Free chapter · Read without an account

MADINA ALMUNAWWARA

by Hau—waah · KADDARAR ZUCIYA

*KADDAR ZUCIYA* 

*CHAPTER FIFTY-NINE: 59*  

*MADINA AL MUNAWWARA*

Jirgin ya ci gaba da ratsawa cikin farin gajimare, komai ya yi shiru, sai ƙaramar ƙar engine ɗin jirgin da kuma sautin numfashin fasinjojin da suka fara samun nutsuwa bayan tashin jirgin. Inteesar kuwa… har yanzu kanta jingine yake da window, idanunta na kallon gajimaren da suke ta shawagi kamar auduga. Wani irin kwanciyar hankali ne ya lulluɓe zuciyarta, a hankali ta lumshe idanunta. Sai wani tunani ya fara ratsowa cikin zuciyarta, rayuwa… lallai rayuwa tana da ban mamaki. Wata rana… mutum zai yi zaton komai ya ƙare, washegari kuma… Allah ya buɗe masa wata ƙofa da bai taɓa zato ba. Ta sauke numfashi a hankali, a hankali ta ɗora tafin hannunta kan ƙirjinta, “shekaru biyu da suka wuce…” ta furta a cikin zuciyarta, “ban taɓa tunanin zan sake yin irin wannan tafiya cikin kwanciyar hankali ba.” Idanunta suka ɗan cika da ruwa.

Ahmad… sunan ya faɗo mata a zuciya kamar iska mai sanyi. Ta tuna murmushinsa, ta tuna yadda yake kiranta… “Angelic,” ta tuna ranar da ya yi mata bankwana, ta tuna yadda ya ce, “ba zan daɗe ba… zan dawo.” Sai kuma… wata ƙaramar ajiyar zuciya ta kuɓuce mata, domin ta san… bai dawo ba. Abin da ya dawo… shi ne labarin rasuwarsa. Nan take hoton ranar jana’izarsa ya bayyana a gabanta, mutane, kuka, hayaniya, da ita… wacce ta tsaya tana kallon duniya kamar ta tsaya da juyawa. Ta tuna yadda ta rungume kyautar da ya kawo mata, ta tuna yadda ta yi kwanaki ba ta son magana, ta tuna yadda ta yi watanni tana jin kamar zuciyarta ta mutu gaba ɗaya. Har ta kai wani lokaci… ta yi imanin ba za ta sake yin dariya ba, ba za ta sake son wani ba, ba za ta sake samun farin ciki ba. Sai ta girgiza kai a hankali, hawaye guda ya sulalo daga gefen idonta, ta goge shi kafin ya isa kumatunta. Sai kuma… ba tare da ta shirya ba… wani fuska ya bayyana cikin zuciyarta, Aliyu. Sai wani murmushi mai laushi ya bayyana a gefen lips ɗinta.

Ta tuna ranar farko da ya fara kiranta… “Babygirl,” a lokacin… ta yi kamar ba ta ji daɗi ba, amma a zuciyarta… ta ji wani abu ya motsa. Ta tuna yadda yake damuwa idan ba ta ɗaga wayarsa ba, ta tuna yadda yake farin ciki idan ya ji dariyarta, ta tuna ranar da ya tsaya gaban Daddy cikin cikakken girmamawa yana neman aurenta, ta tuna yadda ya riƙe hannunta har ya rungumeta ranar da yayi fushi, ta tuna gift ɗin da ya ba ta, da ƙaramin paper ɗin nan da ya rubuta… “I always believed in you.” Inteesar ta lumshe idanunta, sai ta yi murmushi cikin hawaye, “ya Allah… lallai kai ne mai sauya hali, kai ne mai musanya baƙin ciki da farin ciki, kai ne mai haɗa zukata, kai ne mai warkar da raunukan da babu wanda yake iya gani.” Ta sake kallon gajimaren da ke wucewa, wani irin natsuwa ta mamaye zuciyarta. A yau… ba ta sake jin zafin jiya kamar da ba, ba don ta manta Ahmad ba, a’a, mutum na gari ba a mantawa da shi, sai dai… Allah ya sauƙaƙa mata ɗaukar ƙaddar, ya ba ta ƙarfin ci gaba da rayuwa, ya sake saka haske a cikin zuciyarta, ya kuma haɗa ta da mutumin da yake ƙoƙarin tara dukkan ƙananan gutsattsarin zuciyarta ya mayar da su guda. Aliyu… ba ya son ya maye gurbin Ahmad, kuma ba zai taɓa iya ba, sai dai… ya zo ne domin ya gina sabon babi na rayuwarta, wannan shi ne bambancin.

Inteesar ta sauke numfashi, ta ɗaga idanunta sama, “ya Allah… ina tafiya zuwa gidanka, ba ni da abin da zan kawo maka sai zuciyata, ka karɓi tubata, ka gafarta mini, ka albarkaci aurena, ka sanya Aliyu ya zama mafi alherin miji a gare ni, ka sanya ni mafi alherin mata a gare shi, ka sanya gidanmu ya zama gida mai cike da rahama, ka ba mu zuri’a ta gari, ka sa mu haɗu a aljannah kamar yadda za ka haɗa mu a duniya.” A wannan karon… ba ta iya riƙe hawayenta ba, suka fara saukowa a hankali. Humaira ta riga ta fara bacci, Mommy Haleema ta lura, ta ɗan juya kanta, ta ga ƙwayar hawaye tana silalowa a kumatun Inteesar. Cikin tausayi… ta kamo hannunta, “Princess…” Inteesar ta waigo da sauri, “na’am Mommy.” “lafiya?” Ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta yi murmushi, murmushin da ya haɗu da hawaye, “alhamdulillah… wallahi ban taɓa jin zuciyata cikin irin wannan natsuwar ba.” Mommy Haleema ta matse hannunta, “alhamdulillah,” ta shafa bayan hannunta cikin taushi, “wani lokaci… Allah kan kai bawanSa gidansa ne domin ya sake gyara masa zuciya.” Inteesar ta gyada kai, “na yarda Mommy.” Mommy ta yi murmushi, “ki yi addu’a sosai, wannan tafiyar… ba kamar sauran tafiyoyin da kika yi ba ce.” Inteesar ta sauke idanunta, ta san abin da Mommy ke nufi, eh… taɓa zuwa ƙasar nan sau da dama, ta san hanyoyinta, ta san yanayinta, ta san harami. Amma… wannan karon daban ne, domin wannan karon… ta zo ne da zuciyar amarya, da addu’o’in da ba taɓa yi ba, da fatan rayuwa sabuwa, da kuma… sunan Aliyu a cikin zuciyarta.

*Arrival at King Abdulaziz International Airport – Jeddah*

Bayan kusan sa’o’i huɗu da rabi a sararin samaniya… muryar Captain ta sake tashi cikin speakers na jirgin, “ladies and gentlemen… we have begun our descent into King Abdulaziz International Airport, Jeddah, local time is…” Inteesar ta buɗe idanunta a hankali, ba ta ma lura lokacin da bacci mai sauƙi ya ɗauke ta ba, ta ɗan gyara zamanta, ta ɗaga window blind ɗin kaɗan. Nan take… hasken rana mai ƙarfi ya bugi idanunta, a ƙasa… tekun bahar maliya, red sea, ya shimfiɗe cikin wani irin shuɗi mai kayatarwa, hasken rana yana walƙiya a saman ruwan kamar an zuba dubban lu’ulu’u. A hankali… jirgin ya fara saukowa ƙasa, gine-ginen Jeddah suka fara bayyana ɗaya bayan ɗaya, dogayen hanyoyi, gadubai, manyan gine-gine, masallatai masu farin minare, da kuma jerin motocin da ke ta zirga-zirga kamar ƙananan ƙwari daga wannan tsayin. Humaira ta matsa kusa da window ɗin, ta yi murmushi, “an kusa.” Inteesar ta gyada kai kawai, ta daɗe tana kallon garin, ba saboda sabon gani ba… sai saboda wani irin jin daɗin dawowa. Sau nawa taɓa sauka a wannan airport? Ba za ta iya ƙirga ba, tun tana ƙarama… Daddy yana yawan kawosu umrah, wani lokaci lokacin hutu, wani lokaci kuma cikin ramadan, har ta kai… ko alamomin airport ɗin… sun zama tamkar wani abu da ta saba gani. Sai dai… yau daban yake, saboda zuciyarta daban take.

Ƙafun jirgin suka taɓa runway, “thud…” jirgin ya yi wani ɗan girgiza mai laushi, sai ƙar tayoyin da suka gogar da runway ta cika cikin cabin. A hankali… jirgin ya rage gudu, har ya tsaya gaba ɗaya, wasu fasinjoji suka fara faɗin… “alhamdulillah,” “alhamdulillah.” Inteesar ma ta lumshe ido, “alhamdulillahi rabbil aalameen.” Mommy Haleema ta shafa kafaɗarta, “Allah ya karɓi zuwanmu.” “ameen,” Humaira ta amsa.

Bayan an buɗe ƙofofin jirgin… mutane suka fara fitowa cikin tsari, Inteesar ta rataya handbag ɗinta, ta jira Mommy Haleema ta fara tafiya, sannan ita da Humaira suka bi bayanta. Ta na taka ƙafarta cikin airbridge… wata irin iska mai ɗumi ta bugi fuskarta, ba irin zafin Najeriya ba ne, wannan… busasshiyar iskar hamada ce, ta yi murmushi kaɗan, “har yanzu dai ba a canza komai ba.” Humaira ta ji abin da ta faɗa, ta yi dariya, “me za a canza?” Inteesar ta girgiza kai, “komai yana tuna min da Daddy.” “ko?” “eh, musamman duk lokacin da muka zo umrah.” Humaira ta yi murmushi, “ni ma.”

Da suka shiga cikin terminal… ƙamshin oud mai daɗi ya bugi hancinsu, wata balarabiya ta ratsa gabansu, abayarta baƙa ce ƙal, niqab a fuskarta, sai ƙamshin turarenta da ya bar wata irin ƙamshi mai daɗi a bayanta. Inteesar ta yi murmushi, “kamshin nan…” Humaira ta kalle ta, “kin tuna?” Ta gyada kai, “da zarar na ji shi… sai na san na dawo saudi.” Duk suka yi murmushi. A ko’ina… ana jin larabci, “yalla…” “ta’al…” “shukran…” muryoyin ma’aikatan airport na gaurayawa da na matafiya daga ƙasashe daban-daban, wasu cikin kaya na alfarma, wasu iyalai ne gaba ɗaya, wasu kuma dattawa ne da sandunansu, wurin ya cika da mutane, amma duk da haka… komai yana tafiya cikin tsari. Bayan sun gama immigration… suka tsaya gefen conveyor belt suna jiran kayansu. Humaira ta jingina da trolley, ta kalli Inteesar, “Inteee… na’am?” Ta yi murmushi, “kin lura da wani abu?” Inteesar ta haɗe gira, “wane abu?” Humaira ta ɗan matsa kusa da ita, ta rage murya, “wannan ba shi ne karo na farko da kika zo saudi ba…” Inteesar ta gyada kai, “na sani.” Humaira ta yi murmushi mai ma’ana, “amma… wannan karon daban ne.” Inteesar ta kalleta, “me ya bambanta?” Humaira ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce cikin sanyin murya… “saboda wannan karon… kin zo ne kafin aurenki.” Maganar ta sauka a zuciyar Inteesar cikin nutsuwa, ta sauke idanunta ƙasa, ba tare da ta sani ba… sai murmushi ya bayyana a gefen lips ɗinta, eh… Humaira ta faɗi gaskiya. Sau da yawa ta zo wannan ƙasar, sau da yawa ta yi umrah, sau da yawa ta yi tawaf, amma… wannan shi ne karon farko da take zuwa da sunan wani namiji a cikin addu’arta, ba Ahmad ba… ba kuma kanta kaɗai ba… Aliyu. Ta ɗan dafe ƙirjinta a hankali, sai ta furta cikin zuciyarta… “ya Allah, ka karɓi wannan tafiya daga gare ni.”

Fitowarsu daga cikin babban ginin King Abdulaziz International Airport bai ɗauki lokaci mai tsawo ba, ƙofofin gilashin suka buɗe… wata iska mai ɗumi ta buge su a hankali, ba irin zafin da ake ji a Najeriya ba ne, busasshiyar iskar hamada ce, mai ɗauke da wani irin ƙamshin ƙasa da oud da baƙon da ya taɓa zuwa saudiyya sau ɗaya ba zai manta da shi ba. Inteesar ta tsaya na ɗan daƙiƙu, ta lumshe idanunta, sai ta sake buɗe su a hankali, wani ƙaramin murmushi ya bayyana a gefen lips ɗinta, “alhamdulillah…” ta furta cikin zuciyarta.

A wajen parking area… jerin manyan motocin kamfanonin umrah ne suke tsaye, wasu farare, wasu baƙaƙe, wasu kuma manyan buses ne cike da mahajjata daga ƙasashe daban-daban. Wani mutum cikin farar thawb da jajayen shemagh ya matso kusa da su, ya yi sallama cikin larabci, “assalamu alaikum.” Mommy Haleema ta amsa cikin fara’a, “wa alaikumus salam.” Ya yi murmushi, “hajjah Haleema?” “na’am.” Sai ya nuna wata baƙar mota mai girma da ke ɗan nesa, “welcome, everything is ready.” Ya miƙa hannu ya karɓi trolley ɗin kayansu, da sauri wani matashi ya taimaka wajen saka manyan suitcases ɗin a boot.

Motar sabuwar ce, mai faɗi, sanyin AC ya mamaye cikinta tun kafin su shiga. Inteesar ta zauna kusa da window, Humaira ta zauna a tsakiya, Mommy Haleema kuma a ɗayan gefen. Driver ɗin ya juya cikin ladabi, “madam… za mu fara tafiya zuwa madinah yanzu in sha Allah.” Mommy Haleema ta gyada kai, “Allah ya sa albarka.” “ameen,” ya amsa. A hankali… motar ta fara motsi, ta bar harabar airport.

Inteesar ta jingina kanta da window, idanunta suna kallon titunan Jeddah, komai yana da tsabta, manyan hanyoyi masu faɗi, palm trees a tsakiyar hanya, fitilun hanya masu tsawo, gine-gine masu kyau, da kuma manyan allunan larabci da turanci. Ba sabon abu ba ne gare ta, sai dai… duk lokacin da take zuwa saudiyya… sai ta ji kamar zuciyarta tana samun wani irin salama. Humaira ta lura tana kallon waje ba tare da magana ba, ta yi murmushi, “me kike tunani?” Inteesar ta ɗan juya, ta yi murmushi kaɗan, “nothing… kawai… na ji kamar na dawo wani wuri da na sani.” Humaira ta gyada kai, “ni ma.” Mommy Haleema ta yi murmushi daga bayan motar, “ƙasar nan tana da wani irin nutsuwa, musamman idan mutum ya zo da niyyar ibada.” Inteesar ta sunkuyar da kai, “hakane Mommy.”

Bayan sun bar cikin birnin Jeddah… hanyar madinah ta fara shimfiɗewa a gabansu, doguwar hanya ce, mai santsi, gefenta kuma… ƙananan tsaunukan duwatsu masu ruwan kasa suna jere, wasu wuraren kuma… sai fili kawai, hamada mai yalwa. Lokaci zuwa lokaci… sai wasu manyan ayarin motocin mahajjata su ratsa, wata mota cike da indonesiyawa, sai wata bus ɗauke da ƴan turkiyya, daga can kuma… wasu motocin da ke ɗauke da mahajjatan afirka. Humaira ta yi murmushi, “subhanallah… daga ko’ina mutane suke zuwa.” Mommy Haleema ta ce cikin sanyin murya, “saboda kiran annabi ibrahim ne.” Shiru ya biyo bayan maganar, shirun da ba ya takura, sai ma ya ƙara nutsar da zukatansu. A hankali… driver ɗin ya rage ƙar rediyon motar, sai muryar wani makaranci ta cika cikin motar, yana karatun al-qur’ani cikin murya mai sanyaya zuciya. Inteesar ta lumshe idanunta, ba ta ce komai ba, sai dai… ta ji zuciyarta tana ƙara samun wani irin natsuwa. Wata irin tafiya ce wannan, ba irin sauran tafiye-tafiye ba, tafiya ce… zuwa wajen da zuciya take samun salama, tafiya ce… kafin sabon babin rayuwarta ya fara, kuma a karon farko… ta samu kanta tana roƙon Allah ba don kanta kaɗai ba, sai don mutumin da yake dubban kilomita daga gare ta… Aliyu.

*Hanyar Madinah…*

Motar na ci gaba da yanke doguwar hanyar da ta haɗa Jeddah da madinah, da farko… ana iya ganin manyan gine-ginen Jeddah daga nesa, sai a hankali… suka fara raguwa, har suka ɓace gaba ɗaya. Abin da ya rage… hanya, doguwar hanya madaidaiciya, mai shimfiɗa kamar ba ta da ƙarshe. A gefenta… hamada ce mai yalwa, duwatsu masu launin ruwan kasa, wasu manya, wasu ƙanana, wasu kuma kamar an sassaka su ne da hannu. Lokaci zuwa lokaci… sai wata babbar mota mai ɗauke da mahajjata ta ratsa su, wani lokaci kuma… sai ayarin motocin umrah su wuce cikin nutsuwa.

Humaira ta ɗan matsa jikinta kan seat, ta miƙe ta leƙa ta window, “subhanallah… wallahi bana gajiya da kallon hanyar nan.” Mommy Haleema ta yi murmushi, “ni ma, kowanne karo da na zo… sai na ji kamar karon farko ne.” Inteesar ba ta ce komai ba, har yanzu idanunta suna manne da wajen, a hankali… ta sauke tafin hannunta kan glass ɗin window, kamar tana jin sanyi daga can bayan gilashin, sai wani murmushi ya bayyana a hankali, ba murmushin dariya ba, murmushin nutsuwa ne. Can gaba… driver ɗin ya nuna wata alama da aka kafa a bakin hanya, da larabci, da turanci, “AL MADINAH AL MUNAWWARAH.” Humaira ta yi saurin murmushi, “Mommy… madinah kenan?” Driver ɗin ya amsa cikin larabci mai sauƙi, “in sha Allah… within one hour.” Mommy Haleema ta ce, “alhamdulillah.” Inteesar kuwa… zuciyarta ce ta fara bugawa a hankali, ba saboda tsoro ba, sai saboda farin ciki.

A hankali… ta jingina kanta da kujera, ta lumshe idanunta, sai wata addu’a ta fito daga zuciyarta ba tare da ta shirya ba, “ya Allah… na gode, ka sake kawo ni.” Ba ta san tsawon lokacin da idanunta suke rufe ba, sai kawai ta ji wayarta tana vibrating a cikin handbag, ta buɗe idanunta, ta zaro wayar, screen ɗin ya haska, “My Amor ❤️.” Wani irin murmushi ya bayyana a fuskarta, ta ɗaga wayar, ta rage murya, “assalamu alaikum…” daga ɗaya ɓangaren… muryar Aliyu ta fito cikin wani irin sanyi, “wa alaikumus salam… Princess…” Ta lumshe ido, “na’am My Amor.” “kuna lafiya?” “alhamdulillah, mun kusa madinah.” Aliyu ya sauke wata ajiyar zuciya, “alhamdulillah, na dade ina kallon lokaci, ina tunanin ko kun isa.” Inteesar ta yi murmushi, “har ka damu haka?” Ya yi dariya kaɗan, “ke ce fa, yaya ba zan damu ba?” Ta sunkuyar da kai, Mommy Haleema ta ɗan kalle ta yi murmushi a ɓoye, ta san da wa take waya, sai ta maida hankalinta kan qur’anin da ke tashi a rediyon motar.

Aliyu ya sake cewa cikin nutsuwa, “kin ci wani abu?” Inteesar ta yi dariya, “My Amor… wannan tambayar ma? Ai tun a airport Mommy ta tabbatar mun ci.” “good, karki manta shan ruwa, saudi akwai zafi,” “kuma idan kuka isa hotel… karki fita har sai kin huta.” Inteesar ta kasa riƙe dariyarta, “My Amor… kana mini magana kamar Daddy.” Aliyu ya yi dariya, “to? Ba dai zan kula da matata ba?” Kalmar… “matata,” sai ta sa Inteesar yin shiru, Aliyu ya lura, ya yi murmushi, “kina nan?” A hankali ta amsa, “ina nan.” Sai ya rage murya, “ki yi min addu’a.” Ta yi murmushi, “wacce addu’a?” Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, sannan ya ce cikin murya mai taɓa zuciya, “ki ce… Allah ya bani ke.” Numfashin Inteesar ya tsaya na ɗan lokaci, ta ji kalmomin sun shiga zuciyarta kai tsaye, ba ta yi gaggawar magana ba, sai ta lumshe idanunta, a hankali ta ce, “ba zan yi maka wannan addu’ar kaɗai ba.” Aliyu ya yi shiru yana sauraro, ta ci gaba, “zan ce… ya sa ranar da za mu haɗu a matsayin mata da miji… ta zama farkon rahama gare mu.” Duk sukayi shiru, dogon shiru, har Inteesar ta fara tunanin ko network ne, sai ta ji muryarsa… ta canza gaba ɗaya, “Princess… hmm? Wallahi… ban san me na yi ba… da Allah ya ba ni ke.” Hawaye suka taru a idanun Inteesar, sai ta yi murmushi, “ka daina, za ka sa ni kuka.” Ya yi murmushi, “ba kuka ba, murmushi nake so.”

A daidai lokacin… driver ɗin ya rage gudun motar, ya nuna gaba, “hajjah… madinah…” Mommy Haleema ta ɗago kai, Humaira ma ta yi saurin kallon gaba, Inteesar kuwa… har yanzu wayar na kunnenta, sai ta ɗaga idanunta… ta bi inda driver ya nuna. A can nesa… cikin hasken yammacin rana… silhouette na birnin madinah ya fara bayyana, kuma daga can… ana iya hangen dogayen minarorin masallacin annabi… suna haskawa cikin wani irin natsuwa… kamar suna maraba da duk wanda ya zo da zuciyar neman Allah. Inteesar ta kasa magana, sai hawaye da suka cika idanunta, ta furta cikin raɗa, “assalamu alaika ya rasulullah…” 🤍🕌

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol