Free chapter · Read without an account
Chapter 48
WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
YOTA
@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha
PAGE 48
NIHLA tunda ta shiga dakinta ta saka key, kan gado ta fada.
Ta saki sabon kuka, kuka mai cin rai. Jikinta na rawa, kirji na bugawa kamar zai fice. Kwata-kwata Irfan be kyauta mata ba.
Ba ta taba tunanin cewa da gaske zai iya tunkarar yaya babba ba. Abin da take guda kenan tun farko, Amma ga shi nan,ya ɓata komai.
Da ya yi hakuri an bi komai a hankali, Babu Wanda yasan tana kula saurayi, yanzu wanne kallo hajiya da sauran Yan Gidan zasu mata, duk abin da zata fada Musu be zama lallai su yarda da ita ba.
Kuma abin da ya fi ɓata mata rai, ko jiya da suka yi waya dare, be nuna mata ya je ba. Ya yi kamar ba komai, Ashe ya riga ya je ya kunna wuta, ya bar ta a ciki.
Kanta ta cusa a cikin pillow, wasu hawaye na kara zubo mata. Ta rasa wane irin tunani zata yi. Kanta ya yi nauyi, zuciyarta na bugawa da karfi.
Tana cikin wannan halin ne kiranshi ya shigo wayarta. Ta kalli screen din, sunan Irfan ne. Ta ƙi dagawa. Ya kira sau biyar a jere, a karshe ta daga saboda ya ishe ta.
"Hello, yan matana..."
Kawai sai ta fashe masa da kuka. Kuka mai cin zuciya. Ba magana
sai shesheƙar kuka.
Irfan na zaune amma be san lokacin da ya miƙe tsaye ba. Gaba ɗaya ya ruɗe, ya gigice.
"Nihla! Lafiya? Mene ya faru? Ki daina kuka ki fada min!"
Amma sai kara kuka take yi.
"Kit" ta kashe wayar gaba daya. Ta kashe wayar tas.
Kira ya dinga yi, amma a kashe ya ke shiga. Ya kira har sau goma, still a kashe. Irfan ya ji kamar zai yi hauka. Hannunsa na rawa.
Ɗaki ya shiga da sauri ya dauko key din mota, daga shi sai jallabiyya. Jabir na falo yana kallo, yaga Irfan ya fito kamar wanda aka faɗawa saƙon mutuwa duk ya rikice, tasowa yayi ya tambaye shi, "Irfan, me ya faru? Lafiya?"
Amma be yi magana ba, kawai ya fice daga falon da gudu. Bin bayansa Jabir ya yi, ya tarar har ya shiga mota, ya kunna. Be jira komai ba, shi ma ya faɗa cikin motar, ko takalmi babu a ƙafarsa.
Da mugun gudu ya figi motar. Jabir da ke zaune a gefe sai da ya tsorata da gudun da Irfan yake yi. Ya fuskanci kamar baya hayyacinsa, idonsa sun sauya kala.hannunsa na rawa a kan steering.
Ganin sun kama hanyar gidan su Nihla ne yasa Jabir ya kalle shi, sannan ya kalli agogon motar.
"Irfan! Karfe 11 saura fa! Wannan lokaci zaka je gidansu? Ka haukace ne?"
Irfan be amsa ba. Burinsa kawai yaga Nihla. Yaji kukan Me take Yi, dan a yanda yaji tana kuka baya raba ɗayan biyu mutuwa aka musu.
A kofar gidan su Nihla ya faka motarsa. Gari ya fara yin shiru, wasu gidaje ma sun rufe kofofinsu.
Gate din ya tunkara, Jabir ya yi kokarin rikosa, gami da shan gabansa.
"Me kake shirin yi? Baka da hankali? Gidan mutane zaka buga da wannan dare?"
"Ko ma menene ka bari sai da safe!" Jabir ya kara faɗa, yana kokarin jan hannunsa.
Hannu Irfan ya sa yana mirza sumar kansa. Gaba daya Jabir ya takura masa.
"Ai tunda na zo kofar gidan nan ba zan koma ba, sai na ji halin da Nihla take ciki," Irfan ya fada, muryarsa cike da damuwa.
Wayarsa ya zaro daga aljihu ya kara kiranta, amma dai a kashe take. Ture Jabir ya yi gefe, ya karasa gate din ya fara bugawa a hankali.
Jabir kuwa yana tsaye yana kallon ikon Allah. Ya san Irfan, duk lokacin da ya shiga irin wannan yanayin, tamkar mahaukaci yake komawa. A haka ma kura ta yi lafiya. Komawa ya yi ya jingina da jikin motar, yana kallon yadda abin zai kasance. Domin shi dai be shirya karbar wulakanci ba. Idan ya tuna abin da Yayan su Nihla ya musu, sai ya ji komai ya fice masa daga rai, amma shi gogan ko a jikinsa.
Me gadin gidan ne ya bude kofar, ya hasko su da sabuwar fitilarsa mai caji, ga wata uwar gora a hannunsa. Sai da ya gama haske Irfan tun daga sama har kasa, sannan ya tambaye shi, "Me kake nema?"
"Nihla," Irfan ya bashi amsa kai tsaye.
Da mamaki Baba Idi ke kallonsa, "Kai kuwa yaro? Da wannan tsahon daren zaka zo neman budurwa? Sha daya fa yanzu! Kuma zuwa yanzu nasan uwar masu gidan tayi bacci."
Irfan ji yayi kamar ya rufe Baba Idi da duka, amma ya daure zuciyarsa, ya hadiye haushinsa ya ce, "Baba, ta san da zuwana. Idan ka ce mata Irfan ne, zata fito."
"Ka kirata a waya mana."
"Na manta wayata a gida," Irfan ya yi ƙarya. Be san yadda zai faɗa masa wayarta a kashe take ba.
Dan jim Baba Idin yayi kafin ya mayar da kofa ya rufe. Kofar falon su Nihla Baba Idi ya fara bugawa.
Jafar ne ya bude, yana tambayar Baba Idi lafiya?
Yace, "Wani saurayi ne a kofar gida. Yace min gurin uwar masu gidan yazo, nace masa tayi bacci, yace ta san da zuwansa."
Shiru Jafar yayi. Nan da nan zuciyar ta fara hasaso masa wani abu.
"Mu je na ga waye tukunna," ya ce wa Baba Idi.
Umsar ✍️
08932144182