarinya ta so a bata ita, amma sam Yaya Babba ya hana. Ya ce wai ta cika buɗewar ido, wayewarta ta yi yawa. Dole ta haƙura ba dan ta so ba.

Hajiya ta kalle shi, "A zubo maka abinci?"

"Na koshi Hajiya."

Sai ya maida kallonsa kan Nihla ya ce,

"Ke zo."

Sai da gabanta ya faɗi. Zuciyarta kamar zata faso saboda tsoro. A hankali ta ƙaraso gabansa ta zauna tana mai sunkuyar da kanta.

Sai da ya gama nazarinta sannan ya bude bakinsa ya jefar mata tambayar da ta sa numfashi ya kusa ɗaukewa.

"Kece kika turo wani yaro wajena?"

Shiru. Babu amsa sai rawar jiki take yi.

"Ba magana nake miki ba?" Ya fada cikin tsawa.

Zabura tayi har tana dan matsawa baya. Da sauri ta ɗaga masa kai alamar eh.

"Hala kin zama kurma da baza ki iya buɗe baki ki min magana ba?"

"Eh... ni... nice," ta fada da karamar rawar baki.

"Aure kike so ko karatu?"

Hajiya wadda ke gefe ta kalle shi cikin mamaki.

"Wai Nihla saurayi take da shi ne? Naji kana maganar aure."

"Gata nan a gabanki, ta ba ki amsa. Wani yaro ta turo min. Jiya ya je gidana ya same ni, yana wasu maganganun da ban gamsu da su ba."

Hajiya ta kama haɓa tana kallon ikon Allah. Ita ma abin mamaki yake bata, yaushe har Nihla tayi saurayi bata saniba.

Yaya Babba ya ci gaba, "Na dai fada masa ba yanzu za a miki aure ba. Idan kuma auren kike so sai ki hakura da karatun a samo miki mijin da ya dace. Dan wannan da kika turo sam be min ba. Ki tabbatar kin rabu da yaron nan na fada miki, domin ba ke kike da alhakin zabarwa kanki miji ba, ko Asiya ma Baba ne ya zabar mata mijin da take aure."

Ganin yadda yake ta zuba ruwan bala'i yasa Hajiya ta janye Nihla daga kusa dashi dan kar yaje ya kai mata duka.

Hajiya ta ce, "Ka bi a hankali mana, kai matsata da kai zuciya kamar kuturu. Idan auren ma take so za a iya yi mata shi, ta karasa karatun a dakin mijinta."

Nihla dai in banda aikin kuka babu abin da take. Tayi luf a jikin Hajiya tana shesheka.

Yaya Babba ya miƙe ya fice daga gidan, kowa ya gane a fusace yake. Su Hafiz da dawowarsu kenan suna gaida shi amma ko amsa musu be yi ba.

Suna shiga suka tarar da Nihla tana gunsheƙen kuka, numfashi na sama na kasa.

Aminu, Hafiz, Jafar suka haɗa baki gurin tambayar abin da ke faruwa, ganin irin kukan da take kamar an ce mata Hajiya ta mutu, gaba ɗaya tsugunnawa suka yi, Aminu ya janyota jikinsa, yana bubbuga bayanta.

Hajiya dai ta rasa bakin magana akan namiji take wannan kuka ko kuwa faɗan da Abubakar ya mata ne ya sa ta kuka.

Jafar ya yi tunanin ko aljanu ne, ya fara tofa mata addu'o'i.

Shi kuwa Hafiz tambayar Hajiya ya ci gaba da yi akan ta fada masa abin da ya faru, amma tsananin mamaki  ya yasa ta kasa magana.

A hankali kukan nata ya fara raguwa, sai ajiyar zuciya take saukewa, tayi luf akan cinyar Aminu.

A hankali ta miƙe ɗakinta ta nufa, Hafiz ya yi yunkurin bin bayanta, Jafar ya hanashi.

"Ka rabu da ita, idan mutum yana cikin wannan yanayin yana bukatar kaɗaici, yanzu Nihla ba yarinya bace, ta fara mallakar hankalin kanta."

Hajiya da ido ta bita har ta ɓacewa ganinta.

Jafar ne ya mayar da hankalinsa kan Hajiya tare da tambayar abin da ya faru.

Hajiya sai da ta sauke numfashi sannan ta warware musu komai.

Idonta ta saukar akan Hafiz, "Ko kana da masaniyar Nihla tana da saurayi, domin nasan babu abinda zata ta yi ba tare da ta fada maka ba."

Ganin duk shi suke kallo ya hau rantse-rantse shi be san komai ba, in banda yanzu da aka fada.

Hajiya dai hankalinta ya kasa kwanciya kwata-kwata. Zata samu Nihla su yi magana, idan har aure take so to gwanda a yi mata, saboda gudun matsala.
Umsar ✍️ 
***


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol