Free chapter · Read without an account

Chapter 17

by Hauwa Salihu · MATAR SALMAN

Follow this link to join my WhatsApp group: ***



*đź’«MATAR SALMANđź’«*



*PART ONE*
*PAGE 17*


Daki na wuce kai tsaye. Ya biyo ni a baya.Juyowa na yi na kalleshi da mamaki, naga duk ya bi ya haÉ—e fuska.
Zama na yi a bakin gado ban kula shi ba. Ya É—auki kusan minti biyar a tsaye kafin daga bisani ya ce, "Me ya kawo wancan É—an iskan gidan nan?"
A fusace na ce, "Ba É—an iska ba ne. Ahmad ne, kuma ya zo ne a kan maganar aurenmu."
Ya ƙara tamke fuska ya ce, "Wa ya ce miki auranki zai yi? Rumaisa, idan ba ki daina kula Ahmad ba, za ki yi da na sani mara adadi, domin yaudararki zai yi kawai."
Shiru na yi masa fuska É—aure.
Ya ce, "Kuma ki gargade shi, kar ya ƙara takowa ƙofar gidan nan, idan ba haka ba........"
Raina ne ya ɓaci sosai. Har ya juya zai fita, na ce, "Yaya!"
Tsayawa ya yi ba tare da ya juyo ba. Ni ma ban damu ba, na ce, "Me ya sa ka hana ni barin gidan nan?"
Ya juyo yana kallona kai tsaye ya ce, "Saboda Abba ne yace in dawo dake ko ta yayane."
Na gyada kai na ce, "Na ji. Ko za ka gaya min dalilin da ya sa duk wanda ya ce yana sona kake cewa É—an iska ne?"

Nan ma ya ce, "Saboda 'yan iska ne kike tarawa ban taba ganin mutumin kirki yazo wurinki ba."

Murmushin takaici na yi sannan na ce, "Yaya, ina girmama ka sosai, ka gane? Domin kana da ƙima a idona. Saboda haka, don Allah ka rabu da ni. Ni yanzu na shirya. Ko ban gama school ba, aure zan yi na bar muku gidanku..."

Shigowar Mama ne ya katse ni. Ta kalli Yaya Salman cikin alamun tsoro ta ce, "Salman, lafiya yau kuma?"
Murmushi ya ƙirƙiro wanda bai ma gama mamaye fuskarsa ba, ya ce, "Lafiya lau, Goggo Amina."
Daga nan ya yi saurin fita.
Mama ta kalleni ta ce, "Me ya haÉ—a ki da shi yau kuma?"
Nan na faɗa mata komai. Sai ta ɗan yi murmushi ta ce, "Hmm, Salman kenan har yanzu yana sonki ni nasani kuma indai Allah ya ƙaddara akwai aure tsakanin ku ba wanda ya isa ya hana, shine kawai nasani."

Anan ta kawo zancen Ahmad. Ko da na faÉ—a mata maganar aure, sai ta ce, "Da wannan yaron mara tarbiyyar?"

Na ce, "Mama, Ahmad ya shiryu kamar yadda na ba ki labarinsa a baya. Shaye-shaye ne kawai dama matsalarsa. Kuma Mama Ahmad yana É—aya daga cikin mutanen da suka taka muhimmiyar rawa a rayuwata a lokacin da na tsinci kaina a cikin wancan mugun yanayi, har na tsira da Mutuncina."
Hawaye ne suka zubo min da na tuna wancan lokacin.
Jikin Mama ya yi sanyi. Ta ce, "Gaskiya ne wannan. Amma ba ki ganin alamun Salman kamar har yanzu bai janye maganar aurenku ba?"

Na ce, "Hmm, Mama, ki rabu da Yaya. Har yanzu shi kansa bai san abin da yake so da wanda baya so ba."

Ta ce, "Rumaisa, Salman yana buƙatar mu tayashi da addu'a. Ki saka shi a addu'a, don Allah, domin Salman yana sonmu. Wannan abin da yake faruwa mahaifiyarsa ce sila, ba kowa ba."

Ni ma jikina ya yi sanyi. Na ce, "Haka ne, Mama. Insha Allah zan tayashi da addu'a, Allah ya sa mu dace."

Ta ce, "Yawwa, Amin Allah ya miki albarka, kuma ba komai, na amince da maganar aurenki da Ahmad É—in. Kin ga ko ba komai, ki yi aurenki ki huta. Allah dai ya sanya alheri."

Murmushi na yi na ce, "Amin, Mama, Na gode."

Sosai muka sake buÉ—e sabon littafi na soyayya ni da Ahmad. Tsarkakakkiyar soyayya, ba kamar da ba, domin Ahmad ya sauya sosai fiye da yadda duk kuke tunani.

Magana ta yi ƙarfi sosai. Mun yi maganar zai turo magabatansa ma wani satin ayita ta kare kawai.
Salima kam duk ta rikice kamar za ta yi hauka don tsabar kishi. Idan ta ganni a makaranta, kamar tazo shake ni, kawayenta sai zugata suke, sai da na fadawa Ahmad ya shiga tsakaninmu yaja mata kunne sannan ta sarara min.
Bayan tafiyar Lathifa da sati, sai ga wata ma ta zo daga Cameroon. Ita ma 'yar yayan Inna ce, sunanta Nabila. Wai itama an kawota ne saboda in Yaya ya ganta tayi mishi sai a aura mashi.

To, ba laifi, ta fi Lathifa kyau gaskiya, da kuma hankali, sai dai yarinya ce na girme ta, ga kuma bala'in rawar kai, sam bata gama wayo ba akwai yarinta sosai a tareda ita, babu kuma wayewa sam.
Anan Inna ta fara lallaba Salman da ya aure ta. Shi dai sam ba ta kwanta masa a rai ba, ya dai kyalesu.

Zuwa yanzu mun gama exams. Na fara shirye-shiryen zuwa hutu Abuja, don mun yi da su Fa'iza a can za mu haɗu wannan karon. Duk na ƙosa in tafi saboda gidan ya gundure ni.

Na fito tsakar gida ina shanya undies ɗina da na wanke a toilet, sai na ji sallama. Na juya da sauri. Wata mata na gani mai ɗan jiki, doguwa, ta yi bleaching kam ba karya, Kana ganinta ka ga ƙirar manyan mata. Don tuni turarenta ya gauraye tsakar gidan. Idonta sanye da baƙin glass. Daga ganinta za ta yi rashin mutunci.
Gabana ya dinga faÉ—uwa nikam. Na daure dai na ce, "Sannu da zuwa. Mu isa falo."

Girgiza min kai ta yi tana kallona a wulakance daga sama har kasa ta ce, "Amina tana nan?"

Da mamaki nake kallonta don ban taɓa ganinta ba, duk da Mama nada jama'a sosai nasani, kawai na ce mata, "Eh, tana nan."
Ta ce, "Ki ce mata ta yi baƙuwa." Na ce, "To."

Har zan shiga falo, sai ga Mama ta fito tana mika min waya da sauri, Ni kam a rikice nake ce mata, "Yawwa, Mama, ga baƙuwa ta zo wurinki."

Mama ta ƙarasa fitowa cike da fara'a ta ce, "Sannu da zuwa. Mu isa mana."

Tabe baki ta yi ta ce, "Ba sai na shiga ba, don ba zama na zo yi ba. Amina, ina son ki ba ni hankalinki anan."

Cike da mamaki Mama ta ce, "To, ina jin ki."

Ta ce, "Yawwa, ni sunana Dr Surayya Umar. Matar Dr Hakim, sannan Yayar Ahmad Umar da Salima."
Lokaci guda muka kalli juna da Mama.

Taci gaba da faɗin, "Kwara kuwa er gwamna ce a gabanku!....Na zo nan ne domin in gargade ki da ki ja wa 'yarki Rumaisa kunne, ta fita daga harkar Ahmad, domin ba ajinta ba ne shi." Sannan ta cire glass ɗin idonta ta kalle ni a wulakance ta ce, "Ke kuma, duk abubuwan da kike yi muna sane da su, tun daga lokacin da kike tare da Doctor har zuwa yanzu da kika liƙe wa Ahmad. Don haka, yau ce zuwana na farko kuma na ƙarshe. Ina ƙara gargadinki a kan ɗan uwana da mijina, domin idan kika kuskura na sake jin wani abu, to ki kuka da kanki."

Ta kalli Mama ta ce, "Ke kuma, kamata ya yi ki maida hankali wurin nemawa 'yarki dangin ubanta, ko da kuwa ba ta hanyar halak kika same ta ba, domin ko yaya ne mun san cewa da uba ake ado, amma fa wannan shawara ce, don in ba haka ba, 'yarki ba za ta taÉ“a samun mutunci da Ć™ima a idon mutane ba, babu wani É—an arziki da zai iya aurenta a garin nan, don haka ki mai da hankali wajen nemawa 'yarki UBANTA, ba wai ku tsaya kwaÉ—ayi da dogon buri ba. Ina fatan kun fahimceni?” 

Ni kam kallon Mama nake hawaye tuni ya ciko min ido.
Sai na ga ta É—an yi murmushi ta ce, "Shikenan abinda ya kawo ki kenan ko akwai wani abu kuma?"

A yatsine ta ce, "Eh shikenan, Amma fa idan 'yarki ba ta fita harkar É—an uwana ba, za ku fuskanci wulakanci da rashin mutunci da tozarci..."

Mama ta girgiza kai ta ce, "Ba za ma a kai ga haka ba, In Allah ya yarda ta rabu da kaninki kenan har abada koda kuwa shine autan maza, ki kwantar da hankalinki."

Ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Kun kyautawa kanku." Ta juya ta fita. Muka bita da ido har ta ɓace. Ni kam kawai na fashe da kuka da sauri na wuce ɗaki, Mama ce ta ƙarasa shanya min kayan.
Ahmad na kira, bai É—auka ba har ya tsinke, sannan ya kira ni, na É—auka da sauri.....Cikin nishaÉ—i yake ce min, "My Queen! Sarauniyar mata ina fatan kina lafiya dai?"

Na share hawaye nace, "Ahmad, ba lafiya, akwai matsala."
Da sauri ya ce, "Subhanallah wani irin matsala kuma?"
Nace, "Yanzu Doctor Surayya ta bar gidan nan bayan ta gama shimfiÉ—a mana rashin mutunci nida mahaifiyata kuma ta min barazana akan ka......."
Nan na gaya masa komai. Hankalinsa a tashe ya kashe wayar. Aikuwa bai zame ko ina ba sai asibitin da take aiki. Ya shiga sauke mata bala'i, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, sai da ya mata tass, haɗe da yi mata gargaɗi sosai a kan kar ta ƙara shiga rayuwarsa, don ba shafe ta bane. Har ya fita bata ko daga ido ta kallesa ba bare ta tanka, ya ma za'ayi ta biye masa ya tara mata jama'a tunda ba hankaline dashi ba.

Bayan nan gida ya zo, ya yi ta ba Mama haƙuri. Mama ta ce ita dama ranta bai ɓaci ba, kawai dai tunda abin ya zama haka, dole ne ya rabu da ni, domin ba za ta yarda in shiga familinsu ba tunda abin ya zo da haka. Juyin duniya ya yi da Mama ta fahimce shi, amma sam ta ƙi yarda, hasali ma, ta ƙi bari mu haɗu. Jikinsa a mace ya bar gidan, ni kam ina ɗaki, ba abin da na sani sai kuka.

Shikam yana komawa gida, ya je ya sami His Excellency ya kai ƙarar Surayya, bai taɓa tunanin mahaifinsa zai juya masa baya ba, amma sai ga shi ƙiri-ƙiri ya nuna masa yana sane da maganar, kuma shi ma yana goyon bayansu su Surayya, domin baza su taba amincewa ya auri yarinyar da bata da asali ba. Anan Ahmad ya fahimci haɗa baki Surayya ta yi da Salima da mahaifiyarsa suka rusa maganar aurenmu ta hanyar ɓata min suna a cikin familinsu. Bakin cikin wannan abun ya saka ya bar ƙasar gaba ɗaya don in har ya zauna komai zai iya faruwa.

A ɓangarena, ba rabuwa da Ahmad ne kawai ya dame ni ba. Kashi casa'in da tara cikin ɗari, abin da ya fi damuna shi ne maganar waye MAHAIFINA? Ina matukar son sanin asalina a yanzu don na gaji da gorin nan har ga Allah.......Ranar ko abinci ban ci ba. Mama ta yi ta shigowa tana min magana, amma sam ta kasa gane kaina. Haka muka kasance har dare, hankalinta ya kasa kwanciya, don haka ta shigo ta same ni. Zama ta yi a bakin gado ta kalleni ta ce, "Haba Rumaisa! Har yanzu ba za ki bar kukan nan ba? Tun safe kike abu ɗaya."

Sai kuma ta É—anyi shiru sannan ta sa hannu ta É—ago ni ta ce, "Kinga kiyi shiru, ba amfanin kukan nan. Addu'a zamu ci gaba da yi Allah ya kawo miki wani mijin..."

Ina shesshekar kuka nace "Ni ba shi ne ya dame ni ba Mama.”

Tace, "To mene Rumaisa?"
Nace, "Ni so nake in san waye MAHAIFINA da danginsa, don Allah Mama ki daure ki gaya min.”
Ta zuba min ido kamar tana nazarin amsar da zata bani sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Shikenan abinda kike bukata?"

Na É—aga mata kai ina share hawayen.
Ta gyada min kai sannan ta ce, "To shikenan, yanzu ki tashi ki ci abinci, sannan kiyi wanka, sai ki kintsa, ki same ni a É—akina."
Ta jawo tray É—in abincin da ta shigo da shi tace, "To bismillah, sauko ki ci."

Ba don na damu da abincin ba na sauko na É—an ci, amma ba mai yawa ba. Sannan na shiga wanka bayan na fito ban ga Mama ba. Don haka sai na shirya cikin kayan barcina na tafi É—akinta, amma ba ta nan, Zama na yi a kan gado ina jiranta.
Can sai gata ta shigo yayinda take cire hijabinta tace min, "Na je wurin Yaya ne kin shigo baki ganni ba koh?"
Ta tafi ta buɗe wardrobe ɗinta ta ɗauko wata jaka irin na mutanen da sai da ta sa keys kanana ta buɗe sannan ta zo da ita ta zauna gefena tana buɗe cikin jakar ta kalleni sannan tace "Rumaisa, komai naki yana cikin jakar nan koda ace na mutune sanin inda mahaifinki yake bazai baki wahala ba..... Saboda haka zan faɗa miki inda mahaifinki yake yanzu, kuma za ki tafi goben nan insha Allahu. Amma sai na ba ki labarin rayuwata da yadda aka same ki har zuwa yanzu. Ban sani ba, ta iya yiwuwa ki ji daɗin labarin, ta iya yiwuwa kuma baƙin cikin da kike ciki ya ƙaru, amma komai ya faru, ki yi haƙuri."

Ta sunkuyar da kai tana share hawayen da suka taru a idonta, sannan ta miƙa min wani hoto, na karɓa ina kallonta cikeda son jin karin bayani don haka tace min "Wannan shi ne mahaifinki Rumaisa wato IBRAHIM."

Na zuba wa hoton ido sosai, kyakkyawan saurayi ne, kuma daga gani bafilatani ne usul. Don fari ne shi sol ga tsawo, ba shakka, a wurinsa na É—auki hasken fatar nan, domin su Mama ba su da haske sosai, Kuma daga gani wayayye ne É—an boko, daga yanayin shigarsa ta kananan kaya gashi yasha facecap ga agogo, duk da ma shigar ta mutanen da ne. Kawai na tsinci kaina da sakin murmushi ina jin farin ciki har cikin raina.
Mama ma ta yi murmushi tace, "Rumaisa, mahaifinki É—an babban gida ne, kuma É—an manyan mutane, suna da tarin arziki bana wasa ba, kuma mutane ne masu kirki, karamci da sanin ya kamata ga mutunta É—an Adam."

Fara'a sosai ta bayyana a fuskata, haka ma Mama ta ci gaba da faÉ—in, "Wani babban albishir ma da zan yi miki shi ne, ni da mahaifinki aure muka yi muka haife ki ba ta hanyar da mutane ke miki gori ba, Kuma mahaifinki ya fi sonki a cikin dukkan yaransa. Amma daga baya da kansa ya koremu daga rayuwarsa kuma ya min kashedin cewar har abada kar in koma gareshi kuma kema baya bukatar ki kwata kwata a rayuwarsa, ya yafe min ke duniya da lahira, wannan dalilin yasa, bana son a min zance waye mahaifinki, domin yana fama min wani ciwo a cikin zuciyata........
Ta ƙarasa maganar cikin kuka mai ciwo, wanda in kaga Mama na irin wannan kukan to tabbas abun ya mata ciwo matuka, don macece mai dauriya.

Ido na zuba mata jikina kuma yayi sanyi sosai.


*🌹LABARIN AMINA 🌹*
Amina Suleiman Yakasai, wacce aka fi sani da (Meenah) a wancan lokacin. Amina ta taso ne cikin kulawa da gata daga Yayyunta Kasim da Mohd, domin iyayensu sun rasu tun tana primary. Asalinsu Kanawa ne, domin dukkan danginsu a nan suke. Amma tun bayan rasuwar mahaifinsu, babu wanda ya kula da su a dangi. Kowa ya yi watsi da lamuransu.

Mohd shi ya É—auki dawainiyar kannensa da É—an leburancin da yake yi a lokaci har Allah ya dubeshi ya samu aikin gwamnati a matsayin malamin primary, sai ya fara haÉ—awa da É—an kasuwanci da bai wani taka kara ya karya ba, da haka yake biyan kudin makarantar kannensa.
Kasim a lokacin ya gama Jami'a yana bautar ƙasa a Kaduna. Yayinda Amina take SS2 kuma boarding school. haka suke ci gaba da rayuwarsu cikin rufin asirin Allah.

Mohd ya haɗu da Shatu ne a lokacin da suka tafi Kamaru ɗaurin auren wani amininshi kuma abokin kasuwancinshi. Anan Allah ya haɗa shi da Shatu wacce ta matuƙar fizgar hankalinsa, saboda kyaunta, dama kun san Kanawa da son farar mace, Shatu kam duk ta hada komi da ake bukata a jikin mace, bayan haske ga kyau, ga gashi, ga kuma diri.

Nan fa ya liƙe mata. bai wani sha wahala ba, ya sami amincewarta har maganarsu ta yi ƙarfi a wurin iyaye, ba su cika shekara ba aka yi bikin aurensu. Shatu ta tare a gidan Mohd na Kaduna, domin a can aka yi masa transfer ya koma. A lokacin Amina tana SS3, Kasim kuma ya ƙare bautar ƙasarsa, yana taya yayansa kasuwanci, don samun aiki baida sauki.

Da su Amina suka yi hutu, Kasim ne ya tafi Kano domin ya É—auko ta. Aikuwa tana ganinsa ta kama tsalle da murna tana cewa, "Kai Yaya, na yi kewarku irin sosai É—innan, wannan term ko visiting ba ku zo min ba fa naita zazzare ido shuru."

Yana murmushi ya ce, "Ke dai bari, ƙanwata. ni ɗin na zama busy ne, kinsan lebura......”

Tana dariya ta ce, "Kai, Yaya, ina Aunty nane?"

Yayi murmushi yace, "Tana gaishe ki. Au na manta albishirinki?"
Tayi fari da ido sannan tace, "Goro fari so Yaya na."

Yayi murmushi sannan ce, "Yayanki fa yayi aure last 2 weeks, yanzu haka in mun koma, za ki ci girkin amarya..."

Cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa ta ce, "Wayyo Allah na Yaya amma na ji daÉ—in wannan labarin, domin ina son Yaya ya yi aure dama. Masha Allah ni har ma na Ć™osa in ga mun isa gida, bari in je in sallami friends É—ina." Ta juya da sauri, shikam ya bita da kallo yana dariya kawai. 

Sun iso Kaduna da yamma sosai. Amina tun daga ƙofar gida take ta rafka sallama haɗe da faɗin, "Ina Aunty amaryar Yayan nawa take?"

A lokacin da ta isa tsakar gida, suka yi arba da Shatu wacce take shara, ko a jikinta kamar ba sallama ake ba. Turus Amina ta yi tana kallonta baki sake, Kasim ne ya ce ma Shatu "Madam ba ki gan mu bane?"

Ta É—ago tana É—an murmushi ta ce, "Na gan ku mana sannunku to."
Sannan ta kalli Amina cikin hausarta da bai gama nuna ba ta ce, "Sannunku da zuwa ga taburma."

Ta wuce ta É—auko tabarma ta shimfiÉ—a. Kasim kam cewa ya yi, "Ni dai na zauna a kujera, zo ki ba ni abinci na ci in wuce shago. Nasan Yaya na yana jirana ya samu ya dawo gida ya ga amaryarsa."
Murmushi ta yi ta ce, "To, Kasim."

Ta wuce kitchen. Amina har lokacin tana tsaye Kasim ya ce, "To wai ba za ki shigar da kayanki ki je ki zauna ba? Kin wani tsaya kina binta da kallo babu ko gaisuwa?"

Amina tace, "Yanzu fisabilillah Ya Moh'd ga 'yan mata cike a gari, wayayyu, shi ne ya tsallaka Kamaru har ƙauye ya je ya ɗauko wannan bigidajiyar yarinya da ko Hausa ba ta iya ba? Gaskiya ni wallahi matar nan ba ta min ba, wannan ai abin kunya ne ma in nuna ta a matsayin matar Yaya na."

Ta ja tsaki ta suri jakarta. A lokacin Shatu kuma ta fito daga kitchen, anan suka yi karo, Shatu ta zuba wa Amina ido kawai.
Tun daga wannan lokaci tsakanin Amina da Shatu babu shiri don sam jininsu bai haÉ—u ba, har Amina ta gama secondary ta dawo gida, a lokacin Kasim Allah ya hadashi da ubangida mai sonshi don haka ya jashi a jiki ya bashi aiki a karkashin shi, kuma Allah ya haÉ—a goshinsu, lokaci guda komi ya bunkasa, don haka Alhajin ya dauki ersa ta cikinsa Zuwaira ya baiwa Kasim aurenta, saboda ya yaba da halinsa na gaskiya da nagarta, akayi biki, Zuwaira ta tare a gidan da Moh'd yake, duk da ba babba bane amma ya ishesu. A lokacin Amina ta fara zuwa jami'a, sosai take son Zuwaira, don komi tare sukeyi, tunda ita wayayyiyace er boko er'uwarta ba kamar Shatu ba.

 Ranar bayan sun taso school Amina da kawayenta, suka dawo gida, tunda suka shigo tayi arba da Shatu nata amai, sai taji ranta ya bala'in É“aci, ta watsa mata harara haÉ—e da jan tsaki, ta kalli Ć™awayenta ta ce, "Ku zo mu isa ciki wurin Auntyna."
Nan suka wuce gefen Zuwaira wacce take ta fama da laulayi a lokacin

Bayan sun gaisa anan suka shiga hirarsu ta en boko. Amina ta fita ta je wurin Shatu dake kwance ta kalleta a kyamace ta ce, "Wai kin gama girkin ne kika zo kika kwanta? Kin bar mutane da yunwa alhalin kinsan Aunty Zuwaira batada lafiya"

Shatu kam tana fama da kanta itama, sai dai kunsan halin bafilatani kan zurfin ciki da ƙyar ta iya faɗin, "Na gama miya, saura tuwo ne kan wuta yana karasawa ki duba in yayi ki kwashe muku"

Amina ta É—an yamutsa fuska tace, "To da kike kwance anan kina wani langwabewa kin faÉ—a wa Yayan ba ki da lafiya ne?"
Girgiza kai Shatu ta yi. Amina ta ja tsaki ta ce, "Ke dai ban san yaushe za ki waye ba."

Ta fita zuwa kitchen ta debo kwanuka ta kwashe tuwon, duk ta kai wa kowa nasa.

Bayan sun gama cin abinci, ƙawayenta sun tafi. Ta kalli Zuwaira ta ce, "Aunty Zuwaira Shatu fa ba lafiya ɗazu mun shigo sai amai take, kuma ko girki ba ta ƙarasa ba, ni na karasa mata.”

Zuwaira ta ce, "Subhanallah! Shi ya sa mana yau ba ta shigo ta biya karatunta ba, ina son inje in tambayeta nima jikin yaki."
Amina ta yi dariya ta ce, "Kina ƙoƙari da kike koya mata karatu Allah, wannan mata ba za ta taɓa wayewa ba. Yaya dai hasken fatar nan da ɗan kyawun nan ya ruɗe shi, ya je ya auro wacce idan sun haihu ba za ta iya tarbiyantar masa da yara ba."

Zuwaira ta ce, "Don Allah Amina ki rabu da matar nan haka mana haba."
Amina ta tashi tana dariya ta ce "Bari dai in je in same ta mu je asibiti don ta bani tausayi, tunda su Yaya ba za su dawo da wuri ba sai dare, ba amfanin jiransu."

Zuwaira ta ce, "Gaskiya ne kam,gara a kuje É—in, duk yadda ake ciki ki fada min don Allah."

Anan Amina ta je ta ce wa Shatu ta shirya su tafi asibiti. Sun fita a kan hanya suna jiran mai keke napep. Sai kawai wata sabuwar mota daliliya ta zo gabansu ta tsaya. Mai motar ya fara sauke glass a hankali. Wani matashin saurayi ne kyakkyawa fari sol, ga hanci har baki, yana sanye da jumper da wando sky blue, ga hularsa mai tsada ya kafa wanda ya tafi da yanayin kyawun fuskarsa mai cike da saje. Ya kalli Amina wacce kwata-kwata hankalinta ba yama kansa. Ya saki murmushi ya ce, "Meenah!"

Sai lokacin ta kalleshi cikin mamaki mara misaltuwa ta ce, "Laa! Ib, yaushe a garin namu?"

Fuskarsa cike da fara'a ya ce "Tun fa last week, Ina nan KD tunda ku kun share mu, dole mu muzo ai how far?"

Ta yi dariya ta ce, "Kai Ib, wai mun share ku?"
Ya ce, "Eh mana Meenah ko a waya ba a samunku."

Ta ce, "Ohh sorry Ib wancan layin ya daÉ—e bana amfani da shi ai."

Murmushi yayi kawai sai a lokacin ya kalli Shatu yace, "Sannu Aunty, ina wuni?" Kamar bataso ta amsa da lafiya, ta kauda kanta gefe.

Amina taji haushin yadda Shatu tayi don haka tace mishi "Bata ɗan jin daɗi ne Ib. 'Yar uwar matar Yayana ce ta zo daga ƙauye."

Ib ya kalli Shatu da damuwa ya ce, "Eyyah sorry. Allah ya ba ta lafiya, ynzu asibiti za ku je kenan?"

Amina ta ce, "Eh wallahi."
Ya ce, "To mu je kawai nayi dropping dinku mana."

Amina ta ce "No Ib ka tafi harkokinka kawai."
Ya ce, "Ai Meenah ke mai tsada ce, bai dace a bar ki anan kan hanya ba gaskiya."

Dariya ta yi sannan ta ce, "Shikenan Ib mun gode."

Sannan ta kalli Shatu ta ɗan yi ƙasa da murya ta ce, "Wallahi, kika kuskura kika masa amai a mota hmm, kin san saura kuma ba wai in kin shiga ki dinga kalle-kalle kina zazzare ido kina kauyanci ba, nutsuwa za ki yi, don ma dai na riga na faɗa masa ke ɗin daga ƙauye kika zo Allah ya soni, Amma dai ki kula, wannan mutumin da kike gani wayayye ne, ɗan boko, ba ya son kauyanci."

Shatu ta haɗe rai ta ce, "To ai ni ban ce miki ina buƙatar shiga motar saurayinki ba Amina, da kike wani cewa daga ƙauye na zo, dolenki dai ni matar Yayanki ne ba yadda kika iya dani kuma mijina yana sona a hakan."

Amina tayi kasa da murya ta ce "Ba shakka, kuka asirce shi dai ko? Hmm"

Ta buɗe ƙofar motar ta baya ta ce, "Zo ki shiga nikam."
Shatu ta shiga ba don ranta na so ba,Amina ta rufe sannan ta buÉ—e gaba ta shiga tana murmushi, ta kalli Ib bayan ta rufe ta ce "Ib kuna shagalin ku a kasar nan."

Yayinda suka fara tafiya ya ce "Amina ke dai banda zolaya. Kin ga yadda kika dawo kuwa kina haskakawa kamar wata zara a cikin taurari wai meye sirrin ne?"

Murmushi Amina ta yi ta ce, "Kai ma ka rama to, ni da nake ta koduwa a school?"

Haka suka manta da wata Shatu suka dinga hirarsu, har da juya harshen turanci.
Wani haÉ—aÉ—É—en private hospital ya kaisu, ya haÉ—a su da doctor, Nan aka yi wa Shatu gwaje-gwaje. aikuwa ciki ne, har na wata biyu da sati biyu. Anan Amina ta hau murna har abin ya baiwa Shatu mamaki, duk da itama kanta Shatu farin ciki ya gama cika ta. Bayan sun gama komai, Ib ne ya biya duka bills din kuma ya dawo da su, yayinda ya cika su da kuÉ—i. Ya kuma ce wa Amina zai zo daga baya.
Suna shiga gida Amina ta kalli Shatu ta ce "To saura in ji kin kuskura kin gaya wa Yaya labarin Ib."

Zuwaira ta kalli Shatu tana murmushi ta ce, "Shatu me kike ɓoye mana ke da ƙanwarki?"

Shatu ta ce "Hmm, saurayi ta samu ya riƙa dawainiya da mu baki gani ba Zuwaira."
Zuwaira ta kalli Amina tana dariya tace, "shine ake boye min kenan?"
Amina ta ce "Aunty Zuwaira share ta, Ib ne fa."
Zuwaira ta ce da mamaki "Kai! yaushe ya zo?"
Amina na murmushi ta ce "Hmm wai fa tun last week ashe, wai akwai aikin da aka turo shi ne anan KD."
Sai kuma ta ce "Aunty Zuwaira albishirinki?"

Zuwaira ta ce "Goro fari sol!"

Amina tace "To takurunkus! Shatu ma ciki ne da ita kunyi anko, kinzo mana gida da alkhairi, kuma har wata biyu da sati biyu. tare ma za ku haihu, don watannin cikinku É—aya."

Zuwaira ta kalli Shatu cike da tsantsar farin ciki ta ce, "Wayyo 'yar uwa ta na taya ki murna wallahi. Na kuma ji daÉ—i sosai, yanzu hankalin kowa zai kwanta."

Shatu kam ba ta yi magana ba, ta wuce É—aki ta kwanta don kunya abin ke bata ita.
Da daddare su Kasim suka dawo. Bayan sun ci abinci sun huta, aka fara taɓa hira. Amina ta kalli Moh'd tana murmushi ta ce, "Yawwa Yaya,m akwai albishir da zan maka mai girma."

Mohyd ya ce,
 "Keda ba'a rabaki da shiririta Ć™anwata, ina dai jin ki to."

Ta kalli Shatu tana murmushi, wacce ita kam tuni ta mike ta yi É—aki saboda kunya irin namu na Fulani.
Ta ce, "Yaya Shatu na É—auke da ciki har na wata biyu da sati biyu. É—azu na kai ta asibiti wallahi, sai mu godewa Allah da karbi adduarmu Yaya."
Ta miƙa masa takardar scanning fuskarta da walwala.
Sosai Moh'd ya nuna murnarsa a fili, ya dinga godiya ga Allah. Kasim na tayashi, nan da nan ya mike ya bi matarsa É—aki. Amina da Kasim suna masa dariya.
Tun daga wannan lokaci Amina ta É—auki nauyin hidimar gidan duka, bata bari ko tsinke su É—aga, domin babu abin da take so a rayuwa da ya wuce ta ga sun tara zuriyya su ma, tunda dangi sun guje su, saboda maraici.

Shatu kam duk kulawar da Amina take bata gani take kamar ta haÉ—a baki ne da Zuwaira don su cuceta a cikin ruwan sanyi, don a ganinta sam ba sa wani sonta, don haka taki sakin jikinta sai taka tsantsan take dasu.

Amina da Ib sun ƙulla soyayya mai ƙarfi a tsakaninsu har ta gabatar da shi wurin Yayyunta. Amma abin mamaki, sai ta lura sam ba su yi na'am da shi ba. Domin a ganinsu bai kamata Amina ta yi nitsa da su ba, Kamata ya yi ta yi aure kusa da su domin su san duk abin da take ciki.

IBRAHIM AHMAD GALADIMA, wato Ib, cikakken ɗan Adamawa ne a garin Yola. Ɗan babban family ne, domin in ka je Yola ka ce Galadimas Family, to babu wanda bai san su ba. Ib ya haɗu da Amina ne sakamakon wani aiki da ya kawo shi KD. Bai ɓata lokaci wurin nuna mata yana sonta ba, amma ta dinga ja masa aji har ya zo ya koma. Dawowarsa a wannan karon ne ya samu ya shawo kanta har ta amince, amma ya lura kamar Yayyenta ba su karɓe shi ba sam. Hankalinsa ya tashi ƙwarai, don a ganinsa zai iya yin komai domin ya ga ya aure ta.

Akwai Yayan Zuwaira, Farouq da yake matuƙar son Amina. Amma ita kuma ba ta sonshi. Yayyenta kuma sun fi son shi ba don komai ba, sai don ɗan uwan Zuwaira ne, sannan ɗan Kaduna. Mahaifinsa mutumin kirki ne, ya riƙe Kasim kamar ɗan cikinsa. Don haka suna ganin auren Amina da Farouq shi zai ƙara musu dankon zumunci. Amma sam Amina ta ƙi yarda, Ita dai Ib take so.

Zuwaira kam har ga Allah ba ta yi fushi da Amina ba, don ta san yadda soyayya take, har ƙoƙari take ta ba wa yayanta haƙuri da ya haƙura ya nemi wata kawai, Amma Kasim ya hana ta, ya ce ta bari za su shawo kan Amina.

Shatu kam, ta so ace Amina ta fuskanci tsanani daga wurin yayyenta, don ba ta son su lallaba ta ko kaɗan don haka ta dinga ingiza Moh'd tana ƙara cusa musu ƙin Ibrahim, tana nuna musu ai shi yake zuga Amina, yana hure mata kunne ta bijire musu.

Da Amina ta fahimci Shatu na shiga harkokinta, anan ta zage ta rufe ido ta zuba mata rashin mutunci, ta zage ta tass. Tun Shatu na amsawa har wasa ya koma gaske, taga Amina ta fi ƙarfinta, ta koma sai kuka take yi, ranar dai sun yi babu daɗi. Sai da Zuwaira ta yi da gaske sannan Amina ta kyale Shatu. Moh'd na dawowa ya tarar Shatu ta ci kuka har ta godewa Allah anan ya shiga tambayarta ko lafiya?

Cikin kuka ta ce, "Wallahi ni abubuwan da Amina ke min a gidan nan sun ishe ni Malam, me na yi wa Amina a rayuwa ta tsane ni haka? Wai yau Amina har da buÉ—e baki ta zagi iyayena. Amina har cewa ta yi duk matan garinmu karuwai ne fa, sannan ni ma asiri na yi maka ka aure ni, ba wai kana sona ba."

Murmushi ya yi ya ce "Haba Shatu yaushe za ki biye wa maganar Amina har ta dame ki? Ai ni nasan ko ke wace ce, nasan kuma iyayenki mutanen kirki ne sannan kuma ni har ga Allah saboda soyayyar da nake miki na aure ki, ba wai asiri kika min ba. Don haka ki yi shiru kinji, zan ja wa Amina kunne sosai."

Hankalinta ya É—an kwanta, amma sai ta ga ba wani kwakkwaran hukunci da Moh'd ya É—auka a kan Amina. Don har sannan Amina idan tana gidan Shatu ba ta da zaman lafiya ko ruwa ba ta isa ta sha ba. Nan ma Zuwaira ce take hana ta.

Cikinsu na wata bakwai 'yan uwan Shatu suka zo suka ce za su tafi da ita ta je ta haihu a garinsu, kuma har sai ta gama wanka za ta dawo.

Mohd bai so haka ba, amma dole ya haƙura. suka tafi da ita tunda al'adarsu ne. Cikin ikon Allah, a kwana a tashi ba wuya a wurin Allah, cikinsu ya cika wata tara suka haihu, yara maza dukan su, Shatu ta fara haihuwa, bayan kwana biyu ita ma Zuwaira ta sauke.
Murna a wurin Amina da yayyenta ba'a magana. Ranar suna aka sanya wa yara suna iri É—aya Suleiman, wato sunan mahaifinsu

Mohd kam yana can Kamaru sai da aka gama hidimar suna ya dawo ya bar mai jego da É—an ta cikin koshin lafiya.
Shatu na gama wanka, Moh'd ya kasa hakuri ya kira yayyenta ya ce zai zo ya É—auke ta. Da yake su ma iyayensu sun rasu.
Anan Shatu ta shiga shirye-shiryen komawa Nigeria, Ta kama shanunta har uku ta siyar suka tafi wurin wani malaminsu ita da matar yayanta.
Anan Shatu ta faɗa wa malamin dukkan buƙatarta, shi ne a shiga tsakanin Amina da yayyenta su tsane ta har zaman gidan ya gagare ta na har abada. Domin idan ba haka ta yi ba, Amina ba za ta bar ta ta sha ruwa ba a gidan mijinta. Don haka kuɗi sosai ta zuba wa malami a yi mata aikin gaske. Kuma tana so ya kasance duk abin da ta faɗa, Moh'd da Kasim su bi ta kamar rakumi da akala.

Shatu ba ta dawo Nigeria ba sai da ta gama shirinta tsaf!

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol