Free chapter · Read without an account

Chapter 1

by Maryam Usman · KOWA DA RABONSA

╔══════════════════════╗
  🌺🌺 *KOWA DA RABONSA*🌺🌺
╚══════════════════════╝

 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺

 ✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

✨ FIVE STAR WRITERS✨

📞 ***

📚 BOOK 2

📖 Page 1
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Bismillahir Rahmanir Rahim.

> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.

~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
  
Murmushi ta yi, za ta kama hannunsa ya yi saurin nufar bedroom ɗinsa, dariya ta yi tare da fita da gudu dakatawa ya yi yana kallon bayanta har ta fita, girgiza kansa kawai ya iya yi, ya koma bedroom ɗinsa, domin lamarin Shatu sai addu'a a kullum sai ya yi mata maganar gudun nan amma bata ji.

A tsaye ta samu Mummy da gudu ta rungumeta tana bata labarin abin da Abbanta ya faɗa, farinciki ne ya kama su suka zauna murnar har lokacin ya tafi sai da M.Madawaki ya shigo domin ganin abin da ya hanata fitowa ya je falon Daada Hajiya Safiya ta faɗa masa Hajarah ce ta hana Shatu fitowa su tafi school.

Kallon da yake binsu da shi ne ya saka Shatu shiga cikin nutsuwarta tana kallon agogon da yake falon da saurin ta shiga bedroom ɗinta wanda Inayaa take bacci a ciki har lokacin, bathroom ta shiga da sauri.

M.Madawaki kuwa tana shiga bedroom ɗin ya biyo bayanta, da kallo Mummy ta bi shi, ganin bai amsa gaisuwar da take masa ba, yana shiga Inayaa ta farka da sauri ta saka hijabi a saman kayan baccin jikinta tana gaida shi, bai amsa ba sai agogon hannunsa da ya nuna mata.

Da sauri ta sauko a saman bed ɗin za ta nufi bathroom ɗin ta ji alamu Shatu na ciki dole sai na bedroom ɗin da yake kusa da na Shatu ta shiga, zama ya yi a gefen bed ɗin yana amsa waya, har Shatu ta fito ɗaure da towel ɗan ƙarami wanda ko cibiyoyinta bai rufe ba, sai da ta zo tsakiyar room ɗin ta kula da shi zaune yana kallonta.

Juyawa ta yi, za ta koma bathroom ɗin, ya kawai da wayar hannunsa gefen yana tashi taku ɗaya ya yi ya koma hannunta zaro ido ta yi ganin towel ɗin jikinta zai cire, dama riƙe shi ta yi, ga kuma Abbanta ya kamo hannunta da yake riƙe da towel ɗin.

A ɓangaren M.Madawaki kuwa ba ita yake kallo ba wayarsa ya cigaba da amsawa ɗaya hannunsa kuma ya kamo hannunta yana zaunar da ita a gefen bed ɗin, sannan ya fita daga bedroom ɗin, yana fita Shatu ta sauke ajiyar zuciya tare da yin sauri ta shirya kafin ya dawo.

Mintina biyar tsakanin ya shigo har lokacin kuma waya yake, kallonsa ta yi tare da ɗauko school Bag ɗinta, tana kama hannunsa da ya miƙo, a falo ta samo Mummynta tana yi mata Allah ya kiyaye, ko da suka shiga falon Daada ta so ya saketa su gaisa da su Baba Malam da yake mata murmushi tun fitowarsu.

A jikin motucinsa ya tsaya yana magana da Yusuf da kansa yake ƙasa A.Maina ne ya fito daga cikin ɗaya daga cikin motocin da suka waje yana kallon fuskar M.Madawaki.

"MAMUB muna da baƙi fa gashi takwas ɗin ta wuce."

Maganar A. Maina ce ta saka shi kamo hannunta suka shiga mota, Yusuf ma ya shiga suka fita da gudu daga gida, tun fitarsu take son yi masa magana amma tsoro take yi, domin ta san ita ce ta saka shi makara bai fito office ba da wuri ba, ita suka fara kaiwa idanuwanta da suka cuko da hawaye take kallon gefen fuskarsa.

Bai ɗago ya kalleta ba, ya yi ƙasa da murya ko Yusuf da yake gaban motar ba ji abin da yake faɗa ba, ya furta.
"Yusuf zai kawo miki breakfast ki kula."

Da gudu ta bar wajen tana kuka, Yusuf na ganin tafiyarta ya jagoranci motucin suka fita daga school ɗin.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Kamar yadda ya faɗa Yusuf ne ya kamo mata breakfast ɗin, har suka tashi tana fushi duk yadda su Rima suka so ta yi magana ƙi yarda ta yi, har suka dawo gida Daada ce ta yi mata faɗa akan biye Hajarah da ta yi har kowa ya tafi school ya barta.

Sai a lokacin ta fara fara'a, labarin auren Mummynta da Abbanta ta basu tana murna, mamaki duk suka yi, Daada kuwa rai a ɓace ta kira A.Maina tana tambayarsa, shiru ya yi yana kallon fuskar M.Madawaki masifar Daada ce ta saka cewa.
"Daada za mu yi magana zuwa dare."

Yana gama faɗa mata haka ya kashe wayar gudun ta sake cewa wani abu, kallon tambayar da yake wa M. Madawaki ne ya saka M.Madawaki faɗa masa gaskiyar maganar.

"MAMUB ba na so Eshaa ta shiga damuwa shi ne dalilin faɗa mata haka amma babu aure tsakaninna da Hajarah har abada."

Shiru A.Maina ya ɗan yi, yana kallon fuskarsa, sai ya girgiza kai.tare da sauke ajiyar zuciya yana jingina bayansa a jikin kujerar da yake zaune, idanuwansa na kan fuskar M Madawaki wanda tun fara maganar yake kallonsa.

"MAMUB, ka san matsalar da hakan zai haifar kuwa?"

Shiru M Madawaki ya yi kamar baya wajen, tashi A Maina ya yi tare da fita daga office ɗin nasa, dama wani File ya zo nuna masa.
━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
A ɓangaren Shatu kuwa tana gama faɗawa Daada maganar auren Mummynta da Abbanta, ta nufi ɓangarensu, zama saka yi da Mummy suna tsara bikin da za su yi, a tsakaninsu bayan dawowar M Madawaki daga wajen ɗaurin aurensu da Mummy.

Domin a cewar Shatu daga office zai wuce inda za'a maida auren, suna yin sallar la'asar suka fita domin zuwa a yi wa Mummy gyaran jiki, wanda Shatu ta nace sai Mummy ta yi, su biyu suka fita ko Daada bata san da fitar ta su ba.

Ko da suka je wajen gyaran jikin, sun samu mutane da yawa, ganin da mutane ne ya saka Shatu ƙaran kuɗin gyaran jikin akan wanda ake biya domin a yi musu da wuri, ana gamawa wacce ake yi wa,aka fara wa Mummy.

Cikin ƙaramin lokaci aka gyara Mummy ciki da waje, cike da farinciki Mummy ta ce dole sai Shatu ta zauna an yi mata, turo baki Shatu ta yi domin ita bata ƙaunar wani ya ga jikinta, Abbanta ya dasa mata wannan aƙidar tun tana yarinyarta ko da ta zama buduwar ma, baya yadda ta je gidan gyaran jikin ko shago sai dai ta faɗa masa abin da take buƙata ya saka Yusuf ya siyo mata.

Ta yi komai da kanta, tun bata iya ba har ta koya, shi yasa da Mummy ta ce sai ta zauna an yi mata take faman turo baki, murmushi Mummy ta yi domin ta san akan me Shatu take turo baki, daɗin baki ta yi mata har ta yadda ta zauna aka yi mata.

Kamar yadda aka yi wa Mummy ita ma aka yi mata, har lalle da kitso, sun yi kyau sosai, sai bayan sallar isha'i sannan suka nufo gida, sai lokacin Shatu ta duba wayarta da take mota, faɗiwa gabanta ya yi sakamakon missing call ɗin Abbanta da ta samu a wayar wajen talatin.

Da mugun gudu ta ja motar, sun yi nisa da tafiyar ne Mummy ta kalle ta tare da cewa.
"Shatu mu ƙarasa gidan ina so mu gaisa da Baba, ga dama Abdul Rahman yana neman ki....."

Katseta Shatu ta yi ta hanyar cewa.
 "Sorry Mummy, Abbana ya dawo na san nemana yak..."

Dariya Mummy ta yi tana shafa kanta ta ce.
 "Babu wata matsala, karki manta yau fa Abban naki sabon ango ne, babu faɗan da zai yi.."

Dariya Shatu ta yi, tana rufe fuskarta, daɗin baki Mummy ta yi mata, ta yadda suka shiga gidan tun shigarsu gidan take jin zuciyarta na bugawa, ganin Abdul Rahman ya kafeta da jajayen idanuwansa yana murmushi.

Cikin sanyin jiki, ta gaida iyayen Mummy, sannan ta jiyo tana gaida Abdul Rahman ɗin da yake fama lashe baki, Ƙawar Mummy ce Amina ta shigo suka shige ɗaki, Malam Sani ma tashi ya yi ya fita, falon ya rage daga Shatu sai Halimatu da Abdul Rahman, dama Mama ce ta fara tashi daga falon.

Washe baki Abdul Rahman ya yi tare da matsowa daf da Shatu, da sauri Shatu ta matsa domin har gobe ba ta manta dukan da Abbanta ya yi mata akan Abdul Rahman ɗin ba, matsowa ya sake yi tare da rungumota.

Da karfi Shatu ta ture shi tana tashi tsaye, kallonta Halimatu ta yi tare da cewa.
"Lafiya Shatu M Madawaki?

Hanyar fita ta nufa za ta fita Abdul Rahman ya yi saurin rungumota ta baya tare da ɗora kansa a kafaɗarta.
 "Haba Baby ni ne fa, gaisawa nake so mu yi kullum na je gidanku bana samu damar hakan yanzu kuma...."

Fashewa Shatu ta yi da kuka tana ture shi, dariya Halimatu ta yi tare da cewa.. 
 "Yaya wai dama Shatu M Madawaki Yar ƙauye ce? 

Dariya ya yi tare da juyo Shatu, yana son ya yi kissing ɗinta, kawar da kanta ta yi tare da ture shi da iya ƙarfinta, fitowarsu Mummy kenan suka ga abin da yake faruwa, murmushi Mummy ta yi tare da cewa.
"Ana shan soyayya ne?"

Ɓata fuska Abdul Rahman ya yi tare da cewa.
 "Aunty wannan yarinyar taki taurin kai ne da ita, kullum kanta sake shiga duhu yake."

Murmushi Mummy ta yi tare da kamo hannayen Shatu da take hawaye, kallon fuskar Amina ta yi suna yin magana da ido, Abdul Rahman ne ya yi saurin kamo fuskar Shatu yana ƙoƙarin ɗora lips ɗinsa saman nata ta ture shi, tare da fita daga gidan da gudu.

Dariya Mummy ta yi tana nunawa Amina, Shatu da ta fita da gudu, tsaki Amina ta yi tare da cewa.
 "Yarinyar nan taurin kai ne da ita, so nake ko sau ɗaya Abdul Rahman ya ɗan more amma duk ta hanyar da muka biyo sai ta ƙwance...."

Tsaki Mummy ta yi cikin baƙinciki ta ce.
 "Ai haka suke ita da uban riƙon nata masifar taurin kai ne da su, ga iyayin masifa yanzu fa, tana turo baki ta yadda aka yi mata gyaran jikin nan wai ita ala dole babu mai ganin jikinta ki ji shegiyar yarinya fa."

Dariya duk suka yi Abdul Rahman na cewa.
 "Aunty ki shirya min wani shirin har cikin Madawaki Dynasty zan zo kuma na cika burina na mallakar yarinyar nan, na gama sakawa raina sai na lashi zumarta na san wannan yarinyar za ta yi ɗanɗano..."

Tsaki Halimatu ta yi tare da cewa.
 "Aikin kenan, To wallahi zan baku shawara kada zilamarka ta halakar da kai, Ke! kuma Aunty wallahi a banza aurenki zai mutu kuma wallahi M Madawaki ba zai barki ba....

Katseta Mummy ta yi tare da cewa.
 "Ke bana son rashin kunya fa, ina ruwanki? Abdul Rahman ka shirya kowanne lokaci zaka ji kirana, ni ma a yanzu bani da burin da ya wuce na ga an raba Shatu da buducinta...."

Shiru ta yi sakamakon shigowar Malam Sani yana faɗa ta barar Shatu a waje tana kuka, fita suka yi har Amina da take sake jaddada mata yadda za ta yi amfani da maganin da ta bata.

A mota ta samu Shatu sai kuka take sosai fuskarta har ta sauya kala, dole sai ita ce ta ja motar, suna fara tafiya ta fara yi wa Shatu faɗa, tana cewa.
 "Yanzu aka kissing ɗinki da Abdul Rahman zai yi, shi ne kuke wannan kukan? Ni ai kin bani mamaki na yi tunanin Abdul Rahman ya fi karfin komai a wajenki ashe ba haka ba ne ko Shatu?

Cikin kuka Shatu ta ce.
 "Mummy kiss fa kika ce? Haba wallahi ba zan iya tsayawa wani mutum ya yi kissing ɗinna ina kallon ba, yin haka cin amanar tarbiyyar da Abbana yake bani tsawon shekaru ce, me na rasa? Me ye Abbana baya yi min? Da har zan sakarwa wani namiji jikina a banza....

Cikin tsawa Mummy ta ce.
"Ke! Ya isa bana son suruntun banza, ki riƙe kalamanki domin za su yi miki amfani wata rana."

Baki sake Shatu take kallon Mummy tana mamakin abin da take faɗa, har suka shiga Madawaki Dynasty babu wanda ya sake magana a cikinsu, Shatu ce ta fara fita da gudu tana shiga cikin gidan.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol